Showing 117001 words to 120000 words out of 167215 words

Chapter 40 - CIKI DA GASKIYA complete

khaleel zaisan mahaifiyarsa ta asali agidannan, lokaci yayi baffah zaisan komai, 6oye-6oye yak'are, dama burinmu bai wuce khaleel yakama Hajia laurah dumu-dumu da laifiba, to Alhmdllh, dakon shekaru 37 dakikayi kina rik'e wann

an sirrin yakamata ayau ki fesar dashi kowa yasani, kodan khaleel yasan kansa shima, yakuma samu farin ciki irinna kowanne d'a aduniya.

Kowa afalon kallonsa yadawo kan mama, dake k'ok'arin kwantar da Ammah, "a'a fad'ima barni azaune, aini abinda

kefaruwama yahanani jin zafin yanzun".

Kai jama'a, dakyarfa Ammah ke magana wlhy, amma bakinta yak'i mutuwa

πŸ˜‚

.



Mik'ewa Mama tayi tana takawa ahankali cikin falon, gaban Anty Mamie taje tatsaya, ta had'e hannayenta waje d'aya alamar rok'o, B

ilkeesu ki gafarceni, kikuma fahimceni, batajira amsartaba takoma gaban baffah, kaima kamin gafara Alhaji, kakuma fahimceni, banida za6i sainayin hakan, shima bata jira cewarsaba takoma inda khaleel yake uwa butun butumi, hannunsa takamo tarik'e, idonsa ak

anta, itama kallonsa takeyi, kayi hak'uri yarona, nayi hakane saboda nema maka kariya, idan bahakan nayiba nasan kasheka zasuyi, shiyyasa naza6i rik'e maganar araina har takawo yanzun, amma ban bartaba saida Na tabbatar kana zagaye daduk wani kulawata, had

'eda kwakwkwaran bincike domin tabbatar da gaskiya yanda kowa zai fahimceni aranar dazan bankad'a komai".

Ya khaleel bai iya cemata komaiba, saidai kwayoyin razanannun idanunsa masu kamada Na jan gauta daya zuba mata, badamuba taja da baya gaban Mom

y da hajia khaltum da'aka gurfanar ak'asa, bayan Taheer duk yasaka musu handcuff ahannu.

Kukuma inason Ku maida tunaninku baya, shekaru 37 zuwa baya dasuka wuce".

Harara hajia khaltum tazubama mama, momy kam rok'on mama tafarayi, please

fad'ima kibar zancennan, narok'eki, zan biyaki konawa kike buk'ata, bank'i kowanne sirrina yafitoba amma banda wannan sirrin......

Baki isaba laurah, bakida kud'in dazaki biyani, ko a baya ba tsoronkine yasakani shiruba, bakuma biyana kukayiba, nayi

hakane saboda yak'inin Ibrahim zai kwato mana 'yancinmu agurinki wata rana, Dan nasan ubangiji bazai ta6a barin azzalumi nasaraba, nasan CIKI DA GASKIYA, wuk'a bata hudashi.

*_WANI LOKACI MAI NISAN ZANGO

😒

_*



Bayan aurena da Alhaji

Abdallah rashin zaman lafiyarmune nida laurah yasakashi auro Bilkisu, dukda kasancewar Bilkeesu k'arama acikinmu hakan bai canja komaiba, saima dad'a hargitsewa da komai yayi.

Cikina yazube har karo biyu dukmun d'auka tsautsayine, hankalina bai fara k

arkata akan hajia laurah ba sai lokacin dasuka haihu tareda

Bilkeesu, ALLAH ya jarabcesu da nak'uda rana d'aya, amma laurah tariga Bilkisu.

Kuma tarigatama haihuwa, saidai k'in fad'a mana abinda laura ta haifa k'awarta khaltum tayi gatanan da rant

a, har saida Bilkisu ta haihu.

Kafin afad'a mana abinda Bilkeesu ta haifa doctor yabuk'aci kayan haihuwa, da ruwa dawasu magunguna daza'a sakama Bilkeesu.

