Showing 30001 words to 33000 words out of 34383 words
kishiyar maman acan tayi sallarta
Taga kauna kuwa agun wannan tsohuwar Dan itace uwar gida gata da haba haba da barkwanci tai ta Jan Zubaida da wasa da dariya
Acan Zubaida ta sake taji dadin zuwan gidan.
Dayake Haidar shine Dan fari na mama sai innar tace mata"kar Kiga ko mama taqi sakar miki kiyi wata fassara ta daban shi din Dan fari ne shiyasa bazata sake Dake ba.
Murmushi kawai zuby tayi Dan bata yarda Akan hakan bane kawai dai innar tunda ta fahimta
bari ta kawar mata da tunani tace hakan sbd ta kare maman,amma tasan rashin kaunar ta ne kawai da batayin tunda gashi Nan ta sakarwa Zulaihat fuska.
Da zasu tafi Zubaida ta kawo turarika da dambun Naman data taho musu dashi a fararen robobi ta mikawa kowa
.
Dayake innar na gun sai mama ta nuna murnarta da godiya.
Zulaihat tayi mamakin wannan kyautatawa ta zuby ita dayake Yar gudace bata taho musu da komai ba tasan Kuma Zubaida tayi hakanne Dan asota to abanza ita kam.
Zubaida tayi tunanin yanda zata siye
zuciyar Iyayan mijin nata ta kyautatawa Tasha Alwashin Nan
Dan haka DUK juma,a sai tayi girki na musamman an Aika musu
Da kudinta take yin wani abun Dan Aike ta ware kowacce sai ta aika mata abin baka sai girkin uban miji na musamman.
A bangaren shag
onta Kuma yana Kara bunkasa Dan yaranta na kular mata bakin gwargwado
Ita nata zuwa lissafi da Kuma Kai kaya insun iso
Haidar ya bata dama takanje Lagos ko Aba Tayo sare sarenta Amma bata dadewa akwai lokacin ma da sukaje tare suka dawo ya Kara mata Jari
.
Ba karamin shaqar bakin ciki Zulaihat take ba kuwa.
Amma bata da yanda zatayi Bata isa tayi magana ba sbd tana tsoron bacin ran Haidar tasan zuby ta gaban goshi ce.
DUK da itace uwar gida Amma yakance mata inkinson farin cikina da kyautatawa gareni sa
i kin bi Zubaida sau da kafa sbd ta girmeki a shekaru dolene kibata girma kin fahimta?
Takance To Allah yabani iKon bin nata
Akan hakan take ma Zubaida biyayyar ba don taso ba
Ba zaman hira suke ba bama sa wani haduwa sosai sai in zubaidar zata
fita inta sauko ne ma sukan hadun.
Me musu cefane dayace ita ke Aikin gidan na share koina da goge tile ita take yo musu cefane tare suke Aikin girki da zuby bata yarda ta bata girkin mijinsu ba kamar yanda ita Zulaihat ke bararrajewa ta kwanta tai bacci
Mero na Mata Aikin komai har girkin miji
Ita dai kawai tace kiyi kaza da kaza ki ajiye ko ki zuba a plask ba sai nazo na Gani ba.
To ata Nan kadai tayi failed Zubaida ta ciri tuta na yiwa miji girki me Dadi.
Abu na farko Daya fara kawo mata tsaiko ciki
data samu me laulayi.
Taji dadin samun cikin Amma ya fara katse mata rayuwar Jin Dadi
Bata iya cin abinci sai zabi,gashi arana farau farau sai Tasha sau uku ko biyar Wanda Mero ke hadawa ta bata inyai sanyi Tasha.
Kamshin turaren jikin mijinta ma bata s
o adole in yana part dinta yake daina fesa turare
Shima samun cikin ya faranta masa yaiwa Allah godiya Amma Kuna Jin dadinsa ya ragu Dan rage bashi kayan Dadi ba son yin sex take ba
Hakuri ya fara da ita takance masa yaje gun matarsa yayi ita kam bataso
A dole yake ragewaa agun Zulaihat don ba komai ta iya ba.
Yanda Haidar ke lelen zuby da nuna doki da kaunar cikin yasa Zulaihat take shaqar bakin ciki kusan kullum sai tayi kuka adaki gashi ita har lokacin da Auren nasu yakai wata biyar batai ko batan w
ata ba....
