Showing 30001 words to 33000 words out of 38364 words

Chapter 11 - RUMAH COMPLETE

26 Aug 2026

40

tsananin farin ciki yace “Hajiya ki tayani godiya gurin ubangijin da yake bawa wanda ya fidda rai yau dai burinmu na shekara da shekaru ya cika Rumah ta haihu ɗiya namiji amma bakwaini ne sannan itanma aiki akayi mata.....



*OUM HAIRAN*
[1/11, 9:36 PM] OUM HAIRAN: *BONUS RUMAH*



*11/1/2023*



Da mugun ƙaraji tace “What? Ta haihu garin yaya ta haihu?" Bai kawo komai ba saboda farin cikin da yake ciki yaci gaba da cewa “Eh Hajiya yanzu haka ma jinina aka ɗiba leda ɗaya aka sanya mata sannan an ɗebi biyu a jikin excourt ɗina....” ƙit ta kashe wayar ya sauketa yanabin screen ɗin da kallo zuciyarsa na kai kawo akan kashe wayar da Hajiya tayi me hakan yake nufi? Jikinsa ne yayi mugun sanyi ya nemi guri ya zauna yasan Rumah bata a zuciyar Hajiya Tushi saidai baiyi tsammanin ƙiyayyarta zata shafi abinda suka haifa ba musamman da yake abune da suka daɗe suna neman Allah ya basu baiyi tunanin ko a waje yayi ciki akace ɗansa ne zata karɓa ta goya.
Miƙewa yayi ya tari likitan ya rusuna cike da ladabi yace “Ranka shi daɗe akwai yiwuwar jinin nan sai an nemi wani har yanzu mara lafiyar nan bata farfaɗo ba" numfashi ya sauke yace “in yakai leda ɗari akeso a nema amma ayi da lura zanje na dawo sannan ko Hajiyata ce tazo ban amince abarta ta shiga inda Fulani take ba bare bbyn"




Mota ya nufa ya shiga yaja ya nufi gidan sarautar a saitin part ɗin Hajiya Ummah yayi parking ya fito ya nufi ciki sukayi clear da Fulanin Daura yanayin data ganshi yasata saurin tararsa tace “Ɗana yada sauri haka?" Shafa kansa yayi yayi murmushi yace “Mamana wlh haihuwa akayi mana yanzun nan..."
“Waye ya haihu?" Ta faɗa tana kafesa da ido dariyar da bai cika yinta ba ita yayi yace “Fulani ƙarama ta haifi Yariman Katsina..." Ya karshe maganar yana ɗaga wayarsa tare da juyawa ya nufi cikin sashin Fulanin Sokoto yabar Fulanin Daura tsaye cike da mamakin hukuncin Ubangiji, Fulani Sa'ade dake tsaye ta juya da sauri tana harhaɗa hanya ta nufi sashin Tushi ta tarar da ita tsaye da Fulani Amina tace “Mun shiga uku Hajiya Haƙanmu bai samu idon ruwa ba munyi don ciki ya zube ciki bai zube ba ɗa ya fito"
“Wai da gaske ta haihun?" Cewar Hajiya buɗe ƙofar yasa kowaccensu jan bakinta ta tsuke ya tsaya jikin ƙofar yana kallonsu kowa da irin fassarar da yakewa saƙon da fuskarsa take fitarwa domin hausawa sunce labarin zuciya a tambayi fuska.




Juyawa yayi ya fice da sauri zuciyarsa a zafafe ba komai yakeson yin magana akai ba tabbas yau ya ƙara dasa ayar tambaya kan Hajiya Tushi anya kuwa da gaskene itace ta haifesa da sanya hannunta cikin abinda ya faru da Rumah wanda badon nisan kwana ba kafin likitoci su zo kanta komai zai iya faruwa, zama yayi gefen gadon kansa na sarawa zuciyarsa na tuƙuƙi yaci gaba da tambayar kansa amsar da bashi da ita ya miƙe ya buɗe wardrobe ya fara duba kayan da zai ɗaukar mawa Ruman baisan meye zata buƙata ba ya ɗauki wayarsa yana laluban Number da zai kira duk wani wanda yake rayuwa a gidan yanzu zuciyarsa ta kasa yarda dashi hatta da Hajiya Ummah to uwar data haifesa ma ta nuna baƙin ciki da arziƙinsa matansa biyu sun mara mata baya ina ga wani daban.
Turo ƙofar da akayi ne yasashi maida hankalinsa ga ƙofar Maryam ce ta shigo fuskarta a sanyaye yanayin takunta ya nuna masa tsantsar kasalar yanayi, isowa tayi gabansa ta kama hannunsa tace “Ina taya mijina murnar samun ƙaruwar arziƙin da yafi arziƙi haƙiƙa godiya ta tabbata ga Ubangijin da yake azurta wanda yaso a lokacin da yaso tabbas na amince Rumah haske ce a gidannan kamar yanda ta zama haske a zuciyar mijina...




