Showing 114001 words to 117000 words out of 158622 words
kawa
i Ibrahima suke jirada admission letter ta.
Karfe biyar yau Dady yashigo gidan parking yayi yafito, bangaren mamarshi yawuce direct, Granny yasamu a falo da matarshi suna hira ganinshi yasa sukai shiru da hiran dasuke Granny tace "kadawo Maza" akan ku
jeran datake yazauna sanan yabude file din hannunshi yaciro wani takarda da aka rubuta admission letter akai sanan yamikama Granny yace "amshi Grandma saiku shirya mata komi, ranan gobe da yamma zamu kaita makaranta sabida ranan Monday dasafe tanada class,
anbata admission na national diploma a Health Information Management, sune suke managing all hospital record, suna coding and indexing, suna statistics da sauran su, idan tagama ND zata iya amfani da result din tai applying direct entry tashiga university
idan kuma batason course din xata iya next year tasake jamb, but course din nada kyau shita samu" da sauri Granny tace "yo ai babu course din banza aduniyan nan, barinma bangaren lafiya data samu, Allah maka albarka Ibrahima Allah sa kagama da duniya lafi
ya" tai maganan tana bama Mum admission latter tace "yarki fa sai university, su Zara andawo yanmata" tashi Dady yayi yace "nasa anmata registration dakomi kawai kuhada kayanta gobe 4 saina kaiku, lemme go and shower" yawuce yafita sosai Granny da Mum suka
i murna, Mum ta kwala mata kira. "Fatima, Zara Zara" daga kitchen ta ansa da naam sanan tafito tazo har gabanta, tana sanye dawata doguwan rigan atampa sabuwa dayay mata kyau sosai, tace "gani Mum" takardan Mum tamika mata tace "ga admission latter ki, anc
e ranan Monday kinada ma lectures gobe sai tafiya school" kaman amafarki taji ankira mata admission latter, saikuma ahankali tadaura idanunta kan takardan tamanta when was the last time tai farin cikin nan batasan lokacin data fada jikin Mum ba saikuma ta
fashe da kuka sosai tana "Mum nine zan fara school, university, Mum dan Allah da gaske kodai wata maisuna Fatima ce baniba" yanda take kuka tamakusa saka Mum kuka, itadai Granny tai murmushi kawai tana kallonsu, cirota daga jikinta tayi tace "kece Fatima b
awata ba, wani private health school kika samu sun vaki health information management ND, shekara, biyu idan kika fara in bakiso kisake jamb next year, idan kin gama u can apply direct entry, idan kinaso zaki continue kiyi HND, so stop crying yanzu kin da
wo university student ba secondary school ba kuma, now zakije daki kihada kayayyakin k tsaf a box, wanda auwalu yakawo miki, mukuma zamu hada miki su foodstuff, gobe dasafe sai muje saloon awanke kanan amiki kitso sabo kitafi school fess" gyadama Mum kai t
ayi tana murmushi sosanan tajuya ta kalli Granny dake kallonsu
tai tagumi tana murmushi, sanan ta tashi dagudu tana share kwalla tana bama Granny admission letter din tace "Granny zan fara school" ahankali Granny tace "Alhamdulillahi natayaki murna diyar k
irki" rungume grandma tayi zata sake kuka tace "nidai abinci na wuta" saikuma tai dariya tabata takardan tace "rikemin Granny" tawuce kitchen dasauri duk suka bitada kallo.