Kullum tunaninta shin zata samu cikin ma dai ko sai ta shiga neman magani....?
*YAR GWAL*
( ~me kayan Dadi~)
_the sugar daddy story_
Na _Nabilancy love_
π
*Auntyn S and S*
______________________________
ππ°
AINUWA
πΌ
RITER'Sβ
πΌ
*
π¦
SSOCIATION
π€π»
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
______________________________
Page 17- END....
Laulayi gaba yake ga Zuby na cikin data samu,don sai da tayi wata uku kana tasamu kanta,abubawan suka fara Raguwa,Dan yanzun komai ci take Kuma ta fara sakarwa Haidar kanta
Alokacin yakara Jin Dadinta ta Kara ruwa Ni,I'ma tafi ta Da.
Am
ma sbd kar cikin ya zube tace masa ayi komai baya baya.
Yace da Ita"gaskiya bazan iya hakurin rashinki ba my zuby,bazan iya ace inyi sau Daya kafin nabar dakinki na hakura ba,yakamata na fanshe wahalar da Nasha na missing abaya.
Ta hade Rai
tace"bazaka ganeba my man,wato likitan tace yawan yin sex ga me ciki kansa asami matsala cikin ya zube Mai zai Hana ka ringa jurewa ayi baya baya,ai Gani nake ma ko hutu na dauka nace sai na haihu zamuyi ka hakura,tunda ga wata matar can kana da ita.
Ya z
abura yace"what!kinsan me kike fada kuwa
π³π‘π€
to walh bawai zan kushe Zulaihat ba,naki ba irin nata ba bane dandanon,zancen gaskiya bazan gaji da gaya mk you are the best ba,bana Jin da na Fara Aurenki zan iya Auren wata,ke fa tamkar zaman mata hudu kike a
guna,inaganin ko gyara kawai kike kina Shan sinadarin Karin Ni,I'ma Ashe dabanne lamarin yanzun da nadau hutu ban yiba Nagano Dandanonki daga indallahi ne,tabbas ki godewa Allah.
Ita Zulaihat tana fama da Jin zafi yayin saduwar Aure shiyasa ma ban fiya ne
man ta ba,takan kafe ba Ni,I'ma sai munyi 'yan dabaru ko ma nahakura na kyaleta idan naga zata wahala,nasan zan fanshe dadina agunki,gashi a fannin iya wasa ta mu,amalar Aure ke gwana ce,ga iya tarairaya tabbas rabuwa Dake Babu Rana zuby.
Tayi dariya Ck
n Jin Dadi tace"naji my man,Amma da zaka sama mata magani komai zaiyi normal wata qila sanyine da ita.
Yace"zan Baki kudi ki hado mata.
Tace"ka bata can ta hadowa kanta zaifi.
Nan suka rufe wannan Babi sbd ya gama fahimtar zuby dabance ackn mata dole za
i taimaki Zulaihat don ta dawo mace itama.
****
Anyi hakan da kwanaki fada ya rincabe atsakaninsa da Zulaihat wai ya daina ta ita sai ta zuby,ko kusantarta ma ya daina ga ba nuna kulawa.
Abu har gaban iyaye,Saida Akai masalaha don kwananta biyar agidan K
uma adakin mahaifiyarsa.
Sai da mamansa ta nuna masa bacin Rai ma Akan abinda yakewa Zulaihat din,tace masa indai Bai dawo daidai da Zulaihat ba Tom zata qi zuby qiyayya mai dorewa ma kuwa har abinda zata haifa din da ake rawar Kai akansa.
Yaji ciwon abu
n,tunda Akai Zulaihat ne hakan ke faruwa adole ya kauda komai ya Nemi Biko yai ban hkr yace zai gyara.
Amma fa ko da ta koma bata canza zanin ba kawai dai Dan tana mugun sonshi ne yasa ta danne wasu abubuwan Kuma ya kafa mata sharudda da doka akan inhar t
a kara zuwa Kai kararsa ko yaji don ta hadashi da iyayansa to abakin Aurenta
Shine ya sami lafiya fa ta zama me hakurin karfi da yaji.
Amma sai ta sauya zani daga wannan mugun kishi nata zuwa yin makirci suka fara zuwa gidan malamai DUK Akan cikin
zuby wai so suke a zubar mata shi ta hanyar sihiri ayi mata turen Aljani.
