Showing 9001 words to 12000 words out of 37135 words
komiba
Hakama dadyn baiyi magana ba har saida tagama bambaminta kana dadyn yakalleta yana murmuahi yace "ayi hkr momy zan ari bakin babana inbada hkr baxai sake mata cin zarafi irin hakaba..."niba haka nakeson jiba.
Dady sarkin yan raha yasan ha
lin matarsa sarai yagyara zama yana murmushin yace "me kk son ji ?fadi ko meye inda hali sai muyi miki.
Ta hade rai tace "nasan kana goyon bayansa tun ba yau ba bakasan laifinsa don haka tunda yana jin maganarka inaso kasa ya amince da Auren lubna inko
ba hakaba za,aga fushina ackn gidan nan koma inbar muku gidan gabaki daya inhar ba a faranta min da wannan ba.
Dariya dadyn yayi harda tafa hannu yace "ho momyn mu kuma Auren dole zakiyiwa dan naki... takatseshi "au wasa ma kamaida abin ko?
yace " a,
a ba haka bane mamaki kk bani ai tunda naga wai namiji xakiyiwa dole alhalin ko mace ayanxu andaina mata auren dole.
"To naji dolen xan masa inkaso kataushe shi inkuma kaso kazugashi yabujire walh aga bacin raina.
Dayaga serious ne abin nata saiya ju
ya ga Dr ma,aruf yace "babana kaji dai abinda momynka tace yanzu ya xa,ayi da xancen aminatun zaka hkr ne ka auri lubna don farin cikin momynka ko yaya?
Dr ma,aruf ya dago kansa yana sharce gumi agoshinsa na tashin hankali yace " dady walh ina son amina
tu hk itanma tana sona.
"Nasani wai ma aminatun nan waye baban tane?bani kwatancensa ko nasa aymin bincike akansa inyaso saika auresu duka gaba ki dayansu ko hankali yakwanta.
Cewar dady
Dr ma,aruf yace "babanta talaka ne kuma makahone suna zaune
a unguwar rimi basuda kowa agarin nan sai Allah amma asalinsu yn chadi ne inaso inga nataimaki aminatu don mahaifiyarta ma makauniyace Amma daga baya suka samu makantar Allah ne yadora musu..."kace kawai "yar makafi ce! cewar momy tafada ranta abace
"Walh baxata sabuba baxaka kawo mana "yar miskinai gidan nan ba yar talakawa yar matsiyata gara ma tun wuri kabinne maganar ta kafin mubata dakai..." dakata Zulaihat bazan lamunci ki kuntatawa danmuba akan son ranki babu ruwana da talaucin iyayanta ko mak
antarta wannan duk na Allah ne shine meyin komi ga bayinsa kuma akwai jarabta wanda muma bamu wuce yajarabcemuba dan haka ki sassauta masa ki bari yazabi wacce yakeso.
Ta harxuka "walh Alhaji kaji na rantse bazai kawo mana yar makafi ba saidai inhar ya
Auri zabina afarko inyaso daga baya saiya auri yar matsiyatan daga baya shima bada yawu naba.
Harta mike zata bar gun yadakatar ta "kinga zauna zulaihat a tsaida maganar da zata yiwu bana so ki fifita yr "yar,uwarki akan wacce danki yakeso ki sassauta
dan Allah
Yakalli Ma,aruf yace " babana kaji dai hukuncin da momynka ta zartas dafatan xakayi abinda tace ka Auri Lubna daga baya sai ka auri zabin naka.
Idonsa yakada yai jajir yace "naji dady nakuma amince inhar za,a barni na auri aminatu domin it
ace zabin raina.
Dady yakalli momyn yace "to kinji ya amince dan haka kijanye kudirinki da kk ce ba yawunki akan auransa da aminatu tunda yazabi farin cknki.
Tace " hhhmmm aini kuma babu qauna tsakanina da *"YAR MAKAFI* me ake da auran yr matsiya wac
ce ba,asan daga inda ta fitoba.
