Showing 12001 words to 15000 words out of 34383 words

Chapter 5 - YAR GWAL COMPLETE

sau daya a sati.

Har gani yake ko batada lafiya ne.

Akwai ranar da yadauketa ma yakaita gun wata me magani aka hado Mata magungunan Karin Ni'ima da Kara sha'awa da kuzari

Amma data Sha abanza baiga canjiba duk da Bata shanye duka ba agabansa ne ta Fa

ra Sha yagani.

Ahakan yake hakuri da Zama da ita sbd Yana sonta sosai.

Ta shirya fita zuwa Lagos don saro lasa lasa Kuma ya barta don har dubu hamsin ya Kara Mata...

Tare da Mahmud zasuje shi ya biya kudin jirgi da zasu tafi

Shima ya Kara Mata da dubu

dari takara jarin.

Hotel suka Kama don sati suka shiryi suyi sai sun huta zasu dawo Kano.

Amma fa suna cikin Nishadi Hankalinsu kwance ga kaunar juna da sukeyi....

To mukam saidai muce Tirrrr!!!!

😏

*YAR GWAL*

( ~me kayan Dadi~)

_the sugar daddy story_

Na _Nabilancy love_

πŸ’˜

*Auntyn S and S*

______________________________

πŸŒˆπŸ‡°

AINUWA

πŸ‡Ό

RITER'S✍

🏼

*

πŸ‡¦

SSOCIATION

🀝🏻

*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

______________________________

Page 07

A can Lagos dai anata gudanar da nishadi tsakanin Mahmud da Besty

dinsa Zuby matar Dad dinsa

Wanda suka Kama hotel daki Daya suke kwana.

Amma har suka Gama kwanakinsu Bai kusanceta ba Kam,Amma nayi romance anyi shafe shafe da tsotse tsotse ahakan ake yin release Kuma suna gamsuwa.

Shima Haka ya Kara Mata kudi ajikinsa

ta Kara jari

Da suka dawo Babban shago ta Kama awata plaza ta bude boutique na kayayyakin saidawa lasa lasai da atamfofi sai English wears da inner wears kayan yara dai na gani na Fada,sai gurin gyaran jiki da make up data saka yara agun Yammata ne da s

uka kware awannan fannin.

Hakanne yabaiwa Zuby damar yawo duk inda taga dama zataje ko Bata Gaya wa Alhaji ba.

Kuma baya taba magana sbd bayason bacin Ranta.

Ba asiri tayi Masa ba Amma juyashi takeyi son Ranta.

Amma acan bangaren

kishiyoyinta abinda suke gani Kenan baya ma Aunty Amarya da Maman yara don Hajiya Babba taja girmanta su ma ba Shiga shirginsu take ba bare Zuby da ba Gida daya suke yanzuba.

A bangaren Mahmud da Ya samu Aikin gwamnati yasamu a gidan gwamnati office yake

shiga tun daga Monday har Friday bashi da time always busy sai yazamo sai weekEnd suke haduwa Amma Koyaushe suna tare awaya sbd takai yanzun sunyi mugun sabo da juna.

Mahaifiyarsa Hajiya Babba ita ta ritsashi da zancen Aure.

"Mahmud kaine Babba Amma har y

anzun Banga alamar zaka kawo Mana wacce zaka Aura ba ko baka yin soyayyar ne a nema maka a Dangi?

Ya hau girgiza Kai Yana fadin"bana son Auren Dangi Kuma abani lokaci me tsayi Dan Kam wacce Zan Aura karatu takeyi na Doctoring Kinga zata Dade Bata Gama ba.

Hajiya tace"Ai Naga Aure Bata Hana karatu ko,da sai ayi taci gaba da zuwa agidanka,Naga ka samu Aiki ga Gida da mahaifinku ya Gina Gida biyu ajere iri daya yace ka zabi daya kabawa mansur daya,Kuma shi

Naga har yazowa mahaifinku da maganar Yana so atura

gidansu yarinyar yanason yakai kudin Aure Kuma shine kasa da Kai.

Ya Sosa keya Yana fadin"bazaki ganeba mom,shi fa Aure lokaci ne,Dole dama Wataqil Allah yarubuta Shine zai Fara kafin Ni,Dan Haka aita binmu da Adduar da ake Mana.

Tace*"To Allah ya tabbat

ar muku da Dukkan Alkairi.

Yace"Amin ya fice.

