Showing 30001 words to 33000 words out of 35664 words
yake da akwai ze taimaka miki," godiya na shiga yi mata,dan kuwa idanuna sun rufe neman d'auki kawai nike,na bukaci "yaushe ake samunsa" tace "ko yanxu zamu iya zuwa".
Mota mukashiga mu
ka nufi unguwar sallari,mun yi nasara bamu tadda layi ba,muka shiga d'akin da yake ganawa da bak'i,sun gaisa da fareedah tare da tanbayar bayan saduwar su,nan fareeda ke sanar dashi mak'asudin abunda ke tafe damu.
Shiru yayi yana nazari tare da cewa
in shaa Allah zaiyi nazari adaren yau,gobe da safe na kirashi danjin feedback,na karb'i numbr dinshi mukai sallama
Washegari da sassafe na kirashi dan na k'agu naji me xece,bayan mungaisa ya sanar dani maganar bata waya bace nasamu naje.
Bayan mun ta
shi daga office gidansa muka zarce,nan malam Auwalu ya ce" diyata ,nace na'am malam Auwal ",abunda nikeso dake shi ne ki hakura da Ahmad kima cireshi aranki"kuka wiwi na shigayi,kallona yake tamkar a film.
"Farhan saurareni da kyau,ki bud'e kunnuwanki
,"baki san masifar da kike ciki ba shiysa,dan kuwa muna da ido bana ganin gari ba ,kisani bak'in Aljanine akanki,koba ahmad ba in maza d'arine zasu zo da zummar suna sanki da aure,walhi duk seya koresu,dan haka kima dena batun a karkato miki da hankalin A
hmad ya aureki,dan bazai taba yiwuba,shawara d'aya ki fara nemawa kanki magani kan kiyi tunanin aure,ita kanta iskar ita ke kara sa miki son maso wani tare da kafeki gareshi ."
Innalillahi wa inna ilai hi rajiun,Allahumma ..........,na bukaci ya sanar d
ani "nawa zan bashi atake dan ya rabani da iskar"dariya yayi me yawa tamkar cikinsa ya kulle," tabbas yarinya bakisan me ake nufi da iska ba,shiysa kika fadi haka,ai lamari na iska babban al-amari ne,kasancewarsu shedanu,ba kowana me magani ke aikinsu ba,s
hi kansa me maganin nasu se an dau lokaci kan ya sha kansu,taurin kai garesu,kuma waiwaye suke,in an yi nasarar koresu ma,in mutum yayi wasa da amfani da magunguna komowa suke su zauna,shi yasa ake musu hauka hauka,cikin hukuncin Allah ana addua Ana magani
se kiga an rabu dasu har abada."
Jikina yayi sanyi da jin maganar malam Auwal,"to yanxu malam ya zaayi,nide a yanxu ban san wanda zan hadaki dashi me kashe auren aljani ba,amma zan cigita miki inda sukeyi sadidan ba cuta ba cutarwa,dan masu maganin isk
a da yawansu mazanbatane,kije kema ki cigita in kin samu kije,nima zan cigita miki",nan mukai mishi godiya muka taho hanya muna kara jimanta lamarin
Fareedah ce tace "haba ruwa baya tsami banza,tsaleliyar budurwa kamarki farhan,full option ace samari na
gudunki,ai lamarin abun adubane,abun da zai faru yanxu xan cigita miki kema ki cigito",
"to yar uwa,dan a yanxu kin tashi daga k'awa kin zamarmin yar uwa."
*****************************
Allah ba ya zalunci,duk abunda bakada hak'k'i akai ,ubangiji
se ya baiyana ma,zaune nike a palo ina kallon shirin dadin kowa da ake a tashar Arewa 24 ,wayana naji yana ringing,a hanzarce na k'arasa gareta,tare d answering ganin me kiran,muryar Ahmad ce ta doki kunnena,hi beb,hy.ya kike? Lafiya ,y ummanmu? oll fyn,
"jst call to inform u that zanyi travelling for 2 weeks koda zaki kira kiji ba ai answering ba ko phone din kashe" ai bama zan kiraba tunda a yanzu babu wata alaka tsakaninmu ,ni yanzu matsayin yaya na dauke ka" ,tom ba matsala ya cemin,Allah y dawo da kai
afiya ,yace amin .
