Showing 9001 words to 12000 words out of 38364 words
ma a cikinsu meye yake faruwa?" Kwashe duk abinda ya faru tayi ta sanar da ita, shiru tayi dafe da kai tace “Ya akayi hakan ta faru?" Kwanciya tayi a jikinta tace “Nifa bansan komai ba kawai hakan ta faru ne Ni wlh ya tsorata ni Ma'u banason sake ganinsa ina gudun kada shaiɗan yayi tasirin huda zuciyarsa ya ɗarsa masa wata damuwar da zata dami kowa"
Dafata Asma'u tayi tace Nima shine tunanina yanzun dai abinda nakeso dake kija bakinki ki kulle ita kanta Jakadiya nasan duk surutunta wannan yafi gaban tattaunawa sai shiru sai kallo wato Rumah nifa na daɗe da ɗiga ayar tambaya akan Mai Martaba saboda yanda yake damuwa da shige da ficenki abin ya wuce tausayi kamar yanda yake furtawa saidai wani abu daban"
Lumshe idanu Rumah tayi tace “Yace zamuyi tafiya da Fulani Sa'ade saidai bansan meye yasa ba banason tafiyar gashi bazan iya cewa a'a ba" “hakanan zaki bita ku tafi kuma kiyi hƙr da rashin albarkarta kay Rumah matan nan na Sarki Ridwan basuda mutumci ko kaɗan musamman Fulani Amina da Fulani Sa'ade har gara Fulani Maryam ita wannan miskila ce baka fiye gane inda ta sanya gaba ba nifa jiya ba ƙaramin tausayi Mai Martaba ya bani ba da naji Jakadiya na bawa Indo labari wai da dare ya turo a kirayi Jakadiya yace yana buƙatar ɗaya cikin matansa tunda su kinsan gidan nan ba lissafin kwana sukeyi ba.
Shine Jakadiya taje ta samu Gimbiya Maryam take faɗa mata bukatar Mai Martaba wai ko kallonta batayi ba ƙarshe da taga zata dameta sai tace ace masa ta shiga kwanakin Hutu bazata samu dama ba, taje wajen Fulani Amina itako cewa tayi ta gaji da kiwon makahon doki bazata iya ba, ita kuwa Sa'ade cewa tayi don dai tanada buƙata ne shiyasa zata amsa kiransa a faɗa masa idan ya amince zai barta taje Yola to zata iya zuwa gareshi in bai amince ba kuma kowa ya riƙe kayansa"
Zubanta idanu Rumah tayi tace “Sai me ya faru?" Murmushi Asma'u tayi tace “sai yace ya amince" jinjina kai Rumah tayi tace “Abinda na lura game da Mai Martaba matsalarsa kawai matansa da uwarsa na fahimci babu cikakkiyar jituwa tsakaninsa da Fulanin Yola wai kinsan wani abu? A gidannan ankusa Auran bayi Mai Martaba ya tambayeni ko kinada wanda yake sonki cikin bayin gidannan, shine nace masa a'a bangani ba gsky"
Murmushi Asma'u tayi tace “To ya tambaye ki game da kanki?" Girgiza mata kai tayi tace bai tambayeni ba duk da naso ya tambayeni ɗin bani da matsala ta zahiri game da gidannan yanzu amma inada matsalar ɓoye Ma'u bansan meye na tsarewa barorin gidannan ba ina ganin ƙiyayyata a idanuwan duk wanda na kalla sannan Fulani Tushe itama bata kaunar ganina ji nayi tana furtawa shekaran jiya da Mai Martaba ya turani wai na gaisheta bance ta taɓa ganina ba amma ina zuwa naga annurin fuskarta ya ɗauke koda na gaisheta fa bata amsa ba ƙarshe cewa tayi na tashi na bata guri na taso zan fito naji tana cewa baƙuwarta ita ta rasa meye yasa tun ranar da Ridwan yazo yake faɗa mata yasa za'a kawo sabbin bayi daga gidan marayu amma matan ba kamar kowanne bayi suke ba kawai taji ta tsaneni wai koda yace zanje na gaisheta Saida tace kar naje batason ganina, to wai ni Ma'u meye yasa yake turani gaisawa da iyayen nasa ya turani gurin Fulanin Daura ya turani ga Fulaninsa yau kuma ya aikani ga Fulanin Sokoto ita ɗaya ce ta karɓeni da Rahma har ta tambayeni ko na iya kitso nace mata eh tace nayi mata Ma'u bakiga yanda take jana da hira ba har tana cemin na saki jiki da ita Nima ƴa ce kamar kowa wai idan babu damuwa zata faɗawa Mai Martaba ya dawo dani Ƙwaryarta ita dai nayi mata, sai naji Nima inasonta"
Dariya sosai Asma'u tayi tace “Wlh kin bani dariya to banda abinki Rumah bakiji abinda Ali Isa Jita yace ba (Wanda ya soka ka soshi, wanda ya ƙika ka ƙyaleshi....) Yanzu ya maganar tafiyar taku Yola?"
