Showing 1 words to 3000 words out of 34383 words
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_YAR GWAL_*
( ~me kayan Dadi~)
ππ
π
_the sugar daddy Story_.
π
οΈ
ππ
*Awnnnn*!!
π
*Nabilancy ta dawo da karfinta,Amma fa kusani fans tsayawarta a rubutu
tsayawar yin comment din kune,Dan haka duk littafin da aka fara in anga bai karbuba gara abarshi domin ku mukeyi,Dan haka acigaba da karfafa Mana guiwa Tanks*
ππΌπ₯°
inayinku masoya Ina kallonku Ina godiya da Nuna kauna.
*daga Marubuciyar KUYANGA Nabila
ncy love Auntyn S&S*
π
Part 01
Ta fito kofar gidan nasu tana yanga tana girgiza kamar kifi taci kwalliya kamar zataje gidan biki ko wata babbar dinner.
Wani material ne ajikinta me fitarda sheki ya Kama jikinta koina adame kamar ajikinta aka Dinkashi,
gashin dokin da akai Mata kitso dashi ta zuboshi gadan baya tamkar nata har mazaunanta suka dira.
Tun daga nesa kafin ta karasa gareshi yahau sakar Mata Kayataccen murmushi don kam ta Gama siyeshi wankan nata ya tafi dashi,ji yake kamar yatafi da gudu ya
taro ta.
Yana cikin motar tashi ta karaso cikin yauqi tana kada idanu ta shiga motar da sallama tana tashin kamshin tsadadden turare.
Kirarin daya Saba Mata shi yahau Yi Mata yau Wanda yake matuqar fasa Mata Kai."kaga zinariya acikin Mata *'YAR
GWAL* Me abin marmari kyakykyawa acikin kyawawan Mata kalar mota kalar Babban Gida.
Murmushi kawai take zubawa tana kada idanu.
"Fatan my sugar kana lafiya.?
Ya kyafa Mata idanu Yana fadin"sumul ma kuwa amaryata.
Tace"yau ShopRite nake son zuwa na kwan
a biyu banci shawarma ba my sugar.
Yayi Saurin tada mota Yana fadin"to atafi yanzu ko sai anjima?
Cikin Jin Dadin yanda yake mata tace"Eh ma iya tafiya yanxun.
Take ya tada kan mota ya kadata titi sai Ado bayero mall.
Sunfi awa guda acan tun 6pm da suk
a shiga sai after 7 suka fito
Tasha Ice cream taci shawarma sannan suka shiga bangaren shopping ta Loda kayan cima danginsu alawowi da mint cingom da chocolate dasu biscuits wafa da take loving
Haka suka fito suna nishadi suka nufo Gida amma Saida yabi
ya da ita ta yahuza suya yasai Mata kaza.
Ahanya tanata zuba Masa Shagwaba Wai ita tafiso yahado Mata lefe a Dubai.
Shikuma yace kwantar da hankalinki aike Yar gwal ce ta gaban goshi abinda duk kikeso shi za,ai Miki aduk inda kikeso acan za,a hado,inma k
udin kikace abaki ki hada da Kanki sai abaki my madam.
Ta lumce Ido cikin Jin dadi ta bude idon tana kallonshi tana fadin"Kai my sugar gaskiya inajin Dadin nunamin kulawar da kk,Ina godewa Allah daya bani Kai.
Dariya yayi yace"kinsanfa Ina sonki ban
Kuma taba Auren so ba sai akanki nasha fada mk matata ta fari bani ita akai Auren dangine,ta biyun Kuma ubanta nake bin bashi yakasa biya shine yabani ita sbd baida abinda zai iya biyana to ke kuma Mata ta uku danakeji da ita tunda naganki naji duniya Bab
u wacce nakeso saike Kinga meye bazan Miki shiba,ai babushi adoron duniyar Nan ke nifa ko cewa kikai inringa goyaki akullum agadon bayana Ina yawo dake zanyi don samuwar farin cikin ki.
Dariya tayi tana fadin"to naji my sugar Ni kasan me Nakeso?
Yace"sai
kin fada.
Tace"mota nakeson kasai min in munyi Aure ka bani ita amatsayin gift marriage.
Yace"Ah wannan ba damuwa bane,Zan duba wata yr Vibe nasiya Miki wacce kala kikafi so?
Tace"kalar Mata Dai Pink ko Ash suna min kyau,wane kala ne da matanka?
