Showing 18001 words to 21000 words out of 34383 words

Chapter 7 - YAR GWAL COMPLETE

dama Engineering na karanta Kinga Allah yataimaka Miki yakawo Miki engineer.

Ta harde hannaye akirji tana kallonsa ya nufi motar ya Bude gaban motar ya tokareta.

Tana kallo yaita tabe tabensa ya jika kana can

yai wani tunani sai yadawo kan tankinta na Mai ya Bude,sai ya Kama Baki Yana dariya ya dago ya kalleta yace"Madam ya akai Kika Bari man motarki ya kare?

Cikin mamaki da fargaba tace"bangane ya Kare ba jiya fa Alhaji yaimin full tank,sake dubawa dai kagan

i.

Yace"to taho muduba tare dai idonki ya gane Miki.

Ta karasa taga yanda man yake tace"to Amma abin yabani mamaki baici ace man Nan ya kareba,Dan walh Dana fita banyi nesa ba iyakata S and S shop fa.

Yace"to koma dai menene ki Dena wannan saken may be

Kuma daga gidan man ne akai Miki wannan cutar Dan wasu sun iya hainci walh Kuma in akai maka bazaka ganeba alokacin sai in matsala ta Afku.

Tace"hakane,Zan ringa dubawa kafin na hau

Yaje ya tada motar yaga yanda malejin yake sai yace"Kinga ko daga Nan y

akamata ace kingane ko?

Tace"kwarai kuwa Kai dai nagode.

Yaje ga motarsa ya dauko galan na Mai ya zuba a tankinta kana ya tada motar,take ta tashi.

Taja ajiyar zcy tace"Nagodewa Allah Daya kawoka ka taimakamin.

Yace"Kuma Kinga kamar Kar nataho Haka

na daure nayo hanyar Nan walh megidanane ya Aikeni.

Tace"ikon Allah Wai Haidar Aiki ka Kama ne ko Yaya.?

Yayi dariya yace"kasuwanci aka tsundumani Kuma nashiga a sa'a waccen motar ma Alhaji Auwan megidan nawa yabani ita Daya sakewa Yaronsa Ni sai aka ban

i,sannan yanzu ma gini nake sbd Alhamdulillah Nasami rufin asiri cigaba yazo karatu ma na Dade da gamawa.

Murmushi tayi tace Masa"Kai Amma dai na maka murna Haidar Tabbas Allah me Taimakon bawane alokacin dayake neman taimakonsa Amma idan ya dage da Addua

.

Ya gyada Kai Yana fadin"ansha rokon Allah Akan sauyin rayuwa me kyau kuwa,Kuma gashi ckn sauki ya canzamin rayuwa me kyau yanzu Kam nafi karfin ci Dasha saidai nayiwa wani walh,Nagodewa Allah sosai.

Tana kallonshi tana murmushi burgeta yake Aliyu akwai

Nutsuwa da ita kalami.

Tace"kaga sai Aure kenan.

Ya shafa qeyar Yana fadin"Kai ba Yanzuba walh,Dan cikin dangina ma sunata kawon Hari naqi.

Tai ajiyar zcy tace"to kaiko me yasa Alhalin ka Kai munzali tuni ma,sannan ga rufin Asirin Allah kasamu.

Yace"A

duniya Abu daya Dana rasa yasa komai ya fita araina sai Nan gaba sosai ke dai kitayani da Addua.

Tace"to Allah yazaba maka mafi Alkairi.

Yace"Amin 'yar,uwa.

Ta nanata kalmar aranta'yar uwa Kuma,?to ko yadaina sonta?kawai ita ji tayi ta tadawo da sonshi

cikin Ranta,inama Aurenta ya mutu da ta rabu da kowa sbd Haidar to dama Dan bayadashi ta qishi yanzu kuwa yayi rufin Asiri itama tayi.

Ta kawo kudi ta bashi ya girgiza Kai yace Mata bazai karba ba Yanzu Kam shi yake baiwa Wanda Bai dashi.