Hmmm ashe Ahmad yamin hakane,sabida aure d za'a d'aura mishi a gobe.zaton shi duk da abunda ya min ban daina sansa ba.ai ko yaro yasan masoyi da makiyin sa.
*GOBE DAURIN AURE*
Kamar yanda mahaifin feedo ya bukaci yaje,ya is
a kofar gidan,tare d sanar d feedo din,cikin kwarkwasa d rausaya ta isa gareshi bayan sun gaisa ya sanar d ita dalilin zuwan shi,tayi mamakin jin hakan,kasancewar mahaifin nata be sanar d ita ba
Ta umarci yaran abban nata ya sanar wada Abban, zuwan Ah
mad din ,ya buk'aci ya shiga ciki,nan sukai sallama ta shige gida
Da sallama ya shiga palon,kan shi ak'asa ,gaba d'aya zubewa yayi ak'asa yana kwasar gaisuwa,Abban firdaus basarake ne kuma babban malami,zaune yake ya dora hannu kan matashi ,kafafunshi na
kan wani.
"Ahmad kake ko?" Eh Abbah,yawwa "na kirakane na gaya ma sharudai kan na baka auren diyata,ni bana bawa rago ko talaka ko me k'aramin karfi diyata,kanaji na?" girgixa kai yayi alamun amsawa,ya cigaba d cewa" naga an kawo kaya labari ya is ko ni
kaya basu yi ba,karanta ce tsagwaro cikinsu ,haka zalika na tanbayeta kudin daka bata na taron biki da na sauran abubuwa tabbas kayi mana bazata,shi yasa na kira na baiyana ma sadakin 'yata,dan karka bani kunya a gobe gaban dubban jamaa,dan kuwa yanda b
akaji kunyar yarfani gaban abokaina ba,bazan ji kunyar janye aurenku ba,"da nasan kai d'in d'an k'ananan mutane ne masu k'anana zuciyoyi da ban aminta da bukatarka ba,dan haka sadakin yata dubu dari ne ba yawa,in kaga zaka iya to ,in baka iyawa afasa",gya
da kai ya shigayi tamkar k'adangare,ba komai abba "za'a bayar,inma yanxu kakeson dana bada se na bayar",da hannu ya dakatar dashi,tare da umartarshi xe iya tashi ya futa, mik'ewa yayi bayan ya mishi godiya,har ya kusa isa bakin k'ofa yace dashi d'aurin Aur
e se bayan sallar juma'a zaayi," ya amsa da to,ba to nike san ji ba,kada wani mutum yazo min kofar gida sai 2:30pm , ya amsa da in shaa Allah abbana.
Jiki sanyaye Ahmad ya futo daga palon abban feedo kota kanta bebi ba,saboda ranshi yayi masifar bac
i,
allah ne kad'ai ya kawoshi gida cikin kiyayewarsa,dan kuwa dushi dushi yake gani cikin idanunsa.
Wayatace ta dau ruri,na basar nasan ba me kirana a irin wannan late hours din,cigaba da kira akai b kakkautawa,raina yayi masifar baci kasancewar na s
anyata a cajine,nikuma ina kwance a kan gado akwai tazara tsakaninmu.
A fusace na nufi wayar da niyyar switchng off dinta,naga sunan baby ya baiyana cikin mamki na yi answering,muryar shi naji cikin shessheka,hankalina yayi masifar tashi nace "Ahmad yad
e,incedai lafiya" , "lafiya kalau baby" ,to "Alhamdulilahi tunda lafiya"
"Baby ba'a taba cimin mutunci irin yau ba," waya bataka? "ni da ka sanar dani zakai tafiya tun jiya,dats why i didnt call,nasan ba lallai na sameka ba" "baby ina nyja ban tafi b
a" "fasa tafiyar kayi?",ehh a'a dama da wasa nike miki," baka tabamin irin wannan wasan ba amma" eh baby hkne.