Tsaki taja tace “Idan Mai Martaba ya sake neman zaɓina zance masa banason zuwa nifa na rasa meye yasa kwata² matan Mai Martaba basuyimin ba musamman Fulani Sa'aden nan rashin mutuncinta ya shahara" dafata Asma'u tayi tace “Ai ta samu ɗaurin gindi gurin Fulanin Yola kinsan ance ƴar ƙaninta ce ita ta ƙulla auren"
Shigowar Jakadiya ne ya sanya su tsuke bakinsu ta nemi guri ta zauna taname ƙarewa Rumah kallo tare da duban agogo tace “Mai Martaba ne yakeson zaiyi tafiya zuwa Austrelia cikin barorin daya ware zaiyi tafiyar dasu har dake kuma gobe ne tashin".......
*Oum Hairan*
[12/15/2022, 1:12 PM] OUM HAIRAN: *Oum Hairan Paid page 17-18*
Dukkansu suka ɗago suka sauke idanunsu kan Jakadiya bakin Rumah na rawa tace “nin...ni kuma? Jakadiya nifa...." Jajayen idanunta ta zuba mata abinda ya sanyata yin ƙasa da idanunta zuciyarta na bugawa da ƙarfi Asma'u ta sauke nannauyan numfashi tace “Wai dama haka tsarin rayuwar waje take Jakadiya komai sai abinda akeso zakayi ba abinda kakeso ba, shin zai yiwu ace kai bakada zaɓi?"
Wani ɗan iskan kallo Jakadiya tayiwa Ma'u tace “ke har wata rayuwar yanci kike nema bayan wanda kika samu daga gidan marayu matsayin mara galihu zuwa gidan sarauta harda darajar kusanci ga kololuwar daraja wanda kowa yakeson yaga ya raɓi jikinsa hakika ɗan adam butulu to kuje ku sameshi sai kuyi masa bayanin yanda kukeso ayi Nikam nayi nawa" ficewa tayi tabar musu ɗakin abinda yasa Rumah kwanciya zuciyarta na ƙunci na rashin mafita itakam tana ganin rayuwa shin meye Mai Martaba yake nufi da itane da komansa saiya sanyata, a zahiri batason bin Fulani Sa'ade amma da ta tafi tare da Mai Martaba gara tabita duk tsiya ita babu wanda zai ɗora mata ayar tambaya don tayi mata rakiya ta rikenta jaka.
A daren nan cikin su biyun nan babu wacce ta rintsa Asma'u zafin rabata da yar'uwarta da za'ayi tsayin watanni ita kuma tunanin halin da zata kasance a wannan tafiya washegari da safe ya aiko kiranta fitowarta kenan daga wanka tana shafa man coco butter a jikinta Samira ta shigo tana watsa mata harara tace “Tsugudidi sai a tashi aje takawa na kira" tunda ta ambaci takawa kawai taji ranta yayi ƙunci hakanan don rashin isa ta tashi tasa doguwar rigar Shadda baƙa ɗinkin yaji stone abinka da farar fata duk da ba wani murjewa tayi ba tayi matuƙar yi mata kyau Rumah babbar mace ce akwai manyan kaya sanin yanayin halittar ta yasa bata rabo da hijjab.
Yau kawai taji tana ra'ayin sanya mayafi ta ɗauko wani milk da takalmi flat shima milk tasa ta bata ɗaura ɗankwali ba sai dogon baƙin gashinta data ɗaure da milk ɗin ribbon da Black abinka da kyakkyawa nandanan tayi wani kyakkyawan kyau mai burge idanu kallo. Fita tayi tana ratsa gidan sarautar tunda take a gidan bata taɓa yin kwalliya kwatankwacin yau ba dalilin da yasa ta zamewa kowa abar kallo so da yawa barori maza sukanso kulata saidai takanyi musu kwarjini saboda batada fuskar wargi sunfi raina Asma'u domin sukan bata saƙo ta faɗawa Rumah kulawa ne batayi abinda ya ƙara mata baƙin jini a gurinsu kenan su kuma yammata tunanin zata hana a kallesu yasa suke ƙyashinta.
