Showing 12001 words to 15000 words out of 167215 words

Chapter 5 - CIKI DA GASKIYA complete

ina babu alamar mutum, kowa yashige gida, Dana birnin Abuja dawuya kaga mutane nayawo ak'afa hakanan, g

a anguwar dama babu yawan gidaje sai kamfanonu, zuwa yanzu kuma antashi aiki, wani k'arfe ta d'auka a gefen titin, cikin sand'a tak'arasa wajen motar, mai cire wando dahar ya danne d'iyar mutane yana shirin afka mata ta kwalama k'arfen a k'afarsa data fito

waje.

Azabace tasakashi sakin gigitacciyar k'ara, adaidai nan kuma ruwa ya sakko.

d'an daya toshe bakin yarinyar Dan hanata ihu yay saurin sakinta yana fad'in Arfan miya farune? Da sauri yazagayo garesa, ganin Aysha da k'arfe a hannu tana k'o

k'arin jawo yarinyar dazasuma fyad'en yace kutumelesi, mikika masa? Wlhy yau sainayi kaca-kaca dake, yay maganar yana damk'e hannun Aysha.

Ihu Aysha tafarayi, Wanda takwalama k'arfen shima yataso yana d'ingishi, aii wlhy yau yarinya sai munmiki abin

da bazaki sake moruwaba aduniya, ki yankemin jin dad'i sannan ki kwalamin Abu, aii saina fanshe ajikinki Dan ubanki.

Suka fara k'ok'arin cire hijjab d'in Aysha.

Hankalin budurwarnan yatashi, ganin Aysha ta taimaketa kuma abin ya juya kanta, ras

a mizatayi musu tayi, sai kawai takwasa aguje babbar hanya tana kuka dafad'in a taimaketa....

Emanuel! Kamar yarinya nake hange agabanmu tana kuka?....

Eh sir, ammafa Baka tunanin ko wasune suka d'ana mama tarko....

Ya khaleel dake z

aune abaya yanata danna lap-top nashi yace mike faruwane Adams?.

Babu komai sir, dama wata yarinyace gatacan mund'an wuceta take kuka, shine nace koza'a taimaketa, Emanuel yakecewa k'ila tarkon mak'iyane.

Da Sauri ya khaleel yajuya yana kallon

bayansu, hango yarinyar yayi tana kuka da gudu tana tsaida motoci, amma babu mai k'ok'arin tsayawa.

Emanuel!!! Mujiya, ya khaleel yay maganar cikin matuk'ar tsawa.

Aii babu shiru Ema yajuya kan motarsa, sauran motocin suka biyo bayansa.

A

gabanta suka taka birki, tana ganin haka tabud'e k'ofar baya dasauri tana fad'in Ku taimaka zasu keta mutuncinta, please yayana kataimakeni karsu cutar da ita.

Ya khaleel yatsura mata idanu yanason gano ainahin gaskiyarta, ganin yanda take yasakashi

gaskatata, da Sauri yafito amotar batareda ya kula umbrella d'in da Adams yasaka masaba saboda ruwan yafara k'arfi.

Ita kanta batasan tarik'e hannunsaba tana jansa saboda kid'imewar datayi.

Sun k'araso lokacin da samarin ke kokawar cirema Ay

sha dogon wandonta, amma tarik'e kam tahana, d'ayan sai marinta yakeyi amma tak'i saki, mamakin taurin kanta sukeyi da k'arfi, farar fuskarnan tayi jajur saboda mari, garuwan sama ya jik'asu.

Bai tsaya bin ba'asiba yahau jibgarsu.

Aysha tami

k'e da Sauri tana kuka, ganin ya khaleel yasakata zuwa da sauri Inda yake ta k'ank'amesa tana kuka da fad'in ka taimakeni ya khaleel zasu cutar dani, karka barsu, azzalumaine su.....

