Showing 33001 words to 36000 words out of 53720 words
yanzu zakaga mutum ƙato idan yaga wani abin tsoro to fa baxai ambaci sunan Allah,sai kaji ya ce wayyo wayyo!!me makon kiran sunan Allah,don haka iyaye mu kula don Allah don ita tarbiyya tana farawa ne tun yaro yana ƙarami,do
n shi icce tun yana
ɗ
anye ake tanƙwarasa,idan iccen ya girma baka isa tanƙwarasa ba.
*Noor Pov*
. . . . . . .Alhmdh jiki na ya warware sosai,don ƙafar ma da kai na nake taka ta,Hadiza ma ta koma gida daga ni sai Umma ranar muna zaune ni da
Umma sai ga Yaya Ahmad ya shigo.
Da sauri na
ɗ
aga kaina ina kallonsa,na yi kewarsa sosai don yau ƙwanansa biyu kenan ba tare daya leƙo asibitin ba,sai naga kuma duk ya rame sosai,da sauri na sunkuyar da kai na saboda ganin ya kamani ina kallonsa,murm
ushi ya yi ya zauna yana gaishe da Umma ya yi kyau sosai cikin shigarsa ta manyan kaya,ya saka shaddarsa me kalar ash,wacce ta amshesa sosai duk da shi ba fari ne cen ba,amman masha Allah kyakkyawa ne shi sosai.
Ɗan satar kallona ya yi sannan ya ce"
a'ah ƙanwata Noor babu gaisuwa ne?".
Sunkuyar da kaina nayi cikin shagwa
ɓ
ar da ban ma san ina da ita ba na ce.
"To ba kai ne ƙwana biyu kaƙi zuwa ba"?.
Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce"shine laifin nawa?".
Ɗ
aga kaina nayi a hamkal
i ina turo baki.
Murmushi ya yi yana kallon
ɗ
an ficicin baki na,ya
ɗ
an murmusa sannan ya ce"to yi haƙuri ƙanwata nima bani da lafiya ne".
Ni da Umma dukanmu muka kallesa cikin tsoro,sannan muka ha
ɗ
a baki wajen ce wa"Innalillahi wa inna ilaihi r
aji'un,me yake damunka"?.
duka a tare muka ha
ɗ
a baki,saboda yadda muka tsorata don alamunsa sun nuna cewar lallai
ɗ
in ba shida lafiya,don ya rame sosai sai idanuwa kawai kuma ya yi wani irin yin fari sosai sai duk tausayinsa ya kamamu.
Ganin d
uk mun tada hankalinmu sai ya ce"ayya babu ciwon da fa yake damuna yanxu,daman maleria ce yanxu kuma na samu lafiya don haka kada ku damu."
Umma ta ce"haba Ahmad saboda me baza mu damu ba?kai
ɗ
in fa ka kasance mutum na farko acikin rayuwarmu ni da ƴa
ta wanda bazamu ta
ɓ
a mantawa da kai ba,to ta yaya zamu samu ƙwanciyar hankali alhali kuma kai ba ka da lafiya?".
Ɗan murmushi kawai Ahmad ya yi,sai dai kana ganinsa kasan yana da wasu ƴan damuwowi wa
ɗ
anda zasu tabbatar maka cewa tabbas yana ciki
n damuwa.
Kallona yake sosai na sunkuyar da kaina,na kalli Umma na ce"Umma kinga Yaya ko?".
Murmushi Umma ta yi sannan ta ce"a'ah ni fa babu ruwana don idan ma na shiga fa
ɗ
anku kunya zanji".
Sai lokacin naga haƙoran Yaya Ahmad,ya ce"to ku
ma ni me nayi ƙanwata?tunda bakison ganina yanzu zan koma inda nafi kauri,daman ƙwana biyu banje aiki ba?kinga yanxu sai in shirya in tafi Abuja tunda ƙanwata bata son ganina".
Ya fa
ɗ
i hakan cikin sigar zolaya,ni kuwa da yake shagwa
ɓ
a
ɓɓ
iya ce ai sai
na fara murje murjen ƙafafu ina murza ido kamar zanyi kuka,ammanfa ba kukan bane kuka shagwa
ɓ
a ne kawai don gani auta kuma gani ta fari.
