Showing 6001 words to 9000 words out of 38364 words
gidan sai ki dawo" godiya tayi me yawa ta fara haɗa masa abinsha kamar yanda aka karanta mata yauma karɓa yayi da hannunsa yakai bakinsa ya lumshe idanunsa yace “Rumah anayi muku tatsuniya a makaranta"
Dariya tayi tace “Lahh! Mai Martaba dama kasan tatsuniya ne?" Ɗaganta kai yayi yace “Nasanta kakata Hajiyan Loko kafin ta rasu tanayi mana nasan kema kin iya ko?" Jinjina kai tayi tace “Malamin Hausar mu yanayi mana lokacin muna primary school" murmushinsa ya faɗaɗa yace “zaki rinƙa yimin?" Kunshe bakinta tayi da dariya tace “Ai manya kamarka baayi musu tatsuniya saidai ƴaƴanka" hannunsa yakai ya tsinki Ƴaƴan inibi guda biyu yasa ɗaya a bakinsa ya miƙa mata ɗaya yace “Shekararki nawa?" Dafe kuncinta tayi tace “Uhmm sha bakwai" iska ya furzar yace “Ok nima shekara ta sha bakwai banda yara har yanzu yaro ne Ni" langwaɓar da kanta tayi tace “Allah sarki kai ai babanka da mamanka duk suna kusa dakai Ni kuwa banma sansu ba....
Maganar ce ta sarƙe kuka na neman ƙwace mata yayi saurin kai ɗaukar handkerchief ya miƙa mata yana girgiza mata kai yace “karki rinƙa yawan zubar da hawaye Rumah kinsa damuwa a zuciyarki akan abinda bazaki iya canza shi ba ko kinsan saboda ke yasa na buƙaci sabbin bayi a gidanku..."
“Ni?" Ta faɗa tana dafe ƙirji ya ɗaga kai yace “Zuwa na na farko gidanku kinyi bayani akan haƙƙin marayu akan al'umma yanda kike bayani ya tabbatar min akwai kwantacciyar damuwa a ranki tunda na taho na kasa samun nutsuwa shine dalilin da yasa wannan satin muka koma nayi bincike sosai akanki an tabbatar min da abinda na gani a fuskarki naso daukoki ke kaɗai Chief na gidanku ya bani dama gudun shigarki kaɗaici yasa muka hadoki da yan uwanki.
Meye yasa kina sanya damuwar da tafi ƙarfin brain ɗinki a ranki babu wani bawa dake wuccewa ƙaddararsa so ki saki ranki kiyi rayuwa kamar kowa zaki samu dacewa insha Allahu, tashi kije magrib tayi ki ɗauki abincin nan ki tafi dashi, yauwa abinda nakeson sanar dake kiyi mu'amala dani kamar mahaifinki yayanki kuma abokinki idan mun samu keɓancewa Ni dake saidai inaso ki ɓoye kusanci ko sabon dake tsakanina dake a idon jama'ar gidannan kinji kyakkyawar ƴata"
Fitar furucin yana murmushi tare da kai tafin hannunsa kuncinta yasata murmushi me ɗauke da hawaye karon farko a rayuwarta da ta sami arziƙin kalma me daɗi daga wani mutum bayan Asma'u tabbas yau rana ce ta musamman kuma ta daban a rayuwarta mamaki al'ajabi da tambayoyi sune narke cikin ranta saidai bazata iya sake furta masa komai ba domin ya gama bawa rayuwarta ta yau farin ciki.
Tashi tayi ta ɗauki basket ɗin da aka aje abincin ta shiga kitchen na bangaren ta juye a leda farfesun kayan ciki ne da farfesun kifi sai tuwon alkama miyar kubewa ɗanya murmushi tayi ta kulle kowanne ta kurbi lemon me daɗi ta lumshe idanu a ranta tana raya masu dukiya da masu mulki sunajin daɗinsu wata miyar sai a maƙota, dake lemon babu yawa zuƙe abinta tayi sannan ta fice ranta wasai wani farin ciki takeji yau wanda bata taɓa jin irinsa ba a rayuwarta har tuntuɓe takeyi saboda sauri a hanya suka haɗu da Asma'u saboda tace hanyar tayi jeji bazata iya bari ta rinƙa tahowa ita kaɗai ba.
