Showing 24001 words to 27000 words out of 167215 words
datuna gudun da'akasha
🤣🤣🤣
.
Canna hango muku xoxo da buje a hannu, mom of 12 kam filet d'in shinkafa tasaki ak'asa, su Aysha Umar anac
an mamuke da Manshat data kusan sakin Zunnurain a k'asa.
Hadiza muktar harda fitsari a kayan ankonta, tab danbakuga halinda Maman Khaleed da Zarah maigari sukashigaba da kdeey
😂
, jamila zozo da mamybmj ana can bayan durom, kuttt kunga nasiba a bokit
in ruwan datti kuwa,
🤣
, Uwargida can Na hangota tasaka kai a drom d'in ruwa, y'an group d'in cikin da gaskiya kam ba'a magana, duk zumud'in tafiya bikin ya khaleel da ankon dasukeyi baihanasu kwasa agujeba, wasu takalma ahannu wasu d'ankwali, harda masu z
ani a hannu
🤣
, kuttmelesi kunga y'an taskar littafan Hausa kuwa, tashin hankali
😌🤣🤣🤣
, wasu harsunkai k'arshen layi, anasu dawo ga kaji suna fad'in sun yafe wlhy
🤣🤣🤣
, radu sunga mutuwa yau babu kwad'ayi.
Falfala kenan wai Malam bud'e mana litta
fi, yaukam naga gudun gayu aradu, abin ba'a cewa komai, Na hauwa'un Janu yafi nakowa, idan nafad'a saikun toshe kunnuwa
🤣
, su d'an mom kuwa tuni aka baza babbar riga aka ranta cikin Na kare,.
Hakama abokan Ango su Nawaff dabasusan da shirinba kowa
yanemi ma6oya
🤣🤣🤣
.
Abin yabirge ya khaleel, Dan baisan da wannan shirinba, aikam saigashi yana tuntsura uwar dariya
😆
, ya khaleel an iya dariyar mugunta
😏
.
Damma baiga mata acikin gida baneba, dayayi wadda tafi wannan
😜
.
Fans d'in ciki
da gaskiya wlhy kun iya gudu zazuuuuuu
🤣🤣🤣🤣👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻
kenan.
Lokacin da zance yashigo cikin gida and'aura aure sai Aysha ta rushe da kuka, Dan sai yanzu tasamu damar yin kukan datakesonyi tun d'azun.
Nanfa dangi suka rufu akanta dasonj
in ba'asi, kasa cewa komai tayi tacigaba da kukanta, (dolene duk macen da akace and'aura aurenta saitaji wani iri tareda ita
😥
, bawai Aysha kawaiba).
Ganin tak'i yin shiru ifteehal takira Anty meerah.
Babu dad'ewa tashigo d'akin, ita ta lallashi
ayshar har tasakata tayi wanka, dak'yar tayarda aka mata simple makeup, tasaka doguwar rigar farar shadda kamar yanda sauran y'an uwanta suka saka.
Bayan d'aurin aure aka zauna yin saukar alkur'ani, domin nemawa amare tabarraki, bayan ankammala sauka
ne su Anty Mamie suka shirya tafiya, Dan tarbar amaryarsu gobe idan ALLAH ya kaimu.
Sai lokacin nagano muku ya khaleel dayaci kwalliya cikin farar shadda d'inkin babbar riga, Wanda yasha adon golden d'in surfani, hular kansa golden, hakama agogo da taka
lmansa sau ciki, fuskarnan washar da annurin angwaci, said baza kamshi yakeyi, Dan kusan kwalbar turare Taheer ya zazzage masa ajiki Dan shak'iyanci.
😂
kwarjininsa da sihirtaccen k'yawu sunk'ara fitowa, babudai dariya, amma anama jama'a murmushi
😊
.
Yanata gaisawa da abokansa, dakuma manyansa a wajen aiki dasuka halarci d'aurin auren.