Abban feedo ya cimin mutunci,baby da umma zata yarda ta aura min ke,babu abunda xe hana a d'aura mana aure gobe,kina ganin in mukazo da abok
aina da iyaye na zata yarda.
Murmushi nayi",haba ahmad daurin auren budurwa sai kace na bazawara ko tattabara,ai ak'alla ba'a k'asaraba,se an sa rana tsawan lokaci,kuma se iyayena sun aminta, sune suke da alhakin fixing date na wedding fatiha ba k
ai ba.
"Baby Abban feedo yamin xagin da tunda nazo duniya ba'a tab'a min rabin shi ba" "Wai wace fido? "Nidea nasan wifey dinka jidda sunanta",yar uwarkuce feedo d'in? "a'a ba yar uwata bace",to wacece?" Ita ce wadda za'a d'aura mana aure tare gobe.
*TEAM FARHA*
[08/02, 22:36] Fulani Khadija Group: *UNIQUE WRITERS ASSOCIATION*
*MATAR SARKI*
*STORY N WRITEN*
*AYUSH ILIASU*
*DEDICATED TO*
*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*A TRUE LIFE STORIE*
*FABRAIRU 2018*
6
⃣
1
⃣
to6
⃣
2
⃣
*SAKON FATAN ALKHAIRI DA GAISUWA GAREKI AUNTYNA UWA MABADA MAMA AUNTY HADIZA .A. ILIASU,WADDA AKAFI SANI DA AUNTY UMMA,UBANGIJI YA K'ARA GIRMA DAI DAUKAKA,ALLAH YA RAYA ZURIAH,YA KAIMU LOKACIN BIKIN NUSAIBA DA RAI DA LAFIYA,INA
MIKI FATAN ALKHAIRI*
Aure Ahmad? "Eh mana ba na gaya miki ba",hmmm "Ahmad kenan dama ai biri yayi kama da mutum ,banyi mamakin haka daga gareka ba." Cikin fushi yace baby ni kike cewa biri". "
"Biri ba na dabba nake nufi ba,a'a ina nufin hakan daka
min ba abun mamaki bane"
"Dama namiji d'an kunama ne kuma kanin ajali ne tuni dama minal tace i should expect worst from you."
Ok!"wato nine d'an kunama",dariyace taso sub'uce min,"wai kai ko b goyon kasar hausa bane duk yanda akai goyon gwari ne,duk
salon maganar dana ambata sai ka mishi direct translation".
Kace min zakai tafiya ?,kada na kiraka ? "cox ba lallai kai answering ba,sannan yanxu kana cemin ka fasa tafiya, gobe za'a d'aura ma aure,cikin wadannan zantukan wanne zan kama(Among the two ,
wic one is d truth),kana nufin de kazama me baki biyu."
" *Farha* pls babu lokacin da zamu tsaya ana k'ananun maganganu,kiranki nayi dan ki share min hawayena,baby ki tausayamin ki amince zaki aure ni a gobe".
Hahahaha "haba Ahmad kode cikin bacci ka
kiranine,yi maza ka farka daga shirmen da kake yi,wonders shall never end,in kana da rai zaka sha kallo,har me akai da zaka saduda?
" Iyayena bazasu tab'a yarda na aureka ba koda kuwa nan da wata d'ayane,kayi hak'uri ad'aura muku aurenku,ubangiji ya ba
ku zaman lfiya da zuriah dayyiba,Ay yiri yiri yiri Ango kasha kamshi.
Gudar da nayi ce ta tashi fayrouxa dake kwance kusa dani,cikin magagin bacci, tace Aunty keda wa haka?da hannu na mata alamun tayi baccin ta,nan ta juya ta cigaba da kwasar bacci.