*****

*****

Nafisa kanwar Mahmud me bin mansur ta haihu su biyu Alhaji ya Aurarsu tare dama ita da Anisa kowacce tana Aure a gidan Rufin Asiri ita Anisa Babban Dan kasuwa take Aure,ita Kuma Nafisa Wani Dan

siyasa take Aure shine shugaban jam'iyya ne Wanda shine ma yasamawa Mahmud Aiki acikin gidan gwamnati.

Ita Anisa matar Dan Kasuwa har yanzun Bata Sami ciki ba shekara huda da Aurensu.

Nafisa kuwa tayi Bari sannan ga twins ta Haifa mace da Namiji

An

shiryi gagarumin taron suna a hotel za,ai.

Har anko aka fitar mijin mejego yasaiwa Mata 50 na zuwar dinner abangaren ta Mata 25 anashi bangaren ma Mata 25

Hajiya Babba ta Aikowa Zuby tata Ankon.

Taji Dadi sosai ta kuma yaba da Atamfar tuni ta nema Mata

gyalen da zaishiga.

A kullu yaumin shiyasa take kaunar Hajiya Babba macece Adala me sanin yakamata shiyasa take Bata girmanta takanji inama batasan Alhaji ta Aureshin ba Mahmud take Aure.

Amma zata Yi duk yadda zata Yi don taga ta dawo mallakin Mahmud t

a ruwan sanyi.

Wata zcyr tace Mata "!Kai!! To ta Yaya!Ai Abu ne da kamar wuya ko Mutuwa Alhaji yayi ba Zaki Aure da Mahmud ba ko Baki haihu da Alhaji ba.

Ranar suna taci Ado sosai anyi Mata make up ta hadu iya haduwa.

Da taje gun dinner ita akai ta kall

o domin tafi me jegon ma haduwa.

Gashi ta fito tana ta liki ta lika kudi Rafa biyu duk Rafa daya dubu biyar ce.

Aiko sai mawaqi wato me DJ Yahau wasata, yaringa babatun Kiran sunata da Bata suna Gimbiya zubaida Amarya ga Alhaji.

Ta dunqula Masa rafa day

a.

Wannan Abin ya tsayewa Aunty Amarya arai taga ta muzanta Amma maman yara ko ajikinta

An kusa tashi ta Kira Mahmud awaya tace Masa yazo ya maidata Gida ta Gaji.

Shi ma alokacin Yana kusa da gun baije aiki ba Amma baiyi nisa ba.

Kafin yazo tana

farfajiyar hall din tana jiransa tana latse latse awayarta sai Jin tayi anzo wucewa ta kusa da ita an bangaje ta.

Ta dago Ido ahankali tana son ganin wacce me karfin halince ta bugeta kuma bama ban hakuri.

Ganin kishiyarta ce Anty Amarya sarkin Yan kishi

sai tayi Saurin janyota ta baya saida kuwa rigarta ta yage Allah yataimaka Babban gyale ta sanyo.

Da takaici Aunty Amarya ta dawo da baya ta wanke zubaida da Mari adaidai lokacin da Mahmud ya shigo farfajiyar Kuma yaga abinda yafaru..

Yayi farkin ya is

o gun da sauri Yana kokarin tsaidashu da rigimar

Dafe kuncinta zubaida tayi tana fadin"Lallai Zaki San kin Mari mace me aji da Matsayi mace me fada agun miji 'YAR GWAL kafi zinare.

Aunty Amarya ta yatsina fuska tace"walh karya kikeyi,Ina matsayin yake,Ai

da bamusan tarihin balbelaba da sai muce daga misira take,to Dadin abin munsan ba Yar gwal bace Yar Makauniyace....da sauri Zuby ta zabgeta da Mari Kau!!kau!!!

Tsakiyarsu Mahmud yashiga yana Basu hkr don su bar cacar Bakin

Ita Aunty Amarya tana

fadin"zakisan Ni kikawa wadannan marukan,walh sai nayi maganinki banza mushirikiya Mai bin malamai akan mijinmu.

Ita kuma Zuby Fadi take"wannan Marin da kikai min daya na Rama da biyu Dayan na sakamakon Marin ne Dayan Kuma na alamun sakinki da zansa ayin

e,banza jahila.

Sosai Aunty Amarya taji dacin wannan zagin ga zafin Marin da zubaida Tai Mata ga muggan kalamai masu zafi.

Janyeta Mahmud yayi ya turata mota yaja yabar farfajiyar hotel din.

Ita Kuma Aunty Amarya nan Jama'a suka Fara fitowa Ana

kallon sai Bala'i takeyi.

A masifar tata Har Mahmud ta hada Wai Bai tare Mata ba ai ita yafara sani kafin Zubaida sai fa yai laifi.agunta"banza boyi boyi direban mace kawai,ai Kai da uwarka nasan anshanyeku ne.