Makwabciyar tasu a gun saloon suka hadu suka Jone Dan Haidar Bai barta yin mu,amala da 'yn unguwa don bata fita
Ruky ce jagorarta gun malam amma tashin farko malamin ya gaya musu
gaskiyar cewar akwai rabon dirowar jariri yasha ruwa a Doron duniya ya Kuma Sha nonon uwarsa,saidai ko ayi abunda zai ringa Saka Haidar da zuby rigima sannan idan ta haihu su kashe yaron ko yarinyar ta hanyar poisoning dinsa.
Ahakan sukai Na'am da maganar
malam sannan suka dire masa kudi masu kauri ya hado musu turarika da rubutun da zata ringa yayyafawa a sashin zuby DUK don asamu a farraqasu.
Ita kuwa zuby baiwar Allah bata ta wata Zulaihat ma don sam bata gabanta ita koyaushe ta mijinta takeyi taga ta
kyautata masa ta zama ta gaban goshi Kuma tana ganin hakan.
Cikinta na wata na bakwai Akai hakan,arana ta Daya da aka fara yayyafen Allah ya baiwa Haidar iKon taka rubutun Nan da hayaqin da Akai ya shaqa sai ya kwana da ciwon Kai abangaren zubyn ya ringaj
in zcyrsa na hasala baisan dalili ba
Ita kanta Saida ta Gane,Amma bata takurashi da tambayar ba kawai magani takawo masa yasha.
Suka kwana Babu hira me Dadi ko nemanta baiyiba,shida baya iya hkr da ita Tasha mamaki Amma bata damuba.
A lokacin ma sai abu
n yazo mata asauki don bikin Uwani ne yazo za ayi agidan kawunsu.
Sai ta koma gidan da kwana Kuma ya barta taje tayi sati.
Ahakan Zulaihat tayi asarar wannan Abu Dan Sam zuby bata shafeshiba,haka Haidar din ma Bai Kara riskarsaba tai ta baza Ido da kunne
taji ko zasu hautsine asamu sabani shiru.
Sai dataga yana kwana abangarenta ne ma ta nemi Jin ba,asi don har ga ranta ta zaci ko fada sukai yasa yai hijira yadawo gunta.
Sai taji Ashe wai zubyn ma bata gidan taje biki.
Da takaici kamar tai kuka take ga
yawa Ruky
Rukyn tace"hhuumm lallai ke yarinya ce har yanzun wato kin yarda da cewar biki taje knn,to da alamun samun matsala sukai taje gida yaji zai boye miki,walh maza suna hakan Dan karkiyi masa dariya.
Zulaihat taja ajiyar zcy tace"to Allah yasa
hakanne ai kuwa zanta bibiya inji gaskiyar magana.
Acan bangaren zuby kuwa sunsha bikin Uwani anKai uwanin Dorayi tasamu mijinta saurayi bashida mata Kuma yaron me zcyr nema gidansa me kyau na Rabin filoti Da Dan mashin dinsa yana zuwa kwari yaron shagone
Amma yana samu.
Sai da Akai kwana biyu da gama biki sannan Haidar yaje ya daukota yadawo da ita gidan dama acan dinma yakanje ya ganta har ma in takaishi dakin kawu susha soyayyarsu acan.
Ba karamin kishi da haushi ne yacika Zulaihat ba dataji dawowar z
uby gidan Kuma ta fuskanci kamar Babu damuwa atattare dasu.
Sai ta Kara cin Alwashin cewar sai ta Rabasu sannan sai ta zama sanadin mutuwar yaron cikin ko aduniya ko aciki.
Bayan wasu watannin Allah yasauki zuby lafiya Kuma haihuwa ta ban mamaki Dan twin
s ta haifa mace da Namiji,Wanda Sam scanning Bai nuna musu biyu bane.
Murna agun Haidar fal baka.abokansa sukaita zuwa ganin jarirai masu kyau,Kuma namijin sak Haidar macen Kuma sak kammanin zuby yara tabarakalla ga farin jini da sukai.
Yan
gidansu Haidar sunzo barka da kayan jarirai akwatina biyu kowa na da Daya Wanda Mahaifinsa ne yabada kudi akayo wannan siyayyar sbd son da yake ma zubyn,tana masa biyayya Kuma Allah ya hada jinin nasu ga kyatatawar da take masa yanajin dadin Aiken datake m
usu na snacks ko girki sakakke ranar Friday.