Ya koma

motarsa ya tayar Yana dago Mata hannu.

Ta kasa tafiya jikinta ya mace murus lallai Aliyu ya Zama handsome mutum cikakke yanzun.

Tan kallo ya wuceta a motarsa Yana Mata hon,alamun sallama.

Data bar gurin a sanyaye ta dawo yin tuqin har taje gidansu Bata d

aina tuno Aliyu Haidar ba.

Da taje gidansu ma daga gaisuwa ta daukowa Innar maganarsa.

Inna tace"to ai wannan Yaro cikin wata guda Allah yai Masa gyadar dogo,bakiga yanda ya gyara gidan su ba,ga mota da yayi ga kula da uwarsa da yakeyi kamar dai ke anan,

sannan Nima yakanzo yayi min dan hasafi tabbas inacin Albarkacin haduwar da kukai abaya kukai soyayya,yaro me farar zcy da ace ya rikeki da bazai kula Ni ba.

Zubaida tace"Tabbas Nima nasha mamakinsa Amma yin Alah ne,shike azurtawa ackn karamin lokaci Amma

Aliyu bansan me zance Masa ba sai Addua Allah yabashi mace tagari kawai Amma yakyauta.

Bayan Gama hirar Aliyu da sukai sai ta Dora da Yi Mata Albishir na tafiyarsu Umara da Kuma biya da Alhaji zaiyi taje wata shekarar tare da iyayansa.

Innar taji Dadi s

osai tace zankuwa tayin Addua Allah yasaka da Alkairi.

Wuni tayi agidansu,wajen magriba ta tafi.

Yau tana ta Jin farin cikin ganin da tayiwa Aliyu a kyakykyawar Shiga

Tabbas yakamata tunda Bai fidda macen Aureba wataqila ita yake jira fa,tayi wani Abu

na kokarin dawowa gareshi, murmusawa tayi kana daga baya ta tsuke fuska tuno ai Bata ma karbi nambar Aliyu ba,sai ta aiyana aima zata iya samu gun abokansa intaje don sun santa.

Ta ciji yatsa tuno cewar abokansa najin haushinta ganin yanda ta azabtar da

shi abaya,ta ajiyeshi agefe Bata son saurararsa sai anciza.

Haka ta hakurewa Ranta Amma fa tafara Dana sanin rabuwa da kyakykyawan Gaye kamar Haidar Amma Ina Aikin Gama ya Gama dai yanzun sun wuce juna tasan ko Batada Aure bazai dawo gareta ba.

Aranar ya

u Alhajinta ba agidanta yake ba,ita yanzun ma haushinsa takeji ya Gama fita Aranta ba tare da yai Mata komai ba,Ada ne tafi kaunar Tsohon jini sugar daddy,to Amma yanzun soyayyar yaro sabon jini takeji aranta,ta wuni tunanin yanda zatai ta kashe Aurenta ka

wai don ta samu ta Mallakin Mahmud ko Aliyu Haidar.

Da safe Alh kafin yashiga kasuwa ya biyo gunta agurguje Yana me sanar Mata cewar zaiyi tafiya zai Dan Dade kamar sati biyu kafin yadawo.

Aranta murna tayi Amma a zahiri saita hade Rai ta Nuna irin

Kamar bataji Dadi ba.

Yacikata da kudi Yana me rarrashinta.

Tace Masa"to Amma Dai my hubby zantafi Gida in zauna kafin ka dawo.

Ya girgiza Kai kana yace"Ina ba da yawuna ba babyna,kiyi zamanki adakinki har na dawo Kamar yau ne fa.

Tace"to naji Amma

plz Karka Kara.

Yace"ai ba Ni kadai bane bama,Zan dawo insha Allahu akan lokaci ke dai kici gaba da kulawa da Kanki.

Ta daga Masa gira tana murmusawa.

Bayan ya tafin tasa waya ta Kira Mahmud ta zaiyane Masa yanda takeso ayi na haduwarsu"kaga tunda ba Al

haji yai tafiya to ai kawai muyi holewarmu agida ba sai munje wani gurin ba ko besty.

