Showing 21001 words to 24000 words out of 167215 words
Amal Ku kwasa kukai wa Ammah kawai tunda komai yayi.
Kai amma kinsha kud'i Anty Mamie, ALLAH yak'ara bud'i Na alkairi, lallai ya khaleel d'an gatan Anty Mamie.
Fita Anty Mamie tayi tana murmushi batace komaiba.
.............................................
Ohni Halima, yanzunan duk bilkisunce ta had'a wad'annan kaya haka? Ya ALLAH ka albarkaci wannan yarinya da zuri'arta, ALLAH yakareta daga dukkan wani sharri itada zuri'arta.
Su Amal sunata a
msawa da ameen cikin jin dad'i.
Bayan baffah yadawo Ammah tasaka aka kaimasa kayan, dakanta taje tamasa bayani, shima yaji dad'i sosai, sai albarka yake sakama matar tasa.
Yace amma gawata shawara.
To inajinka.
Mu 6oye kayannan, akuma garg
ad'i yarannan suyi shiru dabakinsu, inason naga lefen da laura tace zata had'o itakuma, hartake masifa kar wanda yamata shishshigi.
Ah wannan shawara taka tayi d'annan, aii babu matsala, amaidasu 6angarena to.
*_Washe gari._*
Hajia babba
zaune da bataliyarta, dansu Anty zuwairah ma duk an iso, harda y'ay'anta, hakama Anty shukurah, akwatunane guda 3 agabansu, said'an kit karami, daga ganin akwatunan kasan irin wad'anda sukayi muguwar dad'ewar nance ashago ba'a samu masu siye da wuriba, Dan
harsun fara tsufa.
Shukurah tayi tagumi tareda zubawa momynsu ido da y'an uwanta, ganin yanda suketa d'aga kayan suna shewa da dariyar mugunta, gaba d'aya kayan ciki babu ko fasali, duk irin atanfofinnane leda aka zuba, saiwani shegen leshi da kalars
a kamar kagudu Dan muni kala uku, sai shadda d'aya dadai sauransu, ko'a k'auye baza'a had'a wad'annan kayanba.
Komaidai babu tsari da mutunci aciki.
Hajia babba ta ta6e baki, yo dakuke dariya badan gidannan banebama zata samu kamar wad'annan d'inn
e? Kuhad'asu akaima babanku da kakarku su gani.
Shukurah batace komaiba, amma saida tayi kuka dan bak'in ciki.
_____________,,,
Baffah yagama ganin kaya tsaf yace ALLAH ya sanya alkairi, hakama Ammah abinda tace kenan.
Su Anty
Mamie ma duk sun gani, umme amarya data kasa shiru saida tace amma alhaji ba kayannan za aikaba dai?.
To basu uwarsa tahad'aba Saudah?, suza'akai kuwa.
A'a Dan ALLAH alhaji, wlhy bai daceba, gsky acanja shawara, nidai gatamu gufunmawar nida y
aran d'akina, ayi hak'uridai babu yawa, 1.5million ne.
Aii sune masu yawan saudah, ALLAH yasaka da alkairi kinji, amma tashiga saka mata albarka itada baffah, hakama Anty Mamie tanata godiya.
Baffah yakira ya khaleel dake tsaka da aiki a o
ffice.
Bayan sun gaisa yace dasafe naga baka shigo baneba lfy dai ko?.
Wlhy lfy lau baffah, muna dawowa sallar asuhi nafita saboda akwai aikin danakeson kammalawa, yau da daddare jirgina zaitashi zuwa saudia kuma inagama sai ana jibi d'aurin aure
zan dawo, shiyyasa nake had'a ayyukan dasukad'an cushemin.
OK, tom zaka shigo gida dai ko?.
Eh insha ALLAH, yanzuma Dana gama wannan aikin zan taho.
To saikazo.
Bayan la'asar yashigo gidan, saida yashiga ya gaisa da dakowa, sanan yaje
wajen baffah, bayan sund'an tattauna akan bikin yanuna masa kayan auren, Na Anty Mamie Dana momynsa.
Baidaice komaiba gameda kayan Momy amma fuskarta tanuna alamun 6acin rai, yakumayi godiya sosai akan Na Anty Mamie da umme amarya.
Baffa
h ma baice dashi komai akan kayan momynba.
4days ago.
Bayan tafiyar mama da kwana d'aya aka kai lefen Aysha Kano.
Anmusu tarba ta mutunci da girmamawa, a 6angaren haiya babba Anty shukurah Ce kawai taje, saida sukaje Kano taga baka
yan da Momy tahad'a baneba, tayi farinciki sosai Dan dama Abin nata damunta azuciya.
Sunso ganin Aysha amma tak'i yarda, Dan bamata gidan, suna gidan Anty zainaba d'iyar kawu bilya itadasu Sadiya sauran amaren.
Aranar suka juyo da shatara
ta arzik'i, kowa yanata yaba lefen Na Aysha, suma sauran duk ankawo nasu Dama.
Abinda kecin zuciyar Aysha baiwuce ya khaleel ba, musamman intaga yanda sauran y'an uwanta keta shirye-shirye da angunansu, amma ita banda ita, indama tad'anji sauk'i d'aya
ne Taheer yakirata akan zaizo kanon gobe danyaji abinda suke buk'ata Na y'anmata shidasu Joseph.
Wannan ne yad'an rage damuwar tata
kad'an.............
✍
🏿
💋💋💋💋💋💋💋💋
❤❤❤❤❤
😍😍😍😍
[9/7, 1:21 PM] Aysha Galadima: *_Typing
📲
_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{
🔪
wuk'a bata hudashi
🗡
}_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_
*_Sadauka
rwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
*_part 2_*
(littafi na biyu
📕
)
9
⃣
Washe gari da yamma saiga Taheer da Joseph, dukda babu angon nata taji dad'i sosai, batada wasu k'awaye
dasuka wuce y'an uwanta, sai maleeka da Tasleem, komai a hannunta suka damk'a, dukda tasanar dasu babu wani Abu dasuka shirya.
Kafin tafiyar nasune ya khaleel yakira wayar Taheer, bayan sun gaisa da maganganinsu yasanarmasa suna Kano.
"Kano
kuma? Mikukajeyi a kano?".
Taheer yace, "Munje wajan amarya mana, kaibaka cemana komaiba gameda shirin biki, shiyyasa mukaga yadace muje".
"Uhmm OK, to yanzu yakukayi?".
"No babu komai, Gatama muna atare".
"Bata wayar".
Aysha dake
magana da Joseph Taheer yamik'ama waya, ta amsa batareda sanin dawa zatayi maganarba Dan sanda aka kira Taheer matsawa yayi daga wajensu.
Asanyaye tace, " Assalamu alaikum".
"Wa'alaikissalam!, muryarsa tadaki dodon kunnenta, maganarsa takat
se tunaninta"...
"Kinajina? Banason wani shirmen day day d'inan, karnaji ance kunhad'a wani events na banza da wofi, dan bana buk'ata, nabama Amatullah sak'o tabaki, tundasu ranar Friday zasu zo nan kano, ni saima ranar zan dawo dasafe".
Mu
ryar Aysha a sanyaye tace, " ALLAH yatsare hanya".
"Ameen ya amsa" yana yanke wayar.
Su Taheer sukamata sallama suka tafi.
_________________________,_
Ranar Alhamis aka sakasu Aysha a lalle, bawani taro akayiba, irin al'adar Malam ba
haushe tada akamusu, matar yayansu Qaseem ta feshesu da turare da fauda, aka rangad'a gud'a akansu, shikenan.
Sukad'an cigaba da sabgoginsu Na a are da k'awayensu.
Aranar su Ameerah suka sauka daga Canada, Aysha tayi murna sosai tamkar anyi
mata bishara, baby Raudat tayi girma sosai, yarinyar abin sha'awa wlhy, ifteehal tashige cikin k'awayen amarya anata abubuwan arzik'i, meerah kam tanataredasu Hafsat fadeeala dasu amal.
Washe gari su Anty Ama... Suka iso suma, harda Anty Mamie da Amm
ah, su inna ma y'an Jigawa sun iso.
Gidafa yayi dank'am dajama'a, abin ba'a cewa komai.
Ranar juma'a aka d'and'asama amare k'unshi, gaskiya sunsha k'yau abin har ba'a cewa komai, sunje wankin kai da yamma, sanda suka dawo gidan ko'ina bak
'ine, anata aikin gyaran kayan miya dadai sauransu.
Aysha tafad'a jikin Anty Mamie tana murnar ganinsu.
"Eyee kaga d'iyata amaryar kamshi, k'unshin yayi k'yau sosai wlhy, waye yamukune?".
"Anty Mamie wata k'awar Anty Nasara ce".
"Wacec
e Anty Nasara?".
"Matar ya Qaseem.
Kai gaskiya ta'iya sosai, kunsha k'yau kuduka".
"A'a amaryar Yaya babu magana?"..
"Hannu Aysha tasa tarufe fuskarta, kai Anty Ama....ALLAH ban gankiba, dama kinzo?".
"Wai Aysha babumu abikin babban Ya
ya aii gayya ta 6aci, kintaho da kwana biyu Na iso, randa muka kawo kaya kuma kika 6uya mana, ya hidima?".
Y'ar dariya Aysha tayi kawai batace komaiba.
Nan dai abokan wasa suka cigaba da tsokanarsu.
_____________________________
10:
23am jirginsa ya sauka Nigeria, su Adams sukaje suka d'akkosa, yana bayan mota zaune, sai amsa calls na jama'a yakeyi, musamman abokansa dasukasan da dawowar tasa.