Sosai yake min dariya don daman su yake yaga wannan shagwa
ɓ
ar tawa,don ba ƙaramin burgesa abin yake ba sai kuwa y
a ce.
"Ah lallai ƙanwata ta warke,don gashi har ƴar karyayyiyar ƙafar ana ta wurgamin ita,ashe dai ban ragewa ƙanwata fara shi ba,ashe kuma dame ƙafa za'a ha
ɗ
aki ba da gurgu ba".
Sai ya farayin wani abu da ƙafarsa alamar shine gurgun.
Ai
sai na fashe da kukan da banyi niyya ba,kuka har da majina Sosai abin ya bashi dariya har yana tintsirowa daga kan gado.
Umma ma sai da ta
ɗ
an dara ka
ɗ
an,sannan ta ce"a'ah kinji min shashanci ke kuma daga ana tsokanarki sai kuma kuka?".
Ina kuka
n na ce"to Umma ba shine ya ce min wai gurgu zan aura ba,ni kuma wallahi bazan auri gurguba me ƙafa zan aura kuma kyakkyawa."
Sosai ya ƙara sautin dariyarsa sannan ya ce"inye ashe ƙanwar tawa me kyau ce?tunda gashi sai kyakkyawa zata aura,ni da walla
hi har na fara shawarar anya kuwa ba da Audu
ɗ
an gurgu zan ha
ɗ
aki ba"?.
A'i da sauri na tashi ina wurga masa filo ina kuka har da majina,shi kuwa sai biyemin yake yana ƙara jin wani irin mugun son Noor aransa,bai san so ba?bai san menene hakan ba sai
akan Noor,lallai ya yarda kuma ya tabbatar yana masifar son Noor,kuma Insha Allah nan ba da da
ɗ
ewa ba sai ya mallake ta.
Suna cikin wannan darar,Ya sayyadi ya bu
ɗ
e ƙofa ya shigo sosai yaji wani abu kamar mashi ya daki zuciyarsa,don har sai daya
ɗ
an
ta
ɓ
a ƙirjinsa saboda sukar abinda yaji,sai yaji wata irin zuciya ta
ɗ
ebesa tamkar zai je ya shaƙe Ahmad
ɗ
in.
Sosai ya taushi zuciyarsa da kiran sunan Allah,don ayadda yake jin kansa zai iya aikata komai,don ya sayyadi yana da wata irin zuciya don zuc
iyar ta
ɗ
akko asaline ga sunansa wato Aliyu(Haidar).
Kasa shigowa
ɗ
akin ya yi,ya yinda gabansa ke wani irin bugawa kallon masoyiyar tasa ya yi tare da wani suna ta zuba soyayyarsu a bakance.
Umma ce ta fara lura dashi sannan ta ce"a'ah y
a sayyadi shigo mana".
Wayan cewa ya yi ya shigo cikin
ɗ
akin duk jijiyoyin jikinsa duk sun mutu murus,
ɗ
an karsashin daya shigo dashi asibitin duk sai yaji ya koma,don
shi gani yake yaushe ma Noor tasan Ahmad ballantana ma ace wai har ta fara soyayya
dashi?.
Tun Noor tana ƙarama suka saba da i'ta sosai,kuma tun tana ƙarama yake masifar sonta amman bai gaya mata ba,saboda yana ganin ƙanƙantar shekarunta wanda ayanzu haka tana da shekara 15 kenan sai yake ganin kamar bata san wani abu so ba.?
Yana cikin tunanin Ahmad ya miƙo masa hannu cikin fara'a.kamar babu wani abu dake tsakaninsu sai dai shi fuskar ya sayyadin babu yabo babu fallasa suka gaisa.
Sannan ya sayyadi ya gaishe da Umma,ta amsa cikin kulawa har take tambayarsa ya
ɗ
alibai?.