Saida komai yanatsa sannan suka tafi wajen waleemar da aka shirya, manyan malami sunyi lectures mai ratsa jiki, anci ansha kam alhmdllh.
Bayan antas
hi baffah da gayayyarsa suka tafi, su ya khaleel kam sai washe gari zasu tafi da amarya Aysha.
Dan haka da daddare suka shirya d'an biki a hotel d'in dasuke iyasu kad'ai abinsu, wajen ya k'ayatar sosai, sunyi nishad'i Alhamdllh.
Adaren akakai su R
ufaida, Aysha duk saida taje gidan kowa batareda ansan tabi y'ankai amarya ba
😀
.
Bayan dawowarsu kam mama takirata, itama dangi suka sakata tsakkiya anata mata nasiha, tasha kuka kam, ranar tareda mama takwana.
Washe gari...........
✍
*_k
owa ya shirya, yau sai abuja
😜
_*
🚗🚕🚙🚌🚎🚘🚓🚔🚖
😍😍😍😍😍😍😍😍😍
[9/8, 1:56 PM] Aysha Galadima: *_Typing
📲
_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{
🔪
wuk'a bata hudashi
🗡
}_
*_Bilyn Abdull ce
🤙🏻
_*
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home of experts and perfect writers~_
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
🤲🏻😭
*_part 2_*
(littafi na biyu
📕
)
1
⃣
0
⃣
Jama'a sunata shirye-shiryen tafiya Abuja, domin rakkiya ga Aysha.
Itakam tanacan k'uryar d'aki sai zuba kuka takeyi, gabad'a tausayin kanta takeyi, tasan tana son ya khaleel, amma shi takula baidamu da itaba ko kad'an, jib
afa tunda aka d'aura aurennan bataga idanunsaba, ahaka za'ayi rayuwar aure kenan?.
Hayaniyar jama tafara jiyowa suna fad'in mitocin d'aukar amarya sunzo, gabantane yacigaba da fad'uwa, kukanta yak'aru, har rawa jikinta keyi saboda tashin hankali.
Ahaka gwaggo Asma'u tashigo ta sameta, "haba Aysha, kekuwa bazaki daina kukannan bane hakanan? Kowafa dahaka yafara, yanzu y'an uwanki basun kwana gidan nasu mazajen ba, kinsandai tafiya babu fashi aii, kikamaje wata k'asar kikayi hak'uri zama babu mu
bare nan gaki ga Yaya fad'ima, kinga tashi ki saka wannan hijjab d'in da nik'af kinji, yihak'uri bar kukan hakanan?".
Haka taita lallashin Aysha harta kuma sakata ta k'imtsa, ankai Aysha tayi sallama da dangin mahaifinta tsofaffi maza da mata, aka kai
ta wajen Umma wadda takasa magana sai kuka itama, dak'yar aka 6an6are Aysha daga jikin Ummah, mama ankaita tayi sallama da ita, (ita sai zuwa jibi zata koma abujan).
Haka akafita da Aysha tana 6arzar kuka, sanye take cikin atanfa ruwan zuma mai duhu
da ratsin ruwan shanshanbale mai haske, hijjab d'intama ruwan Zuma, sai bak'in nik'af, tana kallon kowa tacikin nik'af d'inta, dukda har yanzun tanata kwarar da hawaye kuwa.
Gabanta yafad'i lokacinda idonta ya sauna akan ya khaleel dake jingine da
wata farar mota, rabonda taganshi harta mantama ita, sanye yake cikin shadda galila ruwan sararin samaniya, (sky blue) ya murza hula kalarta, hakama takalmansa, agogonsane kawai bak'i, yayi masifar yin
k'yau, mayun idonsa k'yam akan Aysha da fuskarta ke li
llu6e da Nik'af, dukda baya ganin fuskartata hakan baihanashi cigaba da kallontaba, baka Isa gane wane yanayi yake cikiba.
Gwaggo Asma'u tace, "wainikam ko wancanne angon? Naga yakafe d'iyar tawa da idanu?".
