Showing 33001 words to 36000 words out of 38364 words

Chapter 12 - RUMAH COMPLETE

26 Aug 2026

46

haka ne? Ace ɗanka ma na cikinka baka barshi ba ita kuwa meye take nema a duniya?




Shiga tayi sashinta ta zauna ko mayafinta bata cire ba kiran Hajiya Maimuna ya shigo tana ɗagawa tace “Nifa ina zargin sanya hannun Hajiyanmu a cikin lamarin nan..." “Al zanni zanbuk walau kana haƙƙun, Maimuna kul kiyayi kanki da zato ko kyakkyawa bare mummuna" cewar Fulanin Sokoto numfashi Hajiya Maimuna ta sauke tace “Abin ya tsumani ya gigitani Fulani sai nakega Fulani ƙarama a yanayin da akace tana a ciki bazata iya barin asibitin nan ba dole akwai wani abu da yake faruwa ɓoyayye kodai sanya hannun hukumar asibitin ko kuma wani isasshe" iska Fulanin Sokoto ta furzar tace “Ni kaina ya jima da kullewa na rasa abin da zance wannan lamari addu'a kawai za'ayi insha Allahu gsky zata bayyana da gaggawa" aje waya sukayi dukkansu suna jimamin lamarin.



Shikuwa Ridwan bayan kowa ya tafi yayi murmushi ya koma motarsa yaja ya nufi wani super market ya kashe musu manyan kuɗaɗe duk wani abu da yasan za'a buƙata Saida ya siyeshi sannan ya koma Dikko Layout a ɗakin ya tarar da Dr Mansura tana jorner mata wani jinin ya matsa ya karɓa yaci gaba da aikin tace “Allah ya taimake ka hukumar asibiti tanata kirana game da ɗauke petiant ɗinka" baiyi mata mgn ba har Saida ya gama abinda yake yi sannan yace.
“10 millions idan kin iya rufe wannan sirrin Mansura Koda ba komai kika sani game da gidana ba nasan kinsan matsalar dake damuna domin kece likita mafi daraja da nake gayyatowa ta duba iyalai na, kinsani banida cikakkiyar baiwa ta ajiye ƙwai a mahaifar kowacce mace hakan yasa mukayita ɓarnar kuɗi manya ba ƙananu ba duk don ganin wannan abu ya tabbata.
So abinda na fahimta ashe don anga banidashi ne akeso na samu har ana nuna anfini damuwa da rasawata yanzu dana samu kuma so ake aga bayansa da uwarsa, abu ɗaya dana sani kece kaɗai kikasan ina tare da Rumah so kici gaba da riƙewa a ranki banso wata magana ta fita daga gareki"



Fita yayi daga ɗakin ya koma cikin asalin gidan ya kashe wayoyinsa ya kwanta bashi da damuwa kamar yaƙi damuwarsa ɗaya samun lfyr amanarsa tabbas yayi alƙawarin zaiyiwa Rumah gata zai nemo mata danginta domin bai taɓa yarda Rumah shegiya bace kamar yanda kowa yake tunani, raba dare yayi yana tunanin ta inda zai fara gari yana wayewa yaje yayi mata abinda ya dace Saida ya jira Dr Mansura taje gida ta dawo sannan ya fitar daga gidan ya nufi Gidan marayun daya ɗauko Rumah.
Kai tsaye ofishin shugaban gidan ya nufa bayan sun gaisa da girmamawa yayi masa bayanin abinda ya kawo shi nan yasa aka kira masa Baba Lami ita ce ta bada bayanin abinda yakeson ji tayi ƙasa dakai cikin girmamawa tace “To Allah ya taimake ka gsky bazan iya cewa komai game da wannan yarinya ba Abu ɗaya dana sani.....


