Showing 42001 words to 45000 words out of 167215 words

Chapter 15 - CIKI DA GASKIYA complete

/>
Tsorone yafara kamani danjin kamar takun mutane, hhhh yaukam tak'arema bilynku, karfa su kwamishine su zata Ayshan ce

😿

.

Addu'a nafara da fatan ALLAH ya fiddo ya kha

leel nikam

😩

.



_______________________________

Su gwaska suka gama zagaye gidan, kowa yatsaya inda yadace, suna hasashen yanda za'ayi sushiga ainahin cikin gidan.

Ya khaleel kam yanacan rungume da Aysha daketa kukan da muryartama bata f

ita, wani irin tausayinta da k'aunarta Na ratsa dukkan wata ga6a da magudanar jini ta jikinsa, yana godiya ga ALLAH daya masa k'yautar samun mace tagari, wadda tarik'e mutuncinta, takuma kawoshi inda yadace, sosai kukanta ke sukar zuciyarsa, amma yakasa ha

nata, Dan shima bashida wani k'arfi, ga wani zazza6i dake Neman rufesa.

Dukda ba lokacin sanyi baneba, amma rawar sanyi yakeyi, yanaso yaja bargo yarufesu amma yakasa hakan, kuma matse Aysha yayi ajikinsa daboda taimako da d'umin jikinta ke bas

hi.

Aysha tafara tsagaitawa da kukan datakeyi, saboda jin ya khaleel na rawar sanyi, gawata matsa dayamata ko numfashin kirki batayi, dukda d'akin akwai duhu hakan bai hanata bud'e idanuntaba da k'yar, dansun mata jingim saboda kukan data 6arza, bata

ganinsa sosai, d'akin babu fitila dukya kashe, sai hasken fitulun waje dana farin wata dasukad'an hasko glass d'in windows d'in.

Tana k'ok'arin mik'a hannu ta kunna fitilar gefen gadon kuma aka d'auke wutarma gaba d'aya, yarage asken farin watane

kawai.



Hakan yayma su gwaska dad'i sosai, zasu gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali kenan.

Dukda tayi bala'in wahaltuwa hakan baihanata son tashi danta taimaki ya khaleel d'inba, rawar sanyi yakeyi sosai, har hakwaransa Na had'uwa waje d

'aya.

Kuma matseta yayi, Dan bayason tabar jikinsa.

Muryarta a dakushe cikin wahaltuwar tace, "ya khaleel kabari natashi, ko fitila Na kunna".

" karkibar jikina A'eesha, sanyi nakeji, kedai lullu6emu". 'Yaya maganar cikin dauriya'.

Bata iya cewa komaiba, Dan itama bawai lafiyar garetaba, da k'yar ta yunk'ura tajawo jargon takuma kullu6esu da k'yau.

Kamar wasa ya khaleel ya rikice mata sosai, ga jikinsa yayi masifar zafi, sai rawar sanyi kuma yakeyi, ita kanta kamar

zazza6in keson kamata, ga azabar zugi da k'asanta keyi, gakuma ya khaleel yahanata koda motsin kirki yamanneta tsam da jikinsa, sai hawayen wahala da tausayin ya khaleel d'in takeyi, tarasa yazatayi.

Kamar wasa tafara jiyo motsin takun mutum ta ba

yan windows d'insu, tad'aga ido da k'yar saita hango inuwar mutum.

Wata irin fad'uwar gaba tasameta, itama sai jikin NATA yafara rawa, ahankali cikin rad'a tace, "ya khaleel kalla mutum jikin window d'inmu".

Baijitaba saboda muryarta a dasa

she take, bata fita da k'yau, takuma matsar da bakinta saitin kunnesa tafad'a masa.

Dukda halin dayake ciki bai hanashi d'ago kai cikin hanzariba ya kalli window d'in shima, shiru yayi yana nazarin inuwar mutum d'in.