Gaba d'aya arikice take, sai yanzu ya khaleel yaga Aysha, hankalins

ane Yakuma tashi, danhaka ya tureta daga jikinsa tareda damk'osu ya gwara kansu, dukansu yakeyi afusace, dak'yar securitys d'insa suka kwacesu, dansunga zaiyi kisankai.

Abirkice yajuyo kan Aysha dake gefe tana mak'yar k'yar sanyi, Dan ruwa aketa tsul

awa kamar da bakin kwarya, mari ya falla mata, yana fad'in ubanmi yakawoki nan wajen?!!, nace miya kawoki?!!!!!!!.

Cikin matuk'ar tsawa yayi maganar, Dan harsu Adams saida suka zabura Dan tsoro.

Aysha tarik'e kumatunta tana matsawa baya saboda

tsawar daya daka mata, wani Marin Yakuma kai mata Adams yatareshi yana fad'in please sir cool dawn.

Ya cije le6ensa tareda kuma kaimata duka saikuma yafasa ya rumtse hannun yana ciza la66ansa da k'arfi, jiyake tamkar ya had'iye zuciya awajen, rans

a amatuk'ar 6ace yake, ya tura hannunsa d'aya a aljihun wandon oxblood d'in suit nasa, dasuka gama jik'ewa da ruwa, idanunsa sunyi jajur, ya watsama Aysha harara yana fad'in Adams kallafa kaga wajennan?, shin miya kawo yarinyarnan har suke shirin k'etaram

in gonata? batareda ni Nayi koda gewayentaba?.

Yanzu dabamuzoba mikake tunanin zai farune? Mutuncinafa zasu Shiga saboda Mara hankalin yarinyarnan, Na mauje tama nahuta da ganinta.

Yay maganar yana ture Adams gefe tareda kaima Aysha wawura.



Yanzunma Adams kuma tareshi yayi, dukda bai fahimci zancen ogan nasaba, Dan baisan alak'arsama da yarinyarba.

Budurwannan ne tak'araso tana kuka dabama ya khaleel d'in hak'uri, tamasa bayani akan balaifin ayshar baneba, taimakonta tazoyi, itama

a d'aya daga kamfanin take aiki, motartace tasamu matsala, daga Neman taimakonsu shine suke shirin mata fyad'e, Aysha ce ta taimaketa.

Zuciyarsa tad'anyi sanyi, amma bai huceba, Dan saiyaji ubanwa yasakata biyo hanyarnanma mai had'ari?, ina driv

ers d'in dake gidansu? Dahar ta taho ak'asa.

Ya watsa mata harara dayin kwafa, rigar suit d'insa yazare ya jefa mata, saboda farar rigarta ruwa yajik'ata dukta nuna jikinta, har kalar bra d'inta ana gani.

Jikin Aysha Na rawa tad'auka tasaka, dama

Duk kunya tagama isarta.

Dariya nayi azuciyata, Dan hannun rigar yamata tsawo, gata tayi tsumu arigar kamar antsamo zomo aruwa

🤣🤣

.

Da kansa ya tattara kayanta, bag d'inta da hijjab, sai lemon green d'in rigarta data d'aure k'ugu, ijjab d'in yaku

ma jefa mata tasaka, dukda gyararren gashinta data d'aure a tsakkiya yagama jik'ewa jalab da ruwa bar d'iga yakeyi.

Yadaka mata tsawa, bazaki shige mujeba saina 6alla kasuuswanki anan......

Bata bari yak'arasa ta zuba dagudu, saida batasan mot

ar dazata shigaba, dolene tajira ya k'araso.

Samuel karaka wannan yarinyar, kukuma Auwal ajeda yarannan kucimin ubansu dai-dai gwargwado, Adams kumuje.

Atare suka amsa,, aka kwashi samarinan dasuka gama fita hayyacinsu saboda duka.

Yana

hararta yabud'e mata mota tashiga, sannan yazagaya Inda Adams yabud'e MASA shima yashiga shima.........