Taja tsaki ta mike ta barsu nan tahaye sama abinta
Kama kansa ma,aruf yayi jin yana sara masa momy tasa masa tension
Dady yatausaya masa don yasan ciwon so nan yahau tausar sa yana cewa "kayi hkr halin momynka har
yanzun yaki canxuwa kabari in anyi auranku da lubnar sai ayi da aminatun ckn wata biyar ko shida kuma saikayi transfer din aikinka ka koma wani garin da zama da aminatun kabar lubnan anan takarata ita momyn ba shikenan ba tunda matar shige bata daraja (ku
njifa uba me son farin cikin dansa ho l! Dady knn)
😊
Ko dayaje zance gun Aminatu bai nuna mata komiba don xuwansa na uku knn sunsha hirarsu ta masoya tasaki jiki tana nuna masa qauna
Murjanatu taxo sungaisa yabata dubu uku yace tasa kati tayi masa
godiya
Waya yakawo mata yr karamar android techno me dauke da layin MTN
Yabata dubu goma tayi masa godiya don ayau kam yasata farin ciki koda yatafi tashiga gida da murna tagayawa mama tabata wayar taita shafawa tana shi masa albarka
Haka baba
nta ma yasa albarka ta dankawa baba kudin yace "ajiyesu agunki mana Aminatu aikece gidan
Aranar kasa bacci tayi ma,aruf yafaranta mata ranta lallai dole ta amince dashi domin jin dadin duniya yana gareshi tunda aminullah baida kudin daxai sai mata waya
balle harya iya bata dubu goma iya gejin kyautarsa dari biyarce.
Tofa tun daganan son ma,aruf yafara samun matsuguni azuciyar Aminatu
Zasu dau tsahon awa suna waya ta soyayya sunfara sabo inyai kwana uku baizoba sai taji wani iri
Murjanatu ma ta
na taka rawa akan soyayyarsu don itake dorata akai
Akullum takan nusarta akan taso Dr ma,aruf shiyafiye mata domin yanzu ba gwaninta bane yin soyayya da talaka wanda baida aikinyi
Dr ma,aruf yai kwance malemale axuciyar Aminatu yakan kawo musu kayan
abinci buhu buhu ko yadauketa yakaita store yai mata siyayyar kayan kwalliya sannan sutura me tsada yake sai mata yatanadar mata babban tela kwararre yana bashi kudi me tsoka yana tsara mata dinkuna
Mayuka masu kyau da tsada tadawo shafawa aiko fatarta
har kyalli tadawo yi tabbas kyan Aminatu yanata fitowa tamkar balarabiya
Turarikanta masu tsada har murjanatu take daukarwa duk da murjan ma tana gara mata samarinta masu kudine yawancinsu duk sugar dadyne masu nera
Dr ma,aruf yasai musu gidan da su
ke ciki sannan yasa aka buge aka sake masa fasali ginin bulo da bulo yasha fenti yai kyau
Abu daya daya burge Aminatu yakara mata kaunar Dr shine taimakon dayai mata wanda bakowa zai iya mata ba yabiya kudi a asibitin malam aminu kano don yiwa babanta a
ikin ido
Satinsa guda ana abu guda da Allah yataimaka cikin ikon Allah saiga ido yasamu Amma kuma dishi dishi yake gani a ido daya
Ahakan ma angode Allah
Aranar da aka sallamoshi farin ciki suka kasance mara musaltuwa agidan baba yaringa shi masa
Albarka
Mama cewa take "wannan yaro yagama mana komi Allah yasa rabonkine.
Aminatu tace "mama kema yace ai xai sa ayi mk aikin.
Maman tace "to Allah yabada iko Allah yasaka masa da alkairi dai.