Aysha zata k'ara magana y

ay saurin rufe bakinta alamar tayi shiru.

Shirin kuwa tayi, saidai Duk tsoro ya dabaibayeta.

Dak'yar ya iya mik'a hannu yad'auki wayarsa dake gefen gadon, komai yanayinsane cikin dabara da taka tsantsan, Yakuma Jan bargon ya lullu6esu

sosai sannan yakira number Adams.

Atak'aice yamasa bayani yakashe wayar.

Itadai Aysha dukta Shiga damuwa, gani takeyi kafin su Adams d'in suzoma mutanene sunyi yanda zasuyi dasu.



Su gwaska kam nacan suna nazarin yanda zasu Shiga gidan,

d'aya daga cikinsu yana gwada wani d'an k'arfe a k'ofar falonsu kozai bud'e, cikin ikon ALLAH kuwa k'arfen yabud'e k'ofar falon su Aysha.

Dad'ine yacikashi, ya dunk'ule hannu yana fad'in yeees!.

Jin haka Wanda ke a kusadashi yamatso yana tamb

ayarsa tabud'e?, yace Masa eh tabud'e.

Zagayawa yayi domin sanar dasu gwaska, shikuma d'ayan yashiga cikin falon.



Hankalin Aysha yayi masifar tashi, Dan batasan dami mutanene sukazoba, amma amamakinta saitaga ya khaleel ta Kans

a kawai yakeyi bawai damuwa da mutanenba, Dan haryanzu yana manne da jikinta, data yunk'ura danta tashi zaice please karki barni, sanyi nakeji, Abu goma da ashirin inji Aysha.

Motsi sukafaraji alamun ana ta6a k'ofar d'akin, amma anjita GAM a kulle

, sunata k'ok'arin sakab. k'arfennan dansu bud'e amma sun kasa, saboda key d'in yana ajiki ya khaleel bai zareba.

A tsorace Aysha tace, "ya khaleel zasu shigofa, Dan ALLAH katashi, wlhy k'ila kashemu zasuyi".

Tabashi tausayi, amma bashid

a k'arfin tunkarar kowa awannan yanayin dayake ciki, shikad'ai yasan halin dayake ciki, baita6a tsintar kansa acikin wannan halin ciwonba tunda yay wayo, yasandai yana ciwo, tunda yasha kwanciyama a asibiti, amma baita6a jin mai azaba irin wannanba, gabad'

aya ga6o6in jikinsa kwankwatsa sukeyi, ga bala'in sanyin dayakeji.

Ahankali yace, "ki kwantar da hankalinki gasu Adams nan zuwa, bazasu iya bud'e k'ofarnanba saboda akwai key aciki, kibar kuka".

''Ya khaleel idan suka 6allafa?".

Shi

ru yayi yakasa bata amsa, ana cikin haka sukajiyo alamar ana dukan Abu, ya khaleel ya sauke ajiyar zuciya, Dan yasan su Adams sun iso, magana suke jiyowa sama-sama.

Su Adams ne suke dakama su gwaska tsawa, bayan sun tattaresu waje d'aya, katafila ne

zaimusu gaddama Samuel ya dakesa, shine su Aysha sukajiyo.

Su Samuel suka tasa k'eyar su gwaska zuwa waje, mamaki yakama Adams ina ogan nasu yashiga haka? Har wawayennan suka shigarmasa gida?, gashi yaji maganarsa kamar a mawuyacin hali d'azun da

ya kirasa, tomeke faruwane?. wayarsa yad'auka yakirashi.

Ya khaleel yad'auka murya a dakushe yace, " Adams kunzone?".

"Ye sir, harma mun kamasu, amma kana inane?".

Da k'yar yace, " inan ad'aki kwance banida lfy, kuje dasu kawai, saida

safe idan naga yanda natashi zan shigo".

"Oga kodai akira doctor k muje asibiti?, nake ganin baikamata kazauna cikin ciwoba".

