Showing 24001 words to 27000 words out of 38364 words
Fulanin Sokoto ita kuma tana koya mata salon sace zuciyar mijinta tun tanajin kunya harta saki jikinta ga kuma Maryam da shaƙuwa kullum take ƙara shiga tsakaninsu sai ya kasance tsamarsu tsakanin Amina da Sa'adatu ne bata damuwa da isgilancin Sa'adatu tunda tasan dama itace abokiyar burminta dole kishinsu zaifi zafi amma irin ƙiyayyar da Amina ke nuna mata abin har mamaki yake bata takanyi murmushi bata biye mata duk inda suka haɗu tana basu girmansu tunda a shekaru dukkan babu sa'arta sun girme mata aunty sama Aunty ƙasa haka take kiransu duk da basa mutumta kansu.
Yau ya kama ita keda turaka tun safe take tsaye ita da Asma'u da Haulat baiwarta suna shiryawa Mai Martaba Alkubus kamar yanda yace yanaso sai magrib suka gama ta shiga wanka ta tsantsara kwalliya cikin wata dakakkiyar Shadda tayi masifar kyau abinka da kyakkyawar ta zuba ɗankunne da zubban gold daya zuba mata a lefe ta fito kenan taji ana kwankwasa ƙofa ta nufi ƙofar tana kara wayar a kunnenta Matar abokinsa Zahra ita ce ta kirata sunata dariyarsu ta buɗe ƙofar saurin kashe wayar tayi tana cewa “Zan kiraki, san...sannu Hajiya...." Raɓata Hajiya Tushi tayi ta wucce tana binta da wani mugun kallo tayi tsaki tace “ƙyalƙyal banza" ba ƙaramin ciwo kalmar tayi mata ba sunkuyar da kanta tayi tana wasa da zoben yatsanta hakanan Hajiya Tushi ta matso gareta tace “Kinzo daga baya kina neman canza min lissafin dana daɗe ina tsarawa da zuwan lokaci"
Sakin baki tayi tana kallon Hajiya Tushi ta kwance gefen lifayarta ta miƙa hannu Amina da Sa'adatu dake take mata baya suka miko mata ɗan kaskon dake hannun Sa'aden ta kwance wata leda ta watsa a cikin wutar take wani hayaki yayi tsiri sama ya nufi Rumah tabi hayakin da kallo tana karanto addu'ar neman tsari amma ina ta mskara haka hayakin yazo ya rufe ta ta kama tari tana kokawar rufe idanunta taji kamar an shafa mata wani abu a mararta take ta saki ƙara tayi ƙasa riƙe da mararta cikin fitar hayyaci.
Kallon juna sukayi sukayi murmushi Sa'ade tace “amma Hajiya babu damuwa idan muka tafi muka barta a haka?" Harara Amina ta zafga mata tace “To meye ta mutu ma mana nifa wlh na tsani yarinyar nan gabaɗaya zuciyar Takawa ta koma gareta baya kallon kowa sai wannan figaggiyar yarinyar" murmushi Hajiya Tushi tayi ta buɗe wammer ɗin ta zaro ido tace “Wow my favorite cokali tasa ta diba takai bakinta ta shige kitchen ta ɗauko kula ƙarama ta zuba Alkubus ɗin da miyar taushe ta ɗauka Sa'adatu ce tace “Haba Hajiya ai sai a gane mune muka shigo...
Tsaki taja tace “Saidai in ke zaki fada munafuka domin babu wanda yaga shigowar mu" itadai Sa'a jikinta duk sai yayi sanyi tausayin mijinta ya cika zuciyarta duk da boka yace cikin satinsa biyar itama Rumah batasan dashi ba bare shi Ridwan ɗin amma tasan tabbas idan ya fahimci abinda ya shafe shekaru goma sha biyu yana nema shine su da mahaifiyarsa suka salwantar saboda dalilin da su kansu basusan wanne ne ba haƙiƙa tana tunanin wa'adin zamansu a gidan ya ƙare.
Fita sukayi daga part ɗin daidai lokacin da Maryam ta shigo ta kofar Mai Martaba ta iso da sauri don isar da saƙon Takawa ta ishe Rumah kwance male² cikin jini a hali na fitar hayyaci aikuwa ta fasa ƙara ƙarar data janyo hankalin Takawa daya fito daga wanka ya nufo ƙofar da sauri har yana tuntuɓe idanunsa yayi tozali da Rumah cikin wannan yanayi aikuwa kamar karamin yaro ya ɗora hannu aka ya fasa ihu yana faɗin Rumasa'u waye yayi Miki haka? Shikenan maganar Mal Kurra ta tabbata dama ya faɗamin za'a sami rabo kuma za'a salwantar da rabo idan ban tsaurara tsaro ba Innanillahi wa inna ilaihirraji'un Shikenan an cuceni Rumah waye ya illataki haka wanne mara imanin ne?"
