Showing 9001 words to 12000 words out of 167215 words
damu kuma, wlhy harna
k'agara naga mai sa'ar data samu wannan jarumin jarumai, mai k'yak'yk'yawar zuciya da rik'on gaskiya, mai martaba k'asarsa da kare mutuncin al'ummar cikinta, koda basusan dashiba.
Wlhy zancenka gaskiyane youseef, boss nadabanne acikin mutane, samun
irinsa saida kwakkwaran bincike irinna masu hikima, da'ana samun ma'aikata jarumai marasa tsoro da kwad'ayi irinka da kasarmu bata lalace hakaba, saidai kash ru6a66un dasuke saida mutuncin k'asar tamu saboda kud'u sunfi nagartattun masu gaskiya irinka yaw
a, gashi kuma har yanzu al'ummar dake cikin k'asar basu fargaba, saboda *_KABILANCI DA 6ANGARANCI_* n dayayi tasiri aruhinsu, ga saka mana k'yamatar addinin juna da'akeyi, koda yake ba laifinmu baneba, laifin manyanmune, suna haddasa mana fad'ace-fad'acen
addini saboda cikar gur6ataccen burinsu akan siyasa, mafi yawan fad'a da'akeyi ak'asarnan y'an siyaysane ke shiryashi, amma da tafiya tafara nisa saiya zama fad'an yazama na addini, wannan wace iriyar masiface, mund'auki amanar kanmu mun dank'a ga siyasa,
wadda dama an kawo mana itane danta wargaza kanmu,, sai d'an siyasa ya d'auki mak'udan kud'i yabama Malamai da pastors, kaga sunata 6a6atu da cusawa jama'arsu mummunar ak'ida azukata, amma da tashin hankali zaizo duk kwashe y'ay'ansu da matansu zasuyi da k
ud'inmu subar k'asar, wad'anda suka kasance malaman kwarai acikinsu sai adinga binsu d'ai-d'ai ana kashe manasu, shin jama'armu bazasu farka daga nannauyan barcin daya d'aukesu baneba? Su nutsu wajen gano nagartattu irinsu khaleel a k'asarmu? Duk mutum ma
i gaskiyade zakaga bashida Pawer d'in hidimtawa al'ummar kasarmu, saboda mak'iya masu gur6atattun halayen dasuka raba hanya da halayensa na warai sune zagaye dashi.
Hakane Taheer, amma aii mungodema ALLAH, tunda Anfara walk'iya munkuma fara tsinto
k'asurguman munafukai, kuma tabbas y'ar manuniya zata cigaba da nuna manasu insha ALLAH, talakawanmu kuma dasuka kasa gano gaskiya haryanzu saboda rashin sanin ciwonkai ALLAH ya farkar dasu kafin lokaci ya k'ure musu.
Ya khaleel dabaice komaiba Tun d
'azun yace amin Joseph, saidai akullum ina tuna muku duk abinda zanyi da taimakonkune, kuma bazan ta6a amsa sunan waneba saida sunanku aciki, wannan zancen naku saiya tunamin dawani Abu mai muhimmanci dayake araina tuntuni.
Atare sukace wane Abu
kenan?.
Saida yad'ago daga kwancen dayake akujera sannan yace yakamata mu kafa kungiyar taimakon matasa, wasu sun kammala karatu babu aikinyi, mukar6i takardunsu mu nema musu guraban aiiki, wasu rashin gata yasaka ko karatunma basuyiba, mu koya mus
u Sana'a dabasu jari, wasu kuwa karatunne ya yanke saboda babu kud'in k'arasashi, mu taimaka musu su gama, yakamata mu juya akalar zukatan matasanmu su farka daga ra'ayin karatu nayi
danhaka sai aikin gwamnati, gwamnatin k'asarmu batada k'arfin d'aukar duk
kan matasanmu suzama a k'ark'ashinta, amma idan ana jansu ajiki, danuna musu basaita silar gwamnati asiri ke rufuwaba, k'asar zata zauna lafiya, ataimakesu wajen ciremusu burin sainayi kud'i nima kamar wane, wannan zairagema k'asarmu cin hanci da rashawa,
ta'addanci da k'abilanci harma da fad'an addini, za'a daina wawaso akan dukiyar y'an k'asa, wadda zakaga mutum shikad'ai yatara biliyoyin kud'i, kama rasa mizaiyi dasune? Ga gidaje da hannayen jari, jikokin jikokinsama bazasuyi talauciba, kaga mutum d'aya
da mota ashirin shikad'ai, sannan duk y'angidansu kowa nada sama da biyu, kai wlhy idan kaje wani gidan saika d'auka anan ake k'era motoci saboda tsabar fariyya, to ba kud'insa baneba, hak'in al'ummar k'asane, shiyyasa baisan ciwonsuba, yawancin zakaga y'a
y'ansune y'an cocaine, kuma sune ke shigomana daduk wani kayan maye ak'asarmu, saboda inama talaka yasamu abinda zaici? Bare yazama d'an safarar miyagun kwayoyi?.
