Showing 27001 words to 30000 words out of 38364 words
har tambayarta nayi ko tanajin wani yanayi tace ita babu abinda takeji"
Jinjina kai Hajiya Mariya tayi tace “Haba Yaya ki dubi yarinyar nan da kyau Allah ba ita kaɗai bace...." Shigowar Rumah yasasu rufe babin hirar ta ajiye musu tarkacen kayan ciye² tace “Ina kwana Hajiya" dogon tsaki Hajiya Tushi taja ta miƙe tace “Mariya in kun gama tattauna takaicin kwa taddani a mazauni na"
Har Hajiya Tushi ta fice daga parlourn Rumah bata iya tashi daga inda take ba Saida Hajiya Maimuna tace “Dama mijinki ne ya turo mu mu tambayeki ko kinada ra'ayin zuwa hajji bana?" Da sauri Hajiya Mariya tace “Yo wacce Hajji kuma Yaya ai saidai a jira baɗi idan da rai?" Ƙasa Rumah tayi da kanta daidai da shigowar Mai Martaba ya nemi guri ya zauna ya kafeta da ido yace “Baki da abin cewa ne?" Sunkuyar da kai ta kumayi Hajiya Mariya tace “Allah ya taimake ka yarinyar nan bazata iya aikin hajji bana ba saidai ko baɗi inda rayuwa" da mamaki ya dubeta yace “Ko miye dalili?" Murmushi tayi tace “aa babu komai yanayinta ne ya nunamin kamar akwai ƙaruwa a jikin...."
“Zubawa Rumah idanu yayi fuskarsa ta ɗan washe yace” “Wai haka?" Girgiza kai tayi ya kuma cewa “Kamar ya aa?" A kunyace tace “Nifa bansani ba" murmushi yayi yace “Ok bari na kira Dr Mansura sai ta dubaki" nan suka shiga hirar su ta zumunci itadai tana zaune cike da tunanin yanda zaace ciki ne da ita batare da tasan dashi ba to dama hakan tana faruwa, wai yama za'ayi ace tanada ciki su sauran matansa fa?
Sallamar Dr Mansura ne yasashi kallonta ta miƙe suka fita suka shiga part ɗinsa dake komai akwai tayi mata izinin kwanciya tayi mata hoto tayi murmushi tace “Bakijin canjin yanayi a jikinki gashi Bby har ya fara kwari 3 mouth"
Komawa sukayi parlourn ta sanar dashi abinda ke faruwa ya shiga tsananin farin ciki mara misali yayiwa ubangiji gdy tafi dari kafin ya miƙe ya rungumota ya ɗagata ya direta kan kujera ya ɗora bakinsa a kuncinta yace “na gde Rumah tabbas ke mahaɗi na ce iya haka kin bani farin cikin da bazai taɓa goguwa a zuciyata ba Rumah meye kikeso a duniya Please ki faɗamin nayi miki alƙawarin ko komai nawa zai kare indai kuɗi na siyansu zan baki"
Lumshe idanunta tayi ta miƙe a wajen a kunyace ta nufi ɗakinta da gudu ya miƙe yabi bayanta da kallo yana Murmushi dole yau yayi sadaka me girma don nuna gdyrsa ga buwayi gagara misali, miƙewa Hajiya Maimuna da Hajiya Mariya ne ya dawo da nutsuwarsa jikinsa ya shafa sumarsa cikin kunyar yayyan nasa sukayi sallama suka fice.
Sashin Hajiya Tushi suka nufa cike da farin cikin ɗan uwansu ya kusa ganin muradinsa shima Hajiya Maimuna tace “Oh Mariya Kinga tabo ɗan uwan ajali wai duk waɗannan girɗa girɗan matan daya tara a gidansa babu wacce ta haife masa sai wannan ƙaramar yarinyar" murmushi Mariya tayi tace “Ke dai ki bari Yaya abin ya bani mamaki fah ashe dai Ridwan shima yanada rabon ganin ƙwansa wlh har na sare da naga anyi ɗaya anyi biyu anyi uku har an tafi huɗu"
Jinjina kai Maimuna tayi tace “Ai kafin wannan auren nasa yaje Rasha kinsan sunada kayan aiki acan ne suka sanar dashi bashi da karfin ƙwayayen halitta shine suka rubuto masa magunguna kinsan magungunan daga London ake kawo masa su" da wannan tattaunawa suka shiga ɓangaren Hajiya Tushi Mariya tayi mata kyakkyawan albishir a cewarta amma maimakon suga farin ciki sai sukaga ta zabura ta miƙe tace “Ci me? A gidan durun uwar wa ta samu cikin bayan boka Ilu ya tabbatar min da ya shafe mararta ya kulle mahaifarta...."