Riƙo hannun Asma'u tayi suka koma gefe tace “Ma'u zo mu cinye naman mukaiwa waccan masifaffiyar matar abincin da kifin" hakan kuwa sukayi suka cinye farfesun naman sukaci tuwon sukayi hani'an suka tashi suka ƙarasa suna shiga Jakadiya ta karɓe ledar hannunta ta buɗe ta haɗiyi yawu tace “Yau abinda sarakin yaci kenan muma bari muci ko mayi mulmul mu rinƙa sheƙi"
Taɓe baki Ma'u tayi tace “Muma saiki fitar mana da rabonmu" duka takai mata tace “Shegiya me kan kwakwa ungo gunduwa ɗaya" murmushi Rumah tayi tace “kema ungo makira Allah yasa ba idanu kike kafa masa yake kasaci yake baki ba" kwantar dakai tayi tace “Kai Jakadiya naga Bama fa yaci yake cemin na dauko" nan suka shantake Jakadiya da son zuciya sai gashi ta fara jan Rumah a jika saboda ta lura yarinyar da sa'arta ta shigo gidan tunda har tayi aikin yini biyu a Sashen Sarki Ridwan bai kirata yace karta ƙara zuwar masa ba tabbas zasu kwashi arziƙi kafin gayyar ta watse.
“Gafaranku dai" Indo ta faɗa tare da shigowa tace “Ranki ya dade Jakadiya Ki amsa kiran Mai Martaba a lambu" miƙewa tayi tace “Na shiga uku Ni Sahura kwarankwatsa banason kiran Mai Martaba yanzu kar yayi mana baƙin cikin wannan rikitiɓa da muke kwasa ke dan ubanki me kikayi masa?" Ta kama kunnen Rumah ta murɗe ta fasa ƙara tace “Wlh banyi masa komai ba Ni...." Ficewa tayi tace “Allah yasa dai kar wani abu ya biyo baya yasin saina yankaki"
Tana maganar tana ficewa a ɗakin bata jima ba ta dawo ɗauke da ledoji niki² ta aje tace “Ni Sahura ji da gani baya ƙarewa sai ranar da kurman bebe ya makance ke Indo nifa kaina ya kulle me wannan bawan Allah yake nufi ne?" Da sauri Indo tace “Uhm ai Sahura na rasa bakin magana tunda naji sharruɗansa akan yarinyar nan “zazzage ledar tayi ta tafa hannu tace Shikenan tazo a bayanmu ta fimu fada Kinga wasu tsala²n riguna da y bayar a kawo mata wai kar ya kuma ganinta da tsummokara kuma ya haramta mata sa kayan bayi ke Rumasa'u kiji tsoron Allah waye bokanki a ƙasar nan?".......
Tun daga wannan rana Rumah ta samu sauyin rayuwa wata shaƙuwa ce take shiga tsakaninta da Ridwan a fakaice shine ya fara aikenta ɓangaren Fulanin Sokoto ganin farko taji yarinyar ta shiga ranta ranar a wannan ɓangare ta wuni saboda dama cewa yayi taje ta taya Fulanin Sokoto hira a hankali cikin hikimarsu ta manya ta rinƙa janta dake batada duhun kai ta saki jiki sosai ita ce harda yima Fulanin Sokoto kitso sunata hirar su tana cewa da Fulanin Sokoto hausarta ba irin tasu ba, a wannan yanayin yazo ya ishesu idanunsa akan Rumah yace “Ke dama kinanan" ƙasa tayi da kanta Fulani tace “Nice nace in ba abinda zatayi tazo ta ɗauke min kewa" zama yayi yace “hakane kije akwai saƙonki wajen Jakadiya" tashi tayi tace “Mu kwana lfy Fulani" bin bayanta yayi da kallo har Saida ta ɓacewa ganinsa sannan ya sauke numfashi yace “Tasa damuwa da yawa a ranta Fulani bantaɓa jin tausayin wani mutum kamar yanda nakejin tausayinta ba saidai na rasa meye ya kamata nayi mata na bambanta ta da bayin gidannan amma zuciyata taƙi nutsuwa ohh God kaina ya kulle meye zai hanata damuwa ne......."
*Share please*
*Oum Hairan*
[12/15/2022, 1:12 PM] OUM HAIRAN: *RUMAH!...*
_Labarin sarauta me taɓa zuciya_
*Oum Hairan*
Some people's sun bini suna son littafin RUMAH amma nayi musu sauƙi wannan yasa nayi musu alƙawarin fitar da wannan Page ɗin da sabon price Normal group 200 PC 600 zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, ne babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN.