Bayan ya cire wayar akunnensa Adams yace, "aii Oga bak'ifa suncika tab wlhy, bakaga j
ama'aba, abin ba'a cewa komai, saidai ALLAH ya kaimu gobe a d'aura aurennan lafiya kawai".
"To ameen Adams, yanzuma youseef ke sanarmin su Sameer sunkusa sauka suma, yazata bamubar airport d'inba mutsaya mutafi dasu, nacemasa mun baro".
"Ai wlh
y oga tunjiya babu abinda mukeyi sai kwaso jama'a kawai, a ciki da wajen Nigeria, aii mutum mai jama'a yamore arayuwa".
Murmushi kawai ya khaleel yayi, amma baice komaiba.
"Oga Asokoro zamuje kokuwa mai tama?".
"Adams muje mai tama tukun,
zanyi magana da baffah, kuma zand'an k'imtsa ko, saiku barni a can kukoma d'aukar su Sameer d'in, zuwa dare zan k'arasa can gidan".
"OK sir, hakan yayi aii".
'Dan gwari yabud'e musu gate suka shiga, nanma gidan akwai jama'a sosai, y'an
uwan mahaifin hajia babba sunzo sosai, hakama 6angaren mahaifiyarta Wanda sukazama dangin gidan, tunda da Ammah da mamanta uwarsu d'aya uba d'aya, danhaka sai dangin sukazama d'aya, wasukuma suna kano sai an d'aura aure gobe su k'araso abujar.
Najwa
d'iyar Anty zuwaira tazo da gudu kamar zata rungumeshi, amma saitaja birki, Dan wargima waje yaka samu, "uncle oyoyo".
Murmushi yamata tareda fad'in "dota ank'araso kenan?".
"Lah uncle yau kwananmu 6 fa a Abuja".
"Eye kunsha Abuja abinku, muj
e ciki to".
Kar6ar jakarsa tayi suka k'arasa ciki, tun afalo suka fara gaisawa da jama'a, wasu nad'an tsokanarsa da ango kasha k'amshi, amsarsa d'ayace murmishi.
Saida yashiga 6angaren Momy suka gaggaisa da jama'a sosai, itama momyn sun gaisa
a tsaitsaye saboda bak'i, yafito zuwa 6angarensu.
Duk samarin gidan sunan hardama k'arin bak'i, sunbaje afalo kowa na harkar gabansa, wasu kallo wasu gugar kayansu na kwalliyar biki, masu danna waya nayi, masu hira nayi.
Duk suka Shiga masa san
nu da zuwa da gaisheshi.
Ya amsa fusakarsa d'aukeda murmushi.
Saida yashige sannan "Hafiz yace a lallai Yaya nason aurenan, irin wannan fara'a haka".
Ramadan yace, "dagedai yajika, dawani kankan like kwakwa".
Dariya sukayi gaba d'aya.
So rayuwar families d'in tana burgeni gaskiya, komai nasu cikin mutunta juna.
Bayan kamar awanni biyu yafito, ya tambayi su Musleem Anty Mamie fa? Yaga baigantaba da sauran yaran?.
"Ya khaleel ai wad'annan sun tsufa a kano, tuda asub
a suka tafi, dagamu sai baffa da umme amaryar saikuma Momy dasu Anty zuwairah aka bari"..
Jinjina kansa yayi sannan yafita, yana nazarin hidimar bikin nasa.
Yaje sun gaisa da baffa, Wanda shima yana tareda bak'i abokansa dasukazo daga Turkey,
dakuma dad d'insu ya Naufal.
Baffa yajashi gefe suka tattauna sosai, akan d'aurin auren na gobe, dakuma walima da aka shirya bayan d'aurin aure, wadda aka gayyaci manyan malamai dazasuyi lectures awajen, sannan baffah yabashi akwati guda na d'unkun
an biki dayamasa.
Godiya sosai yayma mahaifin nasa sannan ya sallamesu yatafi inda bokansa suke.
bayan Momy takar6i kud'ad'e masu yawa a hannunsa.
Acewarta sisinta bazaiyi kuka a bikinba, shida ya yarda sai dai ayi da gumimsa.
Bai
nemi ba'asiba yamata transfer yatafi.
Yana shigowa abokansa suka saka ihun ganinsa, shima yayi farincikin ganinsu sosai, wasu andad'e ba'a had'uba, tun'a schools, harda wad'anda sukayi Secondary dakuma University, abokan aiki dakuma na kasuwa, y'
an uwa da abokan arzik'i, nanfa akashiga hirar yaushe gamo da firar abokan ango dakowa yasani.
Abdul'azeez yace, "wlhy mamaki nakeyi wai J! Da mata?".
