Showing 15001 words to 18000 words out of 38364 words

Chapter 6 - RUMAH COMPLETE

26 Aug 2026

42

ba wannan ya bata damar mikewa ta fito parlourn Luba da Iro har sun gama aikinsu Luba tana tsaye tana ƙarewa parlourn kallo taji takun saukowa tayi saurin kai dubanta ga inda taji takun ta zube tare da cewa “Takawarki lfy burtali matakar shanu shamuwa rabon me saa"




Ta rasa meye yasa bata jin daɗin wannan kambawar da sukeyi mata to yau ɗin ma katseta tayi da cewa “Ina Asma'u" cikin in...Ina tamunafurci tace “Sa...Saro ta tafi kiranta Muna fatan dai ba wani laifi mukayi ba" bata bata amsa ba illa nufar kitchen da tayi ta ishe komai a shirye a dinning taja cup ta haɗa tea ta fara sha tana tuntunin rayuwarsu ta baya da wannan taji sallamarta ta miƙe da sauri suka rungume juna tace “Long time nayi missing blood sister na Asma'u kullum ina yini da tunaninki ke fah?" Murmushi tayi tace “ni har kwana blood kawai na rasa ya zanyi ne inason ganinki da maganganu da yawa a bakina"
Janta tayi suka nufi dakin da yake a matsayin nata suka zauna duk yanda taso Asma'u ta zauna a gefen gadon ƙi tayi sai ƙasan carpert suka zauna Rumah ta kama hannun Asma'u tace “kinajin yunwa?" Girgiza mata kai tayi ta sauke numfashi tace “Ok meye ke son fitowa daga bakinki?" Fasali taja tace “Ina fatan kullum kina shiryawa canza salon takun rayuwa Rumah akwai kwantacciyar rigima kuma mai girman gaske shin baki tunanin meye yasa cikin sati biyun nan Mai Martaba bai taɓa tunanin kusantarki matsayin mata ba?"




Zubawa Ma'u ido tayi itanma murmushi ta sauke tace “Matansa biyu Amina da Sa'adatu sun shirya bin matakin yaƙin sunƙuru dake domin an tabbatar musu da cewa kece hasken wannan masarauta lallai akwai aiki a gabanki me girma"
Kallonta tayi tace “Ina kike samun wannan labarin?" Kallon hanya tayi tayi ƙasa da murya tace “gurin Luba kinsan ai hadimar Amina ce a fakaice fah amma ba kowane ya sani ba saboda aikin ɓoye takeyi mata" jinjina kai tayi tace “Yanzu kuma a haka zamuci gaba da tafiya dasu sunacin dundunniyarmu" murmushi yayi tace “to kina da abinda kike tunanin zakiyi ne?" Girgiza mata kai tayi ta miƙe ta nufi wardrobe ta buɗe ta ɗauko wasu dogayen riguna tace “Jiya da muka fita nagansu sunyi min kyau na siyo mana su" kallonta tayi tace “kuma ni Allah ya taimakeki?" Da mamaki take kallonta tace “Ko baki sone?" Juyar da kai tayi tace “Idan daraja ta bambamta dole yanayi ya bambamta Ruman da muke faɗi tashi da ita a baya yanzu ba ita bace ba meye zai hana ki rinƙa bani kwance ki adana sabbin"



Bata iya cewa komai ba sukaji alamun buɗe get Asma'u ta miƙe ta fice da sauri domin komawa sashinsu itama ta fito ta tsaya jikin ƙofar ɗakin, tsayin lkc sannan taji haurowarsa idanunsa akanta yana nazartar yanayinta ya riƙo hannunta suka shiga ciki ya zaunar da ita yayi kissing hannunta yace.
“Kamar akwai magana a bakinki?" Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da zoben yatsansa ya tallafo fuskarta ya sauke bakinsa saman lips ɗinta yana lasa dole saboda wani saƙon sirri da take karɓa a ilahirin jikinta, ta rasa meye yasa takejin wannan yanayin idan suka kasance a haka.
Janye bakinta tayi cikin bazatar furuci tace “Takawa meye gundarin aure ne?...." Da mugun sauri ya kalleta ta sauke kanta hawaye na zubo mata tace “meye yasa kowa yake cemin inyi ƙoƙarin ganin mun kasance a cikin asalin rayuwa ta gundarin aure bayan nidai na kasa ganewa" miƙewa yayi yace “Rayuwar aure? Gundarin aure?? Rumah waye yake faɗa Miki haka?" Sunkuyar dakai tayi ya daka mata tsawa yace “Tambayarki nakeyi? Cikin firgita da in...ina tace “Jakadiyya ce take faɗamin...."