Da zumundinsa yace"Aiko dai hakan zamui baby Zan ringa zuwa kamar Bayan magrib wataran in kwana wataran in dare yayi sai intafi Gida.

Taja ajiyar zcy tace"wannan ba dam

uwa bace,hakan shine daidai dama na farajin tsoron yanda Zan zauna ackn gidan Ni Daya ne,har na tsahon kwanaki.

Yace"yes baby zamuji dadinmu fa.

Tace"to daga yau zaka Fara zuwa Taya kwana dai,me Zan dafa maka?

Yayi Dan ihu kadan na murna yace"gaskiya ba

nida zabi kiyi min kowanne irin delicious inaso.

Tace"to bestyna saikazo.

A ranar kuwa yazo tayata kwana yasha riritawa da Lele

Akayo Masa drinks kala biyu girki kala biyu,har gadon da Alhaji yake kwana aka kaishi aka Nuna Masa shi amatsayin inda

zai ringa kwana.

Yai tsalle ya dire Akan katifar Yana murna yace"Allah yakai damo ga hadawa besty,inama Alhaji yatafi kenan,ba dawowa da naji Dadi matuqa.

Tasha mamakin kalamansa wato kamar yashiga zcyrta fa.

Tace Masa"Mahmud Anya kuwa Kai din daga tsat

son Alhaji kake?

Ya ware idanunsa akanta yace"me Kika gani?

Tace" naji irin fatan danake araina akullum akansa shi yau Kai Masa Amma meyasa?

Ya tashi zaune Yana fadin"Gwaskan namune akwai kudi Amma baya sakarwa iyalansa Ni abinda ke gabana shine...

Ab

okin Aikin da Zan samu Musace shi ne Aiki,to Amma in Zaki tayani sai muyi,tunda naji kema fatanki kenan.

Tace Masa "Ni ai saidai ince muyi kidnapping dinsa kawai asamu uban kudade,Kai Kuma Naga kamar bayansa kakeson gani why?

Ya gyara Zama tare da janyot

a jikinsa Yana fadin"wato irin wulakancin da Mahaifinmu yaiwa Mahaifiyar mune yasa walh naji ya fita araina,ba ruwana da hidintawa karatuna da yau,kawai burina yanzun shine Naga bayansa sbd idan ya kauce can samu abubuwa biyu...tayi Saurin katseshi"me da m

e knn?

Ya nunata Yana fadin"ke Mana! Shiyasa bana fatan kisamu ciki dashi ma,sai Kuma abokan rayuwa kudi kinsan zamu samesu dayawa ko.?

Ta gyada Kai tace"zancenka Haka yake,Nima xanso ace mun mallaki juna Amma nasan Dole sai munsamu Qaluballe.

Yace"sai

Musa malamai suyi wa danginmu rufin Baki.

Ta jinjina Masa kana tace"hakan yayi,Amma dai na baka wuka da Nama.

Yace"Ni zan shirya hakan,akwai wadanda zansaka su daukeshi akan hanyarsa Amma sai ya dawo daga tafiyar sbd naji wani business ne zai

kaishi Abuja xai Sami kudade Masa kauri,zasu boye manashi har zuwa lokacin da za,a fidda Rai dashi idan mun kwashi kudi sai cillashi lahira.

Tayi fara'a tace"to Allah yabamu sa,a yakiyayemu da Nadama.

Yace"Amin,kizamo me rike Sirri dai,suma wadanda Zan s

akasu aikin na Yan Nan bane.

Agidan ya kwana Mahmud Aranar ya Fara kusantarta Aiko yaringa sambatun Dadi dayaji daga gareta,harcewa yake"Ashe Haka dady ke kwasar Raba my baby,Tabbas Babu me Rabani dake,Muna tare mutu ka Raba.