Saida sukaci abincin dare bayan tagodema Dad shima sanan suka shiga tayata had
a kayanta a akwatunan dasuka saya mata, itadai Granny na zaune tana mata parking dambun nama a jars din dake wajen, daya cikeda cincin, daya da alkaki sai wanda ke hannunta datake zuba dambun nama ciki. Mum da Amna na hadamata kaya kowani kaya a set dinshi
take saka mata a box da gyalensu, da kayan bacci sai wajen 10 da rabi suka gama komi sanan kowa yatafi daga ita sai Amna adaki, sanan tawuce taje tai wanka dan Amna tai bacci tai salla takashe wuta, tana kwanciya as usual yakira, dakata tayi ahankali tace
"ina yini" murmushi yayi dataji sound dinshi tace "congratulations students, sai makaranta" murmushi tayi da shima yaji batare datace komiba, ahankali yace "idan kinje class on Monday, look for the most decent a aji ki karbi note dinta, either you snap ko
kuma ki ara ki kwafe abubuwan da aka muku, banda tara kawaye, keep your heads down, just do abinda yakaiki kina fitowa direct to the hostel, za'a sakaki a haddan su Amna, idan kika dawo gida on Friday, xaki dinga zuwa haddansu Saturday and Sunday kuna dawo
wa one, your life now will be very busy, just arrange and compose yourself anything dabaki ganeba idan nakiraki saiki gayamin, naso nazo this weekend but work yahanani, just take care okay" ahankali tamai nodding kai sanan tace "nagode" gyadamata kai yayi
yace "toki kwanta tun yanzu you have alot to do gobe saida safe" gyadamai kai itama tayi tace "bye" sanan ya katse wayan ta ijiye ahankali agefenta tai shiru ko Allah yasan she is super happy akan makarantan nan, itama zataje school tafara karatu kaman kow
ace yarinya, but deep down she feels so empty babu randa bazatai tunanin Tobi ba, babu randa bazatai kuka da daddare ba sabida shi, she just wish xata iya ganin face dinshi kod sau dayane and tell him tasami admission zata fara school, ita kanta batasan me
ke damunta ba but she can't help yanda take tunanin shi, harji take kaman yadawo nan Abuja yay zamanshi kawai, duk idan ita kadaine afalo saitadau remote tasa tashar kwallo tadinga addu'a Allah sa taganshi a TV amman bata ganinshi, Granny intaganta atashar
kwallo tace "kekuma taki kenan kina mace kwallo kike kallo a TV sabida kin rasa film, nidai sakamin kwana chasa'in" haka zata chanza, tunani kala kala da kuka ahaka tai bacci.
Dasafe shine yatadata still tatashi tai salla tai addu'a tafito ta gyara
gidan ta kunna turare sanan tahada kari, saida tagama komi sanan tawuce dakinta tai wanka tafito tazauna tashafa sabon man da Mum tasiya mata daya karbi fatar jikinta sosai, sanan tasaka kwalli dayama idanunta kyau, tadauko wani riga da skirt na vlisco at
ampa da takalmin shi da gyale dan haka Mum tahada mata kayan, atamfan bakine da ruwan toka, hakan yasa gyalen yazamto mai ruwan toka sanan tadan fesa turare bodyspray kadai tafito, dayake Granny ne kadai da Amna yasa Granny tace "kallabin fa" zama tayi tac
e "idan zamu tafi saina daura" Granny tace "ni banjin zan bikuba fa sonake nai bacci nahuta anjima saina biku mu kaiki makaranta"
gyadamata kai tayi, suka gama breakfast ta kwasa takai kitchen Granny tace "karki wanke wanken nan zata aiko yar aiki ta wanke
kuku wuce ku tafi, Maman ku ta shirya, jeki dauro dan kwalin kidauko jaka kifoto" daki tawuce ta tsaya gaban mirror ta daura dan kwalin da kyar sanan tadau gyalen tayafa tanajin wani iri bata sababa sanan tasaka takalminta mai kyau flat tadauki jakan tasa
ka wayanta aciki tafito, tai wani irin kyau kaman diyar shugaba Buhari, hannunta Amna tarike tace "kinyi kyau Ya Zara muje Mum na mota" bye sukama Granny databisu da kallo tace "adawo lpy" sanan suka fice.
Girgiza kai Granny tayi tace "Muhammadu daka
san meka haifa dabaka wulakanta yarinyar nanba, jibi yarinya yanda Allah yamata baiwan kyau ita kadai, yanzu datasami hutu da kwanciyan hankali cikin sati kawai jibi yanda asalin kyanta da hallitun jikinta kefitowa, wlh zakasan ka wahalar da yarinyar nan"
tai kwafa ta tashi takoma kan doguwan kujera ta mikarda kafa tana chanza tasha.