Kimanin shekaru ashirin baya da yammaci muna tsaka da ayyukan mu wasu mutane sun zo sun nemi ganawa da shugaban gidan nan bayan lokaci shugabar gidan ta aiko akayi kirana tacemin dama wata mahaukaciya ce dake zaune a kangon magajin gari ta haihu anyi duk dabarar da zaayi a karɓi jaririyar don a suturtata ta hana gashi ta hana yarinyar Nono ko ruwa kuma taƙi bari kowa ya raɓeta bare ya bata" dake mun saba samun irin wannan matsalolin take muka tafi mukayiwa Hauka Shuwa Siyayya domin sunan da mutanen unguwar suke faɗa mata kenan kasancewar ko Hausa bata iya ba sosai.
Da hikima da dabara muka samu muka karɓe jaririyar itama muka kaita asibitin mahaukata aka soma bata kulawa muna zuwa ganinta amma babu wani sauƙi daga ƙarshe hukumar asibitin tabada shawarar a nemi malamai su rinƙa yi mata addu'a domin ciwon nata yafi kama dana asiri dalilin wannan fitowa ne ta samu ta sulale ta gudu, ana gobe zata gudu ne munje ganinta da jaririyar kawai sai naga tana binkita kayan haukanta ta zaƙulo wani hoto hotonta ne da wani mutum ta miƙomin sannan da wata takarda anyi rubutu da larabci nidai bansan meye aka rubuta ba na fito nabarta tanata dariyarta tana surutunta da bana gane komai banda Malik da take faɗa cikin maganganunta.
Bayan na koma gidan marayu na kaiwa Hajiya ta karɓa tace idan Al Sheikh yazo gobe zai fassara mana meye a cikin takardar shikuma hoton ta karɓa tace za'a bincika idan Hauka Shuwa ta warke"

Washegarin ranar da muka baro gidan malam Salihu aka kira hukumar gidannan aka sanar dasu wannan mara lafiyar fa an nemeta an rasa tun cikin dare, ansha nema da gaske Allah baisa anganta ba lokacin kafafen sadarwa basu yawaita haka ba iyakar TV da radio da jarida ne haka akayita cigiyar wannan baiwar Allah da hotonta amma Allah baisa an dace ba ƙarshe dole muka zubawa sarautar Allah idanu mukaci gaba da rainon wannan yarinya sannan mukayi mata suna da Ummu-Rumanah kamar yanda muka gani rubuce cikin saƙon wannan takarda da Hauka Shuwa ta bani wannan shine iyakar abinda na sani game da Rumanah"
Jan numfashi Sarki Ridwan yayi ya dubi shugaban gidan yace “Ko zan iya ganin hoton da takardar?" Jinjina kai yayi ya miƙe yace “Bansan sanda akayi duk wannan abin da take baka labari ba amma muje record office ƙila mu samu wata wani abu cikin abubuwan da kake nema"




Sunje sun duba sun samu duk wani abu da suke nema sosai Takawa yaji daɗin wannan zuwa nashi gidan marayun ranar hatta masu gadi Saida suka san da zuwan masu garin gidan sarautar ya nufa gaisawa yake da kowa hankalinsa bayakan kowa har ya isa fada aka ɗan taɓa fadanci fada ta watse ya shiga ciki ya fara binciken wasu muhimman takardunsa ya haɗa a ƙaramar jaka ta zuwa unguwa ya kira wani baransa ya fitar masa dashi bayan yayi wanka ya shirya ya nufi sashin matan nasa.
Bai ishe Amina a part ɗin ta ba yayi murmushi ya fice ya nufi sashin Sa'ade tana zaune da waya a kunnenta tana ganinsa ta katse wayar ta miƙe tana cewa dash “An ganta ne?" Wani kallo ya watsa mata ya aje mata abinda yayi niyya ya fice.




Bai shiga part ɗin Maryam ba domin ita babu hujjar da yake nema a kanta, sashin Hajiya Tushi ya shiga tana kishingiɗe masu mata hidima suna mammatsa mata ƙafa taci uwar kwalliya kamar zata wani babban taro, wuri ya samu ya zauna yace “Barka da yini Hajiya" murmushi tayi tace “Yawwa Sarki barkanka ya gajiya" shafa ƙeyarsa yayi yace “Zan ɗan yi tafiya ne dama zuwa Abuja zan iya ɗaukar sati biyu so bansani ba ko kina buƙatar wani abu?"
Faɗaɗa fara'arta tayi tace “Aa Sarki babu abinda nake da buƙata sai yan kuɗaɗe sannan inason ka tafi da yarinyar nan..." Sai yanzu ya lura da Amina daketa yatsina tana tauna cingam ya miƙe tare da cewa “Bazan samu damar hakan ba Hajiya ta zauna anan kamar yanda kowacce cikinsu zata zauna" ficewa yayi da sauri Hajiya Tushi da Amina suka kalli juna sukayi murmushi Hajiya tace “Lallai malamin nan yana aiki sosai Kinga dai dama yace ko tunata bazai ƙara yi ba Ni so nake ma a goge masa ita daga zuciyarsa Kinga yanzu hankali ya kwanta taje ta ƙarata daga can tayi can mun rabu da baƙin iri mun huta"