Abinda ke matuk'ar tada hankalina shine, bayan satar kud'inmu dasukayi, sukabama y'ay'
ansu sukaje suka siyo kayan maye da kud'in, saikuma adawo dashi cikin y'ay'an talakawa ana saida musu domin gu6ata tarbiyarsu, baza'a barmu muji da zafin talaucin daya ishemubama.
Sometimes idan kaga d'an talaka yazama d'an ta'adda wlhy zafin talauci
ne da bak'incikin zalincin da manyan k'asarmu keyi akanmu, ko shaye-shayen nan da y'anmata sukeyi duk silar masifar da'aka jefamune, kuma wlhy wasu sunkoyone wajen y'ay'an manyan, k'awaye ko samari, saboda shegen kwad'ayinsu, Dan muma talakawan wani lokaci
n bamusan darajar kanmuba wlhy, bamusan ciwon kanmuba, kowa burinsa ace dashi wane. Why!!!!?.
My friends why!!?.
Wace iriyar rayuwa mukeyi aduniyarmu? Miyasa muke mantawa da mutuwane? Miyasa muke mantawa akwai ranar hisabi? Ranar da kowa zai b
aje kolin ayyukansa a kasuwar daba'a ta6a Tara irintaba?. Wlhy muji tsoron ALLAH, mukiyayi ranar da ALLAH zai kamamu, Duk shagalar dazakayi duniya karunga tuna watarana zaka *MUTU*, ko shekaru millions aka Baka saisun k'are, kafinkai anyi manyan tantirai a
duniya wad'anda suka fika shara aduniyarma amma sunzama labari, tofa kaima watarana saidai labarin, kuma bayankama za'ayi wad'anda suka fika, ammafa muringa tunawa akwai *WUTA DA ALJANNAH* kuma kowacce zata samu jama'a.
Suduka jikinsu yayi sanyi da jawa
bin nasa.
Murya a sanyaye sukace sun bada goyen baya, Dan haka saisu fara shirin yanda zasu kafa k'ungiyar.
Alhmdllh naji dad'in amincewarku y'an uwana, nayi wannan tunanin saboda dubi da albashinmu alhamdllh. Ko aure mukayi zai ishemu rik'e iyal
anmu harma da saura, gakuma y'an kasuwancin damukeyi a bayan fage, to damu tarasu abanza alhalin gamasu buk'ata nan aii gara muyi abinda ko bayan ranmu baza'a manta damuba, nifa banida burin barma y'ay'ana d'unbin dukiya dansu gada, Nafi burin natsaya tsay
in daka akansu dansu sami ilimin addini dana zamani watarana suma sunema da Kansu, dansusan wahalar nema, mizaisa Natara musu dukiya sudunga k'agarama Na mutu dansu gada, bayan mutuwar tawa suje suyita iskanci anamin azaba akabarina, _(da abaka gasashshen
kifi, gara akoya maka yanda ake kamunsa a rafi)._
Gaskiyane wannan, kuma duk munyi mubayi'a, ALLAH yamana jagora.
Haka sukaita tattaunawa har zuwa dare, sanan kowa yanufi gidansa.
____________________
Khaleel zaune agaban baffah d
a uncle ma'aruff dayazo yau, sai Ammah, kansa ak'asa yana sauraren iyayen nasa.