Kafin safiya yayi sau uku,ta

jure matuqa sbd son da take Masa sannan taji ya iya salo salo na farantawa mace Rai wajen Wasa,Wanda Sam Alhajinta Bai iyasuba,ta yarda da zarginta akan Mahmud acan turai da sukai karatu yayi sex da Mata kala kala,yakan furta Mata ma yai soyayya da turawa

da Kuma bakaken fata da sukaje yin karatu can yan Nigeria,Daya dawone dai ya daga kafa akan Mata,tun Dora idonsa akanta.

Da safe Haka ta tashi dakyar ta Dora musu breakfast sbd yanda ya gajiyar da ita sallar ma said dasafen tayita ta Asuba,shikuwa sai wa

jen 10am Daya tashi yayi,wa,iyaxubilla an Bata da yawa dai.

Aranar wuni yayi Bai fitaba,itama Bata iya zuwa shagon ta ba na boutique din yaranta kawai tayiwa waya akan su kula da komai bazata iya fitaba batajin dai yau.

Ta kashe wayarta gaba daya Dan Kar

adameta.

Ta bashi kulawa sosai shima yaji Dadin Wannan kasancewar Tabbas idan akace Babu Alhaji a doron kasar zaifi kwasar ganima,zai bararraje akan dukiyar tunda shine Babba.

Dayake Friday ce ranar Bai shiga gun Aikiba tunda dama 2pm insun fito zuwa sa

llar Juma'a basa komawa duka,wasu Gida suke wucewa ko wani uzurin Dan duk Juma,a have day ne,Basu da Aiki dayawa a office.

Mahaifiyarsa kuwa ce Mata yai zaije wani workshop zaiyi sati.

Acikin Wadannan kwanakin sukaita Qulla qullarsu akan yanda Alhajin za

izo hannunsu.

Ita take waya dashi tanajin cikinsa kullum zata Kira tayi Masa yn dabaru na bugun cikin yaushe zai taho me yake ciki Akan business din nasa,yaringa Nuna Mata yai kewarta Yana Allah Allah yadawo ya kwashi kayan Dadi agunta,takance"Nima nayi k

ewarka Alhajina.

A irin wannan waya me dadi da sukeyi Wanda kaf cikin matansa Babu me kiranshi sbd tuntuni shiyai musu sabo da rashin iya Nuna kalawa yasa Suma inbashi yakira aka gaisa ba basa iya kiranshi.

Hakan ne yasa yake ganin yasamu

daidaishi Yar soyayya Zubaida me kayan Dadi,dayasaka Mata.

Ita kuwa duk abinda take Masa yanxu aka son abin hannunsa ne,burinta kawai tasamu kana tacika burinta na son Auren Mahmud ko Kuma Haidar da yanzun tunaninta ya Fara Kar kata gunsa,domin inhar taga

zatasha wahala waje samun Mahmud to Haidar kawai zata komawa Amma sai in Babu Alhajin insun kaudashin.

Cikin satin Da Alhaji zai dawo yatura mata kudi naira dubu hamsin yace tayi hidimar Gida zaidawo lahadi,to dama kafin yatafi ma dubu hamsin din ya Bata

kamar yanda ya baiwa sauran masu Yara.

Tacika da murna tana Masa godiya yace"haba babyna ai kin cancanta tunda kina Nunamin kulawa,Ina samun Nutsuwa da kwanciyar Hankali idan Muna tare,gaki sarkin Dadi fiye da matana, Kuma Alkawarin Kai mahaifiyarki da K

uma ke kanki na Nan zancikashi na zuwa kasa me tsarki tunda ansamu kudi awannan tafiyar Na kasuwancin danaje.

Taja ajiyar zuciya tana fadin "Masha Allah My sugar na Allah yadawo dakai lafiya ya karo maka Arziki me Amfani.

Yace"Amin,me aka tanadar min ida

n nadawo din?,tunda agidanki Zan sauka.

Cikin Nishadi tace"ai Dole na tanadar maka Abinda zai faranta maka Rai nawan,yaushe kenan zaka taso,?sbd xanje gyaran Kai da kunshi.