Wani malolon kishi da baƙin ciki ne ya kwaranye Maryam tace “Ciki kuma Takawa anya kuwa naka ne?" Da sauri ya dubeta duba na rashin rahama takuwa yi saurin saita bakinta tace “Aa ai wai da naga sperm ɗin ka likitoci sun tabbatar da bashida kaurin da zai yi ɗa koda yake abin ikon Allah ne" numfashi yaja ya saɓi Rumah ya shiga da ita sashin sa ya kwantar da ita a wani ɗaki daya zuba na'urori yayi bincike tsaf sannan ya buga waya asibitin gidan ya nemi taimakon nurse ɗaya tazo sukayiwa Rumah duk abinda ya dace, Maryam sai kallonsa takeyi kamar ba Ridwan me bala'in jin iko da izza ba duk ya sukurkuce akan yarinya ƙarama lallai dole ta canza salo don ta lura rakiyar so takeyi tana wahalta masa da matarsa amma hankalinsa ya kasa dawowa gareta dole ta kwace kujerar ta da take neman suɓce mata.
Bayan komai ya kammala ne ya juyo ya dubeta yace “Ta samu bacci" sai hawaye ya kawo idanunsa ya juya zai fice tayi saurin rikoshi tace “Ana asarar cikakken mutum ma a haƙura bare ɗan tayi Takawa" wuccewa yayi yana cewa “hakanne na gde"
Wajajen biyu da rabi na dare ta farka ta jita manne da jikinsa ta buɗe Idanunta a ƙirjinsa tare da karkatasu ga fuskarsa idanunsa a buɗe suke ta shafa fuskarsa tace “Takawa" fasali ya sauke ya ɗora hannunsa a saman kanta yace “Na'am Rumah!" Buɗe baki tayi zatayi magana ya rufe mata yace “Waye ya shigo part ɗinki ɗazu da yamma na ƙarshe?" Gabanta ne ya faɗi tace “Wani abu ya faru ne?" Zaune ya tashi yace “ina tambayarki kina tambayata akanme?" Ƙasa tayi da kanta abinda ya faru yana dawo mata tace “Ban iya tuna komai ba nidai nasan nayi wanka Zahra ta kirani na fito parlour ina waya daga haka bansan komai ba" jinjina kai yayi yace “ Miscarriage kikayi kuma bincike ya nuna ta ƙarfi ya fita..." Da sauri tace “Ɓari kuma ni Takawa yaushe na samu ciki?" Murmushi yayi me ciwo yace “Bansan sanda aka samar dashi ba nidai nasan akwai wani malamina a Maiduguri Mal Kurrah daya bani wani taimako ya kuma tabbatar min indai nayi yanda yace za'a dace Rumah nasani dukkan Matana babu me matsalar haihuwa daga nine shiyasa duk inda naji maganin da zai taimaka nima na samu ɗan kaina to ina tafe amma da yawan mutane suna ganin kamar ban damu ba wlh inason ganin ƙwai na kafin ƙasa ta rufe idanuna kullum lokaci tafiya yake shekaru suna ƙara nauyi"
*OUM HAIRAN*
[1/4, 10:49 AM] OUM HAIRAN: *4/1/2023 Don Allah karki karanta in baki biya ba Nrml 300 PC 600 via acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank.*
Sauke dogon numfashi tayi cike da tausayinsa tace “Insha Allahu zaka gani Takawa komai lokaci ne" “Dake?" Ya furta ƙasa tayi da idanunta tana Murmushi ya kamo hannunta yayi kissing ya shafa mararta yace “Allah ya dubemu Rumah" can ƙasa ta amsa da Amin ya kai hannu ya kashe glub ya sake mannata a jikinsa tunda tace bazata iya cin komai ba.