Sai lokacin ya yi
ɗ
an murmushi ya ce"suna lafiya ƙlau Alhmdlh,sai dai makarantar duk babu da
ɗ
i saboda babu
ɗ
aliba me hazaƙa,gashi kuma yanzu muna son fita musabaƙa shiyasa har mun rasa ma wa zamu za
ɓ
a".?
Umma ta ce"kash!gashi kuma yanzu wani sa
tin zamu fita ƙasar waje don yi min aiki,kuma ka ga itace xa ta rakani amman da babu abinda zai hanata zuwa wannan musabaƙar".
Ya sayyadi ya kalli Noor,wacce take ta dariya yanxu sa
ɓ
anin
ɗ
azu da take kuka harda majina,ya hango Ahmad akusa da ita yana
ta saka ta dariya,amman a zahiri Ahmad kallon Noor yake sosai da sosai sai dai ita bata ma san yana kallonta ba,dariyarta kawai take don ya Sayyadi sai ya lura ma kamar bata san ya shigo ba,yaji zuciyarsa tana amsa masa kuwwar aikata wani abu,sai dai da ƙ
er ya taushi zuciyar tashi saboda gudun aikata abinda bai kamata ba.
Ya taushi zuciyarsa da ƙer,ya
ɗ
anyi gyaran murya wajen cewa"Noor baki kula da ni bane,na ga yau an manta dani ko?".
sosai kunya ta kamani na rufe fuskata wajen fa
ɗ
in"don
Allah Ya sayyadi kayi haƙuri wallahi Yaya ne".
Sosai ran ya sayyadi ya sosu sannan ya ce"oh shiyasa ni aka manta dani ko?to shikkenan na gode".ya fa
ɗ
i hakan cikin sigar tsokana.
saurin rufe fuskata na yi sannan na ce"ayya to yi haƙuri ya sayy
adi,ayimin afuwa amman Allah Yaya Ahmad abin dariya ne dashi sai ya yi ta sakani dariya".
Ahmad kuwa cigaba ya yi da rinjayarta suna ta cigaba da dariyarsu.
Ya sayyadi ya sunkuyar da kansa,idanuwansa sunyi jawur sosai kamar gauta jijiyoyin kans
a sun tashi sunyi ru
ɗ
u ru
ɗ
u.
Dukkansu basu fuskanci halin daya ke ciki ba,sai dai Umma ta fuskanci wani abu a tsakanin ya sayyadi da Noor.
Ya sayyadi mutum ne me kunya sosai da kuma zurfin ciki,ta lura yana son Noor ne amman kuma yana
ɓ
oyewa add
u'arta
ɗ
aya ce Allah ubangiji ya bawa ƴarta miji nagari wanda ko da bayan ranta Noor ba za tayi kuka ba,duk da tasan dai da Ahmad da Aliyu dukkansu yara ne na gari.
Ranar Ahmad bai bar asibitin ba sai dare,atare suka tafi da Hajiyarsa mace me ki
rki da son mutane,Ya sayyadi kuwa da wurwuri ya tafi xuciyarsa na masa ƙuna da kuma tuƙuƙi.
Yana zuwa gida kai tsaye
ɗ
akinsa ya nufa,Surayya ƙanwarsa na ƙwace tuwon dare ta kallesa duk jikinta ya yi sanyi sosai don bata fiya ganin yayanta ahaka b
a,don idan zai shigo gida sai ya yi sallama tafi a sau
ɗ
aya.
Kakarsa ma dake
ɗ
aki ta jiyo ƙarar bu
ɗ
e
ɗ
akinsa,ta leƙo tana ce wa"a'ah gadanga lafiya kuwa yau"?.
Ta fa
ɗ
i hakan tana kallon ƙofar
ɗ
akinsa wacce tuni ya da
ɗ
e da rufe ta,don a yadda ya
keji ba zai iya ko da magana ba,tabbas so makaho ne yanzu gashi yana ji yana gani yau Noor taƙi ko da yi masa kallon arziƙi hankalinta dai yana kan Ahmad.
Iya Abu ta kalli Surayya ta ce"ki tashi ki miƙa masa tuwon darensa,duk yadda akayi ko yunwa ya
ke ji ko kuma ba shida lafiya ne oho?".