Ammah idan baki mantaba, kekad'ai muka bari, Alhaji yatafi d'aukar kaya damuka manto, nikum

a natafi pharmacy d'in cikin asibitin, rabon inzo inga abinda ke faruwa Na yarda 'Yar takardar da doctor yabani, dawo nayi ina dubawa har k'ofar d'akin, ammah tarigada tajuyama d'akin baya shiyyasa bazata san mike faruwaba, naduk'a Na d'auki 'Yar takardar

dana gani, d'ogowar dazanyi sainaga doctor shida wata nurse da khaltum sunfito da baby daga d'akin da Bilkisu ta haihu, suka shiga d'akin da laura take, da sauri Na afka d'akin, babu baby gaban Bilkeesu, itakuma tanata barcima, ina niyyar fita na fad'ama

Ammah saiga nurse d'innan tadawo da da babyn ta kwantar gaban Bilkisu, jinayi hankalina bai kwantaba, amma nakasa cewa komai, gudun karyazam zargi nayi.

Fita nayi ina sak'e-sak'e harna Sayo maganin nadawo, natarar Alhaji yadawo, yana rungume da jariri

ya yana hawaye.

Tambayarsa nayi miya faru?, shine ya sashaidamin babyn Bilkisu batazo daraiba, hajia laurah kuma tahaifi namiji.

Tun anan nasan tabbas zargina gaskiyane, su laurah sun canja yaranne.

Amma bance komaiba har muka dawo gida, yar

o yak'i shan nonon laurah, daga k'arshema da'aka matsa sai nononta yakoma fidda yellow ruwa maimakon milk, anyi-anyi kuma tak'i yarda Bilkisu ta shayar dashi, ga jariri nata azabar kuka.

Saida Ammah Tamata tatas sannan tayarda, Bilkisu sarkin hak'uri

kuma tayarda zata shayar dashi, dukda rashin k'auna da laurah ke nuna mana, ana bashi nonon Bilkisu yakar6a kuwa.

Alokacinne naje hard'aki nama hajia laurah magana, nakuma fad'a mata subama Bilkisu d'anta kokuma Na fallasasu, ga laurah nan da ranta,

itada khaltum sukaimin barazana da mutuwa, kuma sukace inhar maganar tafito wlhy saisun kashe jaririn da ita kanta Bilkisu, acewarta ita bata haifi namijiba wata shegiya acikinmu bazata haifaba.

Ba tsoron kurarinsu najiba, tausayin Bilkisu naji, daku

ma kashe jariri dasukace zasuyi, danhaka nayi shiru inata addu'a daneman mafitar yanda zan ku6tar da jariri Ibraheem wanda yaci sunan mahaifin Bilkeesu, (yamata alk'awarin idan ta haihu namiji zai sakama yaron sunan mahaifinta), dakuma aka samu akasin haka

tunda basusan miya faruba, sai yacanja zai saka sunan mahaifin laurah, ni naita rok'onsa da lallashi har ya amince yasaka sunan mahaifin Bilkeesu kamar yanda yay niyya, Na nuna masa hakan zai ragema Bilkisu rad'ad'in rashin tata jaririyar, bamuwani kai ru

wa ranaba ya amince, aikam ansha rashin hankali aranar, tamkar za'a k'ona gidanan, Dan saida laurah ta hargitsa kowa, Alhaji kuma yaburgeni yace babu canji.

Ban fasa gayama ubangiji ba wajen Neman mafitar hanyar maidama Bilkisu d'anta, amma saiwat

a k'addara ta giftamin alokacin, nayi 6arin cikina, a sibiti kuma sukace magani nasha, dama shinake sha duk lokacin da cikina yazube, sun rufamin asirine kawai, kuma Alhaji yasamu maganin zuwabar daciki ad'akina, da wannan damar hajia laurah tace nice nayi

yunk'urin zubda cikin Bilkisu abaya kuma, Alhaji Abdallah yanason yara, batareda binciken komaiba yasakeni alokacin.

Abu d'ayane yasakani bak'inciki da sakin nan shine sanin laurah ce ta k'ullamin, ga wulak'aci da Alhaji yamin lokacin saboda 6acin

rai dayake ciki.

Natafi ina tausayin Bilkisu, dannasan zatasha wahala agidannan.

Tunda nakoma Kano aketamin barazana da rayuwa, kuma nasan laurah ce ta sanya, Dan akwai lokacin da'aka saceni, aka 6oyeni kusan wata 1, hankalin iyayena yatashi s

osai, har aka sanya malamai addu'a sosai lokacin, ciki harda tsohon mijina Malam Abubakar.