*Last Free Page 13-14*
Zuba masa idanu Fulanin Sokoto tayi tace “Bantaɓa ganin ka damu da shigar wani damuwa kamar yanda ka damu da kasancewar Rumasa'u a damuwa ba gashi bakada ikon canza mata ƙaddara Ridwan duk abinda yafi karfinka ɗaukar sa matsayin wasa yafi maka sauƙi yanzu meye zakayi ka taimaki yarinyar nan daya wucce kamar yanda aka saba duk shekara kana auradda bayi to itama kasata a cikin na wannan shekarar ka samu wani cikin bayin gidannan ka aura mata ka bashi jari ko ba komai kaima ka huta"
Bai iya cewa komai ba ya miƙe ya nufi gurin Hajiya Tushe ya taddata a parlour anata zuba mata fadanci neman guri yayi ya zauna yan fadar na Hajiya Tushe suka fara watsewa ta tashi zaune ta zuba masa manyan idanuwanta sun jima a haka kafin ta katse shiru ɗin da cewa “Waɗannan ƴan iskan yaran suna baka ciwon kai saraki su gasu ba haihuwa ba Ni na rasa wannan masifa anya Ridwan ba aure zaka ƙara ba?" Tunda ta fara maganar ya kafa mata idanu har ta ida shima yaja numfashi ya ɗago yace “Ba laifinsu bane Hajiya wata sabuwar damuwar ce take neman kaini ƙasa shin wai Hajiya meye yasa kike damuwa da lamarin haihuwa ne ita da lokaci ne da ita Sa'adah ce takeson zuwa Yola shine nace zanzo muyi magana ya kamata a barta shekara uku rabonta da gida"
Taɓe baki tayi tace “Ai shi kenan saidai gaskiya ban yarda da zuwanta gida ba in kuwa zataje ɗin to saidai ka haɗata da wata cikin bayin gidannan saboda ta rinƙa sanya idanu a takunta ban yarda da Karime ba uwar Sa'ade babu hali a gurinta ko kaɗan"
Yana miƙewa yace “Babu damuwa zan haɗata da Rumah" cikin ɗaga murya tace “Ridwan ina Jakadiya ne ka haɗasu da ita su tafi" baice komai ba ya fice ta baya yabi inda yasan babu mutane sosai ya rasa meye yasa yau zuciyarsa babu daɗi komai yinsa yakeyi akan dole.
Inuwa ya rinƙa hangowa ransa yana faɗa masa ya wucce yaji bazai iya ba ya juya ya nufi inda ya hango mutanen a tsaye ya jima tsaye a kansu kafin Rumah dake ɓoye bayan wata itaciya ta fito da gudu ta maƙalƙaleshi ta baya cikin wani irin kuka me dukan zuciya tace.
Ka taimakeni Mai Martaba sun kashemin ƴar uwa Nima so sukeyi su kashen...." Da mugun sauri ya birkitota gaba ya riƙe damtsanta sosai yace “Me sukayi miki?" Durƙushewa tayi ta riƙe ƙafarsa tace “Shiyasa kullum nake cewa ka daina fifitani cikinsu ka barni na rayu kamar kowannensu yanzu gashi saboda fifikon da kake nunamin sunci alwashin sai sun lalata min rayuwa sun taremin hanya tsautsayi yasa Asma'u ta taho don tafiya dani shine suka buga mata sanda a bayanta ta faɗi Mai Martaba....
Ɗaga mata hannu yayi cikin fusata yace “ya isa Rumah" yana maganar yana duban mazan dake durƙushe sunata rawar jiki yanayin kallon kawai da yanda idanunsa ya kaɗa yayi jawur ya tabbatar musu yau sun kaɗe har ganyensu, kallo wani cikinsu yayi batare da furuci ba ya kwasa da gudu ya saɓi Asma'u a kafaɗa ya nufi cikin gidan da ita,
Miƙewa Rumah tayi zatabi bayansu ya riƙo hannunta cikin nasa ya jata suka nufi ɓangarensa har zuwa yanzu hawaye takeyi suna tafe yana janta barorin dake hidima a ɓangaren nasa sunata darewa suna bashi hanya kowa da matsanancin mamakin dalilin da ya haɗa Rumah da Sarki Ridwan tabbas har ya damƙo hannunta haka batare da jin komai ba.
Buɗe masa ƙofa akayi ya shiga suka rufe sai lokacin ya saki hannunta ya tsaya cak yana sauke wani wahalallan numfashi yace “Meye ya haɗaki dasu bayan abinda kika faɗamin?" Sunkuyar da kanta tayi matuƙar kwarjini yayi mata fiye da kullum Mai Martaba b irin mutanen da zaka iya sanya idanunka cikin nasu bane.