✍

🏿

💋💋💋💋💋

[9/6, 9:21 AM] Aysha Galadima: *_Typing

📲

_*





🤰🏻

*_CIKI DA GASKIYA........_*



_{

🔪

wuk'a bata hudashi

🗡

}_





*_Bilyn Abdull ce

🤙🏻

_*

*_HASKE WRITERS ASSOCIATION_*

_~Home of experts and perfect writers~_

*_Sadaukarwa_*

_My sweet dady_

~(ALLAH ya gafarta maka)~

🤲🏻😭

*_part 2_*

(littafi na biyu

📕

)

_Na gaisheki first lady, ALLAH yabar zuminci_.



😍😍😍💋

6

⃣



Aysha ta k'ank'ame jikinta tareda takurewa amurfin mortar, sai rawar sanyi takeyi, saboda bak'aramin ruwane yadak

esuba awajen.

Ya khaleel ya gallamata harara yana d'auke lap-top d'insa dake tsakiyarsu, takuma k'ank'ame jikinta, harda rumtse ido, dan azatonda dukanta zaiyi.

Tsaki yasaki mai k'arfi, dububeki, dawani kanki kamar curin dankalin Hausa, af

uska kamar kinada wayo amma wawuyace ashe, atunaninki ko ina ake nuna jarumta? Amatsayinki Na mace bak'ya tunanin had'ari fiyema da wannan? To dabamu zoba mikike tunani zai faru?!!!!, yay maganar a tsawace.

Aysha takuma k'ank'ame jikinta tana h

awaye, wlhy ya khalee......

Ki rufemin wannan d'an banzan bakin naki kafin nazubar da hakwaran cikinsa amotarnan, aii sai kin fad'amin ubanda yasakayi biyo hanyarnan ak'afa Stupid girl kawai.

Acikin ranta tace idan kazubar da hakwaran kaika

huta aii, nibanga dalilin wannan bala'iba haka, bakaji tausayinaba ka isheni da jarabarka.

Adai-dai nan suka iso k'ofar gate d'in gidan, Emanuel yay horn d'an gwari yabud'e.

Motar bata gama tsayawa da k'yauba Aysha tafita da gudu tayi cikin g

ida.

Kwafa ya khaleel yay shima yafito bayan Adams ya bud'e masa k'ofar.

Drivers d'in gidan yashiga kwalama kira, sunata hada-hadar tafiya masallaci saboda magrib data kawo jiki.

Ahanzarce suka k'araso gareshi, Dan sunsan shid'in z

umane, ga zak'i ga harbi, gashi yanayinsa ya nuna a harzuk'e yake.

Gaidashi suka shigayi, batareda ya amsasuba yace wanene yake kai yarinyarcan Aee'sha wajen aiki?.

Jikin lawwali Na rawa yace nine wlhy yalla6ai.

Wani kallo ya wats

a masa, idan an idar da sallar isha'i ina nemanka.

Maganar daya fad'a kenan yajuya zuwa cikin gida.

Adams ya kalli su lawwali daduk hankalinsa yake atashe, wainikam wacece yarinyarnan awajen boss? Duk nasan k'annensa, amma ban santaba.



Itace zai aura, cewar sadisu murya a sanyaye.

Ido sosai Adams yazaro, aransa yace kutttt shiyyasa Oga yarikice, ashe antynmuce? Lallai kingama morewa y'an mata wlhy.

Kayansa ya kwaso yamik'ama sadisu danya shiga dasu ciki.

Afal

o ta Tatar damafi yawan mutanene gidan, jikin Anty Mamie data fito daga kitchen tafad'a tana kuka, a'a Aysha lfy kuwa? Ina kikaje hankalinmu dukya tashi, lawwali yace yaje d'aukarki baigankiba?.....

Anty Mamie nafa kirashi wayarsa akashe, shinefa..

....

Shigowar ya khaleel takatse mata maganartata.

Yaran gidan sai sannu da zuwa suke masa Dan tsawon wata 1 baya k'asar.

Adak'ile ya amsa musu, saboda ransa a6ace yake.

Anty Mamie tace a'a babana ko tare kukene?.

Kansa ya ji

njinama Anty Mamie.

To lfy duk naganku ajik'e haka? Mike faruwane? Mu kun sakamu aduhu aii, ita tashigo tana kuka, kaikuma rai a 6ace?.

Muryarsa cikeda d'aci yayma Anty Mamie bayanin komai, kowa afalon ya tausayama Aysha, amma yanda ran ya k

haleel d'in ya6aci sai abin yabasu mamaki.

Aysha tace ALLAH Anty Mamie tausayi tabani shiyyasa Na taimaketa, kumafa badan niba dazasu keta mutuncin tan........

Idan bakima mutane shiruba ALLAH saina zaneki yanzunnan, ke mara hankalin inace? Mi

yasa bazakiyi kamar yanda tayiba? Zaki wuce ki canja kaya kosaina k'ara kummura wannan janaren fuskar takine?, yay maganar yana matsowa kamar zai mazgeta, Ta k'ank'ame Anty Mamie kuwa.

Baffah dake tsaye yafito dashirin zuwa masallaci tareda y'an uku

da Nuriddin yayi murmushi, Dan yaji dad'in yanda khaleel d'in yanuna kishinsa.

Maganarsace tasaka kowa juyowa gareshi, yace to ya Isa haka, mu'azzam amata hak'uri tayi kuskure, kuje kucire kayan jikinku kar mura takamaku.

Aii baffah fi

yema damura saita kamamu, duk ruwannan nayau akanmu yak'are saboda sakarar yarinyarnan, yay kwafa tareda shigewa 6angarensu.

Girgiza kai baffah yayi yana murmushi. Yaja hannun k'ananun y'ay'ansa suka nufi massalaci.

Suma sauran kowa d'akinsa ya

nufa, Anty Mamie kuma tatafi da Aysha d'akinta itama.

Duk abinnan dake faruwa mama nad'aki kuma tanajiyo komai, ita sotayima khaleel d'in yazane ayshar wlhy.



Anty Mamie tahad'ama Aysha ruwa mai zafi sosai, kije kiyi wanka Aysha, kid'an shi

ga ruwan kona minti gomane.

Tana hawaye tajinjinama Anty Mamie kanta.

Shima yana shiga d'akinsa yafara cire jik'ak'k'un kayan jikinsa, sai tsaki yaketa zubawa, sosai yakejin sanyi, dakewa kawai yakeyi, shidamacan koyaya ruwa yata6ashi saiyayi mur

a, ko wanka yacikayi da ruwan sanyi tosai yayi mura bare wannan dakusan durom goma yak'are akansa.

Gashi anfara kiraye-kirayen sallar magriba, da hanzari yashiga bathroom yahad'a ruwa mai zafi sosai yashiga ciki, baiwani 6ata lokaciba yafito sab

oda za'a shiga sallah, jallabiya yasaka da hanzari yafice.

Sakamakon anad'an yayyafi har yanzun aka had'a sallar har isha'i.

Gabad'ayan mazan gidan suka shigo, sun sako baffansu tsakkiya abin sha'awa, a babban falo aka yada zango.

Har

ya zauna yamik'e, kai bara nasaka rigar sanyi, wlhy sanyi nakeji.

Idan kasako rigar sanyin kuzo ga shayi nadafa muku mai kayan kamshi, Dan ita ayshama fuskar dukta kumbura, harma zazza6i yarufeta.

Anty Mamie ce mai maganar.

Baffah

yace subahanallah, ina ayshar?.

Tana d'akina k'udundune abargo baffansu.

Ya salam, yakamata akira doctor kuwa, Sultan kira Dr Kabeer abokinka.

To baffah

Khaleel najinsu amma yay shigewarsa 6angarensu batareda ya nuna alamar yamaji zan

cen nasuba, d'akinsa yashiga, yacire jallabiyar jikinsa yasaka k'ananun kaya, dogon wando amma, yakawo rigarsanyi yasa, hular yaja har samankansa sannan yadawo falon.