Bacci ne ya daukesu da asuba ya fita Masallaci ita kuma ta lallaɓa ta nufi part ɗinta tayi wanka ta canza kaya ta fito abin mamaki a buɗe ta ishe part ɗin dinning ta nufa duk kwanukan data jera gasunan amma an buɗe su da alamun anyi abinda akeso a part ɗin da sauri kuɗin da Takawa ya bata ajiya suka fado mata ta nufi dayan ɗakin da sauri ta murɗa key ɗin taja ajiyar zuciya tare da buɗe jakar ta gansu a jere taja numfashi tare da hamdala ta mayar dasu ta fito ta koma ɗakinta ta duba gwala-gwalanta suma cif suke hakan ya bata kwarin gwiwa ta fita ta batada ƙarfi saboda jinin data ɗan zubar tana kwanciya Fulanin Sokoto ta shigo a fujajan tace “Ƴata ashe haka abu ya faru babu daɗi gaskiya na girgiza to wai meye ya kawo hakan ne?" Sunkuyar da kanta tayi tana saƙa abubuwa da yawa a ranta ta yanzu ko giyar wake tasha anya tace wani abu ya faru, to me ma ya farun? Bazata iya ɗorar da komai ba bayan shigowar Hajiya Tushi.
Sosai Fulanin Sokoto ta bata shawarin kula da kai tayi godiya sukayi sallama ta fice tananan kwance Fulani Maryam ta shigo cikin shigarta ta alfarma indai batun ɗaukar wanka akeyi a gidan to indai aka sameta batu ya ƙare tayi kyau sosai, sannu da jiki tayiwa Rumah ta amsa mata yanayinta na nuna rashin amincewa da wannan shiga ta zauna kaɗan can sauran matan Amina da Sa'adatu suka shigo tana ganinsu gabanta ya faɗi Sa'adatu ce tace mata “ya jikin?" Ta amsa da “Alhmdllh" itako Amina taɓe baki tayi tace “Wai ɓari shin Sa'a wai kin yarda ɓarin ne?" Murmushi tayi tace “Burum burum ce kawai ita da uwar ɗakin yo inma haihuwar ce don asara ace duk mu da muka cika ƙa'ida ga asali ga kuɗi ga sarauta duk bamu haihu ba sai wannan gantalin gantaltalar"
Zubansu idanu tayi har suka gama zasu fita Maryam tace “Karki damu Rumah baƙin ciki ne irin na ci ayi kashi kinsan abinda ciwo ka riga mutum kwana ya rigaka tashi"
Duk wannan abin da ake yi Rumah batace komai ba saima kwanciya data gyara ta ɗaga wayar da taketa Ring tun ɗazu Asma'u ce tana karawa a kunnenta Jakadiya ta shigo tace “Allah ya taimakeki Takawa yana nemanki" aje wayar tayi ta miƙe itama Maryam ta miƙe tana ɗan karkaɗe guri tace “Je ki dawo kisha tea ki kwanta" murmushi tayi ta wucce ta shiga ta isheshi a zaune kan kujerarsa ta alfarma ya hakimce cikin shigar sarakai yana karkaɗa ƙafa fuskarsa babu alamun walwala.
Neman guri tayi ta zauna a ƙasansa ya zuba mata idanunsa dake cikin tabarau tsayin lkc sannan ta iya saita kanta tace “Allah ya taimake ka gani na amsa kira" murmushi ya saki yace “Kije ɓangaren duba petiant akwai Dr Mansura zata dubaki numfashi ta sauke tace “Babu abinda yake damuna Takawa" kafeta yayi da idanu dole ta miƙe ta nufi hanyar shiga sashin ta zauna a kujera Dr Mansura tana mata tambayoyi tana yabawa da kyawun halittar yarinyar ta gama shigar da komai sannan suka fito tare har yanzu a yanda tabarshi yake saɓanin ɗazu yanzu waya yake dannawa.
Rusunawa Dr Mansura tayi tace “Zaa kawo mata wani magani ta daure tayi amfani dashi tunda mun gano nasara ta wajen ta insha Allahu za'a dace" jinjina mata kai yayi ta fice itama Rumah ta miƙe tunda ta lura yau abin ba arziki sarautar yakeji da gaske.
Bai dakatar da ita ba har ta fice daga parlourn kasantuwar yau haushin kowa yakeji zuciyarsa batada tsarkin da zai iya yiwa wani dariya bai gama aminta Allah ne ya zama silar lalacewar ɗan tayin cikinsa ba kamar yanda Maryam ta ƙyara masa ya kamata ya sanya idanu a lamarin shige da ficen kowa a hankali zai gane me hannu a wannan shiri.