"Bby ki temaka min,ko a baya ban k'iki ba,ayau gani n dawo gareki na zamto miji gareki,"nidea nace kayi hak'uri,haka Allah y tsara *feedo* ce matarka ba *Farhan* ba
"Baby bazan raba biyun d'aya ba feedo asiri tamin dan na aureta",hahaha "ya zaka d'ora
mata haka,tun tuni bakai tunanin haka ba se yanxu,dan Allah kabar fadin irin haka." In rai ya b'aci hankali ke nemo shi".
"Baby right now kuka nikeyi da hawayena,da ina da ikon fasa aurennan a gobe walhi se na fasa" na ce",kadeyi hakuri a daura "
"Baby kece mace tilo dana aminta kina sona dan Allah, badan wani abu dana mallaka ba,feedo kuwa san datake min ba dan Allah bane," Ahmad pls b'acin rai ya dena saka yin maganganu surururu inde nice na barwa feedo kai har abada",cikin shesshekar kuka yace
"baby Allah ke nakeso,kece burina." A raina nace ta baya ta rago ta gaba ta malalaci.
"Ayyah na tausayama gaskiya Ahmad,amma i can't do anytin se de nace ubangiji ya kaimu goben" dan takaici be ce amin ba,se ni na fada,hmmnnnnn wacece ma feedo d'in,
"baby wallahi ni bawani santa nike ba,tunda muka had'u da ita sau d'aya naje gidansu,shikenn ta dunga zuban naci harta ja hankalina na saurareta,zuwana uku aka kai kudi,"
"Feedo irin yaran nan ne marasa tarbiyya,bata mai da na nagaba da ita abakin
komai ba,infact ko maganar iyayen ta ba ji take ba,worst part of it gidansu babban gidane,ak'alla zaki samu zaurawa sama da shida.basu maida zawarci komaeba,zama ki iya saninta."
"Inbanda abunka baby kai da bakaso na sani ba ya zaka gaya min yanxu, Al
lah ne ya toni asirinka ,da soo kayi kayi aurenka batare da nasani ba,nan kuma gefe ka cigaba da foolin dina,Alhamdulilahi ko yanxu ba abunda zance da Allah se godiya."
"ai babu riba ka bud'amin yanxu, batare daya saurareni ba ya cigaba ," Diyar mala
m sudaiz suhail ce",shiru nayi na d'an lokaci ,sannan nace wanne fa,wanda
ke zaune a rijiyr zaki,ai har sarauta ma ya tab'ayi aka tunb'ukeshi,shiyasa suke jinsu tamkar 'ya'yan shugaba,bayan uban nasu ma sarautar ta kwanaki yayi.
Ahmad yanxu na kamo ba
kin zaren,wato kak'i aurena ne saboda ni marainiyace,feedo kuwa ubanta na raye,ni mahaifina dan boko ne,dan haka ba kowa ya sanshi agari ba,yayin da mahaifin feedo well known malam,kuma basarake."
"To Alhamdulilahi ni ba d'iyar malamai bace,amma inada t
arbiyya dede gwargwado, yar malam dinin ma ta fini iya shedanci, dan kuwa tabbas feedo d'iyar malam ce amma batayo halin malam ba".
"ni babana ba basarake bane,amma harya mutu yabonsa ake ,tare da adduar halinsa na gari ya bishi,yayin da mahaifin feedo
duk wanda yaji sunansa garin nan,zai dorama sharhi akansa na batanci,koda wannan Alhamdulilah ,ina alfahari da tsatsona ,kuma a jikina inaji ubangiji ze bani miji nagartacce.
Baby me yayi zafi haka kike gayamin maganganu zafafa ?
ko d'aya Ahmad
maida martani de kawai nake,"Ahmad bada alfahari ba,ba cika baki ba,Allah da wuya kasamu macen da zata soka dan Allah a duniya kamar ni farha,opportunity occurs once in life,kayi miss using naka,kararaf na yi hanging up call din,zuciyata na turiri ,take w
ani b'angare a zuciyar ya shiga tunamin wani labari da Ahmad ya tab'a ani.