_Mahaifina ne babu lfy shiyasa baku jina yanda ya kamata, Alhmdllh jiki yanata sauƙi insha Allahu zamuci gaba kamar yanda muka saba._



Don Allah in kinsan baki biya ba karki karanta saboda kowa ya samu damar karanta halal ɗinsa yasa na sauke masa farashi sabon price Normal group 200 PC 600 zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, ne babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN. Ƴan Niger kuma zaku turo katin Airtel na 200f


*Oum Hairan*
[12/15/2022, 6:39 PM] OUM HAIRAN: *27-28* Don Allah in kinsan baki biya ba karki karanta 300 PC 600 acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN yan Niger kati Airtel na 300f.



Direwa tayi daga gadon da gudu tana kalle² ya ruƙo hannunta ya janyota jikinsa ya rungumeta zatayi magana ya ɗora hannunsa a bakinta cikin fizgar numfashi yace “Sheet-up Please Rumah" lafewa tayi a jikinsa tana sauke ajiyar zuciya sun ɗauki lokaci a haka kafin bacci y ɗauke ta inda sabo ya saba yakan sanyata bacci shikuma ya kwana karatun wasiƙar jaki.
Washegari ma fita yayi kamar jiya tare suka yini da Asma'u sai yamma ta koma ɓangarensu, Shikenan damuwar Rumah taragu kullum suka kasance tare da yar'uwarta idan ya dawo kuma yakan biyewa shirmenta har takanji kamar tan tare da sa'anta wani lokacin ma yakan fita shirme da shiririta da wannan ta samu nutsuwar da yake buƙata cikin watannin biyu tayi wani kyau na ɗaukar hankali jikinta har wani danshi yake fitarwa saboda Hutu sosai Mai Martaba yake jiƙata da duk abinda ya Burgeshi, watannin biyu kamar kwanaki biyu haka suka shuɗe batare da kowa ya ankara da wuccewarsu ba cikin lokacin ne kuma duk wasu shirye-shiryensa ya kammala ranar da kwanakin watansu biyu ya cika ranar ne suka ɗago zuwa gida Nigeria zuciyar Rumah wasai shi kuwa da tarin damuwa, tunda yasan meye dawowarsu Nigeria yake nufi.




KT.

Tun ranar da Mai martaba ya bayyana Rumah matsayin matarsa ta huɗu makullin gidansa abubuwa suka ɗauki zafi a wannan masarauta babu abinda kake gani da fahimta a kan fuskar kowa sai tsagwaron hassada da baƙin ciki kama daga waɗanda suka isa dama waɗanda basukai suyi magana ba, wannan abu ya zama damuwa damuwa a zuciyar kowa musamman Matan Sarki Amina da Sa'adatu waɗanda suke ganin kamar su wannan wacce irin zubewar daraja ne ya samesu ace baiwar mijinsu ta zama kishiyarsu babban abin damuwar ma a bayin ma mara asali mara galihu.
Yini sukayi kowa da saƙonnin da suke zuwar masa da kuma abinda yake ayyanawa.
A ɓangaren Gimbiya Maryam kuwa tunda maganar ƙarin auren ta Sarki Ridwan ta daketa ta miƙe ta fita ta koma sashinta kallo ɗaya tayiwa barorin ta masu hidima a gareta duk suka watse ta shige dakinta ta rinƙa safa da marwa zuciyarta na tafasa ranta suya wani abu na yawo a kanta zama tayi tace “Baiwa? Ridwan baiwa mara galihu yar tsintuwa?"
Tashi tayi taci gaba da zagawa ta ɗauki wayarta ta kira Na'imah wata amintacciyar baiwarta ce da aka haɗota da ita daga Bauchi Tun aurenta.