Yayi
Jim kana yahau fara,a Yana fadin"Eh to Uwar Gida yanxu ba mota a hannunta tun da ta lalace ta siyar kafin asai Mata wata duk da ba damuwa dama tayi da Hawa morarba saidai yaronta yahau dama Wanda ya Gama sch dinnan to ita Kuma abokiyar zamanta Yar karyace
ita Dole sai babbar mota zata hau Kuma ita ba Yar kowan kowa ba inkinga yanda na daukota awahala Amma tafison ta goga Dani irin tawan Nan take hawa kema in irinta kikeso sai atanadar Miki.
Ta girgiza Kai tace"asaimin vibe dinma kafin inzo kan babbar.
Yac
e" to ba matsala baby.
Da suka iso Gida bai wani dadeba ya tafi dayake bikin ya iso saura wata guda ta Kori kowanne saurayi sai shi kadai take kulawa tunda aka tsaida musu ranar Aure.
******
Anyi kwana biyu da rabuwarsu yace Mata yatafi Dubai zai shigo d
a wasu kayansa taringa murna tana cewa shikenan ma ankwa gdn Sauki tasan kayanta zasu iso a ckn sauki Kuma tasan inshine ya zabo kayan zasu fi ganuwa.
Taringa Masa fatan Alkairi.
Aranar da farin ciki ta wuni gashi Kuma kawarta ta kirata tana tafe zuwa gi
dansu.
Taringa murnar zuwan halimatu sbd sun Dade Basu haduba tanaso dama tazo suyi maganar Fitar da Ankon bikin tunda ya matso.....
Muje zuwa
______________________________
ππ°
AINUWA
πΌ
RITER'Sβ
πΌ
*
π¦
SSOCIATION
π€π»
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
______________________________
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_YAR GWAL_*
( ~me kayan Dadi~)
ππ
π
_the sugar daddy Story_.
Page 02
Zubaida ta Gama Girkin data Dora na jolouf din shinkafa Tasha kifi gidan yadau kamshi.
Tana Jin sallamar Shigowar mahaifiyarta sun dawo daga Bara itada kanwarta uwani.
Taja tsaki tana fadin"ya Allah ka azurtani Inna ta daina fita yawon barar Nan. Ta Mike ta Isa wajen rishon da tukunyar abincin data Gama ke Kai,ta dau roba a kwando ta zuba musu abinci taje takai musu.
Innar tace"Ashe kina cikin gidan.?
Zubaida tace"Ina
Nan inna,da Zan fita Kuma sai halimatu tayi min waya tana kan hanya ta taho shiyasa na zauna,dama gidan kawu zanje gun matarsa in karbo dinki,ga abinci kuci.
Innar tace"mungode Allah yayi Miki Albarka,uwani debo min ruwa.
Uwanin ta Mike ta nufi Randa.
Ita Kuma Zubaida ta kalli Innar tana fadin"gaskiya Inna yakamata ki tsaya da fita barar Nan sbd kada wataran Wanda Zan Aura dinnan ya ganki bazanji Dadi ba,ki kalli gidannan Dana gyarashi ta waje Babu me tunanin matar cikin gidan mabaraciyace kina zubar m
in da kimata fa Inna,Kinga dai Yana da Mata kada wataran su goranta min indai abincine Ina dafawa in Baki kici ga kayan abinci can a dakina sannan nayi Alkawarin indai nai Auren Nan Zan ringa kulawa dake tunda gidan Hutu zanje mutumin nan me kudine nasan Z
an huta shiyasa naqi Auren Talaka Dan Kar Nasha wahala,A Dole ba Dan naso ba na Hakura da Haidar saboda Sana,arsa Bata Kai ta kawo ba Dinki yake nikuma Naga me na sama yaci bare na kasa Dan nikam na Raina tela indai a kano yake,gara ma idan a Abuja ko Nija
r yake dinkin to da gwasama Amma Kam Babu Riba a Auren Talaka in kana Dan Talaka.