Maman yara dayake tazo gun dinner din Hajiy

a babbace dai batazo ba ta ja ta gefe guda tana fadin"ke Kam narasa irinki bakya kunyar kitarawa kanki jama'a Ina laifin kibari sai anje Gida ki gayawa mijin nata yai Miki maganin abin,muje da Allah Gida Kar kallo yadawo kanki.

To da dare dama Zuby ta kir

ashi ta hada Mata gurmi tana kuka takai kashedin Aunty Amarya tace ta mareta agun dinner Kuma farkon rikicin bigeta tayi tana tsaye itace ta Fara nemanta da fada,inma Bai yadda ba tana da sheda Mahmud yakira yatambayeshi.

Yana kashe wayarta kuwa yakira ta

Mahmud don Jin Karin bayani.

Shikuwa Mahmud cewa yayi"Eh to zancen gaskiya Daddy ka takawa Aunty Amarya burki Akan akan Aunty Zubaida sbd na tsorata da Marin da takaiwa Aunty Zubaida ba Dan Allah yakaini gun ba da dambe zasui.

Alhaji yace"tsakaninka da

Allah waye ya Fara takalar wani?

Mahmud yace"Wallahi Aunty Amaryace,ita ta Fara Marin Aunty Zubaida gashi har ta fada Mata Wai uwarta mabaraciya wannan ai baiyiba Kam.

Alhaji na tashi akasuwa ya wuce Gida Rai abace antabo Yar gwal.

Yana shiga yafara b

all da Kaya Yana zagin Aunty Amarya Yana fadin tana Ina?

"maza fito Yar matsiyata,ke har kina da abin gorantawa ga wata agidannan Alhalin iyayanki matsiyatane talakawan tilis masu cin rancen mijinki su kasa biya,maza kizo muje ki baiwa zubaida hakuri ko A

urenki ya girgiza yanzun nan.

Tanaji Tai Masa funfurus har yashigo falon ya tararta suna zaune duk su ukun.

Yayi kanta da fada Yana zaginta ta uwa ta uba don yasaba

Dama idan Yana tijararsa ita ke biye Masa shiyasa yake dukanta.

Yanxun ma biye Masa ta

yi tana ramawa tana daga murya zafafan Marika yakai Mata guda uku Yana nunata da yatsa Yana fadin"na ramawa marainiyar Allah,Kuma tunda kikace bazakije ki Bata hakuri ba to kije Gida na sakeki saki daya,can baya akwai daya Kinga saura daya tsakaninmu,ranar

da duk iyayanki sukace zasuzo min ban hakuri na inje bikonki to walh Zan rubu ta cikon na ukune inbasu su kawo mk gara ma inkinje Gida ki dakatar dasu,Kuma karki tafar min da yara kazamin gidan Nan naku.ya kalli Hajiya Babba datayi shiru tana jinsa yace"k

i rikemin Yara na agunki.

Da sauri tace"to Allah dai ya huci zcyrka da kayi hakuri.

Yayo kanta da haushin fada"Zan hada dake ba ruwanki.

Ta gyada Kai kawai.

Ya fuce fuuuuu!!!

Ta fashe da kuka tana fadin"shikenan a dakeka ahanaka kuka walh bazan bar

zubaida Haka ba saita gane shayi ruwane.

Maman yara takalleta tace"gaskiya ke ma fa kina da laifi Baki da hakuri ko kadan zaman mu da Alhaji Babu wacce yake duka sai ke saboda rashin kunyarki gareshi Bai kyautu kina hautsiniyar magana da miji ba Yanzu wa

gari ya waya.

Hajiya Babba tace"kin kasa gane Alhaji,gashi kishinki yayi yawa.

Taja musu tsaki fuuu tayi dakinta taje ta hado kayanta a akwati ta fice ta barsu ko kallonsu batai ba yaranta basa gurin da sun hau kuka sbd Haka sukeyi idan tana fada da Alha

ji suita kuka agurin.

Acan gun Yar Lele kuwa agaba yasata Yana ban hakuri

Ita kuwa Yar gwal Shan kamshi take tana fadin"ai dama kasan Ni me hkr ce da na biye Mata da tuni Muna station Amma darajarka da kimarka tasa ban biye Mata ba Tunda Kuma kasa Baki n

a hkr na ma yafe Mata ta wuce.

Ya janyota jikinsa ya rumgume Yana godiya gareta.

,,,,,,

Sai mundaw cigaba

Ayi hkr da kadan abinne da yawa.

