Showing 96001 words to 99000 words out of 167215 words
zuciyarsa ke alak'anta mutanan
nan da matarsane?. ranar dinner d'insuce tafad'o masa arai, tabbas aranar hankalin Aysha da meerah yatashi saboda ganin kubrah dawasu mata biyu, idanma bai mantaba meerah barin wajen tayi baki d'aya, kuma Aysha batada wata aminiya sama da meerah. Sannan wa
she garin ranar lokacin su Sameer sunje musu sallama kubrah da wata mata sunshigo yima Aysha sallama, harya basu damar shiga inda take a bedroom, kuma yashiga d'akin kiranta saboda tazo suyi sallama dasu Nawaff, saiya taddasu cirko-cirko, tabbas akwai alam
ar tambaya akan matarsa.
To amma idan yace haka kuma, miye alak'ar Momy da kubrah, sannan hajia khaltum kuma?.
''Ya salam!! yafad'a da k'arfi yana dafe kai".
Da sauri Taheer yamatso kusadashi, "j! Miyake faruwane haka?".
Kansa y
a girgizama Taheer, cikin k'unar zuciya yace, " Taheer ina zargin wasu abubuwa biyu, kuma akan mutum biyu, amma bana fatan hakan ta kasance, domin duksun shafi katanguna, ya ALLAH!".
kamashi yayi ya zaunar, yaringa kwantar masa da hankali, saida
yaga yad'an nutsu sannan ya idamasa bayanin yafice.
Gaba d'aya yau ya khaleel yakasa ta6ukama kansa komai, tunani yafaracin k'arfinsa, yanaso yakira gida yaji yajikin Momy da Aysha amma haushinsu yahanashi, kuma yayi alk'awarin inhar suka kasance
cikin abinda
yake zarginsu wlhy billahi bazai d'aga musu k'afaba, saiya hukuntasu, kuma da hannunsa zai kamasu.
Wannan alk'awarine, bazai ta6a barin mai laifi a k'ark'ashin inuwarsaba.
Idonsa yayi jajur saboda 6acinrai, zuwa can magana
r yarannan tadawo masa arai itama, lokacin dayake tambayarsu waye ya turosu, (sunce matar babansa hajia Bilkeesu) kai jama'a miyasa zuciyarsa take karkata dukkan zarginsa akan wad'anda ya yadda dasu? Mafiya kusancu agareshi kuma?, zai sakama dukkan wani da
ke gidansu ido kawai, Dan yanzu ba Aysha kad'aice abin zarginsaba, harda Momy da Anty Mamie.
🤥
____________________
Yauma dai haka Aysha tayini duk babu dad'i, komai taci kamar jira saita amayar dashi, zogalene kawai dataci ya zauna, haka 'yan
Kano suka tafi suna tausaya mata.
Bak'in 6angaren Momy ma duksun wuce, inna jummai Ce kawai tarage.
Misalin 10 Na safe baffah yashiga duba hajia babba, bayan sun gaisa da inna jummai yashiga d'akin.
Duk 'ya'yanta suna zagaye da ita,
har mufeedah dake raku6e gefe d'aya.
Ganin baffah suka fara yunk'urin fita amma saiya dakatar dasu, kujerar madubi husnah tabashi yazauna, Momy Na kwance dukta kuma janga6ewa saboda dagaske batada lafiyar, k'arfin haline kawai, da k'yarma tasha tea d
a magungunanta takwanta yanzu.
Sannu yamata cikin tausayawa, da tambayar k'arfin jikinta, tace, k'irjintane kemata ciwo yanzun, amma tasanarma doctor dasukazo yanzun shida sultan, yace zai kawo mata magani.
"To shikenan ALLAH yak'ara afuwa, sanna
n kuma ki kwantar da hankalinki, Dan kinsandai kinada hawanjini. Idankuma hankalinki ba'a kwanceba ciwon bazai barkiba".
Kanta ta jinjina masa, wasu siraran hawaye suka zirara a idonta na dama, suka gangara har cikin kunnenta, Anty shukurah ce ta gog
e mata.
