Showing 36001 words to 38364 words out of 38364 words

Chapter 13 - RUMAH COMPLETE

26 Aug 2026

49

haihuwa ba abinka da ruwa biyu gani bafulatani gani Balarabe saina zama farin wata sha kallo cikin sa'o'i Babana har babana ya gama haɗa master's da PhD ɗinsa muna zaune cikin soyayya da kulawa da juna.
Kwatsam sai yayi nufin dawowa gida Nigeria da zama sosai Kursum tayi kukan rabuwa da iyayenta ta biyoshi a lokacin Ni ina karatu sai kakana Hamid ya roƙi Ubaid yabar masa Abdul Malik ya ƙarasa karatunsa anan.




Mahaifina baiso ba amma bazai iya hana surukin nasa Ni ba saboda yayi masa halaccin da bai cancanci butulci ba.
Sun dawo Adamawa zaman yaƙi daɗi tsakanin Laure da Kursum babu meyi da wani kowa harkar gabansa yakeyi gashi dama wariyar launin fata tasa gidan Sarki Moddibo babu me ƙaunar Kursum in kika ɗauke mahaifiyarsa Lahira da take janta a jika wannan ya haddasa zazzafar ƙiyayya tsakanin Kursum da Laure kasancewar dama can Lahira bata wani son Laure don ta fito ne daga tsatson kishiyarta Kande ita kuwa Kande bata taɓa ƙaunar Lahira ba daidai da yini, shi kansa auren Laure da Mamman Ubaid haɗin Mai Martaba Moddi ne.
Cikin hakan Kursum ta kuma haihuwar ɗanta AbdulHameed shekara na zagayowa ta kuma haifar Abdul Fatah sai autarmu Ummu-Rumanah sunan kakarmu kenan wacce ta haife Kursum, ƙanne na da mahaifiyata suna rayuwa cikin yan uwansu ƴaƴan da Laure ta haifa Amina Zainab wato mahaifiyarka da Fatima da Sakina sai Autan gidanmu Abdulkarim.




Bakin ƙoƙari mahaifinmu yayi don ganin kanmu ya haɗu amma ina abin ya gagara koda yake Ni banma taɓa zuwa Nigeriya ba labarinta nakeji a Misrah nayi karatuna har na gama lokacin Maddibo ya kwanta dama aka ɗora mahaifina sarautar Yola ya auradda yaransa dukkan matan har Rumanah autar ɗakinmu wasunsu ma sun hayayyafa sun tara zuri'a lokacin ne kuma mahaifinmu ya takura saina dawo kusa dashi saboda na rinƙa ganin dabarun mulki tunda Kakana da nake tare dashi ya rasu tun shekara biyar baya ƙin tahowa nayi saboda bazan iya baro abar ƙaunata Fatima a Misra ba inajin kamar wani abu zai faru bayan dawowata.
Dana faɗawa Mamman Maddibo abinda yasa bazan taho ba, batare daya sanar dani ba kawai sai kirana yayi yace yana airport da farin ciki na ɗauki Fatima mukaje muka taroshi, da dare bayan ya huta y cca kirani dakinsa yake cemin yazo ne akan maganar aure na da Fatima nayi murna sosai indai takaice muku bai baro Misra ba Saida aka ɗaura aure na da Fatima sannan ya taho da alƙawarin sati biyu masu zuwa zamu taho ƙanwata Rumanah da muka fi shaƙuwa da ita wani dare muna kwance ta kirani kamar bazan daga ba Fatima ta matsa min na ɗauka ina ɗagawa najita tana Nishi na zabura na miƙe cikin fitar hayyaci take cemin “Akheey... Malik...sun kashe Na'im sun sawa gidan wuta sun saceni sun kaini wani jeji sun jefar dani... Akheey mutuwa zanyi sun tafi da ƴata Asma'u bansan me zasuyi da ita ba karsu cutar da ita...."