Inna ta nuna son yara sosai kishiyar mama kenan,haka itama maman ta Haidar ba yabo ba fallasa sbd idon mutane ta dauki yara ta yaba tayi musu Addua.
A bangaren Zulaihat ta saki ranta bata nuna komai ba takan s
higo taga yara harma ta tsoma hannu ayi Aiki da ita takan taya me Aikin nasu DUK sbd tayi basaja Amma wannan haihuwa ta tsaye aranta gashi ita har lokacin Babu ciki.
Ranar suna Tasha mamakin Ashe walimar suna a hotel aka tsarata.
Gashi yai musu kaya iri
Daya less da suka Saka da Rana Akai hotuna Sai gashi da za.a tafi gun walimar taga Haidar da zuby sunsha Ankon shadda ruwan Zuma
Shadda dakakkiya sunyi kyau sosai,har kuka tayi adaki walimar ma qin zuwa tayi ta tsiri ciwon kan karya.
Ai ko ansha walima
me jego ta sami kudi sosai sbd yanda abokansa sukai mata ruwan Yan dubu dubu don me DJ ta biyashi abinda duk aka lika mata natane Kuma ta samu ba laifi.
Antashi a taro lafiya anwatse kowa yana sambarka Anci ansha an samu kayan rabo kala kala da Akai
agun.tabbas murnar haihuwar Nan Haidar ya saki bakin aljihu anyi komai cikin bajinta Sannan uban gidansa ya kawo mata sarkar gold daga madam dinsa wacce take Dubai bata gari,shikuma ya bata dubu Dari biyu yace abaiwa yara kowa Dari Dari.
Tabbas haihuwa ta
yi goshi,gashi Haidar na Shirin canza mata mota ita Kuma Zulaihat zai bata ta zubyn.
Cigaba yazowa zuby Dan haihuwar ta mata goshi arzikinta itama ya bunkasa Jari ya karu a shago DUK wani cigabanta Kuma tana alakantashi da Adduar iyaye ta rabu dasu lafiya
cikin shi Albarka inna suka rabu tabbas kyautatawa iyaye akwai riba me yawa.
Takan Kalli yaranta taji sanyi cikin Ranta gasu ko sassu dasu masu kuzari da lafiya gashi suna samun kulawa,Haidar na lelensu yana kashe musu kudi kaya masu tsada dakyau ake Sak
a musu aita musu pic ana dorawa a status da Dp kan WhasApp hakan ke Kara tashin hankalin Zulaihat
Kullum cikin kissama yanda zataga batansu take,shedan na dorata Akan hanya.
Dannewa take tana nuna musu kauna agaban zuby takan shiga suyi hira faran faran
tace tazo ganin twins.
Zuby bata nuna mata komai saima jin dadin hakan zcyrta ba komai
Shiyasa Har Zulaihat ta fara samun shiga takan bar matasu ma tashiga wanka ko tashiga Aikin kicin tabarsu afalo atare ko tace zata tafi dasu sashinta
Ana kan wata na
hudu da haifarsu ne tafara basu Madara a sashinta Dan gayawa zubyn tayi tace Madara me tsada ta Siya sbd su,dariya zubyn tayi tace lallai kinaji da yaran nan sun zama Yan gatan nono da Madara kenan.
Dariya takanyi tace,"ai dama ko da Nono Yan biyu sai an
hada da Madara.
Zuby tace"ai basu da ma Shan nono ba ruwansu da rigima ko takura Amma Usaina tafi hakuri.
Zulaihat tace"Eh kam,nima shi yasa nafison ta ba ruwanta intasaka hannu abaki tana tsotso har bacci ya kwasheta ba zata motsaba.
Zubaida tace"Ai m
ama tace hakurin ubanta Tayo Shima hakan yayi yana jariri.
Zulaihat tace"Amma Daya girma ai ya iya fada
π
Hakan sukan taba hira suna dariya kamar gaske azcyr Zulaihat,qudirinta na Nan koyaushe yaushe zata aikata abinda ke ranta na mugun nufi.
Ranar da tsautsayin ya Faru Wanda yakaita ga Dana Sani shine ranar da zuby ta saki jiki da ita ta barsu a part dinta suka wuni atare da ita
Ta basu Madara da guba aciki ta Saka fita fiya ba tausai ba Imani sbd mugunta da qiyayya.
