Showing 1 words to 3000 words out of 35664 words
[08/02, 22:35] Fulani Khadija Group: *UNIQUE WRITERS ASSOCIATION*
*MATAR SARKI*
*STORY N WRITEN BY*
*AYUSH ILIASU MUSA*
*13TH JANUARY 2018*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.*
*Godiya ta Tabbata ga ubngijin talikai me kowa me k
omai,tsira da Aminci su kara tabbata ga shugabanmu Annabin muhammad SAW*
*TRUE LIFE STORY*
1
⃣
-5
⃣
*I DEDICATED DIS PAGE TO MASOYANA NI AYUSH ILIASU DA MAMBOBIN GROUP DIN AYUSH ILIASU MUSA AND HAWWAH SALEH NOVELLA,INA SONKU,INA KAUNARKU INA MUKU F
ATAN ALKHAIRI ANA TARE IRIN SOSAE DIN NAN*
Fahra zaune a katafaren falon mahaifiyarta ta rasaa meke mata dadi,hawaye ne ke zuba a fuskarta shar shar tamkar an bude fanfo
Fargabar ta guda gobe monday,duk farincikin da take ciki ta tuno g
obe zaa koma school hankalinta tashi yake.
Badan komae ba illa halin da take ciki,A kullum aka turata makaranta sai taki zuwa,mafi lokuta sae de tayi ta tafiya akasa ,tanayi tana duban agogo ,wato sai ta daidaici an kusa gama lectures sai ta juyo ta
nufo gida
Kullum haka ce ke faruwar da ita,in kuwa kaga ta je makarantar to ko registration ko in zaa musu organised text ko individual presentation
Wani lokacin tana tafe tana kuka ,ba komae take tausaywa kanta ba,illa gani take kowa yasan
halin da take ciki ,sau da yawa inta gajine zata nemi soron gidajen jamaa ta huta.
Kamar kullum fahra zaune a palo ana kallon ,sai ummansu tace Fahra ya har yanxu baki fara shirin school ba,bakida lectures ne? Budar bakin fahra sai cewa tai eh bani
da.zaro idanu umma tai,monday guda fahra kice baki da lecture? Eh umma bani da
Tsam umma ta mike tabar falon ta nufi dakin Abbansu fahra,isarta keda wuya tace,abinnan n fahra ya fara bani tsoro,yarinya ace batasan zuwa
makaranta,inna tanbyeta tace
lectures din one hour ne,data futa b dadewa naga ta dawo
Wani lokacinma sai ta kwanta bacci bazata tashi ba har sai lokaci ya kure ,innsi mata magani ya bata shirya ta futa b sai tace ai lokaci ya kure
Abba dake sauraran umma shiru yai yana na
zari,can yace,me yasa baa gayan tun da fari ba sae yanxu,? Umma shiru tayi ba ansa.
Tsam ya futo daga dakin ya nufo palon da nike zaune,fahra fahra fahra kina inane,gabana ne ya fadi,badan komae ba ,illa a rayuwata Allah yasa ina tsoran Abbanmu.
Duk kiriniyata da kin jina dana ji dawowarshi nutsuwa nike,inkuwa ban nutsuba na cigaba,dana nemi rigima an kaimai kara zan falfala a guje n nufi benan mahaifiyarsa dan neman tsira.itama din ban kyaleta ba,in taimin ramawa nike.
Fada Abbah ya shig
a yimin,ya kuma umarceni da lallai na daukomai time table na lectures dina yanxu
Daki na shiga na yago paper cikin littattafaina take na hada time table ta bogi,mondy 9-13Tuesday 2-4,wed 2-4.thursdy 12-2.na miko mishi,duba yakai ga takardar yace co
urses hudu kike yi,gyada kai nayi ah ah,kowana course lecture one hour mukeyi ,gaba daya courses 8.
Nan ya kara min fada da nasiha kan lallae na maida hnkli akan karatuna,nidea to kawai nace badan na daukaba,Abbanmu ya samun ido matuka,dan kuwa in
lokacin yayi baya gida umma yake kira a waya inceko n tafi school,ko bn niyyaba haka zan dau littattafai da mayafi na tafi zaga gari.