Amma muma jiran comment

πŸ‘‚πŸΌπŸ‘‚πŸΌπŸ‘‚πŸΌπŸ‘‚πŸΌ

*YAR GWAL*

( ~me kayan Dadi~)

_the sugar daddy story_

Na _Nabilancy love_

πŸ’˜

*Auntyn S and S*

______________________________

πŸŒˆπŸ‡°

AINUWA

πŸ‡Ό

RITER'S✍

🏼

*

πŸ‡¦

SSOCIATION

🀝🏻

*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www

.Facebook.com/kainuwawritersassociation

______________________________

Page 08

Tunda akai wannan Abu tsakanin Zubaida Yar gwal da Aunty Amarya na rikicin Nan Alh baisake bi ta kan Aunty Amaryar ba,don iyayanta sunata kiransa awaya na ban hakuri don yazo

ya tafi da ita ko su dawo da ita,shikuma sai yawo yake musu da hankali.

Karshe sai da mahaifinta yaje har kasuwa ya sameshi akan zancen.

Bayan sun gaisa Mahaifinta yace"to kasan dai kan batun dayasa nayo Tattaki sbd wancen Mara mutuncin ce,nasan

halin nata ta tafka maka shiyasa ka zuciya ya koro Mana ita Gida,to zancen gaskiya ba Zan iya rikon nata ba saboda kaga tanada ci taliya ma Leda Daya take cinyawa gashi kafin Rana taji Yunwa Haka da dare babbar roba ake zuba Mata kwashiyar tuwa take cinyew

a Amma kamar Bata ci kullum jiya iyau,walh Alh nasan kana kokari shiyasa akullum nake Yaba maka tunda rikon mahaukaci sai Kura,bashi gareniba jarin nawa ma yayi kasa dama kaine ka dorani Ni dai kayi hkr ka daure ka dawo da ita tunda akwai sauran igiyar Au

renku,walh yarinyar Nan Albasa batai halin ruwaba.

Alh ya nisa yace"to Ala kulli halin dai in aka samu matsala tsakanin Ni da ita itance me lefi tunda Ina hkrn Zama da ita kowa yasani,sannan yakamata ace tagama sanin halina zuwa yanzun,Banda darajar ka da

Abinda ta Haifa yarana,da walh da Mun rabu kenan,sbd nagaji da halinta waima tagaya maka Abinda ya hadamu?

Nan baba yace"Eh to kasan dai karya irinta 'ya'yan yau ba lallai in gaskiya tafadaba,sbd tace Akan amaryar da kayo ne,bakason laifinta kan

sunyi fada ne,katare Mata.

Alh yayi murmushi kana yace"to nidai da naji rigimar da sukayi sai da nayi bincike akai Nagano itace Mara gaskiya wacce ta Fara takalar fadan sannan da naje Ina Mata fada tahau min rashin kunya agaban matana shiyasa kawai na dau

ki matakin Rabuwa da ita.

Gyada Kai baba yahauyi Yana fadin"Tab!! Amma dai wannan yarinya ta cika Mara kunya Lallai abinda kayi matan shine daidai da ita Tabbas Zan fara gasata da Yunwa daga yau ma kuwa Dan bazai yiwu ta kaso Aurenta da gangan nikuma tazo

ta kasheni atsaye ba,nidai Ina me Kara baka hkr Inka huce kazo ka dauketa.

Alh yace"ba matsala baba ai darajarka ta wuce Haka,Ina duban tsohuwar abotarku da mahaifina ne.

Nan baba yahau gyada Kai Yana fadin"Allah sarki Allah yajikansa dai.

Alhaji yace"

Amin,kaje Gida baba zanzo Amma ba yanxu ba sai na dawo daga tafiya Zan tafi Egypt Zan Dade Dan Zan dau kimanin wata biyu acan.

Gaban baba sai da yafadi Amma ya daure Bai nunawa Alhajin ba,Dubu goma Alhaji yakawo ya bashi Nan ya danji sanyi ckn Ransa sukai

sallama yatafi.

Amma ko ackn ran Alhaji Babu batun zuwa dawo da Habiba Aunty Amarya sai ta gasu agida sosai ai yanzu Bata Dade ba gashi sati guda har iyayanta sun gaji da ita Tabbas sai Nan da wata biyu zaije yadawo da ita.

*****

*****

Tafiya take a ckn

motarta tana tuki cikin gwanancewa tana Jin wakar music cikin motar nishadi takeji ackn Ranta.