Hajiya Rumah...." Taji an furta a bayanta ta juya da sauri tare da faɗaɗa fara'arta tace “Da kai zamu tashi Lameer kwana biyu bana ganinka ina ka shiga ne" shafa kansa yayi yace “kedai kika ɓuya babban kifi sai babbar gora Rumah ba sa'ar yaro ba wannan wanka haka kamar kece amaryar Sarki...."
Rufe masa baki tayi tana dariya tace “Lameer kanajin daɗin zolaya ta ya kake ya hƙrn rayuwa?" Numfashi ya ajiye yace “Alhmdllh Rumah sai godiyar ubangiji rayuwa cikin babbar jarabawa yanzu ina zuwa ne" farr tayi da idanunta tace “Zan amsa kiran Mai Martaba ne" cikin sarewa yace “Bantaba shiga ɓaryar Mai Martaba ba ko zan iya rakiya?" “Zaka iya amma iyakarka bakin ƙofa bai bari a shigar masa da baƙi sai wanda ya aminta"
Suna tafe suna tattaunawa suka isa ɓangaren akace mata yana ciki tun a ƙofar farko ta fara saita nutsuwarta ta shiga da sallama yana zaune saman wata kujerar ta alfarma duk sanda tagansa a wannan kujera tasan da gaske yau mulkin yakeji domin ko magana bai cika yi ba a wannan yanayin saidai umarnin ido.
Ƙirjinta ta riska da bugawa da ƙarfi ganin wasu kyawawan mata guda uku zaune a kujerun dake falon suma sai muzurai sukeyi, sarai ta kuma shiga hankalinta ta nemi guri nesa dasu ta durƙusa ya ɗago kansa dake ƙasa ya saukeshi a kanta itan kanta a ƙasa yake zuciyarta na lugude saboda tsoron da ya shigeta ko ba'a faɗa mata ba tasan waɗannan damusoshin sune matansa don su kaɗai suke da darajar zaman sama in har yana sama.
Ɗagowa tayi cikin nutsuwar ladabi tace “Allah ya taimake ka Barka da wannan lokaci Samira ta sanar dani kana buƙatar ganina shin ana buƙatar wani abu ne?" Numfashi ya ajiye ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa akanta ya motsa bakinsa kamar dole yace “Rumah!..." Yanda yayi furucin yayi mugun kaɗa hantar cikinta ya sake jan numfashi yace “Kin tashi lfy?" Ɗagowa tayi Idanunta ya shiga cikin nasa da yau ko arziƙin tabarau ɗin babu fuskarsa babu alamar wasa tasan dole ta amsa wannan ta sanyata cikin rabewar kalmomi tana kallon idanun matan dake zaune da suke kallon kallo tsakaninsu tace “La..la..fiy...a ta...ka...wa....." Murmushi yayi wanda ya fitar da sauti ya sanya hannu ya ɗauke hular da tasha naɗi daga kansa ya kalli ta gefensa yace “Maryam!" Ya kuma juyawa daya gefen yace “Amina!!" Ya sake kallon ɗayar yace “Sa'adatu!!!" ya karkata injin idanunsa ya saukesu kan Rumah yace “Rumasa'u!!!!"
Gwauron numfashi ya sauke ya miƙe tsaye ya taka a hankali zuwa inda Rumah take durƙushe ya sanya hannu ya ɗagota yayi mata matsuguni saman kujera abinda ya sanya Fulani Maryam Fulani Amina Fulani Sa'ade miƙewa sunayi masa kallon dake nuna zallar tuhuma.
Murmushi ya kumayi ya rinƙa binsu ɗaya bayan ɗaya yana zaunarwa ya zauna a inda ya tashi yace “Idan baku manta ba wata biyu da suka wucce na sanar daku zan ɗaura aure babu wacce ta tambayeni game da hakan Nima kuma ban samu dama da lokacin yi muku bayani ba, Allah cikin ikonsa tabbas na ƙara aure Rumasa'u itace yarinyar da take amsa sunan matata kamar Maryam kamar Amina kamar Sa'adatu...."
Sake miƙewa sukayi wannan karon harda ita kanta Rumah ta zaro ido tare da dafe ƙirji zatayi magana Fulani Amina tace “Kan uban can Baiwa mara galihu yar tsintuwa Yar gidan marayu shegiya...."