Ya saki dariya ya a fadin"good amaryata,insha Allahu Zan taso karfe bakwai na

asubahi idan nakusa ma Zan Gaya Miki.

Tacee"to hakan yayi,Allah yadawo Mana dakai lafiya.

Yace"Amin,tareda Danno Mata wani hot kiss wanda sai da karar yashigo cikin kunnenta

Ta saki dariya tana fadin"wonderful my husband I love you.

Yaji Dadi sosai Dan

ya mance rabon da wata Diya mace acikin gidansa ta Gaya Masa Haka,shiyasa yakeson Yar gwal dinsa,yanzu abinda yafi so yaga ta Sami ciki ta Haifa Masa yara masu kyau irinta.

******

******

Aranar da zai taho sun Gama shirya duk wata Ajenda ta yanda zasui w

uff dashi wadanda aka sakasu Aikin.

Ita Aranar ma da wani ciwon ciki ta tashi ga wani amai da taringayi da safe.

Tayi zaton ko ulcer ce,Amma zuwa Rana kafin sallar La,asar saiga zazzabi ruf ruf a bargo ta wuni ma sai tashin amai ke dagata agadon zuwa

toilet.

Mahmud yace Mata"inzaki wartsake gara ki wartsake Dan Naga alamun kamar Alhinin rabuwa da Mijinki ne yasaki awannan halin Kuma Babu fashi idan soyayyar sa ce ta tashi aranki.

Saitaji haushin kalaman Nan nashi lallai ta tabbata Mahmud baya tsoron

Allah Babu Imani aransa tamkar ba Alhajine ya haifeshi ba idan taga Yana hakikancewa akan maganar sace alhajin

Haka tanaji tana gani Kiran karshe ya gudana tsakaninta da Alhajin domin ya kirata yaji halin da take ciki yashiga dimuwa sosai Yana Mata fatan

samun lafiya,har yake ce Mata"baby ki ajiya nayi zai Baki wahala?

Tace"inafa zazzabine kawai banajin idan cikine.

Yace"to koma dai meye ne gara aje asibiti Bari nakira mansur ko Mahmud suzo Miki da likita har Gida agwadaki abaki magani,Nima saura awa Da

ya na sauka ajahata,yanzun dai Muna hanyar kaduna.

Tace to kawai.

Alokacin Mahmud na kusa da ita handsfree tasaka yaji komai.

Take ya Kira ma'aikatan nasu ya sanarsu cewar Alhaji na hanyar kaduna yakusa zuwa zariya anan yakamata su farmasa.

Ta Qura ma

sa idanu,tana mamakinsa.banda tana mugun sonshi da saita cire hannunta akai.

Dayake wayarsa arufe take yasanarwa da Mom dinsa sunje katsina wani taro sai yadawo gidan Zubaida sbd idan Batan Alhaji yafito baza,a zargeshiba.

Da Alhaji yaji wayar Mahmud aka

she sai ta mansur yasamu

Shikuwa mansur yasanarshi cewar Yana Kasuwar motoci yaje taho da motar Daya canxa,to dama Alhaji yasan da batun zaiyi canjin motar sbd ya cika Masa wasu kudaden ma.

Sai yasake Kiran zubaida yace Mata"my madam kiyi hakuri yaran d

uka basa kusa,shi wancen marajin Mahmud wayarsa Bata shiga Amma mamansa tace ko yashiga taro shiyasa yakashe,me nutsuwar Kuma

yaje taho da motarsa kiyi hakuri kafin nadawo inkuma kinga abin ya ta,azzara ki Kira Gida uwani taxo ta tayaki zaman kafin nadawo

muje Asibitin.

Cikin tausayinsa tace Masa to Allah ya kawoka lafiya.

Mahmud Yana jinsu ya harareta bayan ta kashe waya yace"nakawo magani Kisha kin ki Sha ya kenan kikeso ayi,Kuma kina wani Yi Masa fatan Alkairi,na fahimci fa mijinki kikafiso Akan

farin cikinmu.

