Showing 3001 words to 6000 words out of 178087 words
raina ya baci kuma nayi alkawari ko zai kasheni tunda har ya tabomin Babana sai naci uwarshi a safiyar nan.
Da gudu nabi motar ina watse hannuwa na yanda ake zagi dakkuwa, ina zaginsa, shima Baba biyoni yayi
da gudu cikin tashin hankali, yana Mamana dawo, wanda yayi nisa bayajin kira, a kofar gidanshi da yake kiwon dokunan shi anan Baba ya sameni ya rikeni, shi kuma ya fito daga motar da bulala dorina irin wacce ake dukan dokuna da ita.
Zagin dana ta
ho inayi shi ya jawo hankalin mutane yasa duk mutane suka fito daga gidajen su, wanda ke waje suka iso wurin da muke dan ganin kwam,
Rikeni sosai Babana yayi tare da rufemin baki saboda yasan ban iya zuciya ba, shima abokansa da sauri suka rik
eshi
tare da cewa *Dikko* karka daketa dan Allah yi hakuri, Babana kuma cewa yakeyi ranka ya dade kayi hakuri don Allah bata san kaine ba,
Raina baci yayi ganin kamar mahaifina yana bawa yaron da haifa hakuri, dan haka na bambare hannun Babana dag
a bakina nace, nasan kaine kuma na zageka, ban kara maganar ba Babana ya wanka min mari.
Tunda nake a duniya magana mai daci ko muni Baba baya fadamin ita, yana tattalin rayuwata yana kaunata amma yau saboda wani sakarai ni Babana ya daka,
In
a cikin wannan bakin cikin Baba ya bashi hakuri da taimakon abokansa ya hakura suka ja banza suka shiga gidan da yake kiwon dokuna,
A raina na dauka alkawari yanda Baba ya dakeni saboda Dikko saina rama dukana a wurinshi...... Hannuna Baba yaja
muka taho yana bani hakurin marin da yayi min, wai yayi haka ne saboda Dikko kar yayimin wani abu, saida ya sakani napep sannan ya koma gida,
Cikin bacin rai na tafi sch amma tabbas Dikko sai yaci kaniyarshi.........
{{{}}} {{{}}}
30/07/2019
Meelat Musa ce
🤙🏻
⚜
*BRILLIANT WRITERS ASSO*
🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA
* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_
👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿
------ 2
Duk sanyi sanyin da akeyi saboda ruwan da aka kwana kwararawa a daren
jiya hade da wani irin iska mai dadi amma Baba zufa yake kamar an tsare mai jegon da a saman gadon kara......
Cikin tashin hankali ya fara cire kayanshi yana dorawa a saman katanga, sai bakinshi dake motsawa babu wanda yakejin abinda yake fada sa
idai lokaci bayan lokaci yakan goge zufar data bulbulo daga jikinsa..
Ganinshi cikin wannan yanayi ya dagawa kowa hankali, gashi ya fita da farar shadda amma ya dawo da shadda kamar miyan goro,
Idan yana cikin yanayin fushi baya so
kowa yayi masa magana haka kuma bayasan ganin kowa kusa dashi, mata da "ya "ya suka gane haka shi yasa babu mai shiga sabgarshi, idan yana cikin yanayin damuwa Sultana kadai ke zuwa wurinshi ta bashi hakuri kuma ya sauka saboda soyayyar dake tsakaninshi da
ita,
Har na isa makaranta tunanin yi hakurin da Babana ya bawa jakin dana manta sunanshi nakeyi, sunanshi ya bacemin kwata kwata na manta sunan da aka kirashi dashi, nidai Allah yayi min jakar kwalwa, saboda ko "yan gidanmu ba dukansu nasan suna
nsu ba, amma na alakanta abun da yawan da muke dashi, yayin da wasu suke ganin rainin hankali ne......
Ko a aji naso na bawa Amisty labari amma na manta sunan wanda zan fada mata, Amisty itace kadai abokiyata duk a ajinmu, abinda kuwa yasa na zabeta tan
a da kokari sosai kuma idan ana jarabawa tana bani satar amsa,
Amisty irin yaran nan ne da idonsu ya waye tun suna cikin zanin jarintaka, bata da labari sai labarin maza, bata da aiki sai kallon B F, duk hotunan da zaka gani a cikin wayar Amisty
hotunan tsiraici ne, walau nata walau na wasu, babu mai tarayya da ita saini kadai domin an dade da canfata cewar tana lesbian, nikam babu abinda ya dameni idan dai zata bani shayi nasha a tashi jarabawa ta bani satar amsa idan anyi rubutu nima tayimin a l
ittafina shikenan banda wata damuwa.