Janyota yayi ya rungume zuciyarsa ta karye hawaye ya zubo masa ɗumin hawayen ne yasata ɗagowa cike da matsanancin mamaki tasa hannu ta share masa hawayen tace “Ba daidai bane hawaye a idanun jarumi duk wani tsanani me wuccewa ne nasan damuwarka Please karta zame maka damuwa abin damuwa shine mu rungumi ɗanmu muyi masa gata"
Lumshe idanunsa yayi ya buɗe baki da sanyin murya yace “Na gode Maryam haɗawa Rumasa'u kayanta bansan abinda za'a ɗauka ba" fara haɗa kayan tayi a hankali takejin tausayin mijin nata da Amaryar tasa suna kwaranye mugun tanadin da takeyi mata mahaifiyarta ta sanyaya mata jiki zuwan da tayi gida da nasihohinta gareta sun sanya taji tana son itama ta zama kamar mahaifiyarta.
Kalma ɗaya da ta tsaye mata a rai game da Rumah bata mantawa tana zaune kusa da Barebari wato mahaifiyarta wayarta tayi Ring ta duba ganin number Ansa Wyf my Husb yasa barebari dubanta tace “Wace cikin abokan zaman naki take kiranki?" Tsaki tayi tace “rabu da ita Barebari Wannan tsintacciyar yarinyar ce wadda ya kwaso a gidan marayu" ajiyar zuciya tayi ta kishingiɗa tace.
“Allah Sarki baiwar Allah wato Maryam ina mamakin zuciya irin taku mara tausayin wanda ya cancanci tausayawa Rumah abar tausayi ce da cancantar ajata a jika kune gatanta ita yanzu a duniyar ta batasan soyayya ba wanda yayi mata dariya shine masoyinta, shin ko kinsan Mijinku yana cikin mutanen da Ubangiji zai yiwa inuwa ranar da babu wata inuwa sai inuwarsa?"




Da sauri tace “Saboda me? Murmushi tayi tace “Saboda yayi soyayya dominsa ubangiji yayi alƙawarin bazai tozarta zuciyar da taji ƙan bawansa mafi cancanta da aji ƙansa shima zaiji ƙan wannan bawan Ridwan ya fara da tausayi ne har yakai ga janyota jikinsa yasota domin Allah tunda batada wata siffa ta zahiri da za'a sota dominta, Maryam ko kinsan ƙorafin da kikeyi na yafi sonta hankalinsa akanta yake yafi damuwa da ita, duk ba komai ne ya kawo haka ba sai biyayyar data fiku tabbas zata fiku yi masa biyayya da kiyaye ɓacin ransa domin shi take gani matsayin iyayenta mijinta kuma gatanta ku kuwa kuna kallon ku ƴan gata ne kuna da uwa uba da dangi.
Abinda nakeso ki sani shine tun ganina da yarinyar na farko ta shiga raina matuƙa shiga rai a taƙaici wlh bantaɓa yarda itan tana cikin irin yaran da kuke mata kallo ba nafi tunanin hatsarin mota ko wani abu me kama da haka shine ya zama silar zamowarta a wannan yanayi, Maryam Rumah tana da wani ɓoyayyen abu game da ita akwai kwarjinin sarauta da izza wanda ba zaman cikinku ko zama da Mijinku ne yasata ɗabi'antuwa dashi ba a'a dama ɗabi'arta ne tabbas asalinta ko babu sarauta a jininta to akwai arziƙi mara misali a tsatsonta, bawai inaso ki sota ki mata gata ki zama a matsayin data ɗauke ki bane don tunanin wataran a'a ki ƙaunaceta don Allah domin inayi miki kwaɗayin zama tare da adalin Sarki kuma mijinki Ridwan a aljanna. Maryam kiso abinda mijinki yakeso da zuciya ɗaya wlh bazaki taɓe ba"