Tayi Masa banza sbd ta kanta take.

Bayan awa guda wayarsa tayi Kara amaimakon ya Amsa agabanta da aka kirashi sai yai Saurin fita.

Gabanta kawai ke faman faduwa sbd tasan yanzu Alhaji ya shiga hannunsu tunda har gashi takira wayarsa akash

e,Kuma ga Mahmud na Amsa wayar munafurci,sai Kuma gashi yadawo Mata da fara,a Yana tafa hannu Yana fadin"End of my work!Aikin Gama ya Gama.

Ta tashi zaune da sauri tana fadin"Da gaske!

?yanzu shikenan,tab Amma dai karku kashe Alhaji Dan Allah ki barshi d

a Ransa.

Yayi dariya yace"bamu yanke hukuncin komai ba,sannan akwai Shirina akan mansur duk wuya duk rintsi indai Alhaji Bai mutu ahannunsu ba to zamu lak'awa mansur akan da sa hannunsa Kuma Dole za,a yarda tunda gashi ya sake mota da gaggawa ta gani ta f

ada,Wanda Ni Dana girmeshi bankai ga canji ba.

Ta gyada Kai tana Masa wani kallo.

Yatashi ya fita,yabarta da tunani barkatai sai zazzabin nata ma ya Karu.

Sai zuwa dare iyalansu su Hajiya Babba da Aunty Amarya da Maman yara sukai Kiran wayarsa akashe su

kaita Jin layukansa daga MTN har Glo da Aitel Nan Hankalinsu yatashi tunda yace musu zuwa Rana ya diro to gashi har dare ba labarinsa.

Sai dare Mahmud ya kunna wayarsa take kiran mahaifiyarsa yashigo Masa cikin tashin Hankali tasanar Masa halin da ake cik

i na rashin Jin wayar babansu.

Yace Mata gashinan zuwa gidan akwai matsala fa.

Daya iso kuwa ya tararsu cirko cirko Hankali tashe.

Alokacin ma har Ankira Hajiya Babba sun sanarta Alhaji na hannunsu mutanen sun Fadi aDadin kudin da sukeso Abasu ko akashes

hi.

Tana kuka take sanarwa Mahmud shima hawaye ya farayi ya dafe kansa Yana fadin"Allah gamu gareka.

Maman yara Tace Masa"gwada Kira Mana mansur muji Dan yace zaije gurin hukuma yakai musu lambar da aka kirashi Dan shi ma sunkira sun Gaya Masa

abinda suka gayawa Yaya Babba.

Nan ya Kira mansur Yana me Nuna tashin hankalinsa a fili.

Mansur yace Masa Yana caji office suna shigar da maganar zakuma a tsaurara bincike sbd layin za,a Fara yiwa taracking Amma zasu saka ayi addu,a A masallatai.

Dafe

kansa yayi Yana fadin"ya Allah ka kawo Mana tallafi.

Ya Mike da sauri Yana fadin"Bari nabi bayansa zuwa caji office din.

Yana fita ya nufi gidan Zubaida don Kai Mata Albishir komai ya kammala,itama idan sukaga zata kawo musu matsala zasui maganin ta ne

kawai don yaga take taken ta kamar jikinta yai sanyi tanaso ta janye jikinta......

To muje zuwa Dan Alhaji me Abin mamaki.

*YAR GWAL*

( ~me kayan Dadi~)

_the sugar daddy story_

Na _Nabilancy love_

💘

*Auntyn S and S*

______________________________

🌈🇰

AINUWA

🇼

RITER'S✍

🏼

*

🇦

SSOCIATION

🤝🏻

*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

______________________________

Page 11

A kwance a kan doguwar kujera Mahmud ya tarar da zubaida tunanin d

uniya yai Mata yawa.

Jikinta ya Gama macewa da wannan lamari da suke kan shiryawa ko ma ace suka Gama shiryawa na shiga hannu da Alhaji yayi gunsu.

Ta Dade da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login