Innar Tai shiru tana jinta.kana tace"Ina rabaki da hangen Dala fa Zubaida,sbd kwadayi mabudin wahala ne,Kibi a Hankali bana son kiringa hangen Dala, kiyi Aure domin Allah,ni
kam indai ta nice Allah zai kula damu,nafison kiyi Auren da Zaki zauna Zama na har Abada,ke marainiyace,A wannan barar da Kika tsana da nakeyi shekara da shekaru nake samu intara kudi inbiya muku kudin makaranta har Kika Gama sakandire ga kanwarki ma tana
kanyi Kawunku Yana Dan taimaka min Amma shima bashi gare shi ba ita
rayuwa Yar hakuri ce,nafison ki kauda kanki akan barar Nan tawa Ina Alfahari da ita tunda Ina samun rufin Asiri kullum Adduata Allah yabani nayi muku,Kinga Ni makauniyace in banyi barar ba
ma wankau zanyi ko surfau? Kinga Babu wannan damar,kiyi hakuri Xanta Miki Addua Allah ya Buda Miki kiyi Mana tunda kinada wannan burin,Amma bana son kiringa hangen Kudi zakije nema agidan Aure,kiyi Aure tsakaninki da Allah shine zakiga dakyau a lamarin,Ku
ma yanzu ahakan adashi nakeyi, Ana bani dashin Zan biya kudin kayan gadon da nasai Miki na hannu.
Zubaida ta zabura ta Kama Baki tana fadin"Kai Inna,kayan hannu Kuma!,sakan fa kenan? Haba Allah ya rufa Asiri inje da kayan hannu Babban Gida ,gidan me kudi,
kawai inkin karbi kudinki ayi wata hidimar dashi Amma munyi da Alhaji zai bani dubu dari biyar na yin shagulgulan biki dasu nakeson insai kayan daki,dama kayan kicin na kammala siyensu tuni,Kuma zai Bada sadaki daban.
Innar tace"to madallah ubangiji yakar
a rufa mana Asiri.
Zubaida tace"Amin dai Inna,yanzu haka ma yatafi Dubai daga can zai tahomin da kayan lefe Kinga ai Nima nazama babbar yarinya wacce Zan shiga sahun manyan mata Adama Dani, tunda fa har mota zai saimin.
Innar tace"hhhuumm zubaida kina da
son duniya,shiyasa Kika guji haidar,nikam walh yaron yayi arayuwa gashi da sanyin Hali ga ladafta manya nikam da uwani ta Isa Aure da ita Zan bashi kawai komai rashinsa, tunda Allah ne me wadata bawa a sanda yaso.
Zubaida ta hade Rai kana tace"lallai In
na,Ni narasa me haidar dinnan yai Miki na Alkairin da kike sonshi mutumin da ko dubu biyar bazata iya fita a jikinsa ba,to ai saikiyta Masa tanadin uwanin.
Ta bar gurin tana mita.
******
******
Tana Shiga daki ba dadewa taji sallamar Shigowar kawar tata h
alimatu.
Tajiyo ta agun Inna suna gaisawa.
Ta tarota da sauri tana fadin"ga 'Yar jirgi ga 'Yar jirgi.oyoyo
Halimatu ta sheke da dariya tana fadin"walh bakida mutumci kawata,wato ma nice me jirgin?,to jirgin me nayi Miki?
Suka zauna akan katifar
dakin zubaida na fadin"To ai Dole na Fadi hakan kawata,sbd kwana nawa kina zakizo bakizo ba gashi har biki yazo gab ko anko ba'a fitar ba anata tambayata.
Halimatu tace'to yanxu dai tunda nazo ba sai muje yau Kasuwar mufito dashiba,karshen jirgin dai ya k
are ke da bakya yiwa mutum uzuri kinsan wahalar higher institution kuwa? To walh Inba Hutu akai ba bakada kwanciyar Hankali ko Rana daya kace zakai missing bakajeba sai kaji anyi Attendance ko test ba Kai,in tsautsayi ya ritsa dakai Kuma Inka Rasa wadanna
n ka rasa C.A dinka Kuma Exam take shafa Kinga ai Dole mu kiyaye karmu matsa can da Nan,ga Kuma unguwar taku da Dan banzan nisa Ni walh tunda Muka tashi a unguwar Nan tafita araina bana son ma zuwanta.
Dariya zubaida tayi tace"lallai wato Dan kin shiga ci
kin gari ko,kinje unguwar 'Yan gayu shine unguwar tamu ta fita aranki,Allah yasa inkinyi Aure a kaiki kauye.
Halimatu tace"Amin, ai walh kinganni indai da Wanda nakeso ne ko inane Zan bishi,banza da zakiymin fatan tsiya to bana shakku.
Dariya zubaida ta
yi tace"to dai Sha ruwa ko ki Fara cin Abincin inkin huta sai inbaki storyn Angon.
Ta janyo Mata Kular Data saka Mata abincin da plate da cokali akai.