Zuciyar ta cigaba da cemin,Tabbas farha kinasan Ahmad,but ya zama dole ki cireshi a zuciyarki,dan kuwa shidin ba nagartacce bane da zaki sha'awar had'a zuriah dashi,ko kin manta
labarin daya baki na budurwar shi mary,inda ya sanar dake cewa.
Mary matashiyar budurwar ce me shekaru 33,sun shafe kusan ak'alla shekaru biyar suna tare da ita,mary dalibace a jamiar bayero dake kano,iyayenta mazauna lagos ne,musulmace gaba da bawa,a
inahin sunan ta maryam,kawayen ta ke kiranta da mary,sanadin tazo nan buk karatu, iyayenta suka bata gida a sokoto road inda zata zauna,soyayya me karfi ta shiga tsakaninsa da mary,in da lokuta da dama ya sanar dake a gidanta yake kwana,be boye miki irin d
awainiyar da mary take dashi ba,kama daga kan kudade da suturu,duk lokacin da iyayenta suka turo mata kudi to akwai share (Kason sa) dinsa ciki,haka suka k'araci rayuwarsu ta badala,batare da ta san yana da mata ba,ko wannan labarin ya isa kiyiwa kanki fad
'a kiyi mishi gudun shekara.
Sake kirana yayi ,bayan na amsa yace "bby ya zaki ajiyemin waya ,bayan bamu gama magana ba",to ina jinka? "baby ki bani shawara mana,Allah kaina ya kulle,yanxu nake bawa jidda labari ,gata se dariya take min da Allah y
a k'ara."
"Wato jiddan kaje kaba labarin yanda kukai da Abban feedo? "Eh mana".na jimanta kai tare da cewa,A zuciyata nace"Allah nagode ma da ka kawo akasi tsakaninmu be aure ni ba."
"Kana nufin da haka zaka dunga kwasar zancena kana gayawa matarka
,to Ahmad bud'e kunnawa da kyau ka saurareni,baka gina gidanka da zaman lafiya ba,tabbas ka wargaza zaman lafiyar gidanka da kanka, tunkan feedo ta tare,muna nan da kai zakazo ka bani labarin gumurzun da zaa nayi."
Nikaina kasa bacci nayi tsawan dare
n,tunani na shigayi tun farkon had'uwata da Nura har zuwa mu'amalar mu da Ahmad,Allah abun tsoro duniya abun tsoro,tabbas fad'ine na ubangiji Allah bazai d'orawa bawa abunda ba zai iyaba,kuma inde ke macece tagari,ubangiji bazai jarabeki da mijin da ba nag
artacce ba,tabbas hakane,dan babu hanyar da banbi ba dan Ahmad ya aure,amma inaa Allah ya kautar da hakan
Tabbas nima naga iyakata naga ishara,ada banida zance illa BA NAMIJIN DAYA ISA NA SOSHI,dan kuwa duk waddama naji tana cewa tana san wane,haukanta
nike gani tare da yin tir da al-amarinta,aganina rashin abunyi ke sa ka bata lokaci ka so namiji,ni farhan nagane ban da wayo,(Hattara mata mu guji cewa Allah ya kiyaye kayi abu kaza.........,in bakai wasa ba seka tsinci kanka dumi dumi cikin lamarin.watak
ila naka situation dinma yafi na wadda ka aibata.ada ummana har alfahari take dani wajen rashin damuwa da al-amuran saurayi,se gashi an wayi gari nice me kuka akan so ina Allah Annabi a aurene,wanda ada nike ganin over ma dead body nayi hakan)
Tsawan da
ren Ahmad be runtsa ba,Ango daya ke kwanan farinciki to shi wannan kwanan takaici yayi,tunda sassafe abokanshi suke zolayarshi angon feedo kasha kamshi da sauran zantukan na barkwanci.