Lokacin dana shiga aji har malami ya shiga ya fita, ga rubutu nan a saman allo, bana gane sunan subject haka nan kawai na kalli allon nadan basar tare da cewa ashe malam harya fita.
Da Eh kusan rabi
n ajin suka amsamin dan ina da masoya sosai, wasu saboda kyauna suke sona yayin da wasu kuma gashin kaina yake daukar musu hankali, okey shine abinda na fada kamar wata shegiyar baturiya dan itama okey din na dade ina koyonta a bakin Amisty dakel dai na sa
mu ta zauna ram a cikin kaina, idan na fadi okey zakayi tunanin nasha turanci na koshi, amma babu abinda nake ganewa duk duniya sai sallolina biyar da Allah yasa na iyasu saboda nacin zuwa islamiya.
Ina zuwa mazauni Amisty tace yau ina kika baro
mana Baban namu ? Wata irin faduwar gaba naji dan nasan Babana shima ba karamin tantirin dan iska bane, kodai itama Amisty Baba ya zagaya ne ?
Kinyi shiru, Amisty ta katsemin tunani na, maganata daukewa takeyi duk lokacin da ake tambayata abu, i
na da nawar magana akan magana karama sai inja lokaci sosai, inayin in ina kadan wannan dalilin yasa ban cika yawan magana ba.
Dan gajeren murmushi tayi tare da matsawa, zauna tacemin tare da maida hankalinta akan allo taci gaba da kwafar note. Zama nay
i tare da cewa wane malami ne ya shigo ?
Malama dai , wace malama ce ? Malamar English ! Me take koyawa na tambayi Amisty, turanci ta fadamin a takaice, murmushi nayi tare da cewa yarinya ai na gane dama dan inji idan zakiyi min karya.
Ked
ai kika sani, ni ciro littafinki na rubuta miki idan kin gama rainin hankalin naki, Amisty ta fada........ Bude jakata nayi sawon wani lokaci na kasa gano littafin da Amisty tacemin, tun ina dubawa a cikin jaka har na fito da duka littafan banga littafin t
uranci ba, dan gajeran tsoki nayi tare da cewa Amisty inajin nabar littafin a gida gaskiya.
Daukar littafin tayi domin shine a sama, ajiyar zuciya nayi dan nima ta gane wata jar wuya ce , nace da yake jiya nayi karatu na dauka na barshi a gida ne
, tou kawai tacemin bata sake magana ba,
Haka malamai mata da maza sukaci gaba da shigowa har aka tashi daga makaranta, a bakin get din makaranta na tsaya ina jiran isowar Babana , tabbas nasan zaizo duk inda yake naji yana kusa dani yana zuwa ba
da jimawa ba.
Banfi minti 2 ba Babana ya iso cikin wata irin kafirar mota yanzu ma yasha wanka ya murza wata irin dakekiyar shadda, sai kasaita yakeyi, murmushin jin dadi nayi domin dai
Babana ya kankaro min mutunci na idan yayo wanka saboda dan
gayu ne na koyi a idon duniya.....
Cikin farin ciki na isa jikin motar na bude gidan gaba na wani kame abuna, zugar kawayena ne sukayo kanshi suna gaishe shi kamar yanda suka saba idan yazo daukata,
Dan murmusawa kawai yakeyi tare da k
arkacewa cikin izza ya jawo wasu irin "yan dubu dubu wanda shi kanshi baisan ko nawa bane , Amisty ya mikamawa tare da cewa ku saka kati.