Dariya meerah tayi, tace, "gwaggo shi
ne kuwa wlhy".
Kai masha ALLAH, "ALLAH yabada zaman lfy dai".
"Ameen ya rabbi gwaggo".
Duk Aysha najinsu.
Zungurinsa Sameer yayi, da sauri yamaido kallonsa ga Sameer d'in, yad'an sauke siririyar ajiyar zuciya.
Sameer ya
ce, " haba alhaji, gidankafa zataje, irin wannan kallo haka?".
Baki ya khaleel yad'an ta6e, "kai nifa karkamin Sheri, ba kallonta nakeba, kawai tunanin yatafi wani wajene daban".
"Hhhh j!, J! Ikon ALLAH, Na Aysha bada kanka asare kajegida ka
ce yafad'i, d'ad'ina dakai komai naka akwai tsari, kana tunanin shan angwancine kenan?".
"Hhmm wlhy Sameer kaima ka canja, yakamata Papa yamaka aure gaskiya".
Dariya Sameer yasaka, hakan yayi dai-dai da isowar Joseph wajen, j! Zaka shiga motar
amaryane? Kozaka tafi daban?.
"Haba saikace wani kai, mubaha akeyiba, bakagama da y'an uwanta suka shigaba?".
"Aii nazata zaka zauna agabane?".
"A'a".
Tom saiku tafi kaida su Sameer ko?.
"Nifa karka had'ani da wad'annan, kasa
n zasu takuramin da surunsune wlhy".
Dariya sukayi, Sameer yace, ''aikam zamu barka a kano wlhy".
___________
Kowa yagama shiga, motocin sun wadata alhamdllh, y'an anguwa anata d'agama amarya Aysha hannu, wadda tacusa kanta akan cinyoy
inta tana kuka.
To Aysha ALLAH yabada sa'ar zaman aure.
Kunsan miya faru?.
Harmun fara tafiya saiga gayyar motocin y'an CIKI DA GASKIYA...FANS, group 1,2,3,4, wai daga baya zasu tsaya kada abokan ya khaleel suk'ara irin najiya
🤣🤣
.
Ammafa antara matsota
😂
.
*_Abuja_*
Sun Isa Abuja 2:pm dai-dai, saboda babu laifi sund'anyi gudu, kasancewar harabar gidan akwai mutane motocin suka tsaya ak'ofar gida, ta amaryace kawai tashiga cikin gida.
Anty Mamie dakanta tazo tafid
do Aysha, Wanda ganin Anty Mamie yasakata kuma rushewa da kuka, lalashinta tashigayi.
Anma bak'i tarbar mutunci, amma hajia babba da Anty zuwairah ko lek'owa basuyiba, Anty shikurah komai itakam tana aciki, ankai amarya Aysha d'akin Anty Mamie, kaf
in da daddare amaidata 6angarenta.
Daga ita sai ifteehal a d'akin, saikuma wasu y'an uwansu su uku, zee da Saleema da Mimi. Hirarsu sukeyi cikin nutsuwa, amma Aysha batacewa uffan, tana kwance kangado tana saurarensu dabinsu da ido.
Amal
takawo musu abinci.
Sukad'ai sukaci, amma Aysha ko saukama tak'iyi daga gadon Anty Mamie.
Gayyar ciki da gaskiya fans kuwa aii dole aka bud'e musu d'aki guda agidan, dukda hakama yamusu kad'an, sundaiyi manege ne kawai, Dan kowa yasan hidimar biki
yanda take, Baka Neman komai kasamu yanda kakeso.
Haka akaciga da y'an hidimomi har zuwa 8 Na dare.
Kowa yafara shirin dinner da abokan ango suka shirya, wadda shima baisan da itaba saida suka dawo daga Kano, babu yanda zaiyi tunda sunriga sungama
komai, amma baiso hakanba gsky.