Itako Rumah tana zuwa ta tarar da Maryam ta hadanta breakfast me kyau ta ɗan tsattsakura ta koma ta kwanta zuciyarta duka babu daɗi gani take kamar ita tayi masa wani abu daya kasa yafe mata har ya yanke shawarar ɗauke mata wuta, to ita ko ya zatayi idan Ridwan ya watsar da ita tasan ta riga ta kaɗe har ganyenta, bataji shigowar Asma'u ba Saida ta kamo hannunta tace “Har yanzu kina bawa zuciyarki dama tana aikenki da nisa Rumah wai meye matsalarki yanzu bayan komai ya dawo Miki daidai mijinki na sonki yanayin tataki ya tsaya Miki akan komai to miye kuma yayi saura?"
Zaune ta tashi ta dubi Asma'u tace “Inajin tsoron wani abu Asma'u takawa yayi tatawa bani nabawa kaina wannan power ba" Nan ta kwashe komi ta zayyane mata sosai ta girgiza tace “Kince wasu mutane sun shigo kafin shigarki yanayin to su waye kuma a gidannan suke?" Ƙwallah ta ɗauke a idanunta tace “Shine abinda keta wahalar da kwanyata tun ɗazu na kasa gano su waye ne amma furucin matansa ya fara damuna Asma'u ina tsoron ranar da hƙrn zuciyata zai gaza wlh bazan iya jurewa ba sun kasa fahimtar ni nafi kowa son ace nafi kowa asali da nasabar nunawa.
Rarrashinta Asma'u ta rinƙayi har Saida taga ta dawo daidai sannan ta tambayeta meye take buƙata ta faɗa mata tuwo takeso miyar kubewa nan suka shiga kitchen suka tsara komai suka gama sukaci sannan sukaci gaba da tattaunawa sai bayan magaruba sukayi sallama Ma'u ta tafi itakuma ta kulle part ɗin ta ta shige ciki tayi shirin kwanciya ta haye gado ta ɗauki wayarta ta kunna data ta hau online sakonni suka fara shigowa bata bawa kowanne muhimmanci kamar na Zahra ba ta buɗe samples ne na magungunan mata ta buɗe voice ɗin ta tana saurara tayi murmushi tace “Zan turo Miki da kuɗin ta acct ɗinki sai ki tahomin dasu in zakuzo"
Hira sukayi sosai har Zahra na sake bata shawarar riƙe mijinta gam da muradansa ita me jiran kaɗan kullum Takawanta ne a ranta aikuwa ta sake ɗammara wajajen sha ɗaya da rabi taji alamun buɗe ƙofa tayi saurin kashe data ta kwanta luf sarai tasan buɗe kofarsa shiyasa bata wani tafi tunanin waye ba taji ya buɗe ƙofar ɗakin nata ya shigo yanda yake takawa ɗaiɗai kasan yau sarakin ne na gaske.
Hannu yakai ya kunna glub na ɗakin ya zubanta idanu tana naɗe cikin bargo idanunta ne kawai a buɗe yace “Me kikeyi a online sha ɗaya da minti talatin?"
A ɗan tsorace tace “Ni...nida Zahra ne..." A fusace ya ɗauki wayar ya sanya a aljihunsa ya juya yana takawa a hankali har yakai ƙofa yace “Kizo in Kinga dama kema..." A mugun gajiye ta miƙe ta zura hijjab ta fito ta nufi part ɗin nasa yana tsaye ya goya hannayensa rannan cuɗu² gabanta ya faɗi ta zame ta zaune a ƙasa tana shirin magana ya juyo ya zuba mata idanunsa masu sanya firgici ga mara gaskiya.