" karka damu kuje, da safe zan kira Dr Abraham".

Badan Adams yasoba yace, "to shikenan Oga, ALLAH yak'ara afuwa".

"Ameen". ya khaleel ya amsa yana yanke wayar.

_______________________________

Haka suka kwana suduka babu mai isashshiyar lfy, duk agalabaice suka wayi gari, da k'yar ya khaleel ya iya raba jikinsa dana Aysha dake barci a wahalce

itama, yana layi ahanya ya Isa toilet d'in, cikin dauriya yahad'a ruwa maid'an zafi yayi wanka tareda wankan tsarki, wani ruwan yakuma had'awa sannan yafito, yad'anji k'arfi ajikinsa, amma haryanzu zazza6in yana nan, kuma yanajin sanyi sosai, jallabiya ya

saka da rigar sanyi mai kauri, ya dogara yay sallar Asubahi a d'akin, Dan bazai iya fita konan da tsakar gidaba.

Bakin gadon ya zauna yana cije la66a, idonsa nakan k'yak'yawan face d'in Aysha dake barci, dagani batajin dad'in barcin, yasan dukda wa

halarnan dayake aciki tafisa, Dan bak'aramin wahalar da ita yayiba, kasa control d'in kansa yayima shi gabad'aya wlhy.

Ya lumshe idanunsa dake jajur sannan yabud'e akan Aysha, hannu yakai ya yaye bargon, Aysha tabud'e ido, kallo d'aya tamasa tamaida

ta rufe saboda kunya.

Huci ya furzo a bakinsa, yad'an huro hancinsa alamun baya jin dad'in jikinsa, yace, "zaki iya tashine A'eesha?".

Shiru Aysha tayi masa, amma tad'aga kanta.

"Daure to kitashi kiyi wanka, kar lokacin sallah

yashige", dagaji kasan a wahalce yake maganar.

Cikin zubda kwallah tace, " to kabani hijjab d'in nasaka".

Hijjab d'in yatashi da k'yar ya d'akko akan sofa, yamik'a mata, tana a kwancen tasaka, ta yink'ura zata tashi, amma azabar zafin dataj

i yasakata fad'in ya sallamm!!.

Tausayi tabashi, dukda jikinsa babu k'arfi haka yad'auketa cak yanufi bayin da ita, Aysha kasa bud'e ido tayi ta kallesa, ya direta, karki cutar da kanki, kishiga ruwan zafi sosai, zakiji sauk'in zafin kafin doctor

yazo.

Kanta ta iya gyad'a masa kawai, amma takasa amasawa da baki.

Fitowa yayi, yacire bargon saman gadon, sannan ya cire bedsheets d'in gaba d'aya, ya nannad'eshi waje d'aya ya ajiye, wani bedsheets d'in yad'ako ya shimfid'a, batareda tsayaw

a wani gyarawaba ya haye yakwanta, ya k'udundune cikin bargo.

Aysha kam tanacan tashiga ruwan zafi, jin zafi yaratsata tamik'e zaram, kuma d'ibar ruwan sanyi tayi ta surka ruwan, zafin ya salamce, ahaka tashiga, shima batawani dad'eba tafita tay

i wankan tsarki.

Fitowa tayi tana tafiya kamar wata y'ar kac.....

🤭

.

Saboda bata gasa jikin da k'yauba.

Ganinsa kwance yasakata ficewa daga d'akin, tanufi d'akinta, a can ta sauya kaya sannan tayi sallah a daddafe takoma kan gado ta kwan

ta.

Ya khaleel yanajin fitar Aysha, tun yana sauraren dawowarta harya fidda rai, yanda tafito daga bayin dawuri ya tabbatar masa batawani tsaya Gasa jikinta da k'yauba, yasan zata sha wahalane, saboda jikinta zai k'ara tsami, amma bashida wan

i k'arfin taimakonta.

