Showing 45001 words to 48000 words out of 178087 words
yanar giza gizo dan inyi suna, kai kuma kana da dama d'aya tak data rage maka, idan har ka bani naira miliyan d'aya nayi maka alk'awari zan goge shi sai in hak'ur
a basai nayi suna a duniya ba...... Idan kuma baka dasu in turawa "ya "yanka
ko suna da kud'in fansar ka ! Sultana, Sultana ce yarinyar mai dogon zamani, idan kuma kace zakayi gigin sako hukuma a ciki na riga dana turama k'awata nace da taji an kamani firr zakaji su sun watsu a duniya kamar saukar tsuntsaye. Ka huta lafiya habibin
ah muah_
💋
Goge zufa Alhaji yayi tare da cewa Allah ka tsinewa yarinyar nan albarka, shegiya tsinanniya ubanta da uwarta basuyi addu'ar kwanciyar aure ba yayin da zasu kwanta Allah ya basu cikin d'ebabbar albarkar yarinyar nan, a daidai wannan l
okacin kiran Dikko ya sake shigowa.
Jiki a sanyaye Alhaji ya kalli wayar tare da cewa mai gida kayi hak'uri wannan abun kunya ina za'a dashi na watsu cikin duniya ina zina, abun bak'in ciki da d'iyar da nayi d'iya da ita, garin ciye ciye na har n
aje na ciwo ma kaina bala'e, kila sai ta k'arar da arzik'ina, kuma tace idan na fad'awa hukuma taba k'awarta vidion zata yad'ashi wannan shine ciwo ya riga ajali zuwa...
Kuka Alhaji yayi tayi tare mitar ya shiga 3 ya bani ya lalace, wannan labarin a
bun kunyar waye ma zai fad'a mawa bare kuma yasa ran zai samu wata sahihiyar shawara, kai ya bani ya bani ya bani........
😰🙆🏻
♂
😭
, a daren nan Alhaji baiyi bacci ba kuma baibi kiran Dikko ba, wayar Sultana kuma ya kirata yafi so adadin yawan dutsinan da
ake jifar shedan dasu amma maganar dai d'aya ce cewa a kashe.......
Da safe , tunda nayi sallar asuba na koma bacci, can cikin bacci naji ana dukan k'ofar d'akina, addu'ar tashi daga bacci d'auke a bakina bayan na gama nace waye ? Na tambaya cikin
muryar bacci tare dakai idona saman agogon dake lik'e a saman bangon d'akina k'arfe 10:36am, cikin muryar murna Nana tace "yan sanda aka d'auko miki Sultana....
Murmushi nayi tare da jawo wayata na kunna sannan nace ma Nana da Allah kije kice way
e ya d'aukomin "yan sanda ? Cikin farin ciki ta koma zaure sannan ta tambayi d'an sanda waye yake k'arata ?
Fad'a mata yayi tayo cikin gida da har yanzu tanajin dad'in k'arata da akayi, a bakin k'ofar d'aki ta tsaya sannan tace wai abokin Babanki
Bello, jinjina kaina nayi tare da cewa tou ina fitowa....
Data na bud'e na nemo lamba 2, hotunan dana d'auke shi jiya na tura mishi tare da yin voice note na antaya ma banza, ina gamawa na kashe wayata, saida nayi wanka naci gayuna na watsa turar
e na d'auku iyakar yanda hankali baya tunani duk wanda ya ganni saina burgeshi, fitowa nayi banma kowa magana ba na tunkari zaure, dan zuwa wurin hukuma a yanayin talauci yana jawo ma mutum raini....
A k'ofar gida na samu d'an sandan nan ya gama
shak'e b'acin rai daga gani yana jira muje can yaci uwata, a yangance na fito cikin aji na kalleshi tare da cewa "yar labai barka da aiki......
'Dan sakin fuska yayi tare da cewa yawwa, gaishe shi nayi tare da ce masa nice Sultana, kallona yayi sa
ma da k'asa sannan yace tou hajiya muna gayyatarki zuwa ofishinmu ai anyi miki bayanin mai k'ararki ko ? murmushi nayi tare da cewa babu damuwa muje amma Allah yasa ba'a cikin motar "yan sanda zaka d'aukeni ba, murmushi yayi tare da cewa ai hajiya napep z
amu shiga, ajiyar zuciya nayi cikin sigar jan hankali sannan nace tou ai har naji natsuwa.