Da kanta ta zuba tahau ci tana fadin shegiya kawata har yanzu zaqin hannun Yana Nan,ke kam ki godewa Al
lah kin iya girki duk abinda kikai sai an yabeshi Kinga bake ba wulakanci agun kishiyoyi.
Dariya zubaida tayi tace"hhuuumm Dan ma yace kowa da part dinsa Kinga kowa kicin dinsa na bangarensa ba girki zamu ringa Yi tare ba,bare su San testing din girkina,g
un miji kadai zaka ciri tuta idan yaci ya banbance.
Halimatu tana Loma tana fadin" Kuma matansa nawa?
Zubaida tace"Sugar babyna matansa biyu Ni ta uku.
Dariya halima tayi kana ta Kora ruwa ta dire kofin tana fadin "Eh lallai sannu ta uku,harma kin Shiga
kenan.
π€π
Zubaida tace"to me ya rage? Saura fa wata guda.
Halima tace"to Allah dai yasa aje a sa'a Dan mazan yanzun abin tsoro ne,ba komai suke fada yake tabbata ba.
Gyara Zama zubaida tayi tana fadin"hhhuumm hakane shiyasa fa na ajiye batun
haidar A gefe na dauko babyna,sbd Auren Magidanci me Hankali yafi,don samarin Nan sai karyar tsiya suka iya ba fus!
Zubaida tace"Aa ba girirn gurinba dai Tai Mai! Walh suma dattijan Ana samun masu shegiyar karya,ai Namiji ko ya tsufa baya daina halinsa,ke
dai kawai Allah yasa mudace Amma mazan nan! tab!! Ai sha'ani.
Zubaida ta janyo shisharta a kasan tebur ta Dora gawayin zata kunna kenan halimatu ta dakatar ta.
Karki sake ki kunna wannan abar agabana,walh Zan tashi natafi.
Kama Baki zubaida tayi tace"ya
ushe Kika daina Shan abar ke,?Naga agunki na koya.
Halimatu tace"tun barina unguwar Nan na tuba,walh Nagano illar Shanta bare mu Mata in bakiy yaqi da shantaba ma walh zata rage Miki kima agun Wanda ke ganin kimarki.
Zubaida tace"an Dade ba,a daina ganin
kimar tawaba walh bazan daina ba nishadi ce fa kema kinsani,abinda ba bugarwa takeba,Ai ko naje gidan Alhaji Shan kayata zanyi Yanzu dai baisan inashaba.
Gyada Kai kawai halima tayi kana tace" to Wanda baiji Bari ba zaiji woho.
Tayi Mata banza ta kunna D
atar wayarta bayan ta turar da kwalbar shishar agefe.
Halimatu na Gama cin Abincin tace Mata"yakamata akiramin Angon ahadamu awaya mugaisa ai.
Zubaida tace"ango yatafi Dubai Bari muga ko Yana Online saiku gaisa ta vedio call.
Nan ta dubashi taga
baya on-line tace da halima to sai dai ahaduwa ta gaba yau kam ba rabon ku gaisa Dan baya on-line.
Halimatu tace"Dan kasuwa ne kenan.?
Zubaida tace"Eh Yana kasuwanci Yana taba harkar siyasa yanzun dai yaje shigo da wasu kayansa can sannan zai hadomin lef
e acan din.
Tabe Baki halima tayi kana tace"hhhuumm abinda akeso ya samu kawata,karya zata Karu kenan za,a Auri me kudi.
Dariya zubaida tayi tace"Aa ba zancen karya fa kawata,Annabi ma yace mu nemi Tsari da Talauci Dan haka abarni in zaba in
darje,tunda ba dacewar ace nataso abakin Talauci Kuma na Auri Talaka ai Kinga innai hakan banyiwa kaina Adalciba.
Halima tace"Allah ne dai meyin,me Kuma tsarawa bawansa komai,Kinga shine bai rubuto Miki hakan ba da bazaki tsallake ba.
Zubaida tace"Allah
Yana so na ne,,
π
kema fa idan na dandalo kamar kece Kika dandala mubar wannan maganar mushiga wata huta muwuce Kasuwar ma.
Halima tace"Amma to matar Alhaji ahadomin kwance ma intafi dasu,nasanki da kayan gayu,Kuma ga manya na Dubai suna tafe,kinsan mu dal
ibai kullum ahanyar fita namu kodewa sukeyi.
π
Zubaida tace"angama Zaki samu kamar kala biyar muje mu dawo dai.
Halima tace"tashi muje kawai tunda kwari ne muna da shagon da muke zuwa ai ba dadewa zamui ba za,ai party ne?