Ɗagawa tayi tace “Amincin Allah ya tabbata ga uwar ɗakina...." Katseta tayi da cewa “An yanka ta tashi Na'imah kizo turakata inason ganinki...." Kashe wayar tayi ta ajiye ta buga tagumi kanta na sarawa zuciyarta na tafasa, bayan kamar shuɗewar mintina sha biyar Kuyanga Na'imah ta shigo ta durƙushe gaban Maryam tace “Gimbiya ta Yarima hakikanin gaskiya duk damuwar data kasa ɓoyuwa a zuciyarki ta bayyana kan fuskarki to takai damuwa shin meye wannan da ya taɓa rayuwar uwar ɗakina?"
Zame hannu Fulani Maryam tayi tace “Ya cike Na'imah Nikam ina ganin ƙunci da tashin hankali yanzu kamar ni da aka haifeni cikin mulki da isa na ɓige da kishi da Baiwa tsintacciya..." Sai yanzu Kuyanga Na'imah ta gano bakin zaren tayi murmushi tare da ƙas dakai tace “Inada shawara ya shugabata" da sauri ta dubeta tace “wacce?" Ƙasa ta kumayi da kanta tace “Kina cikin mutane masu ƙima da daraja gurin Mai Martaba Allah ya taimakeki domin ke mace ce da ba'a gane zuciyarki kina iya ɓoye sharrinki domin wanzar da alkhairinki, shin zai yiwu ace kune matsalar mijinku kullum akanku yake neman mafita? Allah ya taimake ki dukkanku akayiwa kishiya amma Sai tafi dukan Sa'ade sai akayi dace Itadin yar fadar Surukarku ce Hajiya Tushi ita tanajin ta isa, ɗazu naji wasu yan ɓaryar Hajiya Tushi suna faɗin tabbas wannan amarya zata shiga uku...."




Katseta tayi da cewa “To Ni meye damuwata ne da shigarta damuwa" dariya Na'imah tayi tace “Shine babbar damuwarki kuma hanyar riƙe kambunki dole zakija yarinyar nan a jikinki ki cire batun kishi da ita ki nuna masa kinfisa murna da wannan auren Allah ya taimake ki kinsan hikimar hakan?"
Kallon sakarya takebin Na'imah dashi tare da girgiza mata kai, ta sake kwantar da kai tace “Ba komai ake kira da hakan ba face makirci da kutungwila irin tamu ta waɗanda sukaga jiya suka kalli yau kuma suke tsammanin ganin gobe. Idan kinjata a jika zata saki jiki dake bazata taɓa yarda zaki cutar da ita ba to Kinga zamuyi amfani da wannan wajan cimma burinmu na farko dai zamuyi amfani da wannan mu hana Mai Martaba samun damar shigarta koma mu cire masa tausayinta ta hanyar rusa masa burinsa na son ganin ya samu sassauci daga abinda ya shafe shekaru yanayi masa yawo a zuciyarsa sannan zaki ƙara ƙima a gurinsa zai sakar Miki ragama tunda a yanzu haka da Hajiya Tushi da Fulani Sa'ade da Waccan yar kuci ku bamun Fulanin tsakiya duk sun ɗauki zafi da muggan nufaƙa suna jiran dawowarsa da matarsa kuma wlh Allah akwai ƙura idan aka nunawa yarinyar nan baƙin taku domin da gaske ta kama zuciyarsa zai iyayin komai tunda ya iya fatali da ƙa'idar gidan ya taketa ya aureta tana matsayin baiwarsa bayan wannan haramtaccen abu ne a wannan masarauta ina fatan kin fahimceni?"




Wani Gwauron numfashi Fulani Maryam ta sauke ta jinjina kai tace “Shiyasa kike da matsayi me girma a gurina indai dake a gefena bazaki barni nayi tafki ba tabbas babu algus ko almundahana cikin tafiyarki yanzu ya zamuyi da Fulanin Sokoto kinsan fah da shawarar ta yake gudanar da komi nasan ko tantanma babu da sanya hannun wannan munafukar a auren nan ma"
“Karki damu da ita idan ya Baki yarda babu me ƙwace Miki" da wannan wannan tattaunawa ta tashi kuma tun daga wannan rana Fulani Maryam ta sanyawa kanta dabi'ar tura masa text kullum sau biyu na gaisuwarsa daya zama na ƙa'ida da kuma na gaisuwar Ƙanwarta injita da faɗa, dake ya riga ya yarda da ita fiye da sauran matansa baya kokwanto akan zuciyarta har waya takan kirashi ta tambayeshi amarya takance “Ina Fulani ƙanwata Abin ƙauna da gaske tunda na fahimci kana tausayinta Ni kuma na kamu da kaunar ta" yana jin daɗi sosai wannan tasa duk wani abu da zaiyiwa Rumah tana Nigeria amma da ita yake shawara.