_________________
Amarya Aysha ansha kwalliya, Hamdiyya tamata danta iya sosai, tasaka popul d'in doguwar riga, aka nad'a mata farin ashoke, tayi k'yau harta gaji, kowa fad'i yakeyi masha ALLAH, itakam gabanta s
ai fad'uwa yakeyi, tana tunani had'uwarta da ya khaleel, tunda tasan dolene amota d'aya zasu tafi.
Isowar Anty shikurah ce ta katse tunaninta, ''Aysha tashi muje Yaya Na jiranki".
Cikin marairaicewar murya Aysha tace, "wlhy Anty Ama kamar
ma afasa".
Dariya Anty Ama tayi, " kiyi hak'uri kinji Aysha, shima ya khaleel d'in bada son ransa baneba, abokansa Na wajen aikine suka shirya batareda saninsaba, kinga kuma babu damar yace bazakujeba yasakasu asara". Kinga tashi muje karsuyita jira.
Dole Aysha tamik'e, Anty Ama tarik'e hannunta, saima yanzu talura duk mutane sungama tafiya, gidan yayi shiru, Dan harsu hajia babba duk anacan
😂
.
Anty Ama tabud'ema Aysha motar dake gabansu, zuciyar Aysha sai harbawa takeyi, ahaka tarum
tse idanu tashiga tana karanta addu'a aranta.
Kamshin turarensane yadaki hancinta, ta sauke numfashi da k'yar tareda had'iyar yawu.
Lafewa tayi ajikin murfin motar bayan Anty Ama tarufesu.
Ema...dake gaba zaya tuk'asu yace, "antynmu barka
da dare".
Yanda hausar tasa take gura-gura yaso bama Aysha dariya, amma saita dake tad'an murmusa tareda amsawa, takula ya khaleel ya yarda ta tuk'in EMA gaskiya, indai bashi zai tuk'a kansaba to zakaga Emanuel ne driver d'insa.
Ta gefen ido tasa
ci kallon boss d'in, Wanda yayi tsit tamkar babushi a motar ma, sanye yake da popul d'in shadda irin ruwan kayan jikinta, d'inkin babbar Riga, sai farar hula akansa, yanata zabga k'amshi. Muryarta can k'asan mak'oshi tace, "ina yini?".
Idanunsa dak
e a lumshe yabud'e ahankali, ya saukesu akanta, kwalliyar Tamata k'yau yafad'a aransa.
Jin bai amsa mataba yasaka Aysha d'ago idanunta masu yalwar gashi ta sauke akansa, azatonta baijitabama.
Da sauri ta janye idanunta saboda kallon ido cikin id
o dasukaima juna, wani kwarjini Na musamman yak'ara mata, kanta tamaida taduk'ar tana kallon zanen material d'in jikinta.
Babu wanda yasake cewa komai har suka Isa wajen dinner d'in.
Abokan ango suka fito domin yimusu rakkiya, sunfara tafiya Tah
eer ya gwargwad'a masa wani Abu a kunne.
Saida ya hararesa sannan.
Taheer yamatsa baya yana dariya.
Batareda Aysha tayi zatoba taji yarik'o hannunta ya rumtse anashi, atare sukaji shock, ya khaleel ya sauke sassanyar ajiyar zuciya, yayinda
Aysha taji wata kasala tadaban, wadda ta k'ara haddasama tafiyarta sanyi ainun.
Wajen atsare kuma cikeda jama'a, suna shigowa aka saki tafi, su Ammah ana gaba-gaba itada inna da baba jummai Maman hajia babba, Ammah sai baza hakwara takeyi Dan da
d'i
😁
.
Saida Aysha ta zauna sannan shima yazauna kusada ita, Dan kujera d'aya aka ajiye musu, amma basu matsuba saboda tanada d'an fad'i.
Anfara gudanar da abinda yatara mutane batareda bata lokaciba, ayshadai tayi tsit tamkar ruwa ya ciny
eta, tamkar ance tad'ago idonta yasauka akan Anty kubrah da glory, bak'aramin tashin hankali Aysha tashigaba, takai dubanta kan Anty meerah wadda tahango itama hankalin nata atashe yake.