Saloon Mum takaisu aka tsefe musu kai aka wanke sanan Mum tasa aka mata kalaba hadaddu kanana, itakuma Amna tasa aka mata normal kitso, tana zaune tana jiransu tana karant
a news paper amman kallon Zara kawai take datai wani irin kyau da aka kusa gamama kitso yarinya ga gashi, saida aka gamamata sanan tasa aka musu gyaran kumbuna sukai kyau, tabiya kudi suka fito tasakasu amota sanan suka dawo gida. Agurguje Mama tasa suje s
u sake wanka dan Dad yakira yacemata su shirya gashinan zuwa sanan suka wuce, kallon kitsonsu Kaka tafarayi sunyi kyau sosai sanan tace "to kuje ku shirya" sanan mai gadi ya shigo yashiga fitarda kayayyakin zuwa school dinta.
Wani simple material tasaka
wanan karan milk mai flowers red, ga red veil dayamata kyau sanan tajanyo akwatin ta daya Amna ya janyo nabiyun Granny datai shiga ta alfarma na ganinsu tace "iyye student" sanan ta kalli Amna tace "kai kwatinki waje kizo kidau dayan zonan Zara" ahankali
tazo Granny tanuna mata waje akasa hakan yasa tazauna itama tazauna tace "Fatima Zara'u kinga makaranta zaki yanzu, bawai kaman secondary school yakeba, zaki hadu da mutane kala kala, iri iri banson ki bata wanan kakkywan tarbiyan naki, babu ruwanki da maz
a, komeke damunki kome kikagani kinaso ki sanardani mu zamu miki, kwadayi kesa yaran yanzu bin maza dan samin abinda basuda shi, daidai da magi idan naki yakare ban yarda ki karbi nakowa ba kifita ki sayo a shagon hostel kokuma ki kira mu aiko direba yakaw
o miki, saikuma last fadan daza miki banson yawan surutu, ba ruwanki da gulma, da labarai da sauransu kinajina ko" ta gyadama Granny kai, sanan Granny tace "kidinga kulle kanki kullum yanda kiked gashin nan hostel akwai aljanu ki tsare kanki da azkar da k
omi, nagode ma Allah ma dayasa two people per room ne hostel dinku so kinada roommate banda fada, zaman mutunci da amana, kidinga girkin ki banda yawan zuwa kanti kinji" ahankali tace "naji Granny, nagode" "tashi to mutafi" tashi tayi taji duk jikinta yama
ta sanyi, suka wuce da manyan motoci biyu suka tafi sabifa kayanta su suna cikin motar Dady direba kuma ya kwaso kayanta, har zuwa makarantan su.
Makarantan yahadu sosai bana wasaba abunka da private school, shiga makarantan sukayi suka cigaba da tafi
ya akan shimfidadden titi har zuwa girls hotel sanan yay parking awaje, security dake tsaron wajen suka fito, takardan room number da aka mata allocating Dady yabama head security na mata ta karba tana dubawa sanan, tace "okay, muje" bayan sauran securitie
s din sun tayata kwasan kayanta, Mum da Granny da Amna dakuma ita suka bisu ciki dan men are not allowed, hostel din yahadu sosai ko'ina kal kal wuta ba'a dauke musu, block C suka kaisu room 8, wanda yake akan bene sanan security tabuga kofa tareda budewa
wata yarinya ce zaune akan gadonta tana sanye da doguwan riga tana rubutu ganin mutane yasa ta tashi tareda gaidasu, security tace "munkawo miki roommate" tanuna Zara, murmushi yarinyar tayi tace "welcome" sanan tanuna musu bangaren Fatima dake left, ga w
ardrobe dinta, na zuba kaya, ga kitchen dinta dan karami, dakin nada girma ga AC ga bayin su aciki, jera mata kayan ta Granny da Mum suka shiga yi, within one hour sungama gyara komi nata sun shinfida mata katfarta da zanin gado, sun jeramata kayan abincin
ta dakomi akitchen dinta ga corn flex nadara milo dakomi saikuma snacks dinta suka saka mata a wardrobe kafin six sungama komi sanan sukace to saitafiya, waje sukayi tabisu saida taga dagaske tafiya zatayi tafashe da kuka saikuma sukahau mata dariya danhar
shi Dad dabaida magana sosai saida yay dariya, yafito da kudi 50k yabata yace "gashi kirike wanan" karba tayi tace "Dady Allah amfana amma dan Allah kabarmin Amna tadinga zama anan" tasake fashewa da kuka dan dagaske take fa, fitowa Mum tayi daga mota tace
"kinga sai kallonki ake kina kuka akan hanya, Amna can't stay with you a hostel itama tana zuwa school dinta, keda just on Friday zaki dawo common zaki ganta zaki ganmu stop crying now, wuce kitafi, bye" hannu tadagama Granny dake cikin mota da Amna itama
tana kuka sanan tajuya ta tafi ciki tana kuka tana share kwallan, sukuma suka tafi cikeda kewanta.