Inna miki titi sanbal nike tafiya ba kwana har sai na gaji sae n huta ,ganin zaa ganeni da bin hnya guda yasa nike
canja hnya,kullum haka nake
A kwana atashi ba wuya a gun Allah har mun fara exams din second semester level 200, Allah yayini me nacin karatu,duk yawan notes bana ganin wahalar kwafa ,balle karatu
Allah ya horemin san karatu,kuma koda bana aj
i malami ya koyar,inde zan samu note na kwafa to in shaa Allah inbanci A ba to B ne.in tayi wuyane zanci C ,mun yi jarabawar mu cikin nasara,munyi hutu.
Al'adar university dinmu itace da zarar anyi hutu zaa koma ake kafemana result kan mu fara regi
stration dan sanin courses din daka fadi
Kamar ko yaushe yauma an kafe mana result,wayatace tadau ruri,saurin karasowa gareta nayi,ganin sunan me kiran gabana ya bada das,dan tunda aka hutu bata kirani ba.
Da sallama na dauka muka gaisa,tace fa
hra kinsan an kafe result ko ? nace a'a,kawai sae ta katse call din,jiki n rawa n kira har ta tsinke bata dagaba karshe danaga bazata dauka ba na hakura.
Akwai wani course mate din mu ana cemai musa se na kirashi nace pls ya duba min result dina ance
departmnt dinmu sun kafe,dayake ba course daya muke ba but muna subceedn tare,yace in ya duba zai kirani
Shiru shiru be kirani ba saina kasa hkuri na kira kawarmu Aysha,kamar bazata daga ba sai can ta dauka,yanayin data min mgn ba haka muka saba ba
.nace Aysha ance an kafe result ko tace eh an kafe,inada 3.50,firdausy tana da 3.40 d carry over,nace Alhmdlh na muku murna walhi,amma n tausayama firdausi Allah yasa hka shi yafi mata alkhairi.
Jin bata fadan nawaba sai nace Aysha nifah,budar baki s
ai cemin tai ita bata gani ba,mamakine ya lulluben ba na komai b saboda tare mukae registration da ita ,registration no din ta 0001 tawa 0002 ta firdaus 003. Nan jikina yayi sanyi na fara zargin wani abu
Ganin musa be kirani ba,suma sunki gayan yasa
hnklina ya kara tashi,koma de nawa naci a gayamin, bawa dole y yadda da kaddara me kyau ko mara kyau,inata sakawa da kwancewa naji txt ya shigo wayata,numbr din musa ce cikin sauri na bude,yayi congratulating dina ina da 3.80 babu C.O babu Absent,ihun murn
ar da nai ne ya jawo hnklin umma dake kitchn tace lfy nace umma result dinmu ya futo banda C.O,na samu 3.80,budar bakinta sai cewa tai sai kace a mafarki wazai baki wannan uban makin keda b kullum kike zuwa ba
Allah umma da gaske nike,inma baki yar
daba,gashi krnta da kanki,mikon glasses dina yana cikin jakarcan arataye sai data gani sannan ta yarda,tare da tayani murna,nidea murna rabi da rabi nake saboda fargabar canjawar da firdaus d Aysh suka min
*Ayush iliasu musa.......
✍
*
[08/02, 22:35] F
ulani Khadija Group: *UNIQUE WRITERS ASSOCIATION*
*MATAR SARKI*
*STORY N WRITEN BY*
*AYUSH ILIASU (AYUSHWA)*_
*DEDICATED TO*
*OLL MA FANS*
*TRUE LIFE STORIE*
1
⃣
1
⃣
-1
⃣
5
⃣
*MY HANAN INA ME MIKI FATAN ALKHAIRI TARE DA ADDUOIN SAMU
N NASARA A CIKIN JARABAWARKI,UBANGIJI ALLAH YA BAKI FIRST CLASS ALBARKACIN ANNABI MUHAMMAD SAW,AMEEN,AYUSH ILIASU NA TARE DAKE A DUK IN DA KIKE*
*Farhan* yarinyace da bata dau duniya da zafi ba,sakamakon futowar result dinsu,da ganin grade di
nta,kawayenta suke nacin tayi musu tutorials
Haka farhan zatasasu gaba tayi ta musu bayani har sai sun gane,cikin kawayenta akwai hafsat wadda kwakwaluwar sae a hnkli (slow learner)dan haka ,ni da kaina nake mata forming note(summarising) da zata k
aranta for exams,na mata explaining saina tabbatar ta gane,in test muke tare muke zama,ba batun n rufe takardata,haka zan basu su kwafa in basu iyaba.in kwa sun iya sae dea na dan kara musu wani abu,lokuta da dama nike karban notes din na musu.