Waya ya d'auka yakira doctor Abraham, dukda likitansune ta fannin aiki ya yarda dashi, duk wata Matsala ta ciwo Indai zata taso masa shi yake nema.

Babu dad'ewa kuwa saiga Dr Abraham d'in, ashema Adams ya Sanar masa yazo

tunda Asubahi, Dan haka ya khaleel yay mamakin zuwan nasa da wuri.

Kwatancen d'akin yamasa yashigo, ya khaleel Na kwance suka gaisa, yace, "ashema kana kusa Na kiraka?".

" yes sir!, dama Adams ya sanarmin tun d'azun, nad'an dakatane gari

Yakuma haske nazo, INA kan hanyar zuwama kakirani".

Ya khaleel ya jinjina kai yana lumshe idanu.

Bai 6oyema Dr Abraham ba, yasanar masa abinda yakawo ciwon.

Sorry sir, inaga ka Tara sha'awane shiyyasa, kadad'e kana buk'atar mace

amma Baka d'auki wani matakiba akai, shiyyasa yau daka fidda (S) Ya haddasa maka da zazza6i da jin sanyi, sometimes irin hakan yana faruwa, idan mutum yakai age d'in buk'atar mace amma baiyi hakanba, sai (s) yarink'a taruwa amararsa, yakan haddasa masa ya

wan mantuwa, 6acin rai, ciwonkai, so duk randa yasamu damar fitarwar saikaga kuma ciwo mai tsanani ya sameshi, kamardai yanda katsinci kanka aciki, please Oga akiyaye gaskiya, Dan hakan had'arine ga lafiyar Dan adam".

Jin Nina kai ya khaleel yayi

yana fad'in "OK doctor insha ALLAH".

Allura yamasa, sannan yabashi magunguna.

Ya khaleel yace, "itama yakamata kad'an bata magani, dannanga kamar zazza6inne ajikinta".

"OK sir! Amma ita NATA ba damuwa baneba sosai, gajiyace darash

in sabo, tasha wannan maganin insha ALLAH zatajita normal".

"Amma yakamata kusha koda tea ne yanzu kafin kusha maganin, musamman kai da akama allura, Dan tanada k'arfi".

"Babu damuwa doctor, ngd sosai".

Sallama Dr Abraham yayi masa yata

fi.



Tunani yafarayi akan waya kamata yakira danya taimaka masa akan Aysha, yakamata yasamu mai tsayawa akanta danta Gasa jikinta, Inda Anty zuwairah mutuniyar kirkice ai saiya kirasa, tunda dai y'ar uwarsace, kuma yayarsa, yaja guntun

tsaki, garama yakira anty shukrah ko Amatullah.

Amatullah k'anwarsace, bara kawai yakira Anty shukurah d'in, tunda yaga ita halinta ya banbanta da su Anty zuwairah.

Harya fara nemanta saikuma yadakata, wani tunanine yazo masa, kodai yakira

Ammah, Dan ita kakarsuce, akwai d'an k'arancin jin nauyinta tartare dasu, yanda zai iya fad'a mata damuwarsa itada Anty Mamie ko momy bazai iya fad'awaba.

Gaskiya kuma yanajin kunyar Anty Mamie matuk'a, Anty shukurah d'inma saiyaji kamar da kunya, ga

radai Ammah, dukda itama yanajin kunyar tata Amman dad'an sauk'i akan sauran.

Wayar Ammah yakira, bugu d'aya kuwa ta d'auka.

"Iro! Injidai lfy?".

Bayason iro d'inan, amma babu yanda zaiyi da Ammah, murya a tausashe yace please Ammah kid'anzo

mana".

''Kaini kamin magana da yaren dazan gane, miye wani falis koma uwarmi kace?".

Dukda halin dayake ciki saida ya murmusa, aransa yace, " Ammah jaraba kenan, afili kuma yace, "to yi hak'uri, kizo bamuda lfy muduka".