Gidansu ta nufa yau tana son tagano mahaifiyarta saboda duk sati take zuwa takai musu kudin Amfanin yau da kullum kayan abinci Kuma duk wata take sai musu sbd

ta hanata fita Bara.

A hanya taga Aliyu tsohon saurayinta Haidar Yana tsaye abakin titi yadawo daga makaranta.

Tayi Saurin taka birki agabansa tare da leko da kanta ta kalleshi daga samansa har kasa taga kayan jikinsa sunsha jiki kawai babu ce take jigil

a dashi.

Ta tausaya Masa matuqa shi Bai gantaba sai da ta matsa hon da karfi tana kwalla masa Kira kana ya farga da ita.

Yasha mamakin ganinta yaga tayi kyau ta canza Tabbas ya yarda da abinda aketa fada Wai ta Auri me kudi ta Zama big madam.

Ya

matsa gun motar Yana fadin"Ah barka dai babbar Hajiya Ashe Ana ganinku ya amarci.

Tayi dariya tace"Haji Haidar kwana dayawa ya karatuya sharce gumin goshinsa yace"Ai karatu sai godiya Dan anzo karshe jarabawa ma muke ta karshe.

Tace"to AllΓ h yataimaka sh

igo ma rage maka hanya don ckn unguwar taku na nufa.

Ya girgiza Kai yace"Ah bazan iya shiga ba,ai Kinga ba kamar da ba,yanzu da Aurenki banida damar jerawa dake,nagode matuka zubaida.

Tayi murmushi kamewar Haidar na burgeta gashi gentle kyansa na Nan Tab

bas da zaisha kudi da ya warware,ta zaro dubu goma ajakarta ta Mika mishi da kyar kuwa ya karba shima Saida ta Bata Rai kana yasa hannu ya karba sukai sallama taja motar ta tafi ta barshi ya tari Dan sahun.

Data Isa Gida ta tarar Innarta ba lafiya,ta ring

a fada tana cewa Kanwarta uwani me yasa Bata kirata tun safe ta sanar Mata ba to da batazo ba fa.

Uwanin tace"walh rashin wayar da Zan sanar mikice matsala zuwana gidan kawunmu biyu bayanan inaso shi yagaya Miki ga wayar makotan mu ba caji.

Zubaida taja

tsaki tace"dole ne ma nasai Miki waya sbd hakan.

Nan tasa uwanin taje ta Kira wani likita alayin yazo yasawa Inna ruwa yai Mata Allura da magunguna.zubaida ta biyashi.

Ta aika uwanin ta siyo lemon bawo da Maltina sbd Innar.

Itako Innar da take magana da

kyar ta ringa shi Mata Albarka.

Kafin ta bar gidan Alert na dubu Ashirin taji daga Alhaji don ta sanar Masa halin datazo ta tarar da Innar.

Baya duba Wai tana da kudi na business dinta kawai idan ta bukata Yi Mata yake sbd kyautata Mata,duk da yanzun ta

rage bashi abinda yake so daga gareta Amman yakan Dan rage don tafi Masa matansa Dadi da abubuwa da Dama.

Taso ta kwana agida Amman yaita rokon ta akan tayi hkr ta dawo tunda agidanta yake,da safe zaikaita Gida da kansa sbd Yana son yaje yaduba jikin Inn

ar.

Yana darajta mahaifiyarta ko da akece Masa tana bara Bai taba ganiba kai Bai yardaba ma sbd atsaf yake tarar da Innar Kuma Babu Rashi atattare da ita,sbd zubaida ta iya takunta tana Kuma kaunar uwarta Bata son araina ta shiyasa take burgeshi Kam

don Alkinta iyaye akwai samun lada yakanji inama nashi na raye,shiyasa fa baya darajta iyayan habiba Aunty Amarya sbd itama ba tasu takeba ita ba ruwanta ma da sabgarsu,ga ubanta Yana yawan rokon Alhaji jari,itama roko da satar Masa kudi.

Aranar ma wuni t

ayi agida Saida taga jikin Innar ya warware kana Hankalinta ya kwanta matan kawunta sunzo duba Innar tabi yaransu da kyautar dubu dubu sukaita godiya suna kallon yanda ta canza tayi kyau fata tana sheki.

Kaji Mahmud ya ciko leda dasu danyu yakawo gidan na

dubiya dayaji Innar ba lafiya,uwani tayi dabgensu

Aiko Inna taci dayawa.

Zuby tai ta masa godiya data rakoshi kofar Gida.

Ya kalleta da murmushi kan fuskarshi yace"Hhhuumm Allah yakar giwa dai.

Tace"kamar Yaya.

Yace"Eh Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login