_Mumies akwai abinda nakeso nagaya muku, shin kunkosan like Did you know........?_
_Scent kamshi shine abu na farko da mutane ke lurada shi
idan sun shiga gidan ka ko motan ka bawani abuba?_
_Be memorable.....in a good way Mumies_
_A Fragrant, shi kamshi is like a signature, kaman wani alamune so even after a woman leaves the room, her fragrance should reveal she's been there. Kamshi abune
dake nuna kinzo waje idan ma kikabar wajen still zai nuna kinzo_
_Turare heralds a woman's arrival and prolongs her departure_
_The beauty of turare speaks to your heart and hopefully someone else's kunsan da haka Mumies?_
_Kamshi is a word, turare is
a literature do you believe this Mumies?_
_Kamshinki amatsayin ki na y'a mace tells more about you sama da handwriting dinki kinsan da hakan?_
_Mata kusaurara kuji, namiji yana iya manta komi naki amman baya iya manta kamshin ki_
_da hakane nake muku i
ntroducing turarukan UMMIE COLLECTION dazai baki duka qualities dinan and even MORE tested by M SHAKUR dinku, suna saida turarukan daki, na jiki, na wanka, turarukan tsinke, body oils da sauran su, zaki iya tuntubar su ta wanan number ko awaya ko a watsapp
08186968736, dan samin karin bayani, zaku iyashiga group dinsu dan ganin duka turarukansu, zakuma ku iya following nasu a_ Instagram @UMMIE COLLECTION.
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/Fov2UbNr4CH0reP9K9zltu
Inst
agram Handle dinsu https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1c3np4d6vwqbv&utm_content=1g4qyjp
_PRODUCT DINSU_
_SANDAL EXCLUSIVE_
_SANDAL FLAKES_
_SANDAL BANGI_
_KAJIJI_
_DOROT_
_DAMBU_
_DEVINE (PURPLE)_
_REGAL (YELLOW)
_LOVELY (MAROON)_
_DAISY (ORANGES)_
_KHuMRA_
_STAR_
_BELOVED_
_Body oils._
SIGN M SHAKUR
7/16/21, 4:44 PM - My Mtn Number:
💫
_DISASTROUS LOVE_
💫
✍
🏾
M SHAKUR
_Mumies akwai abinda nakeso nagaya muku, shin kunkosan like Did you know........?_
_Scent kamshi shine abu na farko da mutane ke lurada shi idan sun shiga gidan ka ko motan ka bawani abuba?_
_Be memorable.....in a good way Mumies_
_A Fragrant, shi kamshi is like a signature, kaman wani alamune so even after a woman leaves the room, he
r fragrance should reveal she's been there. Kamshi abune dake nuna kinzo waje idan ma kikabar wajen still zai nuna kinzo_
_Turare heralds a woman's arrival and prolongs her departure_
_The beauty of turare speaks to your heart and hopefully someone else'
s kunsan da haka Mumies?_
_Kamshi is a word, turare is a literature do you believe this Mumies?_
_Kamshinki amatsayin ki na y'a mace tells more about you sama da handwriting dinki kinsan da hakan?_
_Mata kusaurara kuji, namiji yana iya manta komi naki
amman baya iya manta kamshin ki_
_da hakane nake muku introducing turarukan UMMIE COLLECTION dazai baki duka qualities dinan and even MORE tested by M SHAKUR dinku, suna saida turarukan daki, na jiki, na wanka, turarukan tsinke, body oils da sauran su, za
ki iya tuntubar su ta wanan number ko awaya ko a watsapp 08186968736, dan samin karin bayani, zaku iyashiga group dinsu dan ganin duka turarukansu, zakuma ku iya following nasu a_ Instagram @UMMIE COLLECTION.