Gidan daya ajiye Rumah ya koma ya tarar da ita ta farka Mansura na dubata ya isa gareta da sauri yana cewa “Masha Allah jiki ya fara yin kyau hannunta ya kama ya riƙe cikin nasa yace “Ya jikin" ajiyar zuciya tayi ta lumshe idanunta ta buɗe su akansa a hankali ta motsa bakinta ya sunkuyo daidai bakinta yace “Inane nan?" Zama yayi kusa da ita yace “Gidanki ne!" Da sauri ta dubeshi tace “Mai Martaba..." Hannu ya ɗora a bakinsa alamun tayi shiru yace “In kika warke zamuyi magana kin kuwa ga bbyn namu?" Girgiza masa kai tayi ya miƙe ya nufi inda yaron yake ya daukoshi sai baccinsa yake yaci kayan sanyi sun cikashi sosai dake bashida ƙanƙanta irin ta yawancin bakwaini.
Ɗora mata shi yayi a cinyarta ta zubawa yaron idanu zuciyarta ta karye daƙyar tayi masa addu'a hawaye ya shiga zubo mata Ridwan yasa hannu ya share yace “Please ki daina ina tare dake har abada" murmushi tayi tace “na gode da halaccin karamci amma Takawa nafison kayiwa Hajiya biyayya wlh bana burin saboda Ni da banida gatan da zan maka gata ka samu matsala da mahaifiyarka" cije leɓensa yayi ya miƙe yace “shine ƙarshen furucinki? Jinjina masa kai tayi ya kama hannunta ya durƙusa gabanta yace.




“Wanda yasan daidai shi akewa daidai Matata Hajiya ba saboda girman Allah takeson rabani dake ba batada wata hujja banda son zuciyarta Rumanah ko ubangiji bazai kamani da haƙƙin rashin yiwa Hajiya biyayya ba, kiyi duba da yanayin da kike ciki yanzu yana za'ayi tace na sakeki a wannan yanayin koda wani laifin kikayi mata bare bakici mata ba baki sha mata ba Rumanah Allah ba azzalumin Sarki bane saidai bawa ya zalumci kansa kuma ya hana zalumci tsakanin bayinsa, bancika son doguwar magana ba amma na rantse da Allah aure na dake kwanciya ɗaukar raina mutuwa ajali na shine kawai zai yanke shi saboda haka ki manta da Hajiya da yan zaginta bazata taɓa son abinda nakeso ba tun farko a haka muka faro rayuwa da ita"




Tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah shine ya hanata sake furta komai ya dubi Dr Mansura dake shigowa yace “Meye yayi saura?" Drip ɗin data sanya mata ta duba tace “Babu wata damuwa Allah ya taimake ka komai yana tafiya daidai Fulani zata samu lfy nan bada jimawa ba insha Allahu" ficewa yayi yana cewa “Akwai gajiya a jikina zanje na ɗan kwanta" fatan alkhairi Dr Mansura tayi masa ya fita ta gyarawa Rumah kwanciya itama ta sake tafiya bacci.
Sati guda dayi mata aiki ta fara samun ƙwari sosai kasancewar batada ƙan jiki yaron yaci sunan kakansa Abba Ridwan Abbas sunace masa Taufeeq Dr Mansura tarewa tayi a gidan taci gaba da kulawa da Rumah da Taufeeq shi kuma yaci gaba da fafutukarsa a ɓoye saboda surprise yakeson yima Rumah da abu mafi soyuwa a ranta.
Shi kenan baya Kano baya Abuja baya Maiduguri baya Sudan baya Chadi tsayin wata uku yana fafutuka duk ya baza hotunan Rumah a waɗannan ƙasashe harma da BBC Hausa.




Ranar wata asabar suna zaune a parlour shida Rumah suna yan wasannin su yana biye mata tana kwance bisa cinyarsa Taufeeq yana gurin Asma'u wayarsa tayi Ring ta tashi zaune ta ɗauko masa ya tambaye ”waye?" Tace “Prince Usman KN" jinjina kai yayi ta danna ta kara masa a kunnensa yayi sallama suka gaisa gaisuwar girma can ya zabura ya karɓi wayar yana cewa “Ah haba don Allah tabbas Zai iya zama hakan ka jirani ganinan, a'a Ni kaɗai ne ganinan"
Bai ko jira cewarta ba a bakin ƙofa yace mata “Naje Kano" fatan nasara tayi masa ta koma ta zauna tana tunanin meye yake yawan zuwa yi Kano a kwanakin nan ne ko yaushe sai yace yaje kano wani kishi ne ya bijiro mata data tuna matansa biyu Amina da Sa'adatu ya sakesu Gara ma Sa'adatu maybe ta dawo tunda saki ɗaya ne itako Amina dama ya taɓa sakinta yanzu ƙarƙarewa akayi.
“To ko aure yake nema?" Ta tambayi kanta tana kwantar dakai hawaye ya biyo kwarmin idanunta duk da cewa ta san dama ba darajarta bace ta kaita aurensa zuwa yanzu tasan daɗin mijinta bata fatan dalilin da zaisa yake nesa da ita.