Baffah ya maida kallonsa ga mufeeda, "k kuma kishirya kayanki, 6angaren Ammah zaki koma harki haihu, rashin ganinki zai sassautama mahaifiyarki rad'ad'in datakeji".
Mufeedah kuka tafashe dashi, Dan tasan inhar takoma 6angaren Ammah b
ata Isa zubar da cikinnanba, tasan jarabar Ammah da k'unatar tsiya.
Cikin daka tsawa yace, " kobak'ya jinane?".
Azabure tace, "to baffah".
Yayi tsaki yana maida kallonsa ga Momy dake yunk'urin tashi zaune, Anty zuwairah da Shukurah suka
taimaka mata tatashi.
Muryarnan ta Momy duktayi low, tace, " Alhaji kana ganin ita Ammah baza'a takurataba?, nida canayi tabi inna Jigawa kawai, idan ta haihu saita dawo, koya kagani?".
"Eto kema kinzo da shawara mai k'yau, amma abani nan
da kwana uku nagani".
Murmushin samun nasara Momy tayi, tacigaba dafad'in " to ALLAH ya kaimu, sannan sai kayanta, yakamata akwasosu aii".
"A'a baza'a kwasosuba, Dan zamu maida auren kan Nafisa d'iyar k'anen Bilkisu Hameesu, tunda ta isa au
re, dadai tasleem ko maleeka zan bashi, tokuma duk sunada manema ashe, Dan haka baza'a kwaso kayanba, mungama magana da innah za'a d'aura auren k'arshen satinnan, shukurah
keda Amatullah kuje Ku d'akko kayan sawar Mufeeda kawai, sannan karku d'akko akwatin
an lefen, kubarshi can, sadakintama za'a maidashi Na Nafisane".
Tunda baffah yafara magana Momy take zabura, haryakai k'arshe, " Alhaji ban gane wannan zancen nakaba?, daga INA kuma wannan annamimancin yafito?, asaki 'yata agida, bayan kwana biyu rak
da kaita gidan, sannan amaye gurbin gidan da jinin Bilkeesu, wlhy impossible, wannan wane irin rikitaccen tunanine?, ko ance muku idan mufeedah ta haihu bazata koma d'akinta baneba?".
Mik'ewa tsaye baffah yayi yana guntun murmushi, yace, "Laurah Bak
u Isa hanani abinda nayi niyyaba, Ammah datai sanadin kawoni duniyama ta amince, hakama d'an uwana ya amince, Ameenudden ya amince, ahakama iyayen yarinyar, banida abinda zan sakama Ameenudden dashi saboda zalincin da ballagar 'yarki tamasa, adalilin sakac
inki, babu abinda zai saka aurennan fasuwa saidai mutuwa, idanma zaku kwantar da hankalinki Ku kwantar, idan bazaku kwantarba kune awahale, narigada Na zartar da hukunci babu mai canjashi, wlhy da'ace akwai budurwar danake da ita bayansu Tasleem saina aura
masa, bazankuma aura masa Hasnah ko Husnah ba, saboda suma hankalina bai kwanta dasuba, ki kiyayeni kuma".
Yajuya zai fice abinsa.........
Cikin k'araji hajia babba tace, kayan kicin aida kud'ina nasiya, Dan haka sai an kwasomin kayana, kuma za
rgin dakama sauran 'ya'yana ban yafeba, dama cin zarafina kazoyi gaban 'ya'yana ba dubaniba, dama aii tuni nagama sanin Bilkisu ta shanyeka, kayi nisa bakajin kira, ALLAH saiya mana hisabi tsakanina daku".
Juyowa baffah yayi yana kallonta. Yasaki g
untun murmushi, kiyima kayan kichin d'in kud'i konawane zan biya, sauran maganarki kuma kisameni zan baki amsarsu, amma ba'a nanba, yanagama fad'a ya ficewarsa abinsa.
Kuka rurus momy takeyi, sai zage-zage da zabgama mufeedah ALLAH ya isa takeyi, wa
i itace taja ake cin zarafinta.