Dayaxo da dare gunta tayi masa godiya harda kwal
larta
Yace "meye naki namin godiya iyayanki nima nawa ne aminatu saura mama ma zanyi mata buking asatin nan itama ayi mata ai abun zaizo da sauki itanma tunda dukansu bada makantar sukaxoba waraka zata samu insha Allah.
"Allah yanufa " tace ckn sanyi
n murya
Yace "amin.
Aranar yanaso yagaya mata zancen lubna amma yakasa domin yana tunanin halin dazata shiga
Saida yaje gide awaya suna hira wajen sh dayan dare yafara sanar mata cewar yanada matsala agida anbashi yar kanwar mamansa kuma ance lall
ai saiya aureta kana ya auri aminatun da wata biyar gaba.
"Aminatu ina sonki kada kidamu lubna tasan bana sonta ke nake so dan haka kada kisa damuwar hakan aranki kuma wata biyar kamar yaune
Tace "yaushene za,ai muki auran?
"Satin sama sukasaka d
an Allah kada kishiga damuwa my zinariya i really love you baxan barkiba bakuma zata samu fada azuciyata ba kece uwar gidana ko a aljanna aminatu
Yajita shiru yaxaci ma ta kashene to ashe kuka take nan hankalinsa yatashi yaji tamkar yakoma gidan nasu da
nya rarrasheta
Yai ta bata baki dakyar tayi shiru yaita gaya mata kalamai masu sanyaya rai tareda alqawura kala kala nan ranta yadanyi fari
Da safe kuwa jikinta asanyaye taita yin ayyukan gida
Tashiga gidansu murjanatu sula kule adaki take gaya ma
ta
Aiko ran murja inyai dubu yabaci " jar uba wannan ko tsinan niyar mayya ita dan rashin aji namiji bai sonta amma ta nace toko zamui maganinta walh ba xama zamuiba tashi zakiyi muje gun wani malamina ayi aikin daxaiji yafasa yabujire musu saiya fara
auranki tukun.
Aminatu tace "nifa gara inhakura dashi dama irin wannan matsalar nake gudu.
"Ke banxa ce matsala dake tsoro to bari kiji aure keda doctor kamar anyi dan haka dole kixo muje gun aramma yayi wani abun akai.
Aminatu tace "to bari ingam
a ayyukan gida sai muje.
<><><><><><><><><>
Lubna ta zabga tagumi yayinda tagama waya da kawayenta Aziza da Nabila tagaya musu zancen bikinta da yaya ma,aruf
Momy ce tashigo taxauna kusa da ita tajanye mata hannun datayi tagumin tace mata "to sarkin
"yn saka damuwa arai so kk kirame kafin auran
Lubna tace "momy haryanzu yaya yaki tsayawa mui maganar biki sai binkansa nake yana wulakantani narasa mafita.
Momy ta tausaya mata tace " sha kuruminki diyata nasamo wani malami zamuje anjima Aramma ne
acan tsaunin yadakwari ya iya aiki kawata hky bilkisuce zataxo gobe muje inaso yai aiki akan yadaina son Aminatu sannan asaka masa sonki aransa yaji ba kowa agabansa saike ko ya kk gani.
Da murna lubna tace "haka ne momy naji dadi nagode da taimako All
ah yakara girma.
" amin, tashi maxa kije kixubo abinci kici.
" to momy "
Cikin murna ta nufi kicin don ranta yai fari momy tasata afarin ciki tabdijan aiko inhar yaya ma,aruf yashiga hannunta zaiga wulakanci zata rama duk abinda yai mata....