Zubaida tace"Eh to asona ma kal
a biyu nakeson ayi daya ayi dinner a hotel daya Kuma ayi a restaurant bridal shower ko arabiyan night sai kamu da zamui a gidan Dan hausa Kinga anko Uku yakamata ma afito dashi.
Kama Baki halima tayi tace"gaskiya Zaki hada mutane da aiki,Anko daya za,a fi
to dashi na dinner ko na Kamu ki zaba sannan ki Raya bikinki da Adduar mutane bawai da shagaltar dasu a bidia ba nidai a shawarce ki kansile wani Sha,anin walh Rayuwa tayi tsada gara wasu kudaden kisai wani Abu ki Kai dakinki Amma inkin yarda knn.
Zubaida
tace"to Ayi dinner kawai tunda shi yakama gun dinner din.
Halima tace"zaidai fi hakan,Amma Ni kisani inzanyi Aure taron yini kawai za,ai a kofar Gida ba inda zanje wani Sha,ani.
Zubaida tace"Nima dama ce Allah yabani tunda miji me citta ne,da bashida ko
mai bama Zan tarkaba.
Dariya kawai halimatu tayi ta dau Jakarta suka fice.....
Sunfito da anko me saukin kudi shima Saida halima ta dage da hakan Amma Kam ita zubaida Yar dubu goma Sha biyu taso afitar.
Amma sai halima tace 'Yar 8k zasu fitar
saboda masu yin akeso suyi dayawa.
Sundawo a gajiye Gida,sai gab da magriba halimatu ta wuce gidansu sukai sallama Bayan ta Bata kayayyaki da mayafai da takalma da jakunkuna saboda Aminiyace gashi ita Yar son budawa ce zubaidan,gidansu halimatu na Rijiyar
Zaki iyayanta sunada rufin asiri Dan gini sukai suka koma can....
Bayan kwana biyu Alh yace da zubaida yadawo daga dubai Gobe ko jibi zaisa akawo kayan lefen.
Tace to gidan kawunta za,a Kai kayan tunda ai dama yasan gidan.
To fans atara zuwa karbar kay
an lefe Yan dubai
π
π―π½
ββ
οΈ
*YAR GWAL*
( ~me kayan Dadi~)
_the sugar daddy story_
Na _Nabilancy love_
π
*Auntyn S and S*
______________________________
ππ°
AINUWA
πΌ
RITER'Sβ
πΌ
*
π¦
SSOCIATION
π€π»
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is
to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
______________________________
Page 03
A Daren da Alh yadawo daga Dubai tana daga kwance Bayan tayi sallar magriba tana Shirin Bude data don ta
tutturawa sauran Yan uwa da kawaye Ankon bikin, saijin sallama tayi daga waje yaro na cewa Ana sallama da ita.
Tasha mamaki to waye wannan haka da batasan da zuwansa ba.
Tasan dai Idan sugar love din tane waya zai doko mata barantama daga dawowarsa daga
tafiya bazai fito ba.
Da kokwanto ta fita wajen Dan ganin waye din.
Tasha mamakin ganin Haidar Wanda baya zuciya da abinda take Masa.
Dakyar ta karasa gurinsa Ranta abace.
Yana zuba murmushi Yana kallonta cikin So da kauna.
Tana Isa gareshi taja tsaki
tana fadin"da ace nasan kaine tun kafin na fito da walh bazanyi wahalar fitowa ba sbd kafi kowa sanin ba,a zuwa gurina ba tare da izinin yardata ba.
Dariya yayi Yana shafa sajensa,kana yace"girman kujerarki Zuby walh yau kewarki ce ta tusoni gaba,kaunarki
taqi barin cikin Raina,nakasa jure rashinki Dan Allah Auren da kike cewa zakiyi tabbatacce ne?
Haushinsa fal arai tace"Dawa kke musu in rabaka ne haidar? To kajira zuwan invitation Dan Ina me sanar maka ma gobe ko jibi za,a kawo kayan lefe na ma,Kuma na
Gaya maka bana Ra'ayin Auren Yaro sai Magidanci,bawai Kaunar ka ne bana Yi ba kawai Ra'ayina ne yawuce kanka.
Ya gyada Kai Yana fadin"ba matsala Zuby,Ina Yi Miki fatan Alkairi,ga wannan.
Ya Miko Mata wani Abu a nannade da takarda me kyalli.
Ta karba tan
a yatsina kana tayi Masa godiya a wulakance.
Yai Mata sallama