D
uk sa ilin da zamu shiga exams tare muke zama,in case in sun manta wani abu sae su tanbayeni,ko basu fahinci tanbayarba,cox most attimes wasu lectures na twisting question dansu rikita dalibi
Dayake karatun jamiah bakamar secondary bane da malami za
i zo gaban allo yama rubutu,anan sai de yayi lectures kayi jotting iya abunda Allah y nufeka da ji,da yawa cikinmu basu iya rubuta komae,sai dea su saurara kawai,a bangarena kuma awannan lokacin nake forming notes dina,dan haka da an tashi zakaga sun fara
rububin karba,haka zan basu in wannan ta gama ta ba wannan karshe su dawomin da shi in sun gama
Duk da diplomar da muka fara hakan bai sanya gwiwar mafaifinmu karaya ba,ahaka ya saya mana jamb form muka sake rubutawa,burinshi yaga munyi ilimi me zu
rfi.acewarshi duk tarin dukiya me karewace,ilimine kuwa baya karewa,dan ko ubngiji da yai maganar a nemu ilimi be iyakance na addini ko boko,ko wanne nada iya nashi muhimmncin
Allah yayini da wata irin baiwa,duk yayin da zan aikata abu,ina nemn taimako
a gurin Allah,tunda naji mahaifinmu yace ya saya mana jamb form na fara adduar"Ya Allah in bani da rabon cin jamb dinnan Allah kada ka nufeni da rubutawa ,ka kawo sanadin da bazanyi taba,in babu rabon naci ,Allah kada ka nufeni da cinta kona zana,ubangiji
Allah in babu rabon na samu admission Allah kasanya na fadi,na fidda rai tun kan damuwa bata min illa ba"
Cikin nasara muka zana muka kuma ci,akan mu aka fara gudanar da jarabawar post UTME a jamiar bayero ta kano,ganin ina public Admin yasanya nai
Applying political science tunda dan jumane da dan jummai,ranar post utme mun zana, sakamako ya futo munsamu nasara.
Murna nike tayi dannide jikina ya bani na samu admission,bazan taba mantawa ba,da babbar sallah munje hawan nasarawa muka hadu da
friends dinmu,nan suka shiga yiwa yayata albishir da cewar sun ga sunanta a newspaper ta samu admission a buk,cikin zumudi muka kira dady muka sanarshi
Take yasanya aka sayo mishi daily trust ta ranar,aikuwa sae ga sunanta rangadede,jamiar bayero t
abata admission,duban duniya anyi amma babu nawani *farhan*
Ganin yanayin dana shiga yasa hankalin Abbanmu tashi,ya kira abokinshi dake lecturing a jamiar yake gayamai ,nan yamishi alkawarin zai duba yaga a ina aka samu matsala
Hankalin Abb
anmu ya tashi gashi,anyi resuming school,sauran kawayena da muke diploma sunmayi registration nice na kedan jan kafa ko Allah yasa nima n samu,shiru kakeji malam ya ci shirwa,ayau thursday an sanar damu a gobene zaa rufe registration na duk wasu returning
students na jamiar, Abbana ya bani kudin naje bank na biya.
Abbana da kanshi ya nufi jamiar bayero ofishin abokinshi Doctor ne Asashen English,da ganin abbana saii,duk ya daburce da ganin Abbana,nan yayi mishi jagoranci suka nufi academic office,a
n tanbayi Abbana naci post utme ne?ya amsa da eh naci ,sukace menene shaidarshi tanaci nan yayi turus,dan kuwa kafewa akai,daliban da basuci ba sun yayyage.