Inna jummai tashigo tana mata fad'a.
Dak'yar suka samu yayi shuru kuwa.
___________________
Har bayan isha'i ya khaleel bai dawo gidanba, Aysha Na kwance bisa doguwar kujerar ammah, lullu6e tak
e cikin bargo saboda sanyi datakeji, ga zazza6i mai zafi ajikinta, tun d'azun tunanine da damuwa suka to she kwalwar kanta, duk yau bataga ya khaleel ba, dukda tana zargin yatafi aiikine, amma yakamata yakirata yaji yajikinta, ganin bai kira d'inba takiras
hi har kusan 4times amma bai d'agaba, hawaye masu zafi suka zubo akan kumatunta, tun d'azun take kukannan, saboda lullu6a datayi da bargo har fuskarta yasa ba'a ganin.
Ammah dabatasan abinda ke faruwaba, suna zaune da inna jummai suna hirarsu irinta
zuminci, sai Tasleem da maleekah dake can gefe zaune kowacce suna chatting, inbakama saniba zaka zata suna falonba.
Sallamar ya khaleel tasakasu d'agowa suduka, amma da inna jummai suka masa sannu da zuwa, suma su Tasleem suka gaidashi.
Ya amsa awani yanayi, Ammah sai binsa da kallo takeyi, Dan taga Alamar yana tareda damuwa.
Inna jummai tamik'e tafita, waizata duba jikin Momy tadawo.
Ko kallo bata ishi ya khaleel ba, danshi bayason wanda bai sonsa, tana fitama k'amin tsaki yaj
a, ammah datajisa batace dashi komaiba, Dan tuni
take fuskantar 'Yar tsamar dake tsakanin Khaleel da kakarsa tawajen uwa, kuma k'anwar kakarsa ciki d'aya.
Zama yayi saman hannun kujerar da Aysha ke kwance, wadda tunda taji sallamarsa tashare hawayenta
.
Hannu yakai ya yaye bargon, hucin zafin zazza6in yasakashi fad'in ''ya salam, wannan zazza6in har yanzu bai saukabane Ammah?".
"Yana sauka yadawone iro, aii saidai hak'uri kuma, idan ba kwari yayiba haka za'aita fama".
" ALLAH ya k
'ara lfy, yay maganar yana lek'a face d'in Aysha data lumshe ido, saika d'auka da gaske barci takeyi, ammashi tuni yagano idonta biyu.
K'aramin hannun rigarta ya janye, babu komai a damtsen hannunta, aransa yace k'ila d'ayan hannun tane kunamar tak
e?, saikuma yace amma banta6a ganiba?".
Aysha dai batako motsaba, yamaida bargon ya lullu6eta yana mak'ewa, ammah bara nad'an watsa ruwa, shigowata kenan gidan.
".
A to yakamata aje a kimtsa, kazo ga abincinka Bilkeesu ta aiko dashi".
Kansa kawai ya iya jinjina mata yafice, Aysha tabishi da kallo asace, tabbas akwai abinda ke damun mijin nata gaskiya, to minene?".
Batada amsa, babu kuma mai bata, wannan yasakata tsuke bakinta tayi shiru. Tana binsa da addu'a a zuciyarta........
........
✍
🏿
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*
🙏🏻🙏🏻🙏🏻😭
*_Typing
📲
_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{
🔪
wuk'a bata hudashi
🗡
}_
*_Bilyn Abdul ce
🤙🏻
_*
*_HASKE WRITERS A
SSO......_*
_(Home of expert & perfect writer's)_
*_part 2_*
_(littafi na biyu
📘
)_
3
⃣
4
⃣
Bai shiga 6angaren Momy ba, kai tsaye 6angarensu yawuce, yad'an watsa ruwa sannan yadawo falo yazauna, komai
akashe yake, babu haske Afalon, yana zaune cikin duhune. Sai tunani yakeyi, yarasa yanda zai fassara abubuwan dake tunkaro rayuwarsa, kallon komai yakeyi abaibai, miyasa abubuwa suketa rikid'ar hawainiyane acikin gidansu?, muyasa baita6a kawo tunanin koma
iba dangane da wasu abubuwa sai yanzu?.