Wani ihu na saki ina cewa “Ukteey! Uktee Rumanah su waye kukayi musu ina mijin naki a ina suka kasheshi...?" Tambayoyi ne da ban samu amsarsu ba sai wani Nishi da nakeji ta cikin wayar ina kiranta ina faɗin “ki faɗamin inda kike zanzo zan aiko AbdulHameed yazo ya tafi dake Rumanah kiyi magana mana....."
Babu wata alama da take nuna za'ayi magana hakan yasani kashe wayar na fice a gidan na kira Sarki Mamman Maddibo bai samu ɗaga wayata ba hakan ya sanyani nufar Ambercy namu na saki kuɗi sosai aka samamin jirgin da zai tashi zuwa Kano a ƙarfe uku na dare ina komawa gida na sanar da Fatima muka fara shirin tafiya biyu ma a airport tayi mana munanan har ukun sannan muka tashi a Kano aka saukemu karon farko a rayuwata dana taɓa zuwa Nigeria AbdulHameed yazo yayi mana jagora muka kuma hawa wani jirgin zuwa Adamawa babban birnin Yola muka sauka yan'uwana da muke ɗaki ɗaya dukka sun zo tarata harda Abdulkarim ƙaramin ƙaninmu na ɗakin Laure muka isa gidanmu ashe tun jiya ansa barorin gidan sun gyaramin inda zan zauna da matata.




Kamar yanda na ƙudurta ina dawowa na shiga fafutukar neman Rumanah mun samu gawarta a wani jeji tsakanin Kaduna da Katsina sosai munyi kuka mun shiga damuwar kisan wulaƙancin da akayi masu ita da mijinta gashi an sace ƴarsu iyakar bincikenmu mun kasa samun wannan yarinyar hardai ƙarshe muka dangana bayan mun baza cigiya gidajen rediyo da talabijin.
Watanni suka tura babu labarin Asma'u dole muka ƙara dangana lokacin ne kuma Fatima ta shiga yanayin laulayin ciki me wahalar gaske dake Mahaifina ya samamin aiki a Abuja ina tafiya na barta ita da mahaifiyata taci gaba da rainon cikinta har ya kusa isa haihuwa wata rana nazo Hutu muna zaune Fatima take tambayata sunan da zan sanyawa bbynmu inta haihu dalilin da yasa na ɗauki biro nayi mata wannan rubutun kenan da ya zama shaida ta biyu mai ƙarfi, ina zaune bayan na koma Abuja kiran Sarki Mamman Maddibo ya shigo wayata bankai ga ɗagawa ba ya katse kafin na kirasa kiran Ummu ya shigo na daga da sauri tunanina zasu cemin Fatima ta haihu sai naji saɓanin hakan Labarin daya gigita duniyata da zuciyata labarin daya kiɗima nutsuwata da hayyacina na zabura da sauri nace.




“Ina Fatiman ta tafi waye ta sani a garin nan da zaace ta fice baasan inda ta tafi ba?" Cikin tashin hankali Ummu tace “Sarkin kofa ya tabbatar da babu wacce ta fita a gidannan sai wata mahaukaciya..." Ban gama sauraronta ba na kashe wayar na baro Abuja koda nazo abinda ta faɗamin shi aka maimata min Tabbas zan iya cewa tunda nake bantaɓa faɗawa tashin hankali irin na wannan lokaci ba matata da tsohon ciki ta fice ba'a ganta ba, abu kamar wasa Fatima ta ɓata ɓat wani malamin Mahaifina shine ya tabbatar masa da cewa wannan mahaukaciya data fita tabbas matata ce an tura mata da aljanun Hauka ne sun shafeta kuma bata cikin jaharmu gabaɗaya domin tana fita suka ɗauke ta suka bar gari da ita tanacan sun jefar da ita a wani yankin ta yiwu ƙasar ta yuwu ba ƙasar ba amma kar na ɗaga hankalina zata dawo komai daɗewa naje nayita addu'a.




Nasan addu'a magani ce ga duk wata masifa amma ban gaza shiga damuwa ba mun shafe shekaru muna faman nema lungu saƙo amma babu ita babu dalilinta har shekara goma sha biyar ta shuɗe wata rana na shigo Katsina gidan Saratu yayata dake auren Sarki Abbas kasancewar Allah yayiwa mijin nasu rasuwa na fito daga titin gidan Sarki na ɗauki hanya kawai banyi aune ba wata mahaukaciya ta shigo min na take birki amma ina aikin gama ya riga ya gama na bugeta, tuni mutane sun taru a gurin nayi saurin fitowa ina salati na isa gareta na durƙusa inajin surutan mutane sunata zagina wasu kuma na tausayamin suna cewa ita dama wannan mahaukaciyar ta saba haɗa hatsari a wannan titi.
Hannu nakai na cire gashin daya lulluɓe fuskar wannan mahaukaciya gabana ya yanke ya faɗi cikin tashin hankali da tsananin mamaki nace “Fatima!..." Duk sai kowa ya bini da kallo na cacumeta nace “Matata ce wlh Fatima na ce ku nunamin asibiti" daƙyar wani cikin matasan yayi kasadar shiga motata ya nunamin asibitin muka kaita Saida tayi sati biyu ƙarshe suka turamu Kano Aminu Kano teaching hospital.