A hankali Fulani Amina ta fahimci hakan ta kuwa sanar da Fulani Sa'ade nan suka faɗawa Hajiya Tushi aikuwa ta tako har sashin matan Sarkin ta zage Fulani Maryam tsaf bata kulata ba tunda tasan tanada manufa akan hakan.
To yau tunda gari ya waye gidan ake ta hidindimun taran sarki wannan dogon zango da yayi ko ina kabi sai ƙamshi a gidan sarautar kowa ya zama tsaf shirin tarɓar masu gari, ƙarfe huɗu motocin ɗaukosu sukabar filin parking na Katsina domin zuwa dauko sarkinsu busa ta algaitu sunata tashi tare da jiniya.
Sun zaunu a filin jirgi sai biyar jirginsu ya sauka mutane suka fara saukowa abokan tafiyarsu ne Saida kowa ya fito sannan excourt ɗinsa suka sauko shine ya fara fitowa sannan Rumah a bayansa kamo hannunta yayi suka isa cikin jama'ar tasa sunayita zubewa suna kwasar gaisuwa yana ɗaga musu hannu duk wani wanda ke gurin idanunsa kan Rumah yake hatta da Jakadiya idanunta kanta yake tana mamakin irin cikar da yarinyar tayi cikin wata biyu tayi wani mulmul da ita sai ɗaukar idanu takeyi ba Amina da Sa'adatu ba hatta Fulani Maryam Saida zuciyarta ta doka lokacin da ta sauke idanunta kan Rumah data canza musu tayi bala'in yi musu bazatar siffa.





Kamo hannunta taji anyi abinda ya haddasa mata juyawa idanunta ya shiga cikin na Maryam da taketa washe baki ta kuma juyawa ga Mai Martaba ya jinjina mata kai tare da sake damƙar ɗaya hannunta ya haɗa dana Fulani Maryam yayi musu murmushi gabaɗayansu.
Ƙasa Rumah tayi da kanta daidai lokacin da Maryam tace “Barka da kasancewa Sirri ga adalin Sarkinmu Jijiya tafi da ƙarfin jiki baya goya marayu ubanmu maganin kukanmu Sarki Ridwan mijina aljanna ta alfahari na, Fulanin Katsina inayi Miki fatan kasancewa kamar ni a zuciyar mijinmu kuma ina Invite ɗinki wajen samarwa Duniyarmu farin ciki.....
Kallon da taga Hajiya Tushi tanayi mata ne yasata sake shigewa jikin Rumah tayi kissing kuncinta tace “Ina farin ciki da samuwarki cikin duniyar duniyata ina kyautata Miki zato" da wannan suka wucce wajajen motocinsu duk yanda Rumah taso zamewa daga da'irar Maryam ta hanata tare suka shiga mota suka wucce gida, kai tsaye motar dasu Rumah suka shiga ɓangaren Fulanin Sokoto ta nufa tayi parking suka fito Maryam na riƙe da hannun Rumah suka shiga wasu dattijai dake tsaitsaye suka taresu da waƙoƙin su irin na gidan sarakai daga Rumah har Asma'u abin ya zame musu sabo Jakadiya ke jagorantar waƙen suka zagayesu har cikin turakar Fulanin Sokoto ta kurɗo ta kama hannun Rumah ta shige da ita cikin wata ƙofa dake turakar ta saki labule sai lokacin Rumah ta buɗe Idanunta sosai tana ƙarewa ɗakin kallo.




Turo kofar da akayi yasata sauke idonta ga me shigowar wasu barori ne su uku da manyan tire na tasa suka sunkuya suka ajiye suna gaisheta cikin girmamawa. Bata iya amsawa ba sai binsu da takeyi da idanu suka fito wasu suka kuma shigowa Saida aka jere tire goma sha biyu da tulunan tasoshi akansu bata gama wannan kallon da hangen ba aka fara shigo da ƙore na nono suma Saida aka jere goma sha biyu manyan ƙore ba ƙananu ba.
Daga bisani kuma aka kuma shigo da wasu akwatuna aka rinƙa jerasu a wata ɓarya ta ɗakin Saida aka jera akwatu talatin da shida sannan aka dakata da shigo da kayan, shuɗewar ɗan lokaci aka sake turo ƙofar Hajiya Maimuna Babbar ƴar Sarki Abbas yaya ce gasu Sarki Ridwan ita ce ta shigo tsayawa tayi ta zubawa Rumah idanu tana mamakin kyawun halittar yarinyar, rusunawa tayi tana gaisheta cikin girmamawa Hajiya Maimuna tayi murmushi ta ɗagota ta shafa fuskarta tace “Amaryar Sarki ba ita zata gaishemu ba mune zamu gaisheta" waya ta kira tayi maganganunta can wasu mata su biyu suka shigo Fulanin Sokoto na biye dasu Jakadiya na biye da ita suka shigo wai ashe wannan Nono Nonon kamun amarya ne Fulanin Sokoto tace.
To me ake jira da ba'a fara kamun ba dare yana shiga" rusunawa Jakadiya tayi tace “Allah ya ƙara miki lfy Mai Martaba ya umarceni da inkai masa Fulanin Katsina Turakarsa anjima idan komai ya kammala"