Gya
ɗ
a kai Surayya ta yi tana rufe masa tuwonsa akula tare da zubo masa miyar kuka awani ƙwano wacce tasha man shanu sosai.
Iya Abu ce ke ƙwanƙwasa
ɗ
akin nasa tana ce wa"kai Gadanga lafiyarka kuwa?
ka shige
ɗ
aki kayi shiru,ko dai baka jin da
ɗ
i ne?".
Shiru ya yi ba tare daya ce mata komai ba,jikin Ƙanwarsa Surayya ya yi sanyi sosai don tana masifar son yayanta don su biyu ne rak mahaifiyarsu ta haifa.
Ta kalli kakar tasu sannan ta ce"Iya k
i ƙyalesa ko baijin da
ɗ
i ne?kuma kinsan an ƙwantar da Noor a asibiti to inajin ko damuwar wannan ce"?.
Iya ta ce"a'ah Surayya tun yaushe aka ƙwantar da Noor
ɗ
in ai an ƙwana biyu,kawai dai wata damuwar ce amman bari in ƙyalesa ya fito da kansa sai inj
i ko menene"?.
Surayya ta ce"to shikkenan Iya bari in gyara wajen nan in tashi don yau zanje islamiyyar dare ƙwana biyu banje ba.
Iya ta ce"a to ai ke da yayanki kullum ba kuda aiki sai ha
ɗ
awa kanku zafi,gashi nan yau duk ya gaji idan banyi man
tuwa ba arana sai ki koyar a makaranta tafi uku,to balle kuma alaramma Aliyu kullum da tashi ka fiya naci idan ya kafa hular nan yadda kika san tsohon tukari".
Sosai Surayya ke dariya tana rufe bakinta ta ce"Allah Iya kin cika ƙorafi,to yanzu ba gash
i ina amsar albashi har uku ba?amman idan mutum ya zauna fa shikkenan komai sai anyi masa"?.
Iya ta ce"to ai sai kuyi tayi uwayen son ku
ɗ
i".
Surayya dai dariya kawai tayi,tasan kakarsu na matuƙar sonsu da kuma ƙoƙari akansu,saboda hakane ma yas
a suma suke ƙoƙarin ta yadda za'ayi su taimaka mata,Iya har wanke wanke da shara tayi akansu don haka shiyasa suma yanzu da suka taso suke taimaka mata sosai.
*******
Da Wuri Inna Saude ta bar gida,kai tsaye wajen aminiyarta
ta wuce wato Sahura.
Sahura na sana'arta ta safe wato Fanke da ƙosai,sai taji sallamar Saude sosai ta bu
ɗ
e baki tana ce wa.
"A'ah Saude ta Mlm Isma'il bada kanki asare kije gida kice ya fa
ɗ
i,yau kuma kece da sassafen nan tamkar an koroki?da al
ama dai ruwa ne ya ƙarewa
ɗ
an kada ko"?.
Sosai Saude taji haushin aminiyarta Sahura ta ce"To yanzu kuma Sahura meye na wannan zancen don Allah?ke duk sanda akazo gidanki sai kin nemu ciwa mutum mutunci?."
Sahura ta ce"to ƙawata maida wuƙar ta M
lm Isma'il Uwar gida ran gida,fa
ɗ
a min Allah dai yasa lafiya ko"?.
Lantana ce ke kallonsu wato kishiyar Sahura,tana musu addu'ar fatan Allah ya shiryesu don tasan dai duk maganar baza ta wuce ta cutar da kishiyarta ba,wato mahaifiyar Noor don Sau
de ba tada imani ko ka
ɗ
an.
Ko Naira biyar ta samu to baza ta amfani dashi da komai ba,sai dai akaiwa Boka wato gobe da nisa.
Ɗan muskutowa Inna Saude tayi sannan ta ra
ɗ
awa Sahura wani abu a kunne,masu siyan Ƙosai sai kallonsu suke.
Inna Saude na gama fa
ɗ
a mata suka tuntsire da dariya.
Wani yaro dake wajen zai siya ƙosai,a hankali ya ce"me ra
ɗ
a! me ra
ɗ
a !! Ɗan wuta,me ji !me ji!!kafiri".