Napep muka hau muka nufi c p s , kuma nice na biya kud'in 1k ne na bayar kuma daya anso canji nace ya rik'e yasha ruwa, tunda muka fita a napep gaba d'aya wurin s
aida hankalin kowa ya dawo kaina, na farko dai ga wanka ga gayu ga k'amshi uwa uba kyau Allah yayi min kyawun da mutum baya gajiya da kallona, ga gashina na tik'ashi nayi mishi wani irin parking irin na wayayyin mata, baka isa ka rainani ba ko waye kai dom
in sitirar dana saka ita kad'ai ta isa ka gane ni ba sa'ar wasan yaro bace ba.....
Ofishin d c o muka nufa, a ciki na samu Bello zaune tare dashi da wasu abokan Babana, sallama nayi sannan na gaishesu dukansu cikin kyakkyawan yanayi, bayan mun gaisa
nima na samu wuri na kame kamar yanda naga kowa yayi.....
Kallona d c o yayi bayan ya gama karanta wata takarda dake gabanshi sannan yace Maryam miya had'aki da Bello ne ? Murmushi nayi tare da gyara zamana nace ranka ya dad'e ai Baba Bello abok
in kasuwanci ne, halak'a ta mutunci ne a tsakani na dashi bayan wannan babu komai....
D C O yace tou jiya ina kika had'u da Bello ne ? Ranka ya dad'e majalissar su naje gaishe su, bayan mun gaisa kuma ya tambayeni nayi aure nace masa A , a, ya
ce yanzu ina nake zama ? Nace masa ina zama a tsohuwar anguwarmu daya sani, ya tambayeni ko ina kasuwanci ne ? Nace masa Eh yace me nake siyarwa ranka ya dade nace masa karuwanci nakeyi, tsakanin mai saye da mai siyarwa ai babu fushi anan muka daidai suka
d'aukeni muka tafi wani gida, nuna yawan duka abokan Babana nayi sannan naci gaba da cewa ranka ya dad'e dukansu nan babu wanda baiyi ba kuma duk saida suka k'ara zagayawa "yar labai, kuma gasu nan ka tambayesu idan nayi musu k'arya. Kuma cikon kud'in ma h
ar yanzu basu bani ba..
Kowansu zaro ido yayi tare da dafa k'irji cikin yanayin mamaki yace ke mune mukayi iskanci dake ? 'Daure fuskata nayi kamar gaske nace aini banajin kunya tunda dai banji tsoron Allah ba nayi zina wallahi banajin kunya gab
an kowa in fad'a nayi, kunyi mana ko k'arya zan muku ne ? Lokacin da bakuyi ba nace kunyi ?
Gaba d'aya wurin hayaniya ta tashi har bakajin bakin wani, d c o ya dakatar dasu tare da cewa suyi mishi shiru, bayan kowa yayi shiru ya kalleni sannan ya
ce ke Sultana Bello yana tuhumarki kud'in shi da kika d'auka. Cikin natsuwa nace wasu iri kud'i kuma ranka ya dad'e ?
Bayani d c o yaimin kamar yanda na sani, jinjina kai nayi tare da cewa idan sun gama k'arata nima zanyi k'ararsu saboda b'atami
n suna da sukayi, ranka ya dad'e a gaban idon waye na d'auka kud'in ne ? Nifa bana sata amma ina neman maza gaskiya, duk abinda nakeyi bana jin kunyar asan inayi domin dai duk sana'a sunanta sana'a, idan ma na d'auka aka tambayeni idan nasan na sata kawai
zan dawo musu da kayansu in basu hak'uri tunda karuwanci da nakeyi ai ban b'oye ba na fad'a tunda ba abun kunya bane....
Tambayar Bello D C O yayi ko yana da wata sheda ne ? Baida ita tunda an tambayi mai gadi yace shidai bai ganni cikin mota ba,
duk iyakar binciken da akayi dan asamu wata sheda babu ita, dan haka aka rubuta takarda cewa an janye k'ara, bayan an gama rubutu aka bani na saka hannu da larabci nayi sigining ina, an mik'e za'a tafi nace ma d c o naga fa sunamin wani kallon hadarin kaji
sufa fita ido na, d c o yace ai duk an rubuta, nace to ranka ya dad'e cikon kud'ina kuma sai yaushe zasu bani ?