Haka ta yini babu kuzari Saida tayi sallar la'asar sannan ta fito ta zauna a babban parlour ta kira Asma'u tazo suka zauna tana yi mata kalba a gashinta me tsayi da sulɓi ganin jikinta a sanyaye yasa Asma'u tambayarta ta kwantar da kanta jikin Asma'u tace “Asma'u Wakili yana shirin daukemin ke gashi ina tunanin Takawa aure yake nema s Kano wlh inajin tsoron kar ya kasance Nima wa'adin zamana ya ƙare"
“Bazai ƙare ba" sukaji ya faɗa Asma'u ta miƙe da sauri itama Rumah ta mike ganinsa da baƙi kallon² suka fara yiwa juna yana basu gurin zama, faɗuwar gaban da taji ce ta sanyata zubansa idanu da sigar tambaya yayi murmushi ya matsa gabanta ya kamo hannunta yace “Kin shiga mamaki ƙwaƙwalwarki ta tafi tunanin abinda bazata iya hasasowa ba ko? Rumah kalli wannan mutanen da kyau ki hasaso dawa sukeyi Miki kama?" Sosai ta kafawa namijin ingarma kyakkyawa fari tas wanda ya ɗan sanya girma idanu ta sake kallon macen da tunda suka shigo take hawaye idanunta akan Rumah tace “Takawa wannan yana kama da Taufeeq" murmushi yayi yace “Shi kuma Taufeeq dawa yake kama?" Cikin rawar murya tace “Da...dani" yayi murmushi yace “Alhmdulillah Wannan shine Abdul Malik Ubaid shine mahaifinki wannan kuma ita ce Fatima Nazar ita ce mahaifiyarki...." Tsananin farin ciki ya sanyata damƙo hannunsa tace.....


“Da...da gaske Takawa ina ka samosu?" Rumah ta faɗa tana sakin hannunsa ta matsa ga Fatima dake tsaye tana wani irin kuka me haɗe da shashsheƙa ta durƙushe ta riƙe ƙafafunta jikinta na rawa tace “Me nayi Miki kika wofintar da rayuwata a lokacin da nake buƙatarki kika sanya duniya da mutanen cikinta suke kallona a ƙasƙance Meye yasa kika zaɓi samar dani ta wannan mummunar hany...."
Rungumeta tayi tace “Aa wlh ban samar dake ta hanyar banza ba Ƴata ƙaddarar bazaki taso tare damu ba ita ta sanya duk abinda ya faru ya faru ki daina zargina da tuhumata kema ƴace cikakkiya yar Sunnah kamar kowa" janye jikinta tayi cikin kuka ta tashi ta mata jikin Malik Ubaid da yake tsaye idanunsa na tsiyayar da hawaye tana zuwa ya rungumeta yana shafa bayanta cikin kuka me taɓa zuciya yace “Nayi kewarki yake ƴata ko nace munyi kewar juna na rasa meye yasa Fatima ta manta da komai daya shafi rayuwar da tayi bayan barota daga gidana kullum ina tambayarta cikinki data fita sashi saidai tacemin ita kawar ta farka a bacci taganta babu cikin. Naji daɗin ganinki cikin ƴancin rayuwa Mamana ashe da gaske ubangiji bazai taɓar da roƙona garesa ba yana karɓa"




Ya ƙarashe maganar yana sake rungumeta ta janye ta matsa ga takawa dake tsaye cikin matsanancin tausayinsu
Kamo matarsa yayi ya zaunar da ita ya nuna musu mazauni yace "Abbu ku zauna hausawa sunce shirin zaune yafi na tsaye ashe kenan In kun zauna Fulani zatafi fahimtar ku" zama sukayi kamar yanda ya buƙata shi da kansa ya buƙaci ma'aikatan gidan da su kawo musu abin taɓawa" bayan komai ya nutsa ne Usman ya dubi Abbu yace “nasan yanzu haka Fulani ta matsu taji ya akayi haka ta faru daku kuna raye ta zamo abar tsangwama sannan abar zargi da kowa yake gudun haɗa jini d ita?"
Share zufa Abbu yayi yaja numfashi tare da gyara zama cikin hausarsa da daga ji kasan ba asalin Bahaushe bane yace.