Da mamaki suke kallonta sukace “Me kike cewa ne Hajiya?" Cije leɓe tayi tace “Tab wlh ba'a isa ba inda na farko yabi dole shima wannan yabi can..." Da mugun ɓacin rai Mariya tace “Waini Hajiya yaushe zakisan Annabi ya faku ne gabaɗaya kin hanawa Ridwan kwanciyar hankali bayason sarautar nan don yayi Miki biyayya ya karɓeta bayasan auren Amina kika jorner masa bayason Sa'ade kika liƙa masa shin meye kike nufi dashi ne da bazaki sakeshi ya iddace ba to gsky mun kasa gane inda kika dosa saboda haka zan sanar dashi yayi takatsantsan"
Murmushi Hajiya Tushi tayi tace “in kika fasa Mariya ba nono na kikasha ba, ki tashi yanzu ma kije ki faɗawa Ridwanu nice na zubar da cikin wannan shegiyar gantaltalar matar tasa in yaso yasa a harbeni kinji"
Hajiya Maimuna ce tace “Ba zaisa a harbeki ba Hajiya amma dai ko meye a ranki yayi tsauri na girgiza kuma nayi mamakin da kikace kece kika zubar da wancan cikin gsky akwai firgici uwar data haifeka ta rinƙa neman hana burinka cika akan wasu banzaye da bazasuyi mata sakayyar abinda tayi musu ba sannan Hajiya meye Rumah tayi Miki da kikeson rabata da mijinta ne kullum maganar ki Rumah meye yasa zaki zaɓi ɓangare cikin matan ɗanki? Ni a ganina kamata yayi ki so abinda ɗan ki mai ƙoƙarin sanyaki farin ciki yakeso...."
Watsa mata mari tayi tace “Tsaramin abinda zanyi da rayuwata Maimuna wannan haihuwa ta da kikayi to ubanki ma har ya mutu da ra'ayina ya tafi ya barni na rantse da Allah ko ta tsiya ko ta tsiya² sai Rumasa'u ta fita cikin matan Ridwan ko a raye ko a mace wadda kuma takejin takai ta kawo a cikinku taje ta tonamin asiri Ni kuma na lalata rayuwarta ta hanyar tsine mata albarka....
_Kuyi hƙr na jina shiru Bby nace batada lfy._
OUM HAIRAN
[1/8, 9:05 PM] OUM HAIRAN: *8/1/2023 Don Allah karki karanta in baki biya ba Nrml 300 PC 600 via acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank*
Da mugun sauri da razani suka dubi juna Hajiya Mariya ta dubi Hajiya Tushi idanunta cike da ƙwalla tace “Koda zaki raba Rumah da Ridwan na roƙeki ki barta ta haihu sai mu karɓi abinmu ita kuma taje ta ƙarata...." Tsawa ta buga mata tace “Rufemin baki munafuka kama hanya ki tafi ɗakin mijinki kafin na kwance Miki dauri ki zama borar gida...."
Dukkansu jiki babu Kwari suka fice duk wannan abinda ake yi a kan kunne Fulani Maryam aikuwa ta cika da farin ciki ta samu dama don itama taci alwashin wannan ciki bazaikai labari ba yaushe ma zata barshi yakai kamar wata asararra tana zaune wata tazo ta haifi yarima.
A ɓoye ta koma part ɗin ta ta fara tunanin wanne salo zata shigo dashi don cimma burinta Hajiya tana batun Rumah sai tabar gidan ɗanta idan aka barta ta tafi da cikin nan ai an cuci mutane gara a fara cire cikin sannan ayi musu mugun farraƙun da da bakinsa zai koreta.
Kunun gyada ta dama ta wadata Suger da madara a cikinsa ta ɗauki ta nufi part ɗin Rumah ta murɗa ƙofar tajita a kulle gam ta shiga kwankwasheta shiru sai can wata cikin barorin dake hidima a ɓangaren ta fito tana tambayar waye?