Subahanalilahi, to ganin zuwa, aidama inada shirin lek'oku yau, amma dakam sai anjima, to amma ganina yanzu.

To saikinzo.

___________________________

Hhhhhh

🤣

, momy dai har Around 7am bata farkaba, tanata kwasar barci, babu Wanda y

atada ita, su azatonsuma tatshi tayi sallar Asubahi takoma barcinne, basusan hajia momy ko motsima batayiba

😆

.

(Aikin amma yayi k'yau

😂👍🏻

).

__________________________

Har barci yafara figar ya khaleel yajiyo Ammah Na kwad'a sallama daga

falo, bai iya amsa mataba, Dan bashida k'arfin hakan.

Jiyota yayi tana fad'in "yoni halima ina kuke y'ay'annan?, yad'an murmusa yana gyara kwanciyarsa, can saiya jiyo ta turo k'ofar d'akinsa, talek'o kanta, saida ta hangoshi sannan ta ida shigowa,

"o, kajimin d'an nema, iro dama kanajina inata kwad'a sallama amma kamin banza?".

Yi hak'uri Ammah, banida k'arfin amsa mikine".

''Wayyo, to sannu, ina ita Aysha d'in?, tun d'azun tafita, inaga tana d'akinta kwance".

''To ALLAH ya sauwa

k'a", tad'auki maganin tana dubawa, kaikace tasan mi'aka rubuta, cikin tsokana ya khaleel yace, " Ammah kina karantawane?".

Ta ta6e baki, "yoni iro minasani a wannan shirmen?, to wayazo yabaku magani kuma? Kotun jiyane ciwon?".

" A'a Ammah, y

anzu doctor yatafi, yamin allura, yacene nasha tea da Sauri saboda allurar tanada k'arfi, ita kuma tasha wannan maganin".

''To bara na had'a maka shayin, amma ni halima nata6a ganin ciwo da salo, kakama mata kakama miji, iro wai miyema yasamekune hak

a?".

Yawu ya khaleel yahad'iye da k'yar, yad'an sosai saman girarsa yana fad'in "um, um, Ammah kedai dakin bani tea d'in k'awai, kingafa rawar sanyi nakeyi, ga zazza6i mai zafi ajikina.

Tofa, ninaga wannan aiki, wai kishiya tara rana d'aya

, tafice tana tsogumi akan momy, kai laure ko y'ar banzar yarinya, dasotayi tasaka yara cikin tsaka mai wuya, kullum tahana yaro samun ladan aure, aikinga danayi maganin tsagerancinta yanema ma kansa mafita, shima da munafiki yana min mazurai bayason auren

, to yanzu ubanwa ya aikeshi gunta hardasu ciwo, mtsoww yaran zamani aii akwai iyayi da firfirta, yo inba firfirtaba miye nakirana wai basuda lfy?.

Koda dayake daya fad'ama tsagerar uwarsa d'incan aii gwamma nid'in, Dan nasandai Bilkisu bazai iyaba, b

are waccan shema'un da bata shiga sabgar kowa (umme amarya

🤣

).

Tana had'a shayi akicin d'insu take wannan tsogunguman nata, (nace kai Ammah ikon ALLAH

😀

).

__________

Dakanta tabashi tea d'in, danta lura da gaske bashida lfyar, dauri

yace kawai da jarumta irin tasa, saida ya shanye tas sannan yanuna mata yanda zata bashi maganin yasha, tace, "to kwanta kahuta, itama Ayshan bara naje kanta, ALLAH yak'ara afuwa".

Cikin gyad'a kai yace, " Ameen ammah".

Bargon ta gyara masa, t

a lullu6eshi da k'yar sannan tafice.

Barci mai nauyi ya figesa, tunaninsa nakan Aysha, duk tausayinta yacika zuciyarsa, shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login