Ganin Abbana babban mutum sukace Alhj sae dea kayi hakuri tunda babu shaida,in ba haka b
kuwa,mafita dayace,kaga dakin can,ya nunawa Abbana daki guda shakare da takaddun dukkan daliban da suka zauna jarabawar post uTME a faculty din Social and Management Sciences,yace sae de ka shiga ka lalubo takardarta a cikin can,ta hakane zamu tabbatar tac
in ko akasin haka
Abbana ya kalli tulun takardun dake baje a dakin,ya kalli sama,yayiwa ubangiji bakance da cewa ya Allah nayima alkawari in har naga takardar *farhan* cikin sauki dana futa zanyi sadakar dubu goma ga mabukaci bama sae na je gida b
a.
Allah shine rahmanu kuma rahimu,Abbana na dora hannunsa a takardar farko ,ta biyu ai kuwa sae ga sunana dararere *Farhan* fareed ,gefe an bani marks 70 out of 100 ,Hamdala ya shiga yi,tare da farinciki.rike da takardar ya futo daga dakin
S
u kansu mamakine ya lullubesu ya akai ya iya zakulo takardar cikin jerin takardun dake dakin,sun jinjina lamarin su kansu,nan sukace ya dan basu guri,Abbana ya matsa gefe,maganganu suka danyi sannan yaiwa mutumin sallama.
Abbana da abokinshi doctor
tafe suna jinjina lamarin,abokin Abbah ya dubi Abbana yace wani hanxari ba gudu ba Alhji a gobene jamia zata fidda jerin sunayen dalibai n karshe wato suplementary list,dan haka yace na gaya ma
*farhan* bazata samu course din da tai applying ba saboda ad
adin daliban da akeso sun cika,sae dea ta zabi guda tsakanin courses din faculty of Arts and islamic studies(faiz),ga samu ga rashi,Abbana yace wadannene courses din faiz din,Doctor din yai dariya yace English,hausa,Arabic,history,islamic studies.amma yace
banda English,Abbana ya jinjina lamarin yace,ai da babu gwara ba dadi ,degree ai kona kwasar kashine inde anayi a jamiah ana kuma kiranshi degree ai ba matsala
Xaro wayarshi yai a aljihu ya shiga kiran numbr ta,ganin me kiran nai hanzarin dauka ,du
k zatona zae ce ya karbon admission letter din,yace *Farhan* cikin kwasa kwasan nan uku zabi guda ciki,history,Hausa da islamic studies,kamar wadda aka matsi bakina nace hausa Abbah.kit ya kashe wayar
Bayan nan ne na shiga danasanin dama islamic na
zaba ko ba komai na yiwa addinina hidima,bakin alkalami ya bushe,dan kuwa Abba yayima Doctor sallama ,nikuma n kira abbah,yana dauka yace ina hanya innazo kyaji yanda mukai,duk zatonshi tanbyrshi zanyi,be san so nake nace mai islamic nikeso,turus nae,damuw
a na shiga,can sae n tuna komae daga Allah yake,bawa baida tsimi da tanadi face abun da Allah y jarabamae,ko wana abu da bawa zae yi dama kaddararsa ce,sai dae addua ta kaudamu daga kaddara mara kyau,na yi hkuri Allah yasa haka shine mafi alkhairi gareni,s
un rabu kan cewa mu nemi jaridar daily trust ta gobe zamuga list din candidates din da zaa dauka insha Allah sunana zai futo
Kamar yanda ya alkawarta yana futowa ya ci karo da almajirai kusa d inda yai parking motorsa,cikin aljihu ya sanya hannu ya
zaro yan dudu dubu guda goma ya bada sadaka
[08/02, 22:35] Fulani Khadija Group: *UNIQUE WRITERS ASSOCIATION*
*MATAR SARKI*
*STORY N WRITEN BY*
*AYUSH ILIASU MUSAH(Ayushwa)*
*DEDICATED TO*
*OLL MA FANS*
*TRUE LIFE STORY*
6
⃣
-1
⃣
0
⃣
*Na sadaukar da wannan feji ga yar uwa,kawa,aminiya,kanwa,Hawwa saleh,Allah y barmu tare cikin so da kaunar juna,ya karemu daga sharrin mutum da abunki Ameen*
*Mutuniyar kirki mum sumy n Aneesa of Ayush iliasu n hawwa saleh novella,muna Adduar Alla
h y baki lafiya,yasa kaffara ya kara miki ingantacciyar lafiya Ameen*
*Sakon gaisuwa gsreku masoyana mamn mahbub da zainab musa mmn waleed,Aysh iliasu na nayinku sosae ainun,Allah y bar zumunci*
Kullum Fahra ta kira numbr din Firdaus da Aysha
basa dagawa,harta hakura ta daina kiransu.