Cikin zaƙuwa Fulani Maryam tace “Nice" buɗewa tayi ta rusuna tace “Allah ya ƙara wa me masauki lfy takawa ya keɓe sannan yayi umarnin kada a bar kowa ya shiga yana buƙatar kaɗaici" bataji daɗin hakan ba amma haka tayi murmushi tace babu komai ga wannan akaiwa Fulani ace ina gaisuwa"
Karɓa Ramlah tayi ta shiga dashi ta nufi ciki ta kwankwasa ƙofar parlourn Rumah dake kwance jikin takawa ta miƙe ta nufi ƙofar ta buɗe Ramlah ta bata tace “Fulani me masauki ce ta bayar a kawo" buɗewa tayi ta wani lumshe idanunta tace “kay amma na gode" mayar da ƙofar tayi ta rufe ta koma ta zauna ya tashi tare da janyo jug ɗin ya buɗe, zubawa kunun idanu yayi shi kansa ya bashi sha'awa ya ɗauki karamin cup ya tsiyaya ya saka zubansa idanu ya mayar da kallonsa ga Rumah yace.
“Ya baki sha'awa ko?" Murmushi tayi tare da kwantar da kanta takai hannu zata karɓa ya janye ya ajiye ya kamo hannunta yace “Wajibi ne kiyi takatsantsan da duk wani mutum dake cikin gidannan Rumah wlh wannan karon zuciyata bata yarda da kowa ba inajin kamar wani mummunan abu zai faru dani wanda zai tarwatsa farin cikin rayuwata Please kar wanda ya ƙara baki abu kikaci indai ba mutum biyun nan ba Asma'u da Fulanin Sokoto su kaɗai na yarje in kinason abu ki nema a gurinsu kuma suma ɗin in bada hannunsu suka baki ba ban amince kikai bakinki ba"
Ɗagowa tayi tace “Saboda me?" Murmushi yayi yace “komai zai iya faruwa a kan cikin nan dake jikinki kiyi hƙr Rumah ke kanki ban yarda dake ba domin akwai abinda kika ɓoye min game da zubewar wancan cikin"
Daga wannan rana y kasance ko abinci sai ya tantance takeci saidai wata sabuwar damuwar data shigo cikin rayuwarta kusan wata guda kenan bata iya bacci duk sanda ta rufe idanunta firgici take shiga sai tayita ganin wasu irin abubuwa data kasa gane meye ko kuma zuciyarta tayita bugawa tun tana ɗaukar abin matsayin sauyin yanayi abin ya fara ta'azzara kullum gaba yakeyi har ya fara barin kanta yanzu ko Muryar Takawa taji gabanta idan ya yanke ya faɗi yini zatayi bata samu nutsuwa ba, a hankali ta rinƙa zuƙewa abubuwa na kwance mata har kawo, takai bata kaunar ganinsa ko jin muryarsa tun baya gane irin damuwar da take shiga har ya fara fahimta da kansa yaje ɗakinta ya tarar ta a kwance kan tile tana ganinsa ta tashi zaune a razane gabaɗaya sai yaji ya tozarta haka ya daure ya matsa gareta ya zauna yace.
Na kwana biyu da fahimtar yanayinki banyi Miki magana ba inajin kamar zaki koma daidai maimakon haka sai naga kullum abin ƙara gaba yakeyi Please meye damuwarki? Waye yayi Miki wani abu da kika kasa haɗiye wa?" Sunkuyar da kanta tayi hawaye na zuba a idanunta yasa hannu ya ɗago fuskarta ya share mata hawayen yace “meye dalilin hawayen?" Sake rushe masa tayi da kuka ta janye tace “Don Allah takawa kaje...." Da sauri ya dubeta yace “Akanme zanje?" Sautin kukanta ne ya karu tace “Wlh banason ganinka Nikam ka tashi kaje wlh kaje banason...." Da mugun faɗuwar gaba yace “What?" Da sauri ta miƙe tace “Eh wlh banason..." Rufe mata baki yayi yace “Karki kuma banason wannan kalmar me nayi Miki da zakice bakison ganina?" Durƙushewa tayi tace “Na shiga uku Takawa ka taimakeni ka fita kafin numfashina ya ɗauke wlh bansan meye yasa idan na ganka nakejin kamar ajalina ya iso gareni ba don... Don girman Allah ka fita takawa ka fice nace.....