Innalillahi kawai Aysha take ambata azuciyarta, tsabar rikic
ewar datayi batasan ta d'ora hannunta kanna ya khaleel ba, jin tana Neman jimasa ciwo a bayan hannu yasashi juya hannunta yasak'ala nasa aciki, yatsunsu suka sark'e cikin najuna, tamatse kammm kuwa batareda tasan mitake aikatawaba, kallonsa yamaida directi
on d'in datake kallo saiyaga momynsace awajen da wasu mata biyu da kubra, yamaido kallonsa ga Aysha da idanunta ke zubar da siraran hawaye.
Matso da bakinsa yayi saitin kunnanta, batareda tayi zaton maganar tashiba taji saukarta cikin kunnenta.
Bashiri tadawo cikin hankalinta, tafara k'ok'arin zame hannunta, bai hanataba yasaki hannun nata, tareda mik'a mata hanky d'insa alamar tagoge hawayenta.
K'ar6a tayi, tanamai satar kallonsa, Yakuma maimaita tambayar tasa.
Suwanene su?.
Ga
ban Aysha Yakuma tsananta bugawa, muryarta Na rawa tace, "suwaye?".
Kafeta yayi da idanunsa, tayi saurin janye nata.
Yace, " ya ina tambayarki? Kuma kina tanbayata?, banason shirme suwanene sud'in?, miyasaki kuka akansu kuma?.
"Basu n
akema kukakaba, nibanma sansuba, natuna Abbah ne kawai".
Bai gamsu da zancentaba, amma ya shareta baisake cewa komaiba.
Haka biki yacigaba da gudana, duk motsin Anty Kubrah da Anty glory akan idon ya khaleel da Aysha yake faruwa, kowa kuma da a
binda yake kitsama zuciyarsa akansu.
Meerah kam tuni tabar wajen dinner d'in, saboda bata buk'atar su Anty glo su ganta.
Aysha da ya khaleel suka mik'e a k'ark'ashin jagorancin mc sukabi dukkan manyan iyayennan suna godiya agaresu, (Dan kow
a zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zai kama gabansa).
Lokacin dasuka Isa wajensu Ammah sai Ammah tajawo Aysha ta d'ora akan cinyarta, tana kukan farincikin ganin wannan rana ta auren a khaleel.
Shikam yazauna kusada ita yana share mata hawayen da h
annunsa yana murmushi, nanfa camera tafara aikinta, masu d'auka a waya nayi masu camera d'in da aka d'akko nayi.
Konifa abin ya birgeni.
Momy kam dasukaje gabanta saita dafa kan ya khaleel kawai, taki kallon ko Aysha.
Ganin haka ya khaleel
yakamo hannunta itada Ayshar yahad'e waje d'aya yarumtse, cikin sanyin murya yace, "ga momyna farincikina, ga matana amanata, namik'a muku amanar kaina, banida abokai mafi kusanci dani samadaku Momy & Aee'sha!".
Hakan ya Sosa ran Momy, wai miyasa za
i had'a matsayinta dana Aysha?, tazare hannunta batareda ta tankaba.
Aysha kam taji dad'i harcikin ranta, sai damuwarta tad'an ragu, ganin kodai Yaya, ya khaleel d'in yadamu da ita.
Idanun Anty glo nakan Aysha, sotake tatuna Inda tasan mai iri
n yanayinnan amma takasa tunawa.
Kubrah kam wani d'acine aranta da kishi, tadad'e tana nunama ya khaleel d'in k'auna amma yana shareta, sai yanzu Dan abin kunya zai kwaso y'ar cikinsa amatsayin matarsa, ita kanta hasashen inda tasan matar tasa take
yi amma takasa tunanowa.
Dasukaje wajen Anty Mamie kam tamkar ta cinyesu, itama rungume ayshar tayi tana kukan dabatasan dalilinsaba, tashafa kan