Guntun tsaki yaja, yazame ya kwanta a doguwar kujerar, hakai yayta tunane-tunane har kusan 10, ring d'in wayarsane yadawo dashi hayyacinsa, yad'auki wayar yana kallon mai kiran, baffah ne, harta katse bai d'agaba
, kamar bazai kiraba saikuma yay k'ok'arin dailing d'in number, gamo yayi da miss call d'in mimy har uku, ya furzar da huci, Dan kokad'an baiji kiranba, baikai karshen tunaninsaba kiran baffah yasake shigowa.
'Dagawa yayi, cikin ladabi yagaida baff
ah tamkar yana gabansa.
"Mu'azzama kana inane?".
''Ina gida baffah".
" kazo to ina nemanka, amma yanaji muryarka haka?".
"Babu komai baffah, barcine yad'an figeni, ganinan zuwa dai".
***********
Baffah kad'ai ya tarar zaun
e afalo yana kallom labarai a NTA, harma sunkusa gabawa, zama yayi yagaidashi.
Baffah ya amsa idonsa akansa, danya hango damuwa tartare da d'an nasa, baidai cemasa komaiba dangane da damuwar tasa, Dan yasan bazai wuce awajen aikibane.
baffah
yafara magana " dama nakirakane akan shawarar damuka yanke nidasu Ammah, saboda kafita tunda safe yau, akan maganar Ameenudden ne, da cikinsu tasleem zance yaza6a, amma sai Ammah takecemin Tasleem tana tareda k'anin Naufal ne, Maleeka kuma yaron Alhaji mus
a batsari, kuma duk takula mu'amullar tasu tayi k'arfi, wannan yasa na janye batun akansu, saida bazan bashi Hasnah ko husnah ba, saboda mahaifiyarku bazata barsu su zauna lafiyaba, akwai yarinyar Hameesu, k'anin Bilkeesu, Nafisa, tazo bikinnan, Tanama gid
annan bata tafiba, kawai mun yanke shawarar maidama Ameenu ita a madadin mufeedah."
Jin baffah yayi shiru, ya khaleel yagane yagama, zamansa yagyara shima.
"Baffah shawararku tayi dai-dai, kuma ALLAH yasanya alkairi aciki".
"To ameen, s
aikuma batun mufeeda, da nace takoma 6angaren Ammah, Dan asamu jinin ita momyn taku yasauka, tokuma saitace tafison tabi innah jigawa, idan tahaihu wai saita dawo".
" karka yarda da wannan batun baffah, kasandai halin inna jummai, wlhy dakanta za
ta 6arar dacikin jikin mufeedar".
Hakama Ammah tacemin d'azun.
"Tokagani baffah, kawaima tatattara adarennan takoma 6angaren Ammah, barama dakaina zanje".
" shikenan Mu'azzam, ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka, yajikin matar
taka?".
"Ameen baffah, jiki Alhmdllh".
" ALLAH yak'ara afuwa to, tashi kawai kaje".
Sallama ya khaleel yayma baffah yafice.
6angaren Momy yanufa. Afalo ya iske su suna hira, inna jummai Na tsakkiyarsu, Duk suka gaidashi, sama-sama
ya amsa yashige, innah jummai tarakashi da harara. dariya Anty Zuwairah tayi, tace, "nifa 'Yar tsamar innah da khaleel tana bani dariya, waimi kika masane haka innah?".
Kunyace takama innah jummai, saita fara 'yan kame-kame, tarasa abinda zata fad'a
domin Kate kanta.
Daga Momy har ya khaleel da Anty shukurah suna jiyosu daga d'aki, saidai hankalin Momy nakan khaleel, sosai taga damuwa afuskarsa.
"Ibraheem mike damunkane?".
" murmushin yak'e yayi, babu komai Momy, ciwonkune man
a keda A'eesha, waini momya bammaji kinmin maganar A'eesha ba, kobakisan batada lfy ba?, kinsamu jika Momy, amma banga kin nunamin farincikiba ko sau d'aya".