Uncle ma'aruff yay garan murya irintasu ta manya, idonsa akan khaleel d'in, cikin murmushi yace khaleel anzama manya kenan? ALLAH ya sanya alkairi.
Ammah ta amsa da a
meen.
Alhmdllh munje anyi maganar aurenka da sirikanka mutanan kirki, komai nasu cikin turban addini da yanda ALLAH yace muyi.
Sun yanke mana ranar d'aurin aure nanda watanni 6, saboda sunce ansaka bikin y'an uwanta dama su hud'u, to an daida
ita danasu d'in, kaga yakama cikin sabuwar shekara watan biyu. Sun yanke sadaki naira dubu 50k kacal, dan albarka ake nema acikin auren.
Ya khaleel yakuma yin k'asa da kansa, dama can shi mutumne mai kunya, shiyyas kaf yaran gidan babu Wanda za
ice gashi yata6a ganin ya khaleel da ko sitirar dazata fidda masa jiki.
Baffah yakatse tunaninsa dafad'in yauwa mu'azzam saika za6i 6angaren dayay maka a filayenku dake baya Dan afara ginawa, kakuma za6i kalar dakake buk'ata kamar yanda sauran y'
an uwanka sukayi su Sultan.
To baffah ngd sosai ALLAH yak'ara bud'i.
Gaba d'aya suka amsa da ameen, sund'an cigaba da tattaunawa akan bikin, amma khaleel yayi d'if, baya cewa uffan.
Hardai uncle ma'aruff ya fuskanci kunya yakeji, Dan haka ya
ce yatashi yaje ya kwanta ya huta.
Godiya yamusu tareda sallama yafice.
Yana shiga falon Aysha Na fitowa da gudu daga d'akinsu, rik'e take da wayar fadeelah tana danna wani Abu, fadeelah kuma nabinta tana rok'onta da Aysha karki tura masa, ALLA
H banason haka, Aysha karfa kitura.
Hhh wlhy Yaya fadeelah dama kin hak'ura, yo haka akeyi baza'a turama bawan ALLAH kalaman soyayyaba, bayan yayi hak'uri kusan wata uku kinwani mak'ale wankan jego.........
Maganar ta mak'ale mata amak'oshi sab
oda shigowarsa.
Atare suka kalli juna, ya harareta ta murgid'a baki.
Mamakin rashin kunyar yarinyarnan yakeyi, ko kad'an batajin tsoronsa, yarasa miyasa haka?, shiba rayuwa yayi a waje d'aya da itaba, ko k'annensa basu masa haka, ko mufeeda
datake sakonsa sotsonsa takeji, haka duk jarabar Anty Zuwairah yayarsu shakkarsa takeji, amma wannan y'ar ficiciyar yarinyar take masa yanda ta gadama.
Kwafa yayi yashige 6angaren momynsa.
Aysha takuma murgud'a baki da harar bayansa tana k'unk'
unai.
Ahaka fadeelah tazo ta kwace wayarta tana fad'in mara kunya, watarana koda kud'i akace kimasa bazakiyiba wlhy, Arana d'aya kacal zai koyamiki hankali.
Bata jira cewar ayshar ba tabar wajen.
Itama bin bayanta tayi tana k'unk'uni.
Nace hummm su Aysha ammata
π
, zaki magantune indai ya khaleel ne
π
.
Afalo ya iske Momy, kallon datake masa kawai yasaka jikinsa sanyi..
Ita kad'aice afalon, guywa a sa6ule yak'arasa cikin falon..................
β
πΏ
πππ
π
ππ
[9/6, 5:54 AM] Aysha Galadima: *_Typing
π²
_*
π€°π»
*_CIKI DA GASKIYA........_*
_{
πͺ
wuk'a bata hudashi
π‘
}_
*_Bilyn Abdull ce
π€π»
_*
*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*
_~Home
of experts and perfect writers~_
*_Sadaukarwa_*
_My sweet dady_
~(ALLAH ya gafarta maka)~
π€²π»π
*_part 2_*
(littafi na biyu
π
)
5
β£
Zama yayi kujerar dake kallonta, momy barka da dare.
Ad
ak'ile tace barka.