Ajiyar zuciya tayi tare da ɗago Idanunta da suka ciko da ƙwalla ta kalleshi shima ita yake kallo cike da ta'ajibin dalilin hawayenta, saurin sharewa tayi ta ɗauki trolley bag ta zuba kayan tana cewa “Wannan kaɗai ya isa me hankali nutsuwa dukkanninmu munajin mun kai ace mun haifi Yariman wannan masarauta amma sai Ubangiji ya nuna mana rashin isarmu ya zaɓi kasasshiya a cikinmu wacce mukewa kallon rashin isa ya azurtata da samun arziƙin da dukkanmu muka kasa samu Takawa inason na zama ta biyu da zata ga Yariman mu don Allah kayi wannan alfarmar gareni"
Miƙewa yayi ya nufi ƙofa ta rufa masa baya tanajan trolley ɗin har jikin motarsa drivern ya karɓa ya saka a mota ya shiga yaja suka fice suka barta tsaye da sanyin jiki ta nufi sashin Fulanin Sokoto a hanya suka haɗu Fulani tace “Sai ina?" Cikin sarewa da sallamawa tace “Dama bansan wanne asibitin cikin asibitocinsa yakai Fulani ƙarama ba shine nazo ko ke ya sanar dake mu tafi tare...." “Bazaki ba munafuka!" Sukaji an faɗa a bayansu suka juya a tare Hajiya Tushi ce taci uwar kwalliyar gwala-gwalai tana tauna goro ta tako ta tsaya gabansu tace “Tunda nake a rayuwata bantaɓa tsanar wani ku biyun nan ba tabbas yau zan gwada ƙarfi ikona inda na isa sai abinda nake buri ya tabbata"
Murmushi Fulanin Sokoto tayi ta dubi Maryam tace “Muje in kin shirya" babu wanda yabi takan Hajiya Tushi suka bar wajen suka nufi mota tare da shiga Driver yaja suka fice a gidan
[1/12, 8:47 PM] OUM HAIRAN: *12/1/2023 Bonus*



Paid book 300 via acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank




Suna jiyota tanata masifa da tsine²nta babu wanda ya juya ma ya kalli inda take drivern ya fice a gidan ya nufi asibitin da Hajiya Ummah ta sanar dashi asibitin da ƴar tazara tsakaninsa da gidan, haka yayi parking suka fita suka nufi reception a reception ɗin suka haɗu da Dr Mansura suka gaisa tayi musu jagora suna tambayarta ya me jikin Dr Mansura tace.
“Wato Hajiya nisan kwana ne kawai ya kawo Fulani ƙarama wannan lokacin irin jinin data rinƙa zubarwa abin ya firgitani wlh iya shekaruna a aikin nan bantaɓa gani ba dole ce tasa da muka samu jinin ya tsaya mukayi mata aiki aka ciro bby boy shi kuma lafiyayye dashi kawai watanninsa ne basu cika ba shiya muka sanyashi a kwalba"



Girgiza kai Fulanin Sokoto tayi tace “haka dama Allah yake ikonsa idan lalura ta tarar da nisan kwana saidai asha wahala a tashi" a ƙofar ɗakin da Rumah take suka haɗu da Sarki Ridwan yaja ya tsaya yace “Fulani har an ƙaraso sannu to a shigo" binsa sukayi har gaban gadon tana kwance kamar babu rai a jikinta sai jini da yaketa aikinsa Gimbiya Maryam ta dubeshi tace “Habeebty kuma a haka take tun zuwanku?" Jinjina mata kai yayi yace “Haka take amma kowanne lokaci daga yanzun zata iya farkawa" zama tayi ta kama hannunta ta zubawa dogayen yatsun Rumah idanu ita kanta suna birgeta.
Dubansa tayi shima ita ya kalla yana shirin yin magana aka banko ƙofar hankalinsu duka ya koma ga me shigowar Hajiya Tushi ce da Amina da Sa'adatu tana biye dasu Hajiya Tushi ta matsa gaban gadon ta taɓe baki tare dayin dariya tace “Aikin banza kiwon makahon doki yo baya kilisa, Kai Ridwan!" Ta faɗa da ƙaraji dukkan suka kalleta gabansa yayi wata muguwar faɗuwa ta nuna shi da yatsanta tace.
“Wlh indai nice na haifeka yau ba gobe ba saika rabu da wannan yar iskar watsattsar yarinyar yo banda zubewar albarka wannan irin ko na shuka ne ai baka siya kakai gidanka ba bare irin ɗan Adam da yawuna da yarjewata da sahalewata nakeso ka saki Rumah idan kuma kaƙi zan Barka da ita na cireka cikin yayana kuma na tsine maka ka lalace kowa ya huta"