Yana basu bai jira godiyar da suke mishi ba yaja mota muka tafi......, ba'a hana alkairi amma inajin bakin cik
in abinda yakeyi, yabar gida da yunwa yazo waje yana alkairi, gida bai koshi ba yakai ma na waje banda gori da zagin iyayenmu babu abinda akeyi a cikin anguwa cewa Babanmu yana tsaye akanmu amma duk mu tsinannin Allah ne mu , haka zaisa ayi ta shiga da buh
un na, na shinkafa gero masara katin katin na madara sugar da komai na sarrafawa idon duniya sun gani haka zai biyo dare ya kwashe abinshi yaje ya siyar wannan rayuwar zalinci ce, kuma bai sani ba kanshi kawai yake yaudara,
Kasa hakuri nayi nace gaskiya
Baba ni kadaina zuwa daukoni makaranta daga yau, ba tare daya kalli inda nake ba yace miyasa Mamana ? Kawai banajin dadin abinda kake ne , me nakeyi wanda bai miki dadi ba ? Wannan kudin da kake bayarwa dama gida kabawa su Inna sukaci abinci gidan kowa yu
nwa ta kamashi babu mai wani sahihin abinda zaici maganar daya ce kullum daga gari sai kanzo.
Dariya yayi sosai tare da cewa Mamana kenan, aisu wannan mutane basa godiyar Allah, kima daina biye musu dan kona basu kudin cefane makalewa sukeyi, d
uk wanda kika gani a cikinsu daga mai tumaki goma sai mai shanaye babu adadi, idan na basu kudi boyewa sukeyi su hana ku abinci, suna can sun sayi dabbobi sunkai kauyika an boye musu, idan kuma kina magana akan abinda akayi ma wani kuma wannan halin shi a
ke kiran da hassada idan kikaga anyi ma mutum alkairi koya samu wani abu kikaji bakin ciki a zuciyarki shima hassada ne, kuma ita hassada tana cinye kyawawan ayyuka ne kamar yanda wuta takecin karmami, kuma yawan surutu yana sa mutum ya zama sakarai , ki d
aina hassada kuma bakinki shiru akan fadar wasu maganganu akaina idan kinki ji kuwa jahannama tsaye ko kina san ki shiga wuta ne uwar masu gida ?
A , a Babana, amma zan fadawa su Inna gaskiya su daina irin abinda sukeyi zalinci ne, abun tausayi
Baba kaji yaran nan suyi ta kukan yunwa wallahi ni har tausayinsu nakeji, kyalesu Mamana kina iya fada musu gaskiya suji haushinki barsu da halinsu................Maganarsa ta kare ne a daidai lokacin da muka tsaya wata majalissa.
Fita muje,
fitowa mukayi daga cikin motar muka tunkari taron dandazon mazan, kallo daya zakayi musu kasan cikakkin "yan tasha ne ko wannensu ya koshi da iskanci,
Gaishe su nayi tare da matsawa daga gefe na zauna, kai bata abincin nan taci mu wuce, Babana
yayi maganar a daidai lokacin da yake zama,
Mikomin abinci akayi a cikin ci ka yada, { take away } gyara zamana nayi tare da juyawa inda babu mutane naci gaba da aiki, daga nan bansan abinda yaci gaba da faruwa ba, saidai naji hayani tayi yawa
sosai anata bawa Babana hakuri ana rirrikeshi.
Cikin tsananin bacin rai yake cewa da Allah ku sakeni wallahi saina kwakwale mashi idanuwa tunda nayi rantsuwa saina makantashi duk cikar garin katsina babu wanda ya isa ya hanani aikata abinda na
yi niyya, da sauri na tashi nayi wurin Babana ina bashi hakuri,
Abokin fadan Babana yake cewa, yo kai "ya "yan wasu nawa ka batawa rayuwa, saini kawai dan na kalli diyarka nace babban lambu zaka nunamin rashin kunya, cewa nayi zan shiga ciki ?
Yabawa fa kawai nayi.... Sai kawai hankali ya tashi ?
Sanin kanka ne duk kasuwar data burgeni saina ci ta hanyar shiga inyi siyayya a cikinta, duk gidan giyar daya burgeni idan na shiga saina sha kwalba biyar karanci kenan idan banda kudi, haka k
uma idan naga gidan karuwai zan shiga ne inyi ta ciyayyar abinda ya sawwaka ba tare dana gajiya ba,
Ka sani nima nasan haka, tunda saina gama nake ma gwanjon mata, banyi maka shamaki da matana ba haka diyana, kenan yanzu idan nace ka bani aron Su
ltana mu bata dare haka zakazo bakin kofa kayi tamin babatu ?