_Open this link to join my WhatsApp Group:
https://chat.whatsapp.com/Fov2UbNr4CH0reP9K9zltu_
Instagram Handle dinsu https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1c3np4d6vwqbv&utm_content=1g4qyjp
_PRODUCT DINSU_
_SANDAL EXCLUSIVE_
_SANDAL FLAKES_
_SANDAL BANGI_
_KAJIJI_
_DOROT_
_DAMBU_
_DEVINE (PURPLE)_
_REGAL (YELLOW)
_LOVELY (MAROON)_
_DAISY (ORANGES)_
_KHUMRA_
_STAR_
_BELOVED_
_Body oils._
SIGN M SHAKUR
EPISODE 6
️
⃣
0
️
⃣
& 6
️
⃣
1
️
⃣
Dakinsu tabude ahankali tashige tafada kan gado tanakuka ahankali, itadai roommate dinta
narubutunta abinta, haka tai kukan har bacci ya kwasheta akai Magrib, ganin ana kiran sallan isha'i har lokacin bata tashi, tashi roommate din nata tayi duk tana kallonta saita wuce kitchen dinta tadebi rice a plate tadawo kaman zata wuce kuma saita karas
a gadonta takai hannunta tadan bubbuga gadon ahankali Zara tabude ido, hada ido sukayi da yarinyar ahankali tace "kitashi kiyi salla and find something to eat" gyadamata kai Zara tayi ahankali sanan ta tashi zaune tana dafe kanta dataji yasoma mata ciwo sa
ikuma ta mike tsaye ahankali tawuce dakin datasan nanne bayi, budewa tayi bayin kalkal daga ganin yarinyar nada tfasta alwala tadauro tafito, tadauko daddumanta da hijabi sanan tajuyo ta kalli yarinyar dakecin rice tana daddana waya ahankali tace "dan Alla
h inane gabas"? Da hannu tanuna mata gabas din hakan yasa ta shimfida tai Magrib da isha'i sanan tai nafila ta tashi juyowa tayi saitaga sun hada
ido da yarinyar ahankali tace "nagode" ahankali itama yarinyar tace "you welcome" sanan tawuce kitchen ganin k
okarin fixing abinci take yasa tace "dare yayi inada rice kici" dasauri Zara tajuyo ta kalleta gudun batason yarinyar to feel bad yasa ahankali tace "nagode" taje pot din datake nuna mata tadebi kadan, tadawo tazauna zata faraci saikuma ta kalleta tace "Ya
sunanki" "Maryam from KD" wani irin murmushi Zara tasaki jin sunan kawarta ko ina take yanzu oho, kotai aure kota fara school Allah kadai yasani, faracin abincin tayi ahankali data gama taje ta ijiye plate din.
Darenma saida Imam yakirata ya tambayeta
school dawaye roommate dinta dukta fadamai, washegari tana idar da salla tai azkar ta tashi tazo ta shiga fixing breakfast itakuma Maryam na bayi na wanka, fried Irish tayi da kwai da tea a cups guda biyu sanan ta iiye komi a tsakar dakin tacire kayan jik
inta Maryam nafitowa itama ta shiga, Maryam ta kalli breakfast din tai murmushi data fito tashirya tare sukaci abincin sanan suka fita tare, ashema ajinsu daya da Maryam din, saidai yarinyar nada kokari sosai taga yanda kan yarinar keja, dasuka dawo tasa M
aryam takoyamata all abubuwan dabata iyaba shikenan kuma daganan suka fara shiri, Maryam din itama batada surutu kaman ita batada kawaye koda yaushe tana daki tana karatu kotana wasada waya itama babu abinda batadashi, sosai suka shiryada Maryam, itama Mar
yam ganin Zara nada natsuwa batada shiga kawaye gason karatu yasa taji tanason yarinyar, a ajin har kiransu da yan girman kai ake sabida yanda babu ruwansu basa harka da kowa.
Yau Friday tun safe Zara ta tashi take murna takosa sudawo daga class t
a tafi weekend itama haka Maryam sabida za'a adauketa, tun kafin ta tafi class ta danna ma Granny kira tana shagwaba tace "ita 12 zasu fito daga lectures by one azo adauketa ba harsai 4 ba" Granny namata dariya tace "anyi kewanmu" sanab ta katse wayan.
1 daidai tana daki zaune