Cikin ikon ALLAH nasamu ku6ta kuwa, munje yima Malam Abubakar godiya nida yayata ananne yaganni, yakumace yanaso.

Babu wani 6ata lokaci akasha biki, bad

an inasonsaba, amma kyawawan halayensa yasaka cikin kwanaki kad'an ya mantar dani Alhaji Abdallah, dukda har lokacin ban hak'uraba wajen son ku6tar da khaleel da mahaifiyarsa.



Mafita d'aya nasamu lokacin itace bintu, k'anwar mijina, dukda kow

a yasan bintu jarababbiyace, nima tana nunamin halinta, sannan kuma tagogu da zaman bariki, ahankali naja bintu ajikina, wajen k'yautata mata, saida naga tasaki jiki sosai dani sannan nafad'a mata buk'atata nason zuwa tanemi aiki agidannan.

Babu musu

ta amince, saboda itadama 'yarson hutuce, babu wanda yasan mike tsakanina da bintu saboda Na nuna mata karta wani nuna hakan, saboda aikin sirrine tsakanina da ita.

Bintu batadawo gidannanba saida aka haifi Amatullah, nikuma har sannan ban haihuba a

gidan Malam Abubakar.

Bintu tacigaba damin aiki, wajen kallon kowanne shigi da fici agidannan, batareda sanin kowaba, duk sun d'auketa amatsayin 'Yar raino.

Tafiya tayi tafiya bintu tazomin da labarin hajia laurah tashiga wata k'ungiya, k

uma khaltum ce tasakata, itama la6ewa tayi taji hirarsu wata rana. Sannan k'ungiyar tanada had'ari, safarar yara mata sukeyi zuwa wasu k'asashen duniya, ana sakasu karuwanci.

Wannan labari yata6a zuciyata, nasan laurah zatayi abinda yafima haka, sab

oda tanada son kud'in tsiya.

Ancigaba da shurawa khaleel nata girma dawayo, lokacin yanada k'anne, Dan Bilkeesu ta haifi Rufa'i sultan mujahedeen, Amatullah, Ramadan, abinda yabani mamaki da laurah batayi yunk'urin kashe wad'annan yaranba, kokuma s

acesu, wani tunanine yazomin, nafahimci laurah tabar khaleel ne danya zame mata wata Katanga nan gaba, tunda shine namiji babba.

Ganin hakan ne yasakani amfani datawa basirar domin yin wasa da hankalin laurah nima.

Bayan haihuwar Zunnurain

da Mufeedah nasamo Saudah, k'awa ga k'anwata, Lokacin saudah tafara aiki, dan lauyace mai zaman kanta, narok'eta arzik'i akan ta auri Alhaji Abdallah, tunda dama tasanshi, yayanta abokinsane, , dafarko tak'i amincewa, saida Na zauna Na warware mata komai

akan abinda ke faruwa, Na burin laurah dason tarwatsa gidan Alhaji Abdallah, dukda zai har sannan bansan kwakwkwaran dalilin laurah ba Na aikata hakan kaitsaye.

Jin haka Saudah ta amince, akasha biki kuwa, kundai gane wanake nufi (Ummie Amarya

πŸ˜‚

)....

..........

✍

🏿

✍

Kaina yafara ciwo, amin afuwa muhad'u tomorrow insha ALLAH, danjin aikin mama, (Maman aysha

πŸ˜‰

)

🀸🏻

‍♀

🀸🏻

‍♀

🀸🏻

‍♀

🀸🏻

‍♀

🀸🏻

‍♀

🀸🏻

‍♀

Ayya my sweet Dota Aneeluv ALLAH yabaki lafiya, fans kuma Aneesa A rimi addu'a batada lafi

ya wlhy sosai, kuhad'o da kayan dubiyafa

🀸🏻

‍♀

🀸🏻

‍♀

🀸🏻

‍♀

🀸🏻

‍♀

🀸🏻

‍♀

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

*_Typing

πŸ“²

_*



🀰🏻

*_CIKI DA GASKIYA!!......._*

_{

πŸ”ͺ

wuk'a bata hudashi

πŸ—‘

}_





*_Bilyn Abdul ce

πŸ€™πŸ»

_*

*_HASKE WRITERS

ASSO......_*

_(Home of experts & perfect writer's)_

*_part 2_*

_(littafi na biyu

πŸ“˜

)_

_gaisuwa agareku dafatan Alkairi, Ummu Ameer (comment naki Na k'ayatar dani) Maman Uswan (Ngd da k'yauna), fadeelah Ummu Amal (nagode kwarai

da gaske da ziyarar daki kawomin hargida, ina alfahari dake), miss Maryam maintain (sak'onki ya iso gareni, thanks dear) mom of 12 (comment naki Na kasheni dear), Zarah maigari (keta dabance araina), Leemat (ngd sosai dear, ALLAH k'ara miki haske akan na

ki rubutun), Maman Aysha (ina k'aunarki sosai), fati tage (bilyn Abdul Na alfahari dake sosai wlhy) , Nana yakaku (comment naki nasakani Nishad'i da k'aunarki), Esha qadeer (ina k'aunarki wlhy), alkairin ALLAH yakaimuku aduk inda kuke, bilyn Abdul nayinku

wlhy._

Kuna dayawa wlhy, amma insha ALLAH ahankali zakuga sunayenku

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

❀❀❀❀❀❀❀

πŸ’˜πŸ€ΈπŸ»

‍♀.

4

⃣

0

⃣

"Mama da saninki kenan aka kaini karuwanci?".

Gaba d'aya falon kowa juyowa yayi yana kallonta, Aysha ce tsaye aba

kin k'ofa, sai Khausar dake rik'e da ita, doctor Abraham kuma yana bayansu, kallo d'aya zaka mata tabaka tausayi, saboda rama datayi, sai uban haske da tsayi, idanu jajur saboda wahala.

Aleeya Ce tak'arasa garesu da sauri takama hannun Aysha, sam

an kujera takawota ta zaunar.

Doctor Abraham kuma yak'araso inda Ammah take, domin bata taimakon gaggawa.

Da k'yar tayarda aka mata allurar rage rad'ad'i, dantace babu mai mata allurar barci yahanata jin *Sabon al'amaree*, saida baffa dasu tahee

r sukaita lalla6ata sannan.

Ya khaleel kam nazaune tamkar wani hoto, shidai binsu kawai yakeyi da rinannun idanunsa, amma ko motsin kirki bayayi.

Dukda Aysha taji tundaga farkon labarin hakan baihanata tsare mama da kallon tuhumaba, tarasa yadd

a zata fassara abubuwan.

Ummi amarya tad'ora dafad'in........

............Hakane Aysha, dasaninmu kikaje islands UK, ammafa bada nufin turaki karuwanciba.

Bayan shigowata gidannan nacigaba dabin diddik'in hajia laura batareda sanin

taba, saidai bangane komaiba saboda k'arfin rik'e sirrin k'ungiyarsu dasukeyi, babu wata kafa dasuka bari dawani zai samu shiga al'amuransu.

Nayi iyayina nagaji.

Saida Na zauna nayi dogon nazari sannan nagane yakamata ace munsami yarinyar daz

ataje anufin hajarsu, tawannan hanyarne kawai zamu ringa samun bayanan sirri.

Nasamu Yaya fad'ima da bintu dawannan batun.

Tashin farko bintu tace musamo yarinya daga k'auye.

Yaya fad'ima tace a'a, bazai yuwu mu tsare 'ya'yanmuba mu tozar

ta nawasu, inhar bazamu iya saka 'ya'yanmu awannan had'arinba, to babu d'an dazamu saka aciki, mudaije musake nazari.

Mun amince da maganarta kam.

Kafin muyi zama Na biyu Alhaji yasakani binsa Saudia yin Umrah, Dan lokacin inacikin hutun aik

i Na k'arshen shrkarah.

A Wannan tafiyace ALLAH yahad'ani dawata matashiyar budurwa, masaukinta Na kusada namu, saiyazam kullum tare muke zuwa massalaci. Abinda nalura dashi ga wanan budurwa shine yawan kuka datakeyi dafad'in ALLAH ya canja mata

rayuwarta, Dan ba'a son ranta takeyiba.

Banta6a tambayartaba, sai ana jibi zamukomo gida, nadai kasa hak'uri Na tambayeta, dafarko tayi kamar bazata fad'aminba, saida naita lallashinta sannan takwashe labarinta kaf tasanarmin.

Na tausayama yariny

ar sosai, har hawaye nazubar mata, sannan kuma nayi farincikin jin tanada alak'a da k'ungiya mai tambarin

πŸ¦‚

.