Ganin haka yasanyata shiryawa takanas ta nufi gidansu firdaus dake unguwar zango a jahar kano
Tayi rashin sa'a bata taddata ba,sun gaisa da mama,nan maman ke ce mata ba nisa tai ba ta jira ta yanxu z
ata dawo
Haka na nemi gurina zauna ina jiran firdaus ,irin family house dinnan nada,kamar yanda zamantakewar malam bahaushe take,gidane me sashe sashe,amma dukkansu yan uwan junane
Sallamar frdaus naji,tana ganina sai naga alamun canjin ya
nayi a fuskarta,atakaice bataji dadin zuwana ba,mun gaisa,inda nike tanbayar ta yasu Aysha kuwa,inata kiransu a waya ba wanda y daga,ince ko lfy? Ko wani abu akace musu nayi.
Budar baki sae cemin tai bata gani ba,wai sae de in ba wayarta n kira ba,h
kn ya batan rai wato atakaice ta rainan hankli
Mik'ewa nayi da nufin tafiya,tace ina zaki nace tafiya zanyi dama sauri nake,ki bari ko ruwa kisha ke kuwa,kememe nace a'a,haka muka futo ta rakoni har bakin titi ba in ba ba in in tsakaninmu,mukai sall
ama na tari dan sahu n nufi gida
Ganin haka naja jikina,n daina kiransu baki daya,Allah yayini mace me fushi da zuciya,bansan rainin hankali ko kadan,musammn in nasan banyi laifi ba.
Monday aka fara registration,misalin karfe goma na shiga
schl da zummar zuwa n kwafi courses din da zan xaba,bisa alada tare muke zabar courses dasu,hakan tasa n kira number din Aysha nace kuna inane,sai cemin tai gamu a coke village zami photocopy na credentials,nace mata pls wana courses kuka dauka,dan karmu s
amu banbanci,cemin tai gaskiya na manta amma ga firdaus sai ta gayamiki,kan nayi mgna ta mikawa frdaus wayar
Tana amsa tace yadai fahra,nace gayamin code din courses din da kuka zaba,sai cemin tai gskya ki zabi naki kawai har yanxu bami deciding wa
danda zamiyi ba ,nace haba frdaus kuna da kawayen da suke level 300 fa , nasan kun tanbayesu wadanna courses ne masu sauki da malamai,gudun daukan karada kiyashi
Kinsan wani course dinne me wuya,yayin da wani course din sauki gareshi malaminne me ma
tsala,pls ki gayamin,kit kawai naji layin ya tsinke
Raina yai masifar baci haka n kwafi courses din,na nufi cafe dan fidda remita ta paymnt,bayan na fidda n biya bank nai payment sannan na nufo gida.
Alhji fareed faisal shine mahaifin fahra,
mutum ne dan kasuwa me rufin asiri,fahra da sauran yan uwanta sun tashi cikin jin dadi da wadata,tare da ingantacciyar tarbiya.
Fahra itace ta uku gun iyayenta,Alhji fareed yana da matar aure guda daya, wadda ake cema Fareedah,sun yi aure n saurayi
da budurwa,auren xumuncine dan kuwa cousins ne
Fahra tana da yan uwa mata biyar da namiji guda daya,mahaifinmu mutum ne dayasan hakkin iyalinsa,bai barmu da kukan komae ba,tun muna kanana ya sanya