Hak'uri d c o ya bani tare da nunamin tunda anyi masa sata inyi hak'uri inma barshi da ramuwar biyan kud'in mutane, babu kunya ba komai
nace kenan ni yanzu ranka ya dad'e sunci banza ? Duk wanda ke cikin office in saida ya kalloni, nace ranka ya dad'e kafa duba lamarin nan gaskiya ni ba'amin adalci ba, shiru wurin yayi wutar kowa ta d'auke, murmushi nayi tunda basu da amsa nace nawa ake y
ankar sammaci ? Sammaci ma ake cewa abin ko miye ?
A kotu ake yankar sammaci d c o ya bani amsa tare da fad'amin abinda ake kiran nasu da turanci, oho dai da yake kan baya ganewa kasa maimaitawa nayi saidai kawai nace nawa ne ? Kud'in aka fad'amin
na bud'e jakata na bada sannan nacewa d c o ga wanda nake k'ara nan Bello ina tuhumarshi akan b'atar mahaifina daya tafi babu wanda yasan ina yaje..........
21/08/2019
*JAMILA MUSA...*
⚜
*BRILLIANT WRITERS AS
SO*
🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_
👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmee
nat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿
------ 15
*_Had'inkai group ina tare daku aminan albarka, Allah yabar so da kauna ubangiji ya k'ara yadda da aminci, HALIMATU SADIYYA {{ Leema }} HABIBA IDRIS {{ Hubbi
e }} HAUWA'U USMAN {{ Smasher }} MAIMUNA O . G {{ Aunty Munari.... }} muna tare_*
*_Mrs Abdul-aziz ina godiya sosai da dogon sharhi kuma ngode sosai page 14 na baki shi kyauta...._*
Lahaula walakuwata illah billah, kiji tsoron
Allah ke uwar masu gida a ina na b'atar da mahaifinki ? Sharri zaki min ? Kiji tsoron Allah in babu nan akwai ranar hisabi duk wanda yaci zalin wani daidai da kwayar zarra ubangiji bazai barshi ba, ki daina ganin kin samu dama ta tak'in lokaci yasa ki mant
a da rayuwar gaba, karki biyewa zuciya ki kafa abinda zaisa kiyi nadama wata rana.....
Gaba d'aya jikina yayi sanyi tsoron Allah ya kamani nasan k'azafi da sharri ba abu ne mai kyau ba, kuma addini na bai koyar dani haka ba, amma d'an kamewa na
sakeyi sannan nace ni rayuwar dad'i baza ta tab'a zama takaitacciya a wurina ba, jin dad'i na d'aura insha Allah daga nan har zuwa ranar da numfashi na zai k'are, ina Babana yake wai ina ka kaishi ne............?
Cikin nadama Bello yace na ran
tse da ubangiji daya bani aron lumfashi ya bani aron lafiya nake ganinki nake kuma saurarenki ya bani hankali da tunani idan nasan inda mahaifinki yake Allah ya tsinemin albarka. Wallahi Uwar masu gida bansan inda ya tafi ba na rantse miki da girman Allah.
Tausayi ya bani yana rantsuwar yana wani kwantar dakai kamar an ritse macen da tayi cikin shege ta haihu kuma ta kashe d'an....
Kallon D C O nayi tare da cewa "yar labai shikenan tunda yayi rantsuwa baiyi ba kawai na janye, zan iya tafiya ? N
a tambayi D C O, cewa yayi na zauna zamuyi magana, zama nayi su kuma su Bello aka sallamesu suka tafi ni kuma naci kud'in banza Ehe....
Ta wutsiyar idona na kalli d c o bayan fitarsu Bello domin ina son na gano tashi manufar a kaina, murmushi na
yi bayan na gama fahimtar shi, a bayyane nace lamba 3 tazo kenan, ajiyar zuciya ya sauke tare da tattaro duka hankalin shi wurina yace ranki ya dad'e ya hak'uri da jama' a ? Kallonshi nayi ba tare da nayi magana ba domin wallahi tsarin bakinshi kwata kwata
bai burgeni ba. Amma ba komai zan hak'ura nayi maleji dashi haka nan saboda idan na taro watan aug zai gina min gada nabi na wuce ba tare dana sha k'ashin ruwa ba....
Wayan cewa nayi tare da gyara zama na nace Allah dai yasa aiki zaka d'aukeni
mai girma d c o, murmushi yayi tare da komawa ya kwanta saman kujerarshi irin masu juyawa d'in nan, sannan yace wai gida zan saukeki idan ba matsala, d'an yamutsa baki nayi tare da cewa na gode amma ni ba gida zanje ba...