Marnage
[1/9, 9:27 PM] OUM HAIRAN: *9/1/2023*
Da azama ya janyota jikinsa ya matseta sosai ta saki wani numfashi me ƙarfi take jikinta ya saki ya ɗauketa ya dorata a gado ya samu ruwa ya rinƙa shafa mata can ta farfaɗo tana buɗe idanu tayi arba dashi ta zabura ta miƙe ta diro a gadon ta nufi ƙofa ya ƙwalla mata kira taja ta tsaya ya tako bayanta ya dafata da hannunsa da a baya takejinsa kamar auduga saboda laushi amma yau saita jishi dindinrim kamar guduma.
Hannu tasa zata ɗauke hannunsa ya saisaita muryarsa da yanayin da a baya ya sani indai yayi mata shi jikinta mutuwa yakeyi yace “Wlh banida burin muzgunawa gareki ko a rashin sani ne nayi Miki abinda kikejin bakison kasancewa dani Please ki sanar dani na rantse zan baki hƙr"
Cikin gunjin kuka tace “Ni bakayimin komai ba kawai banas..." Rufe mata baki yayi yace “Shikenan zan tafi" ajiyar zuciya ta sauke lokacin daya juya ya fice ta mayar da ƙofar ta rufe tana sauke ajiyar zuciya ta koma ta kwanta tana share hawayen fuskarta ranta tab da tunanin dalilin da yasa baiyi mata komai ba takejin tsanarsa a ranta to wai dama ana hakane? Ta nason samun wanda zata faɗawa ko da wata mafita da za'a bata amma ta rasa taya zata fara bada labarin ta tsani wand yayi mata gata, ya wanda take bawa labarin zai kalleta me zai ɗauke ta butulu?
Kwana tayi tana juyi ta kasa hassalawa kanta komi taga kiransa yakai uku amma ta kasa ɗagawa tunda tasan ko a lissafin girki yau ba ita keda shi ba duk da cewar ta lura ba lissafin girki akeyi a gidan ba wacce ya buƙatu da ita ita yake sawa a kira masa ita kuwa saidai shi ya kirata tunda take a matsayin matarsa kowacce mace Jakadiya keyi mata iso gareshi amma ita ko sau ɗaya bata taɓa kaita ba saidai idan ya bukaceta ya nemota da kansa ya turota a mafi yawan lokuta ma yafi kiranta a waya taje su gana gashi Allah ya jarabceta da bukatar mijinta a waɗannan watanni musamman da cikinta ya tafi wata na shida kullum cikin feeling take babu damar takai kanta.
Yau tun goma ta fice ta nufi sashin Fulanin Sokoto a zaune ta tarar da Fulani da casbi a hannunta da alama sarrah walaha ta idar zama tayi kusa da ita tana wasa da yatsun ƙafarta har ta idar ta dafa kanta tace “Rumasa'u yadai?" Ƙasa ta kumayi da kanta cikin kunyar abinda takeson faɗa tace “Fulani dama so nake ki taimakeni ki bawa Takawa Hƙr na fahimci fushi yakeyi dani tun abinda ya rinƙa faruwa kwanaki...."
Da sauri Fulani tace “Meye ya rinƙa faruwa?" Cikin kukan da batasan yazo ba ta rinƙa zayyanewa Fulani komi sosai Fulani ta kaɗu da jin abinda Rumah ta faɗa mata tace “Eh lallai Rumah bakida hankali ke waye ya gaya Miki a irin wannan gidan ana sakaci da addu'a kuma anayin shiru da yanayi? Koda yake Ridwan yafiki rashin hankali tunda ya ƙyaleki harma ya janye miki bani wayarki ta faɗa tana miƙa hannu.