Bayan dawowarmu saudiya muka iske tashin hankalin rasuwar Rufa'i, lokacin kwana d'aya tak, rasuwarnan ta girgiza Yaya Bilkisu da khaleel ain

un, hakama dukkan jama'ar gidanan.

Babu dad'ewa kuma sai mijin Yaya fad'ima ma yarasu.

Bayan lafawar wad'annan rasuwa mai ta6a zukata nasake dawoma Yaya fad'ima da zancen baya, harma da labarin matashiyar budurwa nan damuka had'u a saudia.



Lokacin kwanakin mijinta 5 kacal da rasuwa, gaisuwama naje mata.

Atake anan Yaya fad'ima tacemin muyi amfani da Aysha d'iyarta kawai.

Wannan magana bak'aramin razanani tayiba, nacema Yaya fad'ima hakan bazai yuwuba, yaza'ayi musaka rayuwar Aysh

a ahad'ari, tunda bamuda tabbas akan zata iya baro wajennan ba'a 6ata rayuwartaba.

Bud'ar bakin Yaya fad'ima saitace hakane, kuma tayarda da zancena, amma ita bazata saka rayuwar d'an kowa ahad'ariba, itakuma nata 'ya'yan a killace, ta sadaukar da Ays

ha danta ceto rayuwar yara masu d'unbin yawa daga gararin rayuwa, inhar rayuwar Aysha ta lalace awajennan tad'auki hakan amatsayin k'addara, amma tana rok'on ALLAH yama tsare mata ita, kodan darajar maraicinta dakuma sadaukarwa datayi amatsayinta Na uwa ag

areta.

Hummm Na jinjinama k'ok'rin Yaya fad'ima awannan lokacin, Dan masu irin zuciyarta k'alilanne aduniya, bakowane keda irin wannan k'yak'yk'yawar zuciyarba, kuma duk akan kishiya, wadda mutane dayawa suke d'auka amatsayin abin k'yama, (wlhy haka

n datayi yakuma sakama zuciyata salama akan wani Abu waishi kishin banza, tabbas kishin taimakon juna shine kishi, ba kishin hauka Na wannan zamaninba), awannan lokacin naji araina ina addu'ar son dawowar Yaya fad'ima d'akinta Na asali.

Haka nadawo

Abuja cikeda al'ajabin jarumtar mace irin Yaya fad'ima.



Kwanakina biyu da dawowa kacal saiga bintu d'ukeda Aysha kuwa.

Aysha bata sanniba, saboda duk sanda zanje gidansu saida nik'af nake zuwa, ko Ummah abokiyar zaman Yaya fad'ima bazat

a ta6a shaida fuskataba bare yaran gidan, bama koyaushe nake zuwa gidanba, saidai Yaya fad'ima tafito muhad'u awani waje.

Hummm wani al'amarin ubangiji hajia laurah naganin Aysha kuwa saita tanka, dama nasan dawuya hakan bata faruba, saboda Aysh

a tanada k'yau da tsarin halitta irinta mata, dukda alokacin yarinyace ita k'arama.

Wannan tankawa datayi kuwa bintu ta sallama mata bisa yanda muka tsara.

Hajia laurah suka d'auki mak'udan kud'i suka bama bintu, duk Na kar6ar Aysha.

D

ukda yarinyar tana bani tausayi, amma haka muka kauda kai nida bintu aka tafi da ita, da taimakon wata mai dillacin yara muka samu akabama kubrah Aysha kamar yanda muka tsara, ita kuma waccan mai dillacin ba 'Yar k'ungiyar baceba, suna amfani da itane bata

reda tasaniba, saisu sakata samo yara daga k'auye amatsayin za'a sakasu aikatau, data basu shikenan sai'a rarrabasu k'asashen duniya batareda sanin iyayenauba da ita kanta wannan mata.

Alhmdllh Aysha taje islands UK, inda matashiyar budurwar

nan take, kuma ana kaita ta ganeta, Dan nasanar mata komai akanta ta waya.

Hummm kuyi hak'uri, bakowa baceba budurwa nan face meerah!!...



Arazane Aysha tamik'e cikin dafe k'irji, tace, "Ummu amarya kina nufin Anty meerah ta?."



"Yes

lil sholyna haka zancen yake".

Meerah tafad'a daga k'ofar part d'in Ummu amarya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login