WACECE RUMAH?



Ni Alh Abdul Malik Ubaid haifaffen ƙasar Misrah na kasance ɗa ga Mamman Maddibo Sarkin Adamawa a yanzu haka...." “What?” Sarki Ridwan ya furta tare da miƙewa tsaye dukkansu suka bishi da kallo Abbu yayi murmushi yace “kana mamaki dana kasance ƙani ga mahaifiyarka amma baku Sanni ba ko? To karkayi mamaki ka bini a sannu don na warware maka zare da abawa.
Shekaru arba'in da biyar baya tun lokacin mulkin Moddi yayiwa dansa namiji guda ɗaya tal a duniya aure ya aura masa wata bafulanar Jalingo mai suna Laure ita ce ta haifa masa yara Biyar dukkansu mata cikin hakan ne Mamman yaji yanada sha'awar tafiya karo karatu ya sanar da mahaifinsa da mahaifiyarsa sukayi masa fatan alheri ya tafi ƙasar Misra domin faɗaɗa bincikensa akan harkar Addini.
Haka ya sanarwa matarsa Laure tayi tsalle tace saidai su tafi tare daƙyar ya shawo kanta da lallami yayi dabara da cewa yaransu zasusha wahala idan basanan domin ba ƙaunarsu ƴan'uwansa sukeyi ba ƙiyayyarsu gareshi daya kasance shine zai gaji mahaifinsa domin matan Moddi biyu Kande da Maimun babu wacce ta haifi namiji Saida Lahira tazo ta haifi Mamman Maddibo sannan duk suka fara haihuwar mazan bayan Mamman ya girma.




Tafiyar Mamman ta bar baya da ƙura domin tunda ya tafi aketa kulle²n yanda za'a dawwamar dashi a Misra duk don kar yazo ya gaji mahaifinsa abinda basu sani ba shine Mamman tun yana ƙarami Moddi yasan zai shiga wannan matsalar shiyasa ya dage da shiryashi tsaf da karya tambaya ƙaiƙayi koma kan nasheƙiya shashatau saɓani dadai sauransu.
Rayuwar Mamman Maddibo a Misrah abar sha'awa domin shi ba mutum ne me kwaramniya ba gashi da basira wannan yaja masa soyayyar malamai dama ɗalubai ciki harda Kursum da ubangiji ya jarabceta da soyayyar Muhammad kasancewarta wayayya kuma shi Balaraben mutum idan yanason wani abu yakanyi duk me yiwuwa ya fahimta da abinnan ta hanyar kyautatawa da kulawa.
Da haka Mamman ya fahimci inda Kursum ta sanya gaba amma bai nuna mata ya fahimta ba yana dai binta da yanda taso.



Kwatsam wata rana suna zaune tace masa babanta yana nemansa koda yaji Saida gabansa ya faɗi amma dake jarumi ne bai bari ta gane ba yace babu komai suje suna zuwa babanta yace “Kursum tace Nigery takeson Aure munyi bakin ƙoƙari ta canza ta nemi Misry taƙi saboda haka na baka aurenta har sadakin zan biya nidai burina ka rikemin ita amana don ita ɗaya na mallaka matsayin ɗiya a duniya"
Sosai hankalin Mamman Ubaid ya tashi ganin hakan yasa Kasim abokinsa amsar masa wannan kyauta da godiya haka suka fito jiki a salube gashi lokaci bana waya ba hakanan sukaje gurin masu Landline suka kira gida Adamawa ya sanar da Moddi abinda ke faruwa maimakon yanda ya zaci Moddi zai nuna rashin amincewa sai yaji Moddi yayi hamdala yace “Inayi maka fatan alkhairi a aurenka na farko da aurenka na ƙarshe Allah ya sanyawa zuri'arka daga farko har ƙarshe albarka"
Wannan jin daɗi da Mai Martaba Moddi ya nuna yasashi jin cewa auren Kursum zai zame masa alkhairi ya karɓa washegari aka ɗaura aure baban Kursum attajiri ne shine ya basu gidan zama cikin ikon Allah shekararsu biyu da aure Kursum ta haifeni murna gurin Mamman Ubaid kamar ba'a taɓa masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login