Cikin daburcewa Momy tace, "ba....bahaka baneba Ibrahim, in...I..ina farin ciki mana sosai,
Kasan tashin hankalin mufeedar nanne yadanne komai azuciyata. Amma yanzu ya jikin nata?".
" Alhmdllh, saidai tana shan wahala".
Baki hajia babba tad'an ta6e, amma khaleel bai ganiba, afili kuma tace, "ayya Allah Yakawo afuwa, dama ciki said
a hak'uri, barema cikin fari".
"Hakane Momy".
" naga kema aii jikin naki Alhmdllh".
"Uhm da sauk'i kam sosai, saidai abinda ba'a rasaba, kaji wai mi baffanku suke son k'ullawa?".
" naji, Indai akan Auren Nafisa da Ameenu ne".
"To mikace musu?".
" mizance Momy, Addu'ar fatan alkairi namusu mana, ai hakan shine dai-dai kodan halaccin da Ameenu sukamana shida iyayrnsa".
Fuska Momy tahad'e, "wai Ibraheem nikam mikakeson maida kankane?, Kaine babba acikin yara
mazan gidannan, amma kokad'an bakada wata jarumtar kwato mana 'yancinmu nida 'yan uwanka, katunafa kaikad'ai ALLAH yabani namiji".
''Hakane Momy. Amma inason kiringa fahimta abinda yazo akan turbar gaskiya. Kasan cewata wakilinku agidan nan, bashine
zaisa nayita danne gaskiyaba saboda farincikin Ku, itafa gaskiya D'ayace, daga k'inta sai 6ata, shin bakiji masu iya magana nacewa *_CIKI DA GASKIYA WUK'A BATA HUDASHI BA_*, wannanfa zancen gaskiyane wlhy, idan zaka kasance mai gaskiya abuga-abuga, dole ab
arka momy, Idan Abu yazo a turbar gaskiya yakamata kudinga kar6arsafa".
" naji shashasha, tashi ka6acemin anan, sallamamme kawai, basaikaje kaita goyon bayansunba".
Khaleel baice komaiba yatashi yafice, afalo yace INA mufeedah?.
Hasn
ah tace, "tana d'akinta ya khaleel".
Baice komaiba yashiga d'akin muferdah, tararwa yayi tana 6alle magunguna zatasha, jikinta sai rawa yakeyi bataso kowa ya ganta, shiyyasa taketa waige-waige.
Shigowarsa yasaka jikimta k'ara k'arfin rawa, tasaki
magungunan hannunta a k'asa yanayinta kawai ya tabbatar masa batada gaskiya, cikin takunsa Na jarumta yak'arasa gareta, tsugunawa yayi yad'ibi kwalayen maganin yana dubawa.
Fuskarsa amatuk'ar d'aure yad'ago manyan idanunsa da suka koma jajaye gabad'ay
a yinin yau yad'orasu akanta, (humm todama Yaya lafiyar giwa)
idon ya khaleel Na a daidaima ya'aka k'are ballantana yau dayake cikin 6acin rai, fitsari kawai mufeeda tasaki atsaye, jikake tsululululu!!
😂
.
Lafiyayyun Marika hud'u yasakar mata, cikin
daka tsawa mai firgitarwa yace, " ubanwa yabaki maganin zubar da ciki?!!! Nace ubanwaye yabakishi agidannan?!! Wlhy koki fad'amin koma 6a66allaki, dagake har cikin kutafi barzahun 'Yar iska maikama da dabba. Wlhy bak'aramin asarar kud'in Tara akayiba waje
n biya miki kud'in makaranta, mai kwakwalwar kifi kawai, bazaki fad'amin Wanda yabakibane saina miki dukan mutuwa?".
"Wlhy ya khaleel innah Ce, narantse bani nasiyaba..."
Bata rude bakiba innah jummai tafad'o d'akin, saiwani cika da batsewa t
akeyi, Dan duk