Sosai yaran wajen har da ma manya suka saka dariya wasunsu harda tintsirawa don abind
a yaron ya yi ya basu dariya sosai.
Da sauri Sahura ta kalli yaron sannan ta ce"ai indai munafurcine babu wanda ya kai uwarka".
Yaron kuwa ya murgu
ɗ
a mata baki su Sahura girma ya fa
ɗ
i.
Sahura tana gamawa ta leƙa
ɗ
akinta ta kalli b
udurwar ƴarta sannan ta ce"yauwa Barira idan Babanku ya dawo kice masa ni na fita ni da Saude".
Barira dake ta ƙwalliya kamar wadda za taje gasar kyau ta ce"A'ah fa Inna idan kin matsu ki bari ya dawo ki gaya masa amman ni fita zanyi yanzu."
Ta
na fa
ɗ
ar hakan ta
ɗ
akko ficicin mayafinta ta yafa ta fice abinta agaban uwa.
Sahura tayi kukan kura ta cafko Barira sannan ta ce.
"Ke tsigarallahu ina zaki kuma uwar yawo,ke daga safiya tayi sai ki zare gyale ke ba talla ba?ke ba makaranta ba?
saboda wai kema kin zama budurwa shiyasa yanzu kika dai na
ɗ
aukar talla ko?to yasin babu inda zaki ki zauna ki jiremin
ɗ
aki saboda
ɓ
arayi".
ta fa
ɗ
i hakan tana kallon Lantana,wacce ke riƙe da tukunyar
ɗ
ora girki,ƴaƴan Lantana kuwa kowa yana aikinsa gw
anin sha'awa.
Lantana bata kulata ba,don tasan da ita take shiyasa ta bawa banza ajiyarta.
Barira ta ce"a'ah gaskiya ni bazan zauna ba,saboda zaku fita ni da Shamsu don haka bana don inyi latti don haka ni na tafi".
Barira na fa
ɗ
in hakan
tayi ficewarta.
Abin mamaki sai ga Sahura na ce wa"Allah sarki Barira da har na yi miki fassara,ashe ke da yaron kirkirn nan zaki fita,Allah ya bada sa'a Barira a
ɗ
ebo mana da yawa".
Barira na gab da fita ta ce"to Inna ta".
Lantana na ji
nsu ta yi ƴar dariya kawai,amman bata ce komai ba don ita sam bata son kula Saude don sam ba tada hankali ma balle kuma har kayi wani cacar baki da ita.Uwar kirki dai ba zata tura
ɗ
iyarta mace yawo
ba,kuma yarinya mace don Barira duka dukanta bata fi 17 ba
.amman gashi uwarta na tura ta wajen maza wai duk don ta samo mata ku
ɗ
i.
Saude taso ta biyewa Lantana,don taji sanda ta yi dariya amman sai Saude ta hana ta,tana ce wa"Haba Sahura ki taho mana muje inda zamu kada ki zauna biye mata mu
ɓ
ata lokaci.don
kin san ƊINYAR MAKAHO ta nuna a hannunsa gwara muyi sammako, don ma a hakan kin
ɓ
ata mana lokaci wajen tuyar ƙosai.
To Sahura bata samun damar yin magana ba suka wuce abinsu.
*Hmm ko ina su Sahura za suje oho*
🤷🏿
♀
️
Bazan gan
e soyayyar da kuke nunamin ba,har sai kun taya ni share fisabilillahi don yadda kika ƙaru wasu ma su ƙaro.
*@@Miss green ce
🍀
🫵
🏾
*
Domin yin maga na dani kai tsaye ta chart.
07068606171
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss
Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d'aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda
hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo ku
ɗ
inku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
0810 433 5144
Masu turo kati MTN ta wannan number.
0702 616 6536
Ƴ
an Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
0706 860 6171
Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu.
*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai i
n dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na
ɗ
aki to kai tsaye ku ne mi Badi'at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. "Wai ƙamshi kina nufin Badi'at dai marubuciyar nan tamu mai nisha
ɗ
antar da mu?"
"Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake
magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi'at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta