Showing 27001 words to 30000 words out of 178087 words
ihu na zabgaga tare da kashe ihun da gud'a, wanda haka yayi sanadiyyar jawo hankalin duk wanda ke cikin gidan na w
aje da wanda ke d'aki babu wanda aka bari kowa saida ya fito.......
Kirari na fara kwararwa bari ba tare dana kalli dandazon mutanen dake kallona ba.
Bariki ba'ayi miki tilas babu wanda ya rako wani kowa da k'afarshi yazo kuma in yaji wuya shi za
i koma, baki duba mai kyau ko mummuna, haka kuma babu ruwanki da maye ko mayya mai lafiya da mai cuta duk wanda yazo kina da masaukinshi, baki san inda kowa yake ba amma kowa yasan inda kike, gani nazo ki sakamin albarka, baki da tabbas bariki haka nima ba
ni da tabbas, matsalar ubace ta kawoni amma ina tare da had'ari guda d'aya, bana san shiga sabgar kowa karki sake ki bari wani ya shigo rayuwata, ilimi nazo d'auka a cikinki amma ni nafiki rashin tabbas, ina da masaukin kowa amma banda na mata.....duk nami
jin da uwarshi ko ubanshi yace jeka ka gani tabbas idan yazo ina da masaukin shi nima,
Kija da'irarki ki bani tawa, bana shan sigari bana cin goro, abu d'aya ya kawoni shi zanyi na koma, bansan bincike haka kuma bana san bin kwakwaf, kar ku sake n
aji bakin wani nan, idan ba amsa zai bani ba, kuma magana d'aya nake so ta fito bakinku akwai ko babu, itace amsar da nake so a bani, tambayata itace kawai d'akin zama ko nayi gaba.........?
Wani daga can saman bene yace ke "yar cakulkula dake
har kin san dad'in namiji ? 'Daga kaina nayi sama na kalleshi sannan nace daga ganinka gidan haya aka haife ka, kaine matsala da kanka bakaji abinda nace ba ? Akwai ko babu kawai nake so naji.
Daga bayana wani yace ki bashi amsar tambayar shi mana sai m
ubaki taki, murmushi nayi sannan na d'aga kaina sama na kalleshi tare da cewa, duk tayar abun hawa sunanta taya, amma kaga tayar daf tafi ta jirgi girma amma abinda jirgi zai d'auka daf bata iya d'auka, jirgi ya d'auke ka kuma ya d'au kayan ka, kamar dai k
ai kaga ga jibgegiyar mace a gefenka, amma a zahirance gwaram ce tunda har ka samu damar fitowa, saboda haka k'aranta ba matsala bace, abinda wata motar ta kasa sai kaga machine yayi.
Tabbas muna da masaukin ki, d'aki d'aya 5k ne a wata haka kowa
yake biya sai kuma zaki bayar da kyautar dare d'aya ga mai gidan wannan shine tsarin wannan gida me kika ce ?
Wannan ba damuwa bace amma nima ina da nawa tsarin na basu amsa, muna saurarenki suka bani amsa, gyara tsayuwa nayi sannan naci gaba
da cewa ina da ranakun aiki ina da na hutu, yau da gobe da jibi daga nan har zuwa k'arshen satin nan babu maganar kwanciya da ko wane na miji amma zai yadda daga nan zuwa sati na gaba.........? Nayi musu haka ne dan ni kwana ukku kad'ai zanyi na k'ara gaba
abu d'aya zuwa biyu nazo koya kad'ai a gidan karuwai kuma a raina bazan biya kud'in hayar ba haka na yanke..
Na saman benan yace min mi yasa kike da wannan tsarin haka ne An mata.......? Wata irin fad'uwar gaba naji tare da kallonshi da sauri d
omin ya kirani da irin sunan da Dikko yake kirana dashi, janye zance Dikko nayi a raina sannan nace idan har ruwa ya kare a cikin tanki ko ka tara abun ibar ruwa baka samun komai haka nan zaka gaji da jira ka d'auke, amma idan aka bari ya taru kana tarawa
zai cika ma duk abinda kake buk'ata, to nima haka take daga gareni karfina ya k'are dan na kwana ina aiki saboda haka a barni na huta na kwanakin dana iba,
Murmushi yayi tare da cewa gaskiya ku bata d'aki tabbas muna da masaukin ki a gidan nan, s
akaran banza na fad'a a cikin raina nace otiho dakai baka tsan tsiyar nasara ba sai zashi ganin gida, duk shelar da nayi na ce bariki tafini tabbas ka gagara ganewa da gaanin wannan sha ka tafi ne, fuska ta d'auke da mugunta nace mashi idan an bani d'akin
kai ka biya kud'in sannan kuma ka bani rance dubu d'ari, tukuicin d'aki zaka kwana biyu kana morewa dani nima daga cikin irin baiwar da Allah ya bani, dubu d'arin ka kuma da kud'in d'aki duk zan baka su idan na fara kasuwa......
Ba damuwa a bata d
'akin sama lamba 59 ya fad'a cikin zaguwa, ga *kwartuwar* shi gefe ya manta da labarinta, hawa sama nayi aka nunamin d'akin, makulli aka bani na bud'e na shiga ina shiga na kulle d'akin ta ciki.
Dudduba d'akin nayi bayan na shiga, falo ne sai d'a
kin bacci madafar abinci da bayi, d'akin bacci katifa ce irin ta "yan bodyn sch, falo tayils ne babu kujeru sai kafet, k'arewa d'akin kallo nayi sannan na koma jikin tagar d'akin na fara kallon yanda *karuwai* suke rayuwarsu.
Ina tsaye na fara
tunanin fuskar da tacemin An mata, ina k'ok'arin tunoshi kwalwata ta fara jakkancin data saba, a bayyane nace ki saurara kar kimin haka don Allah rayuwa mai had'ari na kawo kaina ki tausamin ki sanar dani ko waye waccan, kwana biyu kad'ai zanyi nabar gidan
nan amma ina so ki sanar dani ko waye shi d'in......
Bugawa zuciyata tayi tare da cewa abokin Dikko ne wallahi, shine ya raka abokin Babanki aka kaiki wurin Dikko....... Kamar kasuwa haka zuciyata da kwalwata suka fara gardama hayani ke tashi da
ga cikin kwalwata da zuciyata, yayin da kwalwata ke cewa bashi ne ba zuciyata tana cewa tabbas wallahi shine, kyarma jikina ya farayi gaba d'aya d'akin naji yana juyamin, kamar ana jijjiga ni naji anayi dan haka da sauri na dafa bango na zauna k'asa tare d
a fara karanto duk addu'ar data zo bakina......
Bayan na samu natsuwa ne, na dafa daidai saitin zuciyata da kwalwata sannan nace idan nayi muku wani laifi da Allah ku gafarceni amma ku daina dakushe wa ku barni nayi
komai cikin hikima kamar yan
da na tsara zanyi. Kuyi hakuri ku daure ku bani gudamwa.
Kwana na biyu a gidan karuwai ina koyon abinda yakaini, safe rana dare wannan d'an iskan yake kawomin abinci, a yanda nayi niya yaune zan tafi amma na fasa tafiya sai naga mai gidan bene....
... Wato mai wannan gidan na karuwai.
Da daddare misalin 9:30pm na sauko k'asa na samu wuri daga gefe na zauna banma kowa magana ba haka kuma babu wanda na kalla amma hankalina gaba d'aya yana wurinsu,
Murmushi nayi a lokacin da naji w
asu *kwarata* na ciniki, kallarni sama da k'asa kaga zubina ai kasan nafi k'arfin ka kwanta dani kace 1k zaka bani, yo wace kala gareki ni keda bakin masai baku da banbanci a wurina tunda kowa ma zuwa yakeyi ya hau ya kama gabanshi, ina ma laifina da zan b
aki 1k idan haka yayi miki in bayar idan baki yadda ba naje wurin Umma.
Mai makon naga taji haushi sai kawai tayi dariya tare da cewa shege kenan, to kawo dubu d'in, d'an sosa kansa yayi sannan yace kai nama manta dubun zan siya ma iyalina bire
di wallahi kuma machine ina baida mai amma bari dai in bada dari biyar, batayi zuciya ba tace to kawo dari biyar in, bata yayi suka shiga cikin d'akin.....
Tsoki nayi tare da ganin wallan matan aure, kuna gida kwance mazajenku suna nan wurin saka
rkarin matan da basu kaiku komai ba, kuna can kuna girman kai da kunyar banza da sakarci aje a yayo cuta a cusa muku babu gari babu dalili.
Me Allah ya rageku dashi ? Me karuwa take dashi wanda Allah bai baki ba ? Naki ma yafi nasu daraja tunda
ke ta hanyar bautar Allah zaki mik'ashi kuma Allah ya baki lada, amma matar malam bahaushe tanajin kanta yai mata girma ji takeyi idan ta nunawa mijinta tana buk'atarshi kamar zai rainata, wata ma macen idan bashi ya nemeta ba saidai ayi ta zama a haka, t
o ya nemiki jiya shekaran jiya kullum har "yar basirar dake gareshi ta kare, ko kuma sai yazo kwanciya dake ki tashi hankalinshi ki tado fitar da kila anyi sati ko wata da yin abu saboda ke kawai za'a kwanta dake, kin b'ata mishi rai yaji gaba d'aya abun y
a fita a kanshi ko kuma yayi shi ba cikin natsuwa ba, da kanki kike jefa kanki halakar da babu mai iya fitar dake sai Allah , daga haka sai shedan ya fara doka masa gangar sa ya barki yaje ya nemi na banza, dan babu zuciyat wanda shed'an baya wasa da ita.
Idan kika had'u da muguwar mace sai ta rabaki da mijin fafur ki kasa gane kanshi, daga nan sai ki fara tattara kaya ke a dole kinyi yaji. Idan an tambayeki abinda ya had'aku ki fara cewa baya dawowa gida da wuri, idan kin kawo abinci baya ci, id
an kinyi kwalliya baya yabawa, bayan duk kece babban da kika jawo ma kanki wannan damuwar...........
Mudai je zuwa zamu gano masu laifin tsakanin matan da mazan su waye masu matsala......
Ina zaune a wurin har 12:30am bai fito ba, tou me akeyi h
aka har yanzu wanda ba'a gama shi ba ? Duk gorin da yayi mata na had'a mata k'addarar ta da bakin masai batayi zuciya ba.
Lallai bariki bariki ce, mutanen cikinta suma sun barikantu kodai taji haushin abun bata wani nuna mishi damuwa ba, ina nan
zaune a wurin har mutumin da nake tunanin mutumin da nake tunanin yana tare da Dikko ya shigo,
Da fito ya shigo babu sallama sai gyara wando yakeyi kamar wani sabon shigar *kwartanci* kallona yayi tare da cewa har yanzu baki bacci ba ? Nima irin
yanda naga *karuwai* sunayi idan zasuyi magana nayi, d'an kashe idanuwa nayi cikin sigar bariki sannan nace banyi ba, to me kike jirane ? Kud'in da zaka bani ina so na shiga kasuwa gobe zanyo siyayya kasan jibi nake komawa bakin aiki na......
Mur
mushi yayi saboda yasan shine farkon layi idan na fara iskanci, kina da account ne ? Ya tambayeni ?Banda shi, to da safen zan baki idan naje wurin mai gida na, Allah ya kaimu nace tare da mik'ewa na fara tafiya cikin *kwartanci* sakaran banza ya bini da ka
llo, zakaci ubanka idan na gano ku, jibi kamar yanzu kana nan zakayi baccin bak'in ciki dan zan b'ace muku b'at kamar jirgi a cikin gizagizan sararin samani............
07/08/2019
⚜
*BRILLIANT WRITERS ASSO*
🖊
_-{{Pen of fre
edom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_
👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿
------ 9
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, itace kad'ai abinda Dikko yake ta maimaitawa a cikin wannan tsalelen dare,
Juyi yakeyi sosai a saman gado sai kace macen
da ciwon ciki ya taso ta gaba, kifa kanshi yayi a saman lallausan bargon dake kusa da kanshi ya goge hawayen dake bi masa idanuwa.
Allah na tuba..., ya fad'a a bayyane tare da gyara kwanciyar shi, girgiza kanshi yayi , yayin da zuciyarshi da kwakw
alwar shi suka hasko mishi abinda yayi ma Sultana, a hankali ya lumshe idanuwanshi na tsawon lokaci sannan ya fad'a a bayyane baiwar Allah baki dace mahaifi ba,
Sai kuma Allah ya jefoki a rayuwar Dikko yayin da nake nemanki, kika zo a daidai loka
cin da na d'auki hud'ubar shaidan , Allah ya baki hak'uri kinji, ya k'arasa maganar tare da bud'e idanuwanshi duka da sukayi jajir saboda kuka........
Ko ina kike ? Me kike yi yanzu ? Wane irin bak'in ciki kikeji idan kika tuna dani ? Ki zama m
ai yafiya a rayuwarki, manta da Dikko ki fuskanci rayuwa, ina nan ke kuma ina ki ke .....?
Ina gidan karuwai,.... Ina shiga d'akina na mayar da k'ofa na rufe, ya zama lallai na gano waye mamallakin wannan gidan, sannan idan har na karb'i dubu d'
ari a hannun wancan garan me ya kamata nayi da ita ne ? Ansar kud'in sune wahala Sultana anso su tuk'una idan suka zo hannu ba'a rasa abinda za'ayi ba, wannan shine shawarar da zuciyata ta fad'amin.
Ajiyar zuciya na sauke tare da hayewa saman "ya
r k'aramar katifata na kwanta bacci.
Da safe ina tashi sallah asuba nayi, na dad'e ina zaune a saman abin sallah ina addu'o'i na neman tsari d'aukaka farin jini da kuma k'war jini a harkar bariki.
Sai 7:00am na tashi daga saman abin sa
llah, toilet na shiga nayi wanka, ina fitowa na shirya a gaggauce domin akwai inda nake so naje.
Ina gama shirina na fito sanye cikin hijabina, sai nik'af dana dabkakawa fuskata, ina rufe d'akina mai kirana da irin sunan da Dikko yake kirana yazo
.
A k'ofar d'aki muka gaisa daga gaisuwa ban sake masa magana ba naci gaba da rufe d'akina.
An mata ina zakije haka da safe ? Ban kalleshi ba nace zanje wurinka ne dama, murmushi yayi tare da cewa kuma gashi nima nazo wurinki yake nan .?
Babu wani damuwa zamu iya maganarmu anan, mudai shiga daga ciki zaifi ko ? Ya fad'a yana kallo na, gyara tsayuwata nayi tare da cewa kayi hak'uri gaskiya na fito bazan koma ba, yana k'ok'arin bud'e bakinshi yayi magana nace kayi hak'uri da Allah b
ana san magana tayi tsayo na wuce, ina k'ok'arin tafiya yace d'an tsaya kiji mana.
Tsayuwa nayi ba tare dana juyo ba, am dama cewa zanyi idan kina da hali anjima zamuje wurin Alhaji yace yana san ganin ki, ba tare dana juyo ba nace wane Alhaji ne
? Mai gidan nan, na bashi labarinki shi kuma ya matsa saiya ganki.
Saida nayi shiru na wani lokaci sannan nace wurin k'arfe nawa zamu je kenan ? Yanzu ma dan zaki fita da munje saboda ba'a gida ya kwana ba yana nan bayan gidan nan yana tare da ba
k'i da sukazo wurinshi manyan alhazawa ne masu kud'i da suka ansa sunansu a kud'i, d'an mugun murmushi nayi a cikin nik'af ina sannan nace tou kai ya maganar kud'in da zaka bani ne ? Suna cikon mota muje, murmushin zalinci nayi irin wanda naga mugu Dikko y
anayi sannan nayi gaba abuna ya biyo bayana.
Cikin motarshi ya d'aukeni, muna shiga cikin motar na yaye nik'af ina tare da kallonshi sannan nace niko na tambaye ka mana ? Tambayarni mana ya fad'a a daidai lokacin daya fara tafiya da mota.
Shiru nayi ban sake magana ba, shine ya gaji da shirun yace kinyi shiru kuma ! Ey zan tambaye ka amma ba yanzu ba dan na d'auka ne baka san tambaya da surutu ne kamar yanda nima bana so, amma tunda ka bani izini zan rik'a tambayarka a duk lokacin da tamba
yar yazo min, amma dai ya sunan ka ...?
Murmushi yayi sannan yace suna na Umar, gyara zama na nayi tare da cewa me yasa Babanku yasa maka suna Umar ne ? Dariya yayi sosai tare da cewa sunan ubangidan shi ne,
Zaici gaba da rattafo min baya
ni na dakatar dashi ta hanyar cewa barmin bayanin haka nan zan tambayeka wani lokaci, babu gardama ya kame bakinshi ta hanyar yin shiru....
Har muka isa bakin get in gidan babu wanda ya sake magana daga ni harshi, horn yayi mai gadi ya bud'e mana
muka shiga, gida ne had'ad'd'en gida na "yan gayu yasha ado da shuke shuke na filawowi, daga gefe kuma wasu irin lafiyayun dawakai ne tsabtatacci kuma k'osashshi aka