Tararta Fulanin Sokoto tayi da cewa haba Kekuwa Fulani saikace baki sha ruwan musulunci ba ko ma dai me kikeso ayi ai kya bari ta farfaɗo to ma in banda abinki meye laifin Rumah ai bata cancanci wannan butulcin daga garemu ba tazo a ƙarshe kuma ta bamu farin cikin da muka daɗe muna nema a gidannan bai samu b...."
Cikin ƙaraji tace “Dakata Shehu tsugul uwar Munafukai waima meye naki da zaki samin baki a magana? Kay dakai nake ko bakaji abinda nake cewa bane?" Tunda ta fara maganar idanunsa ke kanta har saida ta gama sannan ya juya zai fice ta janyo rigarsa tana shirin magana Sa'adatu tace “Haba Hajiya meye kikeyi haka ne ina imaninki yake da bazaki saurarawa yarinyar nan ba don Allah ki bar Takawa ya sarara kada ki ɓata masa farin cikin da yake ciki, ya kamata ko da wani abu a ranki ki ɓoye a wannan gaɓar ɗa fa Hajiya kuma jika a gareki....."ashar ta kundumawa Sa'adatu ta koma gaban Ridwan ta tsaya cikin hargowa tace.
“So nake kayi abinda nace kayi kafin kabar gurin nan" a hassale yace “Bazan iya ba Hajiya..." Ta ɗaga hannu zata sauke a fuskarsa Rumah da tun shigowar Hajiya Tushi ta farka ta diro daga gadon tayi kukan kura ta cafke hannunta cikin wani irin yanayi daya firgita kowa tace “Karki kuskura!" Da sauri kowa dake ɗakin ya kai duba ga Rumah da tsananin mamaki ta saki hannun tare da cewa “Karki ɗagawa kanki hankali indai akan ɗanki ne nayi Miki alƙawarin ko zan mutu saboda soyayyarshi zan bar Miki shi ba tare da naji haushinki ba domin nasan bakida wani laifi da zan bayyanawa duniya matsayin abin dogaro na da riƙarki a zuciyata.
Hajiya soyayya ce tasa kikeson ɗanki ya rabu dani don gudun gurɓatar zuri'a da mummunan jini mara arziƙin nasaba irin nawa abu ɗaya dai da nakeso ki sani bazan iya bari ki kai hannunki jikinsa ba domin kallon uba nakeyi masa yama fi iyaye daraja a gurina domin shi na sani shi ya fara min gata a duniya"



Tana kaiwa nan ta durƙushe tana dafe cikinta kan ɗinkinta tana cije leɓe Sa'adatu da Maryam da Takawa sukayi kanta da gudu ta kwantar da kanta a kafaɗarsa cikin wani irin yanayi na galaɓaita tace “Don...don Allah na roƙeka kayiwa mahaifiyarka biyayya Tat... Takawa" tana faɗin haka ta sume jikinta ya saki yanayin da yayi bala'in firgita kowa Sa'adatu ta fice da gudu ta nufi office na consultant Dr ɗin asibitin suka dawo tare a guje ya isa kanta suka fice da ita shi da Takawa suka shigar da ita emergency room suka jona mata wasu na'urori sannan aka gyara mata plastic surgery ɗin.
Koda ya fito bai koma inda ya baro su Hajiya Tushi ba domin kwata² baya buƙatar ganin kowa ko wata hayaniya zai nemawa kansa mafita kuma zai bawa Hajiya Tushi mamaki zaɓinsa biyu zaɓinta biyu Maryam zaɓinsa ce Rumah ma zaɓinsa ce.
Meye yasa zaɓinsa yafi zaɓinta Quality Tunda ya auri Amina bai taɓa samun wata nutsuwa da ita ba kullum damuwa ce kishinta yayi yawa zai iya ma cewa kishin ƴan wuta takeyi domin babu abinda yake tunanin zata kasa indai don cutar da kishiya ne.



kwatsam bai gama farfaɗowa ba ta kuma haɗashi da Sa'adatu ita kuma makira ce ya daɗe da sanin halinta indai tuggu ne da ƙulle² ta ƙware gata da siffar mage mai kwanciyar ɗaukar rai zatayi maka yanayin da ko ance ta aikata zakace ƙarya ne ya fahimceta tun kafin zuwan Rumah.
Da wannan tunane²n ya isa Dikko Layout jerin manyan gidaje ne na manyan ƙososhin ƙasa da suke da nasaba da Katsina wani ƙasaitaccen gida ya nufa wanda duk unguwar babu samansa kuma alama ma ta nuna gininsa akeyi ba'a gama ba.
Horn yayi masu gadin har rigen buɗe masa ƙofar sukeyi ya shiga yayi parking ya fito ya suka gaisa suna zubewa ya shiga parlourn komai an tsarashi kamar yanda ya buƙata yayi murmushi ya nufi saman ɗakuna ne guda huɗu a saman ya buɗe ɗaya ya shiga ya cire kayansa ya shiga wanka ya fito yana duba agogo 8:30pm