Da sauri Babana ya rufe idanuwan shi tare da kauda kanshi gefe guda, tunda ni bansan abinda ya assasa fitinar ba, tou miye b'ata dare ? Kila shaye shayen su suke nufi,
Jinji
na kai Babana yayi tare da cewa kaci sa'a Mamana tana kusa amma zan maida ita gida na dawo na nuna maka karyar barikanci, yana fadar haka yaja hannuna mukayi gaba, har muka iso gida baiyi min magana ba, saida ya tabbatar na shiga gida sannan ya koma,
Da sallama na daga buhun kofar gidanmu na shiga, gaba daya gidan suna tsakar gida uwaye da yara, yaran mazansu da matansu sun gurfana gaban wani dakekin mutum bakikkirin da cikinshi kamar ace Allah saukeshi lafiya, ni a tunani na assembly ake musu sa
ida naga Inna na tuna ba makaranta bace.
Saida nazo daidai inda suke nayi musu sallama kamar yanda na saba, ina kokarin wuce yace ke zonan, ban
kalleshi ba kuma banzo ba haka kuma ban tsaya ba naci gaba da tafiyata na kusa shiga dakinmu naji
yace waccan yarinyar ta raina mutane wallahi da nayi niyar yin hakuri amma na fasa sai kun tashi kunbarmin gidana.
Hayani ta kwace bakajin maganar wani duk maganar ta koma iri daya yi hakuri , Allah ya taimake ka Allah ya kara arziki ka taimaka
dan Allah karka tashemu, kaji hauka akan wannan rubabben gidan suke wani hadashi da Allah yayi hakuri, Allah ma yasa ya tashemu nayi addu'a ta a bayyane,
Zainab ce ta tashi taje wurinshi tana wani irin karye karye, sai kace karyar gidan karuwa ta
ga maza, magana tayi mishi babu wanda yaji abinda tace, saidai suka fita da mutumin, ganin tafiyarshi yasa kowa ya tashi yaci gaba da sabgar gabanshi,
Babana da Zainab bansan yanda suka kare da mutanen su ba, haka Dikko bansan inda yake ba
, dan an dauki wani lokaci banji labarin yazo anguwanmu ba,
Kwanaki da dama sun shude, rayuwa tana tafiya babu abinda yayi gaba sai ci baya ake samu, amma ni na samu ci gaba na rayuwa domin dai Babana ya siyamin sabon machine kamar yanda yayi al
kawari, a cikin matanshi kuwa maman fa'iza ta samu karuwa ta aihuwa, yanzu mun zama mu hamsin da takwas cas a gidanmu,
Zaune nake a kofar dakinmu ina yanke farce na, "yar kyakkyawar magena tana shan madara, Baba ne ya siyomin madarar da yawa
nake bata danni yanzu na daina tausayin "yan gidanmu tunda na gane duk munafikai ne, Kuma Babana ina gani duk safiya yana basu kudi amma bansan ko nawa bane,
Kadangare ne ya fado daga saman bango fef, yana ganin mage ya ruga, ita kuma daina s
han madarar tayi tabi kadangaren da gudu, nima binta nayi ina kiran "yar madara' dan bana so tana cin kwarika, kadangare ya rugawa mage, ni kuma nabi magen haka muka fita a guje mu dukanmu muna gudu a tsakar santa....
Shima a guje ya shigo kamar
yanda ya saba, ganin yanda mutane ke rike yaransu, masu tumaki na kamawa hakan ya tabbatar min dashi dinne ya sake dawowa,
Nima kokarin kama "yar madara nakeyi, amma kafin in isa wurinta tuni dan iskan yabi ta kanta da mota ya wuce, jininta ya
yi tsartuwa a saman fuskata, yana wucewa na ruga na durkusa wurin magen, saida tayi miyau.......... Sannan ta daina motsi, wata irin ashariya na babba tare da kurma wani irin ihu dan naji bakin cikin takata da mota da akayi.
Cikin kuka na nufi ind
a yake, dama ina jiran zuwan shi saboda marin da Babana yayimin ta dalilinshi, shima din
jirana yakeyi saboda zagin da nayi mashi waccan ranar, kowa yana jiran kowa,
Bayan yayi parking ya fito ya zauna saman bayan mota, yauma bulalace a ha
nnunshi yana wasa da ita, sai