Muryarsa a sarƙe yace “Rumah!..." Ɗagowa tayi Idanunta taf da ƙwalla ya cije leɓe tare da takowa gareta ya sanya hannu ya ɗago fuskarta yasa yatsansa ɗaya ya share mata hawayen yace “Meye a mind ɗinki da kike tunawa meye yasa kikeson sanyani a damuwa shin don Kinga ina shiga damuwa da ganinki cikin damuwa shine yasa kikejin gara ki rinƙa yin abinda zai sanya raina ƙunci?...."
Guri ya nema ya zauna yaci gaba da cewa “Ko kinsan irin rigimar da nake shirin tunkara cikin yan kwanaki akanki meye yasa idan na faɗa Miki magana baki ɗaukarta seriously ko don Kinga bana matsawa akanki? Rumah meye yasa baki kallon yanda dukkan wata halitta dake gidannan takemin biyayya ki ɗauki hakan matsayin ma'aunin da zaisa ki yarda ba yin kaina bane sauke alƙalamin hukunci da kuma Izzar dole akanki? Why da zaki rinƙa barin barorin gidannan suna ƙoƙarin wasa da da'irata?? Shin ko kinsan bansan sau nawa na kasa bacci da rashin baccinki ba kullum burina me zanyi na samawa rayuwarki farin ciki tausayinki ya huda fata tsaka ƙashi da ɓargona ya bi ta ruwan dake gudana a cikin jinina yayimin illah tun kallon farko.
Shin Rumah zaki iya zama dani har abada?"
Ɗago Idanunta tayi ta ɗora su kan fuskarsa ta buɗe baki sai kuma idanunta ya fara tsiyayar da hawayen da taketa son shanyewa saboda sanin halinsa baison kukanta, hannu yakai ya share mata hawayen ya sunkuya a hankali ya zuba gwiwarsa a ƙasa ya ɗora hannunsa a kafaɗarta tare da ɗora bakinsa kan nata ya sanya bakinsa cikin nata abinda ya sanyata sake rushewa da kuka tsoro da firgici yana shigarta yanda takejin tafiyar hannunsa a bayanta tare da zagawar harshensa cikin bakinta yayi bala'in razana duniyar ta.
Rintse idanunta tayi da ƙarfi ta fashe da kuka tanason janye bakinta cikin nasa amma ta kasa gashi ya lumshe idanunsa bare tayi masa wata alama da zata nuna masa rashin amincewarta da hakan ya fahimta, sun ɗauki kusan minti goma sha biyar a haka yana ƙara shigar da ita jikinsa kafin ya samu dauriyar cire bakinsa daga nata abinda ya sanyata miƙewa da sauri a mugun firgice tana neman kwasa da gudu yayi saurin riƙota yana mikewa tsaye idanunsa na wani irin lumshewa yace “Karkiyi abinda zaki ƙara bawa kanki matsala Rumah ku huɗu ne akwai uku waɗanda bakusan da zaman juna ba rigimarki da barorin gidannan tafi kowacce sauƙi akan wacce take gabanki nan gaba kaɗan"
Fasali yaja yaci gaba da cewa “Minti goma baya Jakadiya ta shigo ƙwaryar nan ta fita saboda ta samemu cikin yanayi idan kinje.
Ɓaryarku ki turomin ita" tsayawa tayi cak jikinta ya sake samun saƙon sanyi me kashe gaɓoɓi ta juyo zatayi magana ya tako gabanta ya ɗora hannunsa kan bakinta kawai sai taga ya juya ya nufi wani step na bene ya haye tare da turo ƙofa abinda yasata tura gwiwa cikin mutuwar gaɓɓai ta nufi sashinsu na bayi idanunta na tsiyayar da hawaye ta rasa da wanne irin salo zata fassara baƙon yanayin da Mai Martaba ya shigo mata dashi cikin rayuwarsu ta yau kusan wata sama da biyu ya hanata yi masa tausa sati Uku Baya take tambayarsa meye yasa bayason takeyi masa tausa yanzun, maimakon ya bata amsa sai ya tambaye ta kinason yimin tausa ne? Itako dake wawuya ce ta ɗagansa kai tace “Ina samun nutsuwa zuciyata takan kasance cikin farin ciki idan inayi maka tausa sai na rinƙa jin kamar ina cikin dausayin aljanna Mai Martaba da kallonka ina samun nutsuwa naji kamar banida wata damuwa ko tawaya cikin rayuwata"
Lumshe idanunsa taga yayi ya tashi zaune yace “Da gaske Rumah kina samun nutsuwa da nutsuwata?" Bata gane komai ba amma ta gamsu tana samun nutsuwa da nutsuwarsa dalilin da yasa ta daga masa kai kenan yaja ajiyar zuciya tare da riƙe hannunta yace “Zakici gaba da samun nutsuwa da nutsuwata har ƙarshen rayuwata ko taki shin kin amincewa hakan?" Batada da tunanin komai ba ta ɗaga masa kai ya ciri wani zoben azurfa jikin ƙaramin yatsansa ya kama yatsanta na hannun dama na tsakiya ya zura mata yana murmushin da yake ƙara bayyana bayyanuwar farin cikinsa yace “Da alƙawari tsakaninmu daga yau zakiyi komai cikin da'irar lada insha Allahu ki kasance cikin farin ciki Rumasa'u"........