Jikinta na rawa ta miƙa mata ta karɓa tana danna number sa special wacce iya iyalan gidan ne suke da ita, Saida tayi Ring ta katse sannan ya biyo Fulani ta kara a kunnenta yace “Sarautar Matan gidana Kin tuna dani yau?" “Ba ita bace Son meye ne yake faruwa Rumah tazo tana roƙona na baka hƙr" murmushi yayi me sauti yace “Kayyah to me take tunanin tayimin kenan Fulani Ni Rumah batayimin komi ba hassali ma yanayin da naga tana kasancewa idan na raɓeta shine yasa na ƙaurace mata saboda kar na cutar da ita amma batada wani laifi a wajena"
Murmusawa Fulani tayi tace “Masha Allah amma fah Ridwan yarinyar nan dole ka tashi da addu'a akanta wlh masu farautarka dukka sun koma kanta babban buri aga bata haife abinda ke cikinta ba kai wani ɓangaren ma rayuwarta suke farauta, Nikam na roƙeka in zai yiwu ka dawomin da ita nan har lokacin da zata sauke abinda ke jikinta, nasani Rumah me addu'a ce amma yanayi da kuma sakata a gaban da akayi yasa bata iya hassalawa kanta komi to kai da ka ɗauki nauyin amanarta dole kai aiki ya gani"
Hawaye Rumah ta sharce tace “Na'am" amsawa daga kiran da yake yi mata yace “In har da gaske kin daina guduna kizo part ɗina inason ganinki" ajiyar zuciya tayi tace “To" daga haka ta dubi Fulanin Sokoto tace “Meye yace?" A kunyace tace “Yace naje yanason ganina" murmushi tayi tace “To tashi kije" miƙewa tayi ta nufi sashin nasa zuciyarta cike da zullumi tunda yace tazo taji gabanta ya yanke ya faɗi tana kara kusantar part ɗin faduwar gabanta tana ƙaruwa daidai shigarta part ɗin bayan ta wucce masu gadin sashin taji mararta tayi wata muguwar murɗawa tayi saurin dafeta tare da yin ƙasa tana karanto duk addu'ar da tazo bakinta can taji ciwon ya tsahirta ta miƙe taci gaba da tafiya tana taka step ɗin shiga parlourn ta ga wani duhu ya lulluɓe mata idanu wani jiri me haɗe da wata azababbiyar murɗawar mara sun dirar mata a lokaci guda.
Cikin rashin hayyaci ta saki wata azababbiyar ƙara da ta haddasawa dogaran nufota da gudu amma kafin su kawo ta baje a gurin cikin rashin hayyaci jini ya ƙwace mata, wani cikin dogaran ya bankaɗa ƙofar ya shiga da mugun gudu ya nufi hanyar da zata sadashi da sashin Mai Martaba yana zuwa ya isheshi a kishingiɗe da alamun hutawa yakeyi ya zube a gabansa yace “Allah ya taimake ka jini..." Da sauri ya tashi yace “Jini kuma Madu?" Jinjina masa kai yayi yace “Ka taso Fulani ƙarama ce ta faɗi jin...." Ai bai rufe bakinsa ba Takawa har yakai ƙofa a guje mutanen suka dare suka bashi hanya ya isa kanta ya ɗagota cak ya nufi mota kafin yakai har an buɗe masa ya shiga yajata da gudu ya fice a gidan ya manta da lissafin excourt da Driver yau ba ranarsu bace.
Bayan ficewarsa Amina da Sa'adatu suka kalli juna sukayi murmushi Jakadiya tace “Ƙurunƙus ɗan kan ɓarya anyi an gama ciki kuma anbi shanun Sarki dariya sukayi suka tafa Sa'ade tace “Nikam yau zanyi bacci da munshari in cikin nan ya zube” Amina ta harareta tace “Zakiyi ko zanyi muda muke burin sarauta ta koma gidanmu idan na sake wannan shegiyar matar tasa ta rigani haihuwa kuma ta haifo namiji ai na kaɗe" Jakadiya ce ta cafe da cewa tunda dai nayi muku aikinku kuma kunga yaci to a sallameni ko na tona asiri"
Da sauri Sa'ade tace “muje keda ba'a haɗa abin arziki dake sai kin nemi tozarta mutum" ta baya sukabi saida suka fara zuwa sukayiwa Hajiya Tushi albishir ta ɗauko dunƙuli me girma ta bawa Jakadiya tayi godiya ta fice ya rage daga ita sai Surukanta ta dubesu tace “Yanzu sai aiki na gaba kamar yanda boka ya wassafa kar yarinyar nan ta dawo gidannan domin yace muddin muka barta ta dawo saita zame mana masifar da zamu kasa maganinta domin duk wani kulli da mukasa akayi mata yake shashantar da ita da addu'a zai kwance in kuwa ya kwance babu wani sauran aiki da zai yi tasiri a jikinta" numfashi suka sauke a tare daidai lokacin da wayar Hajiya Tushi ta doka ganin number Ridwan ta suka kama kallon² kowa gabansa na faɗuwa daƙyar bayan tayi Ring ta katse wajen mintina saba'in da biyar ya sake kira Hajiya Tushi hannunta na rawa ta ɗaga tare da sanya wayar a handsfree tace.
“Rilwanu ya akayi ne" cikin