"Aii bakai kad'aiba cewar Nawaff, kasanfa wasanmu na k'arshe a k'asar Argentina damuka
had'u nake masa maganar aure, cemin yayi babu rana".
Mahmud yace, "aii mutumin namu akwai taku, amma dai bahaka zakajema yarinyar mutane kana mazuraiba?".
Hararsa j yayi, "kai banason iskancinkufa, kai ince mazuran karingama Noor da billy, kai
kuma Nawaff saboda jarabarka dafad'a kuka fara da Yasmeen ahad'uwar farko, su mai mata uku Abdul'azeez (Dady) kam aiba'a magana".
Harara Dady ya wullah masa, "kai Malam yanzu matata d'aya my Munnerah kaji".
Dariya suka shek'e da ita, Sultan yace
, "wlhy auren mata biyu da dad'i, Juwairiyya takula dani, itada ikram d'ina haka, uncle G dake gefe yace kai malam my sopy ma ba bayaba, auredai dacene kawai". Mus'aff yace, "wannan gaskiyane, idan INA gaban My Nazeefa tamkar kwai a cokali nake". "Muzzaffa
r ya kar6e dafad'in wlhy haka Ameedah na take, tauraruwata kenan".
Isma'il yace, "kukefad'a anaji, aii soyayya sai Iman d'ita wlhy". hummm kowa nasa yasani, kuje gidana kuga yanda Rahma ke riritani Cewar Abdulmaleek bobo. Umar Fharuk yashek'e da da
riya, "amma sanda aka aura maka ita kanata wani dojewa kai na Ni'ima, hakanayi a lokacin aurena da Asma'u, amma yanzu kam babu kamarta". "kana nufin har Uwargida Lubna?".
"Daga baya kenan malam".
Shureim ya shek'e da dariya, "aiini nida my
badar sai mutuwa".
Khaleel da sauran abokan daketa binsu da kallo suka shek'e da dariya, "to iyayen soyayya, sannunku da k'ok'ari".
"Yauwa Wanda bai iya soyayyaba, kaima aii zaka shiga layinmune, daga gobenefa".
Sameer yace, "ALLAH ka
sadamu da matan kwarai, bilyn Abdull nimafa yakamata labarina yashigo layi gaskiya".
😂👍🏻
.
Babu damu Sameer, kaine next insha ALLAH
😂😉🤝🏻
.
Haka sukaita shafta d'insu, ranardai k'alilanne acikinsu sukayi barci, washe gari tunda 7:30 suka d'auki
hanyar kano a motoci.
Sun Isa lafiya, yayinda suka sauka a hotel, annan suka cigaba da shagalinsu har zuwa 12, daganan akafara shirin tafiya d'aurin aure.
Gidansu Aysha.
Cike gidan yake, da k'yar nake kutsawa cikin mutane, har Na isa inda su Ay
sha suke, a d'akin abbansu marigayi, y'anmatan da amare sunata kwalliya dacin gayu, amma banda Aysha, kwance take kangado tanata kallonsu, dukda d'unbin son datakema ya khaleel sai jikinta yay sanyi k'alau yau, tun
d'azun takeson tayi kuka takasa, sunata r
k'onta tatashi tayi wanka amma tak'i k'oda motsawa daga inda take kwance, hak'ura sukayi suka barta.
*_RANA BATA K'ARYA...._*
K'ofar gidansu Aysha dank'am yake da al'ummar annabi, kasancewar d'aurin aure biyar za'ayi, y'ay'an kawu bilyamin biy
u. Sai Rufaida da Sadiya, sai Aysha.
Dole kasancewata mace natsaya daga gefe har liman yafara sanar da d'aurin auren Rufaida, kasancewar itace babba, sai Aysha, etc...., gaba d'ayansu sadakinsu dubu 30 30 ne kacal.
Ana gama d'aurin aure police
Interpol da ainahin police, da sauran masu d'ammara daban-daban dasuka halarci d'aurin Auren, suka d'ana kunamun bindugunsu atare, kamar yanda suka shirya aka saki harbi lokaci d'aya, gabad'aya wajen ya hargitse, saboda abin yazoma jama'a babu zato,
🤣🤣
z
okaga gudu wajan jama'a
🏃
♀
🏃
♀
🏃
♀
🏃🏻
♂
🏃🏻
♂
🏃🏻
♂
🏃🏻
♂
🏃🏻
♂
🏃🏻
♂
🏃🏻
♂
🏃🏻
♂, Dan harbinne na bindingu kusan 50+, kuttt idan bakayi bani guru, k'afa minaci banbakiba.
Kanawafa sunzata bomb ne zai tarwatse dasu
🤣🤣🤣🤣🤣😆😆
.
Aradu harsu
baffah sun tsorata
😂
.
Saida kowa yafuskanci wasan manyane domin girmama Ango sannan aka koma cin dariya