Hajiya Maimuna ce taja Rumah ta zaunar da ita tsakiyar wani kilishi da aka shimfiɗa ta cire mata mayafin ta zare mata ɗankwali hatta ɗankunne Saida aka cire mata duk wani kaya nau'in sutura Saida aka rabata dashi ya rage daga ita sai under skirt da bra tasa hannu ta maƙale ƙirjinta tare da rintse idanunta batare data tsammata ba taji wani sanyi yana ratsa ta buɗe idanun da zatayi taga ashe wannan madarar shanun ce aka sheƙo mata ita tun daga tsakiyar kanta har ƙafafunta.
Ɗauke numfashinta tayi saboda ita ba ma'abociyar karni bace ji take kamar tace ta shiga uku ta lalace wai ashe wasa farin girki durzar fatarta akayi sosai da dilka an cire mata dattin gaske a jikinta sannan aka sake shafe mata jiki da Nonon aka kunna mata fanka ya bushe sai lokacin aka bata umarnin ta shiga wani guri ta miƙe suka shiga ita da Hajiya Maimuna banɗakin yana fitar da wani sihirtaccen ƙamshi mai kashe gaɓɓan jiki ya daki hancinta ta lumshe Idanunta ta sunkuya ta ɗebi ruwan ta watsawa fuskarta, kallon sosai Rumah takeyi na ikon Allah wai ƙatuwa da ita abarta tayi wanka anƙi Hajiya Maimuna da Salmah Sudan sune suka wanketa tas tare da bata wani ruwa a wata yar buta sukace ta kama ruwa dashi suka fice ta ɓalle murfin saman butar ta lumshe Idanunta saboda ƙamshin ruwan data tsiyayo a hannunta batayi tunanin akwai irinsa a wannan duniya tamu ba haka ta rinƙa tsarki da ruwan tanajin wani ɗumi me yaji² yana shigarta yana ratsa ta har kwanyarta Saida ta ƙarar dashi sannan ta miƙe ta ɗauki rigar da Salmah Sudan ta bata ta wanka ta sanya ta ɓalle bottle ɗin ta fito tana zare idanu ganin wata kujera an sanya kaskon wuta a ƙasanta jajir dashi wai tace ta zauna akai.




Taso gardamewa Fulanin Sokoto ta girgiza mata kai dole don girman matar ta zauna ɗumin garwashin na ratsa ta tare da wani ƙamshi me kama jiki, wani ƙoƙo Fulanin Sokoto ta mika mata da wani jan ruwan tsumi kirtif dashi har wani yauƙi yake tace ta shanye.
Rintse idanunta tayi ta kafa kai ta shanye harda hawayenta na taɓara Fulani Sokoto tayi murmushi tace “Rumah kenan ba'a bori da sanyi jiki duk inda kikaji wane ba banza ba karɓi wannan ki shanye kici abinci dare ya shiga sosai" girgiza kai tayi tace “Fulani Ban...banashan... Nono" “To Fulani abarta mana ga wani shima takanas nasa a kawo shi daga Cameron don wannan dare....." “Dare!” Rumah ta maimata lokacin da Hajiya Maimuna tace “Haka zaki hƙr Kisha wannan haɗin dafa'in gidannan ne duk matar da aka kawo indai anasa mata ran budurci to dole ne tashashi...." Karɓa tayi ta ɗauke numfashinta ta zuƙe nandanan amai ya fara taso mata Hajiya Maimuna ta buɗe alawa ta jefa mata a bakinta.
Cije leɓe Fulani Maryam tayi ta fito da wasu matsiyatan kayan bacci tace “Mai Martaba ya bayar yace akawo" karɓa Fulanin Sokoto tayi kowa ya fita aka fara shiryata sai a wannan lokacin ta fara fahimtar nufin su lokacin ne kuma tsoro da firgici suka dirar mata data fara hasaso irin yanda marubuta ke bada labarin daren farkon kowacce cikakkiyar budurwa da irin yanda ake kasancewa bayan gabatar komai.




Shiri akayi mata na ƙasaita cikin wata fitinanniyar rigar bacci me ruwan gold aka sanya mata barima ta gold da zoben gold sai alƙyabba da takalminta Fulanin Sokoto da Hajiya Maimuna suka rinƙa yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login