Shiru babu Wanda yasake cewa uffan, hajia babba sai cika takeyi tana batsewa, Dan jitake tamkar karta amince da shawarar hajia khaltume, amma kuma wani 6angare Na zuciyarta Na nunamata hakan shine dai-dai.
Ta saci kallon khale
el d'in Wanda idonsa ke kan TV, amma azahirin gaskiya yana nazarin momyne.....
Ibraheem!!.
Na'am momy! Ya amsa yana maido kallonsa akanta.
Na amince da aurenka, amma da sharad'i.
Shiru yayi yana saurarenta, gakuma maganar tata ta dakesa,
Dan baiyi tunanin yardarta da wuri hakaba.
Amma momy miyasa kika amice? Miye kuma sharad'in?.
Karka damu da dalilin amincewata, wannan sirri nane, sharad'in kuma shine nangaba zaka auri Aleeya itama.
Wani guntun murmushi yayi, Wanda yaf
i kuka ciwo, ya kauda kai daga kallonta yana cije le6ensa Na k'asa, babu damuwa momy ALLAH yaza6a mana abinda yafi alkairi.
Tsura masa idanu tayi cikeda mamakinsa, ko kad'an batayi zaton taurin kansa zai saka ya aminceba cikin sauk'i, anya kuwa
bawani Abu yaronnan yake shiryawaba? Koda yake ance basu kama barau modibbo ba.
Yana kallon, kallon da momy kemasa da gefen idonsa, aransa yay k'aramar dariya, yana fad'in momy kenan, *'DAN HAKKIN DAKA RAINAFA....* shike tsone maka ido watarana.
Afili kuma yace momy kokinada damuwane?.
A'a Ibraheem babu komai, amma yanzu ina zaka zauna?.
Zan zauna inda gidana Na Asokoro.
A'a kazauna anan gidan, kaima indasu mujahedeen sukayi gini.
Miyasa momy? Kefa kikace ba
kiso Na zauna agidannan da matana idan nayi aure, miyasa kuma yanzu zaki canja?.
Haka kawai.
Ananma dariya yayi azuciyarsa, afili kuma yace shikenan momy duk yanda kikeso haka za'ayi to.
Farin cikine ya lullu6e kasan ranta, Dan ganin duk a
binda tace baya mata musu.
Daga nan tasaki fuska sukad'an ta6a hira, cikin hikima irinnansu Na manya take sako masa tambayoyi akan aikinsa.
Amsa yake bata kai tsaye batareda tunanin miye manufartaba.
Itakam dad'i takeji yau tasami Ibrahee
m yanda takeso.
___________________________
Washe gari girkin mama, bayan tagama had'ama baffah breakfast agabansa tace Alhaji su Aysha zasu koma gida zuwa jibe idan ALLAH ya kaimu, Dan fadeelah zata koma d'akinta mijinta NATA waya.
d
'ago idanunsa yayi yana kallon mama, baice komaiba yacigaba dacin abincinsa, saida ya mammala tsaf sannan ya fuskanceta sosai, fad'ima fadila ce kawai zata koma, amma Aysha tazo kenan, Dan bilyamin yabani, ita kanta fadeelah badan aure takeba da babu inda
zataje, akoda yaushe inaso ki gane sud'in y'ay'a nane koda banine mahaifinsuba, inajinsu azuciyata tamkar su Mu'azzam wlhy.
Yanzu haka zancennan danake miki angama komai akan bautar k'asar Aysha (NYSCE) insha ALLAH k'arshen watannan zata fara, anan k
usadamu. Dan munyi sa'a abin yazo daidai daza'a d'auki sababbi.
Hawayene suka cika idonmama saikuma taji kunyar abinda tayi, cikin hikima tabama baffah hak'uri.
Murmushi yayi tareda jawota jikinsa ya rungume yana fad'in babu komai first love
d'ina, Dan bakisan irin matsayin dakike dashiba azuciyar Abdallah bane shiyyasa kike Raba d'aya biyu, amma namiki uzuri, daga yau karki sake.
Dad'ine ya lullu6e mama, Dan itama tana k'aunar mijin NATA, tak'ara k'ank'ameshi da k'yau kamar mai gudun ka
r'a kwace matashi.