Acan akayi mata Scan na ƙwaƙwalwarta aka tabbatar da babu wani ciwo a cikinta saidai ayi mata na Muslunci na ɗauki wannan shawarar na ɗauketa muka koma Yola acan ne Ubangiji ya kawo makarin ciwonta ta samu sauƙi ta zama mutum mukaci gaba da rayuwa kullum na tambayeta labarin cikin data tafi dashi abu ɗaya ne kuka zata sanya tace ita bazata iya cewa komai game da cikin ba abu ɗaya ta sani ta haifeshi saidai ina yayi ina yabi bazata iya tunawa ba.




Kwatsam wannan labarin ya ishemu muna zaune muna kallon labaran BBC aka hasko wannan tsohon hoto da mukayi tun lokacin aurenmu da kuma wannan takarda da nayi wannan rubutu na sunan Ƙanwata Ummu-Rumanah da nakeson sanyawa ƴar da Fatima zata haifamin tun a jiyan muka kasa sukuni mun kira wayarka bamu samu ba saita Amininka Usman dake Kano muka samu a daren yaje gidanmu dake tun ɓatan Fatima dana koma Misra Mahaifinmu ya matsa lallai yana sona kusa dashi to dana dawo ban koma Yola ba a Kano nasai gida nake zaune batare da nayi aure ba har Allah ya bayyana min Fatima wannan shine abinda ya rabamu dake Ƙanwata ba yanda kike tunani bane ni na taso cikin wata irin sarkakiya da Yan uwana da muke uba ɗaya da ƙannan mahaifina dukka basa ƙaunata saboda sunajin cewa idan mahaifinmu ya kwanta dama nine sarkinsu gashi Ni ɗin ruwa biyu sunfiso asalin bafulatani ya mulkesu wannan ya janyo aka jeho uwarki duniya a burinsu kar ta ƙara ganuwa har abada koma ta mutu da ita da abinda ke cikinta"



ASALIN LABARI



Wani sabon kuka Rumah ta fashe dashi me tsuma zuciya ta rungume iyayenta tana sunsunarsu tana hawaye tana cewa “Na shiga kuncin rayuwa na shiga damuwa na kasa samun farin ciki duk ta dalilin rashinku na kasa karɓar ƙaddarar cewa ni shegiya ce ashe dai da gaske Ni ba Shegiya bace, Abba bantaɓa kasancewa cikin farin ciki ba saida Allah ya jeho Sarki Ridwan cikin rayuwata shine farin cikina shine walwalata yakan sadaukar da farin cikinsa don nawa ya amince ya rayu da ƙunci da tsangwamar kowa indai zanyi farin ciki ya ɓata da kowa donni ya rabu da kowa donni Abbu Ummu dame zan sakawa wannan bawan Allah alkhairansa gareni? mahaifiyarsa ma ya bari duk domin ni ashe ba iya tausayi bane jini ne tabbas na yarda ko a cikin dubu jini warar kansa yakeyi inama inada abin sakawa duk wani farin cikina Ridwan shine sila Allah karka kasheni saina biya wannan tukuicin...."
Rufe mata baki taji anyi ya janyeta daga jikin iyayenta ya haɗata da nasa yace “Zaki iya ƙanwata inada tabbacin zaki iya bayan wannan cikin dake jikinki a tafiyar da nayi manyan likitocin duniya sun tabbatar min sperm ɗina ya tsinke bazai taɓa gyaruwa ta gurinsu ba saidai in Allah ne yaso Rumanah bazan ƙara haihuwa ba don Allah karki gujen....