Ina zakije haka da rana
? 'Daure fuska nayi dan ya fara cika min ciki nace wurin aiki zanje, wane irin aiki ? Tsoki nayi tare da cewa kai komai sai anyi maka b'aro b'aro kake ganewa ko ? Tou abokin lalata zanje nema.....
Murmushi yayi tare da cewa ke bakya gajiya ? C
ikin wuta wuta nace ka tab'a ganin inda mutum yake rayuwa babu abinci ? Yace a , a, nace tou ni da kud'i da karuwanci sune abokan rayuwata, domin sai nayi nake samu sannan naci nasha na kuma d'aura har in fito na burge abokan harka , idan kuma kaima d'an
hannu ne karka wani cuci kanka kawai kayi magana idan kajira sai an maka tayaki tou fa lallai zaka kwana da yunwa, amma kayi hak'uri da tambayar da zan maka tsakanin ka da Allah nawa ne albashin ka...... ?
Kallona yayi tare da cewa hajiya maryam kenan ,
miya shafi albashi da harkar bariki ne ? Bai shafa ba amma ni ina duba nasabar namiji da cancantar shi kafin wata sahihiyar mu'amula ta shiga tsakani na dashi, dan duk wanda ya jawo maganar aure a rayuwarshi tabbas ya tara abun hidima, bata yuwuwa na biye
maka ka k'ok'ar dani ba tare da ka sake bani kud'in da zan sabon fenti ba, dan kai kanka da ban d'aukar maka ido ba duk yanda nake barikin baza ka taya ba,
Kallon agogon dake d'aure a tsintsinyar hannu na nayi tare da cewa zama wuri d'aya tsaut
sayi inji kifi, malam d c o zan wuce ka rubutamin number ka a jikin takarda idan ayyuka sukamin sauk'i akwai dawowa......
Babu musu kuma ba tunanin komai ya d'auki biro da takarda ya gwagwad'amin number wayarshi, ansa nayi tare da mik'ewa tsaye sa
nnan nace sai ka jini, baki bari mu tafi in ajiye ki ? Ya tambayeni, juyawa nayi na fara tafiya tare da cewa ban hawa mota sai napep a daidai lokacin dana fice daga ofishin....
Ina fitowa wuri na samu na tsaya, wayata na fiddo nayi saving in no d
c o da lamba 3 , sannan na kira wayar Alhaji, babu b'ata lokaci ya d'auka tare da cewa ranki ya dad'e tun jiya inata kiran ki wayarki a kashe ko yau da safe ma na kira a rufe.... Ban bashi amsa ba nace kawomin kud'in yanzu nan ina nan c p s ina jiranka ku
ma karka b'atamin lokaci, ina fad'a na kashe wayata......
Lambar Bello na kira amma bai d'auka ba, daga kira d'aya nima ban sake kira ba, domin dai nasan idan yaga abunda na tura mishi shi da kanshi zai nemeni, k'ok'arin maida wayata nake cikin
jikka naji ana cewa shegiya k'awata kece kika koma wata hajiya haka ? Da sauri na d'ago kaina domin jin muryar Amisty da nayi...
Cikin farin ciki muka rungume juna, bayan gaisuwa sai kuma muka shiga firar duniya, yayin da nake tambayarta wane c
i baya ta samu na bariki naga har yanzu bata fara hawa mota ba, ajiyar zuciya Amisty ta sauke tare da cewa kinsan mazan babu kud'i hannunsu kullum tsuwwa da kukan babu......
'Daure fuska nayi tare da cewa waye ya fad'a miki ana hawan jirgin sam
a bashi ne ? Ai filin jirgi ma baka shigarshi dole sai kana da tikitin tafiya, haka nan kike basu suna hayewa basu baki kud'in mai, tou ina uwar d'akin taki ne ko bata nan bata fad'a miki illar maza ba ? Haba Amisty idan baki ridowa da yawa wallahi bariki
kasheki zatayi, niko kin ganni nan ni zanyi gwanjo bariki kafin ta wurgar dani gefen titi, kinsan bariki bata da tabbas d'auka da ajiyewa gareta, ni zan kashe bariki bazan yadda ta kashe ni ba, zanyi amfani da talata ta kafin laraba ta, ta riskeni, wannan
uwar d'aki taki k'atuwar jahila ce batayi karatun komai ba haka nan ta tara yawan dalibai, har yanzu kuna da dama ki nemi canji makaranta ki dawo makaranta ta zan baki ilimi akan namiji, kud'i kike so ko suna ......?
Horn Alhaji yayi da mota wan
da tun d'azu yakeyi amma magana ta hana na saurareshi, juyawa