Hamdiyya takawo masa tea d'in da Anty Mamie tadafa musu, yanasha suna hira da baffah

da y'an uwansa.

Ana haka Dr Kabeer yakira sultan akan yak'arso.

Bismillah Doctor shigo kawai ciki.

Cikin girmamawa Dr Kabeer ya gaisa da baffah, yabi dukkan samarin yabasu hannu sukayi musabaha

🤝🏻

.

Baffah kaine babu lafiya?.

A'a K

abeer, d'iyatace, mu'azzam kuje yadubata ko.

To baffah.

Yana gaba Dr Kabeer Na binsa abaya har d'akin Anty Mamie.

Dr Kabeer yatsa a k'ofar d'akin Dan amasa iso.

Shikuma khaleel yashiga.

Tana kwance bisa gadon Mamie, gaba d'aya taruf

e jikinta har kanta, saida yamata kallon minti d'aya, sannan yatako a hankali har gaban gadon, hannu yakai ya yaye bargon, Aysha dake k'ank'ame da filo tanata rawar sanyi, dukda sanye take da jibgegiyar rigar sanyi kuwa, kanta kuma nad'e da towel.

Jin

anyaye mata bargo tad'ago kanta da k'yar, ganinsa tsaye akanta yasakata tashi zaune da hanzari, wani mugun tsoronsa takeji aranta, yanzunma fuskarsa a d'aure take babu alamun wasa, wannan yasaka Aysha takasa koda satar kallonsa, dama ga idanunta sunyi nau

yi saboda marukan datasha.

Baice komaiba yabama Dr Kabeer damar shigowa, tunda yaga kayan mutuncine ajikinta.

Dr Kabeer yashigo da sallam, khaleel yanuna masa sofa ya zauna, shikuma ya jingina da madubin tareda zaro wayarsa a aljihu yafara danne-

danne, saika rantse dukkan hankalinsa akan wayar yake, amma bahaka baneba, hankalinsa natareda su Aysha da Dr Kabeer kema tanbayoyi tana bashi amsa murya a sanyaye.

Aransa yace trouble marker anyi laushi yau, fukarta tad'an tasa, takumayi jajur abink

a da fara, tad'an bashi tausayi kad'an, amma haryanzu halayenta mamaki suke bashi, dan kullum da sabon salo take zuwa masa, amma wasu abubuwan nata nasakashi nishad'i kad'an......

Maganar Dr Kabeer takatse masa tunanisa, ya Khaleel kozamu samu tea tad

'ansha saboda za'a mata allura, kuma zai taimaka mata tarage jin sanyin.

OK.

Harya yunk'ura zai fita saikuma yafasa, bazai iya barinta itada Dr kad'aiba.

Wayar Muhseen yakira, yana d'agawa yace ka kar6o mata tea wajen Mamie.

Baijira amsa

rsaba ya yanke wayar.

Babu dad'ewa saiga Anty Mamie da Muhseen sun shigo, lokacin Dr Kabeer yagama ware mata magani, harya fara had'a allura.

Aysha sai hawaye takeyi Dan batason allura dama can.

A'a Aysha kukan kuma namiyene?.

Anty

Mamie wlhy banason allurar.

Dr Kabeer yatsaya da had'a allurar yana fad'in to kiyi amfani da maganin kawai...

No, cigaba da had'a allurarka Kabeer.

Jinjina kai Dr Kabeer yayi, yayinda Aysha ta rushe da kuka.

Ko kallo bata isheshiba, A

nty Mamie Ce kawai ke lallashinta, muhseen kuwa dariyama yake mata, khaleel yad'ago ido ya kallesa.

Zoka fice.

Fitayay yana kunshe dariyar karta fito.

Anty Mamie tarik'ekata Dr Kabeer yamatsa zai mata allurar, takware baki zatayi kuka ya kha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login