*Share please*
*Oum Hairan*
[12/15/2022, 1:12 PM] OUM HAIRAN: *RUMAH!...*
_Labarin sarauta me taɓa zuciya_
*Paid page 15-16*
Some people's sun bini suna son littafin RUMAH amma nayi musu sauƙi wannan yasa nayi musu alƙawarin fitar da wannan Page ɗin da sabon price Normal group 200 PC 600 zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, ne babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN.
Da muguwar mutuwar jiki ta isa sashin bayin a daidai ƙofa sukayi kaciɓis da Jakadiya ta ɗan raɓe alamun rashin gsky Sahura ta kafeta da jajayen idanunta ta damƙi gashinta ta jata ɗaki ta rufe ƙofar tare da lalubo fitila ta kunna tace “Yau Ni Sahura naga masifa naga bala'i Rumasa'u meye alaƙar dake tsakaninki da Mai Martaba na amsa kiransa na riskeku a wannan yanayin?" Cikin kuka tace “Ni babu da komi tsakanina dashi kawai dai..." mari ta ɗauke ta dashi tace “ko kiyimin bayani ko naci ubanki Ni dama na daɗe da saka ayar tambaya akanki shin saɗakarsa ya massheki ko kuwa?" Sunkuyar da kai tayi tana sharar idanu zatayi magana tace “rufemin baki baƙar munafuka zanje na samu Fulani Amina da Fulani Maryam da Fulani Sa'ade naji kosu sunsan alakarki da mijinsu...."
Riƙe Jakadiya tayi ganin tana shirin ficewa tace “Don Allah kada ki faɗa musu Jakadiya bansansu ba amma rashin imaninsu zasu iya sawa a sheƙe numfashina Mai Martaba ma yace kije yanason ganinki.
Dafe ƙirji tayi tace “Na shiga uku an fasa aure na me kuma ya faru ko yaga shigata ne?" Da wannan ta fita ta jima sosai har dare ya fara shiga sannan ta dawo koda ta dawo bata ishe Rumah ba ta fice ta koma ɗakinsu wajen Asma'u da likita yazo ya bata magunguna suna zaune jugun² babu me iya cewa wani zuciyar Rumah sai kai kawo takeyi saboda fargabar abinda ya wakana tsakaninta da Mai Martaba duk ta firgita ranta yana ayyana mata to dama shima ɗan iska ne?
Itadai iya saninta namiji da mace su kasance a wannan yanayin tabbas akwai matsala matuƙar ba ma'aurata bane ajiyar zuciya ta sauke ta ɗago idanunsu ya shiga cikin na juna Asma'u ta sauke numfashi tace “Akwai abinda yake damunki kike kokuwar ɓoye min Rumah shin menene?"
Ajiyar zuciya ta sauke tace “Kawai ina tunanin makomar rayuwarmu ne idan ya kasance barorin gidannan sun fara farautar rayuwa da mutumcinmu, Ma'u yanzu a hakan zamu rayu?"
Murmushi Ma'u tayi tace “Komai na Allah yana da iyaka Rumah ki daina jin cewa ubangiji bazai kawo mana mafita ba wanna ehn kuskure ne Domin ya faɗa cikin ƙur'aninsa ne tsarki komai yayi tsanani akwai sauƙi a gabansa Ni inaji a jikina ko bamu samu salama gabaɗaya ba tabbas sauƙi ya kusanto mu shiyasa komai yakeyi mana zafi kawai dai abin buƙatar muci gaba da tsare kanmu da kuma roƙon Allah ya tsaremu in yaso sai kiga mun kai bantenmu"
Jinjina kai Rumah tayi tace “amma dama cikin manyan mutane akwai ƴan iska?" Da sauri Asma'u ta dubeta tayi murmushi tace “sunfi yawa