*Auntyn S&S &Ummiey Xeey*
[7/27, 6:28 PM] FRESH UMMIEY XEEY:
♦
♦
♦
♦
🎗
🎗
🎗
🎗
*'YAR MAKAFI...*
♦
♦
♦
♦
🎗
🎗
🎗
🎗
```written by.....```
*FRESH U
â“‚
MIEY XEEY*
Da
*NABILANCY LUV
💘
*
_auntyn S&S_
*
â™»
REAL EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*
(ZAFAFAA
🔥🔥
🔥
)
*PG 45-50*
A tsaunin yadakwari nan dan tsibbun da murjanatu ke zuwa yake da sassafe tayiwa Aminatu rakiya xuwa can
Yayinda murjanatu taringa kutsawa da ita har " yar bukkarsa
Suntararda wasu mata su biyu sukaja gefe suna jira ka
fin layi yaxo kansu
Ba,a dau lokaciba yagama ganin matan saisu
Gaban Aminatu nata faduwa waiyau itace daxuwa gun boka duk akan namiji lallai Abun babbane Allah yakawo mata dauki bata fatan ta dore da xuwa
Suna zaune agabansa murjanatu tana rattaba
masa yanda takeso abun yakasance
"So muke yaji yakara tsanar yarinyar aransa sannan yabujirewa iyayansa akanta ya tirje inba Aminatuba yabar gabansu kada yai musu biyayya yabijire kawai
Take bokan yace "angama kudire naira dubu hamsin na aikin sanna
n in angama aiki xaku bada na rago da xa,a yanka ayi amfani da jinin.
Gaban Aminatu yafadi jin kudi tsububu ita ina taga dubu ashirin ma balle hamsin damafa matsalar xuwa gun bokaye knn barnan kudi
Murjanatu tace "Allah yaja da zamaninka dubu sha biy
ar mukaxo dashi saidai aimana lamuni makawo ragowar daga baya tunda duk ana tare.
Yahau girgiza kansa yana fadin "maxa kutashi ku koma baxanyi aikin ba inba andire rabin abinda na bukataba wannan shine lamunin.
Murja babu bakin magana tasan halinsa b
a,a masa magiya magana daya yakeyi
Nan takama hannun Aminatu jiki asanyaye suka fuce
Ahanya Aminatu tace " kinsan aikinsa da tsada kk kawoni gunsa ni ina naga wadannan tsububun kudaden sha biyar dinma dan matara sune inbanda ma ma,aruf din yana bani
ina zan samesu gaskiya nahakura kawai abinda Allah yai Annabi sai ceto.
Murja tagalla mata harara tace "ke kinji matsalarki walh karaya gako da tsoron tsiya to bagudu baja da baya sai munyi abinda mukai niyya zamu sake wani gun akwai me sauki akan tudu
can xamuje ko goma baxai bidaba.
"Nifa nahakura kawai tunda shima nasan damunje tsadar zai mana
Murja tace "aiko me ya bukata aikinki zaici hakan don babban aikine kuma ba daya za,aiba don haka biyo bayana sai munje
Aminatu tace "nifa baxaniba n
afasa gara naje nasai mana buhun shinkafa na ajiye
Murjanatu taharareta tace "banda wanda doctor ya ajiye muku har buhuna 2 don son iyawa da son asani zaki kara siyan wasu to ai saiki siya din inkudin ahannunki yake
Aminatu ta dage akan baxata ba mur
ja kuwa tace walh saitaje inko ba hakaba su raba gari tana son tayi "yanci ne
Adole aminar ta hkr tabita xuwa kan tudu gun wani malamin ammafa baikai na yadakwari zafi ba
Suna barin yadakwari da mintina saiga hjy zulaihat da lubna sunxo suma gunsa
Kawar hjy zulaihat ce takawosu gun itace idon gari tana zuwa yau da gobe
Hjy bilkisu tana gaba suna baya
Suka xaxxauna gabansa shiko yanata tsibbace tsibbacensa
Hjy bilkisu tagabatar masa da hjy xulaihat tareda nuna lubna tafadi dalilin zuwans
u akantane
Momy zulaihat ta fayyace masa komi tareda fada masa yadda suke so abin yakasance "so muke ya amince da auran nan na lubna da muka hada ayi komi ckn sauki yayi rawar jiki akai acire ms son aminar yadawo son lubna fiye da Amina sannan ya mance
da batun aminatu kana yaringa rawar jiki akan lubna duk abinda tace yabi ba musu.