Tsawa ya daka mata data sanyata saita shiga taitayinta ya nunata da yatsa yace “Karki ƙara furtamin wata kalma anan" Guri ta samu ta zauna ya kallesu ɗaya bayan ɗaya tare da damƙar hannun Rumah da kalamansa dana Fulani Amina sukasa jikinta ya ɗauki ɓari yace “Koma meye kuna iya faɗa ba don kun isa ba saidon kar ranku ya ɗarsa wani abu yasa na buƙaci ku sani kamar yanda yake akan kowaccenku haka itama ya zagayo kanta da ita zamu tafi inda mai magana tayi"......
*Oum Hairan*
[12/15/2022, 1:12 PM] OUM HAIRAN: *Oum Hairan Paid 19-20*
Don Allah in kinsan baki biya ba karki karanta saboda kowa ya samu damar karanta halal ɗinsa yasa na sauke masa farashi sabon price Normal group 200 PC 600 zaku tuntuɓe Ni ta wannan number a WhatsApp 09013718241, ne babu VIP ko ku tura ta acct 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko katin MTN. Ƴan Niger kuma zaku turo katin Airtel na 200f.
**********
Miƙewa Fulani Maryam tayi tabar gurin batare da fuskarta ta nuna wata alama da zaka iya fassarawa a matsayin ma'auni ba, kallon Fulani Sa'ade yayi ta kawar da kai domin bata fatan ya fahimci halin da take ciki itako Fulani Amina dama ta riga ta fitar da zuciyarta ya gani da wannan ya riƙo hannun Rumah ya miƙar da ita yace “Muje" bata iya yi masa musu ba tabishi a baya idanunta na fitar da wasu zafafan hawaye suna fita dogarawansa suka rufa masa baya hakan ya bata damar sulalewa tabi wata hanya da zata sadata da sashin bayi ta nemi guri ta zauna ta haɗe kai da gwiwa ta rushe da wani kuka me sautin ban tausayi a fili tace.
“Mai Martaba meye yasa ka aikata haka meye yasa ka biyewa son zuciyarka Innanillahi wa inna ilaihirraji'un Shikenan ka sake sanyani a masifa gashi har an fara yimin gori, Ni Rumasa'u ina ganin rayuwa ya zanyi na iya rayuwa cikin waɗannan matan da suke jin taƙamar isa da gadarar nasaba Ni gashi banida kowanne...."
Kinadashi Rumah...." taji an faɗa ta ɗago takai dubanta ga me maganar ya tsugunna gabanta ya sanya hannu ya dafa kanta yana saisaita fuskarsa daga jin ikon isa zuwa samawa abokin tattaunawa nutsuwar zuciya da sanyin ruhi yace.
Karki bawa zuciyarki wahala wajen kokawar tura mata ƙin hukuncin ubangiji Rumah da gaske nakeyi tun ranar da kikace kina samun nutsuwa da ɗumin jikina naji a raina dole na mallaka Miki shi mallaka ta har abada Please forget about wannan munada sa'a uku da rabi ne daga Katsina zuwa Kano, kina buƙatar tafiya da hadimai ne domin hidima a gareki?"
Saurin girgiza masa kai tayi yaja fasali yace “Ko ɗaya My Bride?" Sunkuyar da kanta tayi yayi murmushinsa na isa ya miƙar da ita ya haɗata a jikinsa ya sanya hannunsa biyu ya rungumeta sosai yace “Da Asma'u ko?" Da sauri ta ɗaga masa kai ya janye yace “Shikenan muje asa a taho da ita Rumah dama zan samu matsayi kwatan na Ma'u na fahimci Asma'u tafi misali gareki"
Suna tafe kanta a ƙasa har jikin motar aka buɗe masa ya sanyata a ciki ya rufe suka buɗe masa ɗayan part ɗin ya shiga ya zauna yana kallon dogarin yace.
“Aje a taho da Asma'u ku ishemu a hanya" zubewa yayi yace “angama Namijin duniya mazan jiran maza uban Abbasu baya goya marayu hauren Giwa maganin me haɗama mijin Gimbiya Maryam angon Fulani Amina mijin Fulanin asali Fulanin Yola Sa'adatu sa'ar mata gidan daba sa'a ba saa....."
Idanunsa ƙurr kan Rumah da tayi kasaƙe tana wasa da zoben azurfar hannunta yanason fahimtar yanda take ɗaukar kirarin a zuciyarta saidai ya kasa gane komai ya fahimci da uwar gidansa Fulani gimbiya Maryam da Amaryarsa Rumasa'u suna da kamanceceniyar halayya duk ƙwaƙwarka in basuso ka gane abu ba bazaka fahimta daga garesu ba.