Rufe masa baki tayi da nata ta makaleshi tare da janye nata tace “Ko bamu da kowa dagani saikai zan rayu cikin aminci da farin ciki bare yanzu Allah ya azurtamu da Taufeeq ga kuma ƙani ko ƙanwar Taufeeq soon zatazo duniya da amincewar ubangiji, mijina wlh babu abinda zaisa na gujeka har gaban abada"
Buɗe ƙofar da akayi ne yasata sakin juna Rumah tayi baya da sauri itako Hajiya Tushi kanta a ƙasa ta zube ta rushe da kuka tace “Na tabbata asararriya dana kasa fahimtar wannan ƙaunar da Ridwan yakewa Rumah ba banza bace ashe jininsa ce ƴar ɗan'uwana na cutar na tsangwama na tsana na hanawa walwala da mijinta...." Sake fashewa tayi da kuka ta riƙe kafar Prince Abdulmalik tace “Ka yafemin ɗan'uwana wlh bantaɓa tunanin wannan sarƙar zata zamo haka ba hankalina baitaɓa ganin kamar nan ba sai yau yaune na tabbatar da gizon da fuskar yarinyar nan takemin ba tsantsar ƙiyayyarta bace zagawar jini ne" sakinsa tayi ta cafko hannun Rumah tace “Na godewa Allah na gde maka Ridwan da baka biyewa zugar da shaiɗan da shaiɗanun mutane sukemin ka saki Rumah ba, Ridwan na cutar dakai nice na zubarwa da Rumah cikinta na farko na kuma yi yunƙurin zubar da cikin wannan yaron ubangiji ya nuna mini ya fini ashe kaina nakewa asara kaico da taɓewa irin tawa yanzu da jika na uku Rumanah zata haifamin...."





Saita sake fashewa da kuka ta zube a ƙasa Rumah ta sunkuya ta kama hannunta tace “Sau da dama nakan jiki a cikin jinina kina yawo nakan ɗauki ƙafa nazo na ganki koda zaki zageni kawai don kallonki yana aika saƙon nutsuwa cikin ƙwaƙwalwata kamar yanda kasancewa da Takawa yake gusarmin da duk wata damuwa Hajiya bantaɓa riƙarki a zuciyata ba domin ko babu wata alaƙa kin wucce na rikeki a raina duba da kin haifamin mafi daraja cikin mazan duniya bayan mahaifina nasan rashin sani ne yasa komai ya faru kuma ko ubangiji baya hukunta bayinsa da laifin da suka aikata bisa rashin sani nikam na yafe miki kema ki yafemin don Allah kuma ki barni na rayu da mijina ɗan'uwana wlh in kika rabani...." Rufe mata baki tayi tace “kina tare da ɗan'uwanki har abada"
Rungume juna sukayi suna dariya Asma'u dake fitowa tace “ko wannan na itace Asma'un da kuke nema?" Ta ɗauko wani hoto ta miƙawa Abbu yana karɓa yace “Tsarki ya tabbata ga Ubangijin dake haɗa dangi waje ɗaya tabbas wannan Asma'u ce ƴar Rumanah ina kika samu wannan hoton?" Durƙushewa tayi ta rushe da kuka tace “Tun ina ƙarama metroom Lami take nunamin tana cewa hotona ne lokacin da aka tsintoni a wani jeji ina yawo ina kuka ina kiran Ummu Abbu a lokacin ko Hausa ban iyawa daga fullanci sai Larabci"
Nan guri ya kuma hautsinewa da murna sukayiwa ubangiji godiya suka rungume juna.
Bayan komai ya lafa ne an yaɗawa dangi na gida dana ƙasar waje cewar anga Ƴar Prince Abdulmalik da ƴar Rumanah da suka ɓace tsayin shekaru tuni Rumah cikinta ya tsufa ita kuma Asma'u aka shiga shagalin bikinta da Imran ƙanin Sarki Ridwan ɗa ga Fulanin Sokoto.
Rumah ta hafo yaranta biyu maza sukaci suna Abdulmalik da Ubaidullahi cikin hakanne Fulani Maryam ta fara rashin lafiya ana dubata saiga ciki ya bayyana haba murna kamar me akaci gaba da rainon wannan ciki Rumah tanata tsokanarta ranar da Maryam ta haihu washegari Rumah ta fara rashin lafiya dake takawa baya gari ya tafi China abu kamar wasa ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa aka kira Dr Mansura zuwanta babu dadewa Rumah ta sake sunkuto yaranta biyu duk mata wannan family ya cika da farin ciki kowa murna yake haihuwar yara uku duk mata a gida ɗaya akasha suna na ban mamaki tun daga wannan kuma haihuwa ta tafi sukaci gaba da rainon yaransu ga kuɗi ga sarauta ga kwanciyar hankali




Tammat bih hamdullah
Nan na kawo ƙarshen wannan littafi na Rumah ina fatan saƙon da nakeson isarwa ya isa ga al'umma kuskuren ciki Allah ya yafe mana taken ƳAR KALE..... Taku a kullum Oum Hairan.





*OUM HAIRAN*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login