π
ββa 100 nafito, Dan lamarin yafi k'arfina, wannan fagen Na manyane
π
irinsu baffah
π
.
_____________
Akwana atashi babu wuya wajen ubangiji, rayuwa tanata tafiya, yau kusan watanni uku kenan da saka bikin ya khaleel da
Aysha.
Saidai babu mai shiga harkar wani shida Aysha, ita bautar k'asar datakeyi ya d'aukema hankalinta gaba d'aya.
Shikam yawon k'asashensa yahanashi zama waje d'ayama.
Yanzu haka yana Mexico kusan kwanaki 13 kenan, daga nanma Franc
e zai sauka a gaba d'aya headquarters d'insu dake Lyon city, sosai aiki ya d'auke hankalinsa a y'an kwankinnan, shiyyasama yakan manta dawata aba Aysha, dama ko number d'inta bashida ita, koyayi waya dasu mama kuma baita6a cewa abataba.
Ya gyara kwan
ciyarsa yana mai tunanin yanda rayuwar aure zata d'ore babu soyayyar juna.
K'aramin tsaki yayi, lokacin daya tuno rashin kunyar yarinyar, yatuna bakinnan nata maikama Dana tsuntsu dake masa murgud'e, kwafa yayi tareda fad'in zan kama kine aii afili.
Araina nace batama San kanayiba
π
.
Aysha kam soyayyar ya khaleel Na nan mak'ale aranta, amma tana danne abinta, tareda nuna halin ko inkula akansa, ga cin kashin da y'ay'an hajia babba kemata da habaici akan auren, ita kanta hajia babba ba d'aga ma
ta k'afa takeyiba.
Hakan baya damunta Dan aganinta kad'an yarage tayi maganin uwarsuma ba suba.
Anty zuwairah ma tazo ta tata tsiya agidan dantaga baffah bayanan, babu cin mutunci dabatayima mama da Aysha ba, saida Ammah tamata tas sannan tabar gi
dan, tabi jirgi zuwa Lagos Dan tasan gidan bazai kwanu agaretaba, saboda ranar Baffah zai dawo daga Turkey.
Sauran yaran kuwa kowa murna yakeyi ya khaleel zaiyi aure, zaikuma auri wacce suka Sani, amma ak'asan ran Zunnurain da musleem sunji babu da
d'i, dansun k'yasa Aysha gaskiya
π
.
π€£
nace boss yamusu wawaso
π
*_2weeks ago_*
Misalin 5pm Aysha tafe a hanya, sanye take cikin wando da riga Na Nysce, bak'armin k'yau kayan sukai mataba, tasak'a k'aramin jijjab fari daya k'awata
k'yawun haibarta, ta d'aure rigar saman kayan a
k'ugunta, tafe take cikin nutsuwarta bayanta rataye da schoolbag, dolene ka kalleta kasake kallo, dukda yanayinta ya nuna a tsorace take.
Kad'an kad'an takan kalli sararin samaniyar dayay murutuk alamun
hadari ya had'u bana wasaba, kuma ruwa zai iya sauka akowane lokaci, kullum driver ke kawota, idan lokacin tashinsu yayi takirasa ya d'auketa, amma yau takirasa wayarsa arufe, itakuma batason yin dare awaje Dan baffah bayaso, wannan dalilin yasakata hawan
napep, saidai sunkusa shigiwa layinsu napep d'in yasamu matsala, ganin zata 6ata lokaci tace bara ta k'arasa kawai ak'afa Dan babu nisa, tama d'an tada jininta.
Tafiya tafara dad'an sassarfa saboda iska tafara kad'awa alamun hadarin yafara tasow
a, kuka da Neman taimako tafaraji ad'an nesa da ita kad'an, tafara waige-waige damson ganin mai Neman taimakon?.
Saitin inda takejin kukan sosai matso, garadan samari biyu tagani suna k'ok'arin tura wata budurwa a mota.
Inadanu tazaro waje, tun
i wata jarumta tazo mata Dan ganin harsun gama turata mota, d'aya nashirin cire wando, da alama ma amotar suke shirin keta mata haddi, Aysha ta waiga ko