Doguwar riga ya saka a jikinsa ya ɗauki wata takarda yayi rubuce-rubucensa ya ɗauki hotonta ya turawa likitan asibitin da Rumah take, can kamar awa biyu da tafiyar saƙon kira ya shigo wayarsa ɗagawa yayi da hanzari kafin yayi magana Maryam ta katseshi da cewa.
“Takawa kana ina kazo asibiti jikin Rumah ya matsa fah ga bbyn ya koma..." Da sauri ya tashi yana furta “Innanillahi wa inna ilaihirraji'un...." Ƙit ya kashe wayar ya fito daidai lokacin da wata doguwar mota ta shigo ya isa ga motar suka fito da gadon marasa lfyr suka shiga dashi cikin gidan wani ɓangare me kama da asibiti saboda tarkacen da ya zuba a wajen buɗe fuskar Rumah yayi tana baccinta cikin kwanciyar hankali tare da sauke numfashin nutsuwa, sunkuyawa yayi yayi kissing goshinta ya juya ga Dr Mansura yace “Duk yanda za'ayi ki basu kulawa zuwa lokacin da zan dawo zamu rinƙa waya bbyn duk abinda yake buƙata ayi masa"




Jinjina masa kai tayi ya fice yana ɗaga wayar Dr Shu'aibu yace “ganinan Dr" mota ya shiga yaja tara da kwata yaje asibitin, Dr Shu'aibu ya tareshi yace “Ina petiant ɗin" da sauri ya dubeshi yace “Ya Ni da nake shigowa zaka tambayeni abinda na tafi na barshi a hannunka?" Sulalewa Dr Shu'aibu yayi ya zauna a gurin yace “Ya Allah ya Dr Mansura zatayimin haka nabarta da petiant na tafi wani aikin gaggawa na fito Hutu take cemin kace za'a kai petiant ɗinnan wani hoto babban asibiti shine na basu dama" wata shaƙa da Ridwan yayiwa Dr Shu'aibu Saida numfashinsa ya tafi Hutu na wuccin gadi kafin ya dawo hayyaci ya sakeshi ya zube a gurin Hajiya Tushi dake zaune zaman jiran ya dawo yayi abinda ta umarceshi ta miƙe Fulanin Sokoto ta tareta da cewa “Wannan ma ai maganar banza ce ina za'a kaita da ɗanyen jiki to ina jaririn?" Allah yayi masa rasuwa sannan shima banga gawarsa ba...." Ya faɗa yana ja baya daga mugun kallon da Ridwan keyi masa.
Murmushi Hajiya Tushi tayi ta kalli Sahura Jakadiya da Amina da Sa'adatu tace “Dagacan suyi can Allah ya raka taki gona Ni dama banyi murna da haihuwar wannan mugun irin ba" duban Maryam tayi tace “Ƙiyamar Rumasa'u ta tsaya a gidannan saura ke kema ki shirya tafiya Bauchi aje ko wani baran a jonawa nikam bana surukuta da Munafuka mara kishin kai irinki"
[1/14, 10:09 PM] OUM HAIRAN: *14/1/2023 Bonus*



Paid book 300 via acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank


Tsallake shi tayi bar gurin ta nufi inda sukayi parking ta shiga Amina ta rufa mata baya Sa'adatu ta tsaya ita da Jakadiya kowannensu da abinda ke zuciyarsa ita Jakadiya tanajin tsoron tayi motsin da zai shafi abincinta ita kuma Sa'adatu tana gudun ya fahimci da sanya hannunta a komai dake faruwa. Fulanin Sokoto ce ta matso tace “Ya kamata ayi wani abu ko ka taɓo ita Mansurar kaji ina suke"
Tashi yayi ya fice a ɗakin tare da bawa Kowa damar ya tafi gida duk abinda ke akwai zasuji.
Jikinsu duk a sanyaye kowa da abinda yake sakawa a ransa suna isa gidan sarautar kalmar data fara dukan kunnensu itace “An sace Amaryar Sarki" tashin hankali wannan kalma tayi mugun girgiza Hajiya Ummah a fili tace “Yanzu banda abin Hajiya wannan labarin har na zuwa a kwazawa barorin gida ne wai meye yake damunta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login