Sunyi tafiya me tsayi tunda Rumah take bata taɓa tafiya me tsayin wannan ba hakan ya sanyata kwantar da kanta jikin murfin mota ta bacci ya ɗauke ta batasan ya kwantar da ita jikinsa ba Saida suka isa Aminu Kano International airport sannan ta farka tajita manne a jikinsa ta janye a hankali yaja ajiyar zuciya ya buɗe fararen idanunsa masu ratsin gold cikin ƙwayar a kan fuskarta tayi ƙasa da nata ya kama hannunta ya ɗora a kuncinsa yace “Kin taɓa zuwa Kano?" Kaɗa masa kai tayi yace “ko mu bari sai jibi mu tashi sai na zaga dake kiga Kanon dabo tumbin Giwa kodame kazo sunfika kirarin da sukeyi mata?" Yanda ya karshe maganar yasata ɗan murmusawa tace “Kuma uzurinka fah?" Murmushi shima yayi yaji daɗin yanda yaga ta fara sakin jikinta yace “Nop Wifey ba wani abune na gaugawa ba sai next week ma meeting ɗin dama tarone na sarakunan duniya so tun Mai Martaba yana raye Ni nake wakiltarsa in kinso sai a bari sai ƙarshen sati ma a tafi ai yanzu kece da kambun nawa na ajeshi a KT"
Alama ce ta nuna masa tanason zaman Kanon ya dubi Labaran Driver yace juya ka koma damu UDB road zamu danyi wani uzuri na kwana biyar a Kano...." Da sauri tace “Kayy takawa kuɗinka fah kuma Nikam dai kada kayi asara kabari idan mun dawo...." Ɗora mata hannu yayi a baki yace “Sheeet Bby ranar biyan buƙata rai ba a bakin komi yake ba inji ƙuda"
Bata sake cewa komi ba motar ta juya dalilin da yasa dukkansu suka rufa masu baya anata buga jiniya wani katafaren gida aka buɗe musu suka shiga sukaja parking Saida kowa ya fito sannan ya fito itama ta fito dogaran da hadiman da suka taho dasu suka rinƙa kallon kallo cikin mamakin meye kuma wannan sabo iyakar saninsu Rumah baiwa ce hadima wa Sarki Ridwan Abbas so meye ya shigar da ita mota ɗaya dashi? Masu buɗaɗɗiyar ƙwaƙwalwa sune suke tunanin kodai ya massheta saɗakarsa ko kuma dai da wata boyayyar alaƙa?"
Rashin isa da samun amsa ya sanya su fara gyatta masa hanya har yayi gaba bata biyosa ba duk jinta take akasin daidai Saida yayi taku yakai uku ya tsaya ba tare daya juyo ba yace “Rumah biyoni" bin bayansa tayi zuwa wata ƙofa aka wangameta suka shiga ciki ta ɗaga kanta tana ƙarewa falon kallo aljannar duniya ta faɗa a ranta tana haɗiyar yawu tabbas masu layya su adda nama inji Hausawa wannan alatun rayuwar duniya haka kamar babu mutuwa.
Tana tsaka da wannan tunanin suka shiga wani parlour daya kere wancan komai parlour na uku kuma na ƙarshe shine ƙarshe haɗuwa cikinsa matattakalar bene take suka taka suka haura sama abin daya bata mamaki wannan benen Bama ka sanin kana takashi saboda taushi da gajarta gabaɗaya step ɗin baifi goma ba suka isa wani hamshaƙin parlour wayyoh badon Rumah miskila bace tabbas data baza ƙauyanci, saidai kash ba'a iya gane abinda ke ranta ta kallo saidai idan ta furta.
Wani ɗaki ya buɗe suka shiga ya mayar ya rufe ya zare mukullin ya ɗora saman bed set ya zubanta idanu itama shi take kallo ganin ya juyo yasata janye idanunta yayi murmushi ya cire alƙyabbarsa ya zare takalminsa na sarakai tare da cire Safar farar ƙafarsa ta zubawa idanu ƙafarsa ta daɗe tana burgeta kamar ba ƙafar namiji ba.
Bata san ya isa gareta ba Saida taji ɗumin hannunsa a ƙugunta ta dubeshi da sauri ya ɗaga mata gira, tare da saita idanunsa cikin nata ta lumshe nata tana haɗiyar wani ruwan tsoro, a baya ta sake dashi sosai amma tun juya ya fara koyawa zuciyarta tsoronsa,