Bata kawo asirinta zai
iya tonuwa ba Dan data maido mata dasu ma cewa tayi "Kinga yau yaran nan tunda nadaukosu bacci suke basu farkaba basu Sha nono ba bare madarar.
Zuby tace"ai Hassan ba lfy ma sosai ita Kuma Kinga ga hkr kedai sannu da Reno.
Ahakan suka rabu sbd alokacin g
ubar bata fara musu aikinba bata yarda Kuna madarar ta zuba ajikinsu ba Dan kar aji karninta arashin basirarta knn ta manta akwai binciken likitoci agaba.
Don alokacin da abun ya tsaga musu ciki suka fara kuka da ifece ifecen ciwon ciki hankalin zuby tash
i yayi.
Ta rasa inda zata Saka kanta
Abin yabata mamaki don da ace Hassan ne ke kukan kawai zata aiyana ko zazzabin Daya tashi dashine Amma sai taga atare suka shiga yanayin Kuma Ussaina dai akwaita da hkr bata taba mata wannan rigima ba.
Sosai hankalin
ta yatashi ta kikkira Haidar Bai dagaba baya kusa da wayar yau yayi busy ko wayar da suke inya fita basui ba.
Ba shiri ta debi yaraa a mota sai Asibiti.
Zulaihat taji tashin motarta da fitarta ta Lego ta window taga fitarta hankali tashe me gadi ya bude
ta fice.
Hamdala tahauyi tana fadin"Allah yasa su mutu kafin ta dawo.
Batasan cewa zata shiga ciki ba,Dan nadama ce mara amfani ta biyo bayanta.
Gwajin farko a Asibiti aka Gano akwai babbar matsala don dama ga bakin Usaina Nan datafi Shan madarar na fid
da Dafata.
Likitoci suka shaida mata abinda suka tabbatar a bincikensu na gubace tayi musu illa.
Taimakon gaggawa aka hau basu
Alokacin kuma haidar yabiyo kiranta Daya samu kansa.
Hankalinsa ya tashi matuqa gaya ba shiri ya taho asibitin wanda suke da file acan
Kukan datake ya tayar masa Hankali yai tunaΓ±in ma ko yaran sun mutune Amma sai yatar ana basu taimakon gaggawa kowanne hancinsa da oxygen
Amma fa Usainar bata kwana ba ta
ce ga garin kunan Dan ta wahala sosai Hassan ne Dai dama ko nono ne Bai fiya Sha dayawa ba, baisha madarar dayawa ba shiyasa bata shigeshiba gubar.
Ansamo kansa an dorashi kan magani yasamu bacci amma fa ya amayar da gubar ya fita haiyacinsa.
Kuka sosai
zuby taci,Shima Haidar yaji abin acikin ransa yana mugun son Usaina sbd hakurin yarinyar ga kyau sosai fiye da uwarta.
Asibitin ya fara cika da yn'uwa ana jajantawa.
Kowa tambayarsa ya Akai hakan tafaru.?
Ita dai zuby Babu bakin magana sai kuka.
Da suk
a koma gida aka sallaci Usaina aka tafi binneta.
Baban Haidar da kansa yasakata agaba da suka dawo da tambayar ya Akai hakan ta kasance?
Taso ta boye ta rufawa Zulaihat Asiri wacce har lokacin takasa fitowa tazo sashin don ta tsorata da taga gidan
yafara cika da JAMA.a 'yan,uwa gashi tajiyo anata maganar yaran guba aka basu.
Haidar yanata tada jijiyar wuya yana fada Akan duk ma Wanda yai masa hakan bazai barshi ba Kuma tasani inhar bata fada ba ita zai dorawa laifin.
Ba shiri ta fadi yanda
Akai a wunin basu wuni gun taba Kuma basu wani Sha nono ba aranar Amma tace atambayi Zulaihat don agunta suka wuni.
Ba shiri aka ritsata kuwa tayi fiki fiki,Amma Dan karfin hali harta iya samun bakin magana Akan cewar ita fa bata basu madarar ba aranar.
Tsawa Haidar ya buga mata yayi kanta zai bugeta a fusace,Baba ne yatareshi da bashi Baki"kabi Ahankali Aliyu Muji ta bakinta yanda Akai har ta aikata hakan.
Musu sosai tayi