Boka yace "angama adiremin dubu dari yanzun nan.
Take ba fargaba balle musu ko neman ragi momy ta dire masa dubu dari
Yace "aiki na akwana uku yakeci zakuga komi yak
asance ammafa a wata uku xai iya karyewa tunda ba fadar Allah bane saidai inkunso zaku dawo ku dora wani akai
"To ai wannan ba wani abu bane mudai muga yacin tukun inyaso madawo adora daga inda aka tsaya.
Inji momy
Lubna ranta fari qal zata rin
ga juya ma,aruf lallai duniya sabuwa yaya ma,aruf zai zama nawa . Tafada aranta
Bayan yabata magunguna dazata ringa wanka dasu danasha da kwalli daxata saka sui toxali saina abinci dazata saka masa in anyi aure harda na tsarki don inya sadu da ita yaji
baxai iya rabuwa da itaba( kai jama,a Allah yashiryamu yadawo damu hanya.)
<><><><><><><><><>
Sai bayan sallar azahar su aminatu suka dawo rubutune leda biyu yabata wai intasha zataga biyan bukata dubu biyar ma yabukata
Murjanatu nata mata mita "
gaki kamar wayayya amma sai ahankali gun malamin ma saina mk dole zakije alhalin kanki xaki gyara aidai kowa rai yaiwa dadi ba ya maishi.
Itada tsabar gajiyar datayi ko uffan batace da itaba jan kafa kawai take tana tuba ga Allah don tana ganin anyi na
karshe
Tashiga gida agajiye tilis
Sallah tafarayi sannan ta leka dakin mama tasameta da kwano agabanta taci abinci dama takan zuba abinci akula ta ajiye mata kusa da ita sbd inbata nan ko zataji yunwa
Dayake ma babanta yana dan futa da sanda duk d
a idonsa daya yana gani abun yaragar mata yakan taimakawa mama inbatanan
"Sannu mama kinci abincin knn.
"Naci tun daxu aminatu kun dawo knn.?
mundawo mama baba fa?
mama tace "yanzu yadan dogara yafuta masallaci.
Aminatu taxuba nata a pal
te ta koma dakinta don taci abincin itama
Tana daukar wayarta daniyyar takira ma,aruf sai taga missed call dinsa har 5
😳
Tuni tabi baya da sauri
Bai dagaba saida takatse yabiyo baya
"Hello zinariya ina kkje haka naita kira no answer?
Tace "nafuta gidansu murjanatu sai yanzu nashigo.
"Ok dama inason ingaya mk ne zanzo indaukeki anjima muje store kizabi irin atamfofin da kk ra,ayi domin kala daya zansiya muku keda lubna baxan bambanta ba.
Tace "to dear saikazo.
"Ki zauna ackn
shiri ana magriba zanxo.
" allah yakawo minkai lfy.
Nan sukai sallama
Alokacin dayake wayar yana dinning table yana cin abincine yyinda lubna ke labe tanajinsa tsaf duk abinda yace da Aminatu
Bakin ciki fal ranta takaici yatsaye mata yanzu dan
wulakancima ita datake amarya yawan kayan ta da kalar babu bambamci da wacce ba ita za.a auraba lallai wannan abin nasa yakai kololuwa zakuwa tayi maganinsa kwanann nan
Dayake ta saka kwallin da ka bata dan haka ta tunkareshi yayin data kirkiro murmush
i taja kujera taxauna kusa dashi
Yaga xuwanta gun amma baikalletaba
Ta gaidashi ya amsa dakyar kansa akasa
Tace " barka da hutawa yayana angona to be.
Ya dago dakansa xai mata bala,i jin takirashi da angonta
Amaimakon yai bala,in dayai niyy
a sai yaji wani abu ya tokare masa kirji idonsa yatsaya cak akanta yakasa daukan mataki n dayai niyya
Kallon kallo sukaiwa juna