Waya ya shiga recieving ta abokanshi,inda suke sanar dashi,"In shaa
Allah tun k'arfe d'aya zasu hallar gurin d'aurin aure" maganganun Abban feedo ne suka dawo mishi,take ya dakatar dasu da cewar se bayan masallaci zaa fara hallara
kasancewar tuni aka raba invitation card ,dan haka wasu basusan ance se 2:30pm za'a hallar
a ba.
*Diyar Dabo ce AYUSH ILIASU MUSA.*
[08/02, 22:36] Fulani Khadija Group: *UNIQUE WRITERS ASSOCIATION*
*MATAR SARKI*
*STORY N WRITEN*
*AYUSH ILIAS*
*DEDICATED*
*SHAMSIYYA ABDULLAHI*
*WATTPAD@AYUSHILIASU*
*FABRAIRU 2018*
6
⃣
3
⃣
to6
⃣
4
⃣
*WANNAN SHAFI NA SADAUKAR DASHI DUNGURUNGUN GAREKI SIS SHAMSIYYA ABDULLAHI,TABBAS BAZAN MANTA DA MAHADAR MU BA, WATO MUSA ILIASU COLLEGE DAKE GARIN KANO RIJIYAR ZAKI,TABBAS GODIYA TA TABBATA GA ALLAH DAYA KARA
SADANI DAKE A WANNAN LOKACI,INA ME ADDUAR UBANGIJI YA JIKAN MOMMAH DA ABBAH,UBANGIJI YA KAI HASKE KABARINSU,A KWANA ATASHI BA WUYA A GURIN ALLAH YAU SHEKERA GUDA DA WANNAN BABBAN RASHI,UBANGIJI YA JIKANSU DA RAHMA,YA BAKU HAKURIN JURE RASHIN SU,TABBBAS ,RA
SHIN MAHAIFA BABBAN RASHINE BABU NA BIYUNSA,UBANGIJI YA KARA MUKU HAKURI,YA ALBARKACI RAYUWAR ABUNDA SUKA BARI AMEEN*
*BAN MANTA DAKU BA KAWAYE ABUN ALFAHARI GARENI DALIBAN. MAKARANTAR MUSA ILIASU CANDY 2004 MUSAMMAN SUMAYYA BATURE ABDULAZIZ ,HALIMA M
AKARFI,DOCTOR HAWWA AMINU INA MUKU FATAN ALKHAIRI A RAYUWAR AURENKU,UBANGIJI YA RAYA MANA ZURI AH,AMEEN,AYUSH ILIASU NA ALFAHARI DAKU*
Haka yayi ta kiran abokanshi yana dakatar dasu,wad'anda ya samu y sanar dasu,yayin da wad'anda basuyi answering ba
ya musu droppin message.
Ganin hakan ba mafuta bace,dan kuwa da yawa wasu ma da aka gaiyata be sansu ba,dan haka ya yanke shawarar tura NURA abokinshi dan yaje ya kasa ya tsare.wayar nura ya kira tare da sanar dashi kud'urin sa,nan ya amsa mishi da
cewa in shaa Allah tun kan masallaci ze halarci gurin.
Kamar yanda ya alk'awarta tun k'arfe sha biyu da rabi ya isa gurin,tsaye yake k'arka'shin wata bishiya yana kallon jama'a,sannu a hankalin yaga mutane sun fara hallara,abunda be sani ba shine da y
awa cikinsu masallacin jikin gidan su feedon sukazo dan gabatar da sallar jumaa.
Duk wanda ya tanbaya ze sanar dashi salla h yazo ba d'aurin aure ba,ganin jam'aa se tuttudowa suke yasa shi bin sahunsu ya shiga masallaci dan jin huduba tare da sallar.
Bayan liman ya gama huduba, aka tada sallah aka sallame,nura ne tsaye gefe wajen wata inuwa,zatonshi tunda an idar da sallah jama'a zasu watse,amma se gani yayi wasu ma inuwa suka nema suka zauna.
K'ungiyar samari ya hango tsai tsaye ,ya nufesu ha
d'e da yi musu sallama,Assalamu alaikum,wa alaikasslm,"barkanmu da jumaa","barka kadai