Takowa yayi ya riƙo ta miƙe ya lumshe idanunsa yana sakin ajiyar zuciya a hankali kuma yanayinsa na saituwa ya washe kamar ba shine ya zame mata abin tsoro ɗazu ba ya haɗata da jikinsa yana sakin ajiyar zuciya me ƙarfi muryarsa can ƙasa yace “Baki iya rarrashin miji ba idan kika fahimci yana cikin damuwa ko?" Sake lafewa tayi a jikinsa ta fara jan zuciya ya ɗago fuskarta yaga tana hawaye yace “Akanme zakiyimin kuka?" Cikin shagwaɓa tace “Ba kaine ba kawai Ni bansan me nayi maka ba kaketa fushi dani..." Bakinsa ya ɗora saman nata ya lasa tare da jan lips ɗinta na ƙasa ya saki tare da matseta sosai yace “Laifinki ɗaya kinƙi faɗamin su waye suka ƙwanƙwasa ƙofa kafin faruwar abinda ya faru jiya"
Fasali taja tace “ka yarda dani takawa banida wani hayyaci da zan iya gane komai nidai nasan mun gama aikin dashishinka da Alkubus nayi wanka na fito muna waya da Zahra an ƙwanƙwasa ƙofa na buɗe wallahi bayan buɗewa ta na kasa tuna komi"
Jinjina kai yayi yace “Shi kenan yanzu meye last?" Murmushi tayi tace “in kwanta a nan" ta nuna ƙirjinsa yayi dariya me sauti yace “Sai me?" “Nayi bacci nayi mafarkin na cika maka gida da bbys mata masu kama dakai" sosai tunanin nata ya bashi nishaɗi yace “Allah Princess Meye yasa bakison maza?" Rufe idanunta tayi tace “naji ana cewa mata sunfi tausayi Kamar Ni da nasamu naƙasun gata in na haifi mata zasuyimin gata"
[1/7, 8:43 PM] OUM HAIRAN: *7/1/2023 Bonus page 300 PC 600 via acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank*
Ɗan ƙaramin bakinta ya zubawa idanu yanda ta ƙarshe maganar da kwantar da kai ya tabbatar masa da zahirinta yayi fasali yace “Tunanin mutanen wannan zamanin ya tafi akan wannan falsafar taki saidai kuma hakan na faruwa ne a mafi yawan lokuta saboda rashin zurfafa tunani, Rumah mu maza Allah ya ɗora mana nauye² da yawa a kanmu mu riƙe kanmu mu riƙe matanmu mu kula da yaranmu idan mun haifa mu kula da iyayenmu idan girma yazo musu mu kula da ƙanne da ƴan'uwa dukka mu ɗaya dole walwalarmu bazata zama kamar ta mace ba ita mace tun daga haihuwar ta har mutuwarta ƙarƙashin wasu take rayuwa, na farko mahaifi na biyu miji na uku ƴaƴanta kuma kowanne yakanyi bakin ƙoƙari wajan ɗauke mata manyan buƙatunta na rayuwa ashe kenan duk abinda ta samu zai zama nata ita ɗaya sai abinda taga dama zatayi dashi? Idan har hakanne to tabbas yara maza ababen sone domin sune suke tallafar mata har su sami damar tallafar kansu da wasunsu.
Amma ni duk wanda Allah ya bani ina marhabun dashi tabbas zanyi farin ciki matuƙar farin ciki" jinjina kai tayi yakai hannunsa ya janyota suka kwanta bayan ya kashe musu fitila duk da tayi addu'a Saida ya sake musu wata sannan bacci ya ɗauke su baccinta me daɗi a kirjin Takawa nutsuwar da take samu ma daban ce.
Kwana yini haka rayuwa tayita gungurawa Rumah ta fara tsikewa da wulaƙancin Hajiya Tushi da Fulani Amina da Sa'adatu sannan rayuwar gidan sarautar me cike da ƙulle² ta fara sabuwa a gurinta da wannan ta zaɓi rayuwa a sashin Fulanin Sokoto fiye da nata ko ba komai zama da mata irin Fulanin Sokoto abin alfahari ne zaka ƙaru da abubuwa irin²
Cikin hakan ne wani yanayi ya sarketa na yawan bacci da kasala tun yanayin baya damunta har ta fara damuwa batada aiki sai bacci sai kwanciya sarai Fulanin Sokoto ta lura da yanayinta amma sai taja bakinta ta kulle cikin hakan ne watarana da yamma tana kwance a parlourn ta da lemun tsami a hannunta tana lasa kaɗan saboda tashin zuciyar da takeyi.
Turo ƙofar parlourn akayi ta ɗaga kai tanason ganin me shigowa Hajiya Tushi ce ita da Hajiya Maimuna da Hajiya Mariya yayyen Mai Martaba. Tashi tayi zaune da sauri tana mayar da murmushin da Hajiya Maimuna tayi mata tace “Lahh Yaya sannunku da zuwa" murmushi Hajiya Maimuna tayi mata tace “yawwa sannu Rumasa'u" Guri suka nema suka zauna ta yunƙura ta miƙe tace “Bari na kawo muku ruwa" bin bayanta Hajiya Mariya tayi tana Murmushi ta dawo da idanunta kan lemun tsamin tace “Lemon Kuma?" Dariya Hajiya Maimuna tayi tace “Tun karon kwanaki da mijinta yace nazo na gyara masa ita na fahimci akwai ayar tambaya akan ta