Showing 24001 words to 27000 words out of 34383 words
kariya daga babbar masifar irin wannan.
Matansa su hudu kaf suna tare dashi kowacce na nuna masa kulawa.
Su har zuciyarsu suke nuna masa Amma ita zubaida iya bak
ine don taso ace Bai dawo ba ya mutu ahannun nasu ko ta samu gado na tumulin takaba sannan ta fita ta Auri Wanda takeso.
Kwana biyu aka sallami Alhaji yasamu sauki yana magana Amma sai ta kama garau yake dai ba inda ke masa ciwo,shiyasa suka bashi
sallama.
Aranar zubaida ta wuni agidansu tare dashi
Kowacce ta jajanta masa ,Nan Kuma yabasu labarin yanda abin yakasance.
Hajiya babba tace"ai mu dole mu gode Allah,domin da baka fito ahannunsu ba da hawan jini zai iya kamani sbd Abu goma da ashirin ne
yahademin,kana tsare bamu San halin da kake cikina,su Kuma yan sanda sun kama min Mansur suna zargin wai da Saka hannunsa aciki.
Alhaji yana ajiyar zcy yace"Ina me shaidar Mansur bazai taba aikata hakan akainaba,Amma kam zan basu ko nawane Akan su tsanan
ta bincikarsu na su fadi Wanda yasasu sukai min hakan.
Gaban Zubaida ya fadi.
Alhaji yakalleta yace"Yakamata ki tafi gidan ki kada dare yayi tukin dare ga mace ba Dadi.
Hajiya babba tace"da ace Mahmud na Nan ma sai yakaiki,Amma ankikkirashi wayarsa bata
tafiya gashi ba,asan inda yajeba,Mansur Kuma yana kwance tunda aka sakoshi ahannun yan sanda yake baccin wahala.
Zubaida tace"zan ma iya tukin bari naje gida kawai.
Ta mike tana me musu sallama.
Da taje gida ta dade tana tunanin wannan
lamari,yanzu idan sunanta ya fito ackn Wanda suke da hannu Akan sace Alhaji me zatace dasu kenan? Dan ma babban me laifin ya gudu.
Tabbas ita kam tana tsaka me wuya domin ayanzun ma idan Alhaji yaji cewar tayi bari sai ya tuhumetan don yasan Bai barta da
ciki ba.duk da tana da dabarar da zatace masa da zai hkrn.
Bacci barawo Bai dauketa da wuriba sai wajen biyun dare ya saceta.
Da sassafe sai ga Alhaji agidanta fuskarsa ba fara,a
Gabanta ya fadi ganin ya cukule sannan dakyar ya amsa gaisuwarta.
Zama y
ayi kan kujera yana fadin"zubaida zauna muyi magana ta fahimta.
.ta zauna adarare idonta akanshi
.yace"wato Nasha mamakin Jin cewar wai kinyi bari to nikuma nasan kafin natafi banyi komai dake ba sannan kina Al,ada natafi na barki Dan haka ko zaki iya gaya
min cikin waye Kuma dama kina bin wasu mazan ne bansaniba?
Taja ajiyar zcy cikin dakiyar zcy tace"nikaina da akace Ina da ciki Nasha mamaki sbd nasan kafin katafi Ina period saidai da likita yaimin bayanin Ashe Ana yin jini da ciki shine hankali na ya kwa
nta...dakatarta yayi da buga mata tsawa yace....karya kukeyi bantaba ji ba....ta bata rai tana fadin"haba my sugar zargina kake kenan.?
Cikin daga murya yace"ke saurara zubaida yau babu batun wani sugar ko baby ki fito ki gaya min gaskiya ko in sakeki.
Taja ajiyar zcy tana fadin"zanfi kaunar Sakin akan zargin da kakemin,da kagen bin maza,Amma inason ka kira wani likitan ko wata likitar katambayeta akan zancen na Ana Ciki da period kuwa?ko ba ayin.
.
Take kuwa Alhajin yasaka waya yakira wata metron yahau
mata wannan tambaya.
Metron bilki ta gaskata masa tare da masa cikakken bayanin Akai,har dai ya gamsu.wato dai zubaida kurman ciki tayi.
Ganin ya gamsu sai tace"Amma kasani Alhaji walh bazan zauna dakai kana zargina ba,kawai kabani takardata tabbas nayi
nadamar Aurenka....ya daga mata hannu yana fadin"bazan sakeki ba zubaida Amma inason kisani indai kin cuceni to kije ke da Allah Amma Alh Hamza baya saki.
Ya fice yabarta Baki bude ta zaro Ido tana mamakinsa.
To wannan inaga Kuma yasan da Saka
hannunta akan saceshin,Ashe ita kam gara da Mahmud ya bar gari da Tasha Kashi gun Alh.yanxu ita saki kawai take bukatar dama ta gaji da Auren nashi Ai
A kwana biyun da Alhaji ya fito wadannan yan ta,addar da suka saceshi sukaji wuya iya wuya ahannunsu saj
ent musu tuni suka magantu saiga sunan Mahmud ya fito amatsayin me Aikin Daya sakasu.
Kowa agun yasha mamaki na wai Da ne yasa aka sace mahaifinsa tabbas duniya tazo karshe.hajiya babba kuka tai tayi.
Alhaji yace mata"ki daina wannan kuka don walh nayi ra
ntsuwa da Allah sai Mahmud ya bar min gida,don bazan masa komai ba Amma zanbarshi da Allah,bakuma zan bari su azabtarshiba Amma kam indai kikai wata maganar Akai to tare zaku bar min gidan sbd akwai sirri tsakaninmu Wanda nake tayaki boyeshi na rufa miki a
siri.
Kuka ta fashe dashi tana fadin"walh ban yarda ba,bazan Kuma aminta ayiwa Dana sharri ba.
Ya buga mata tsawa yace"ya Isha haka kada ki harzukani intona asirinki hajiya,kyaleki kawai nayi ke da danki Amma kam komai yazo karshe bazan kyaleshi agaba ya
kasheni ba,dama arzikin "yan'uwansa
yakeci Amma kam nagaji duk inda yake Kuma sai nasa annemomin shi,bazan bari su azabtarshi ba Amma kam ni zan masa hukunci daidai shi.
Hajiya ta hau fututtukar fada tana cewa Alhaji "walh bazan bari Dana ya wulakanta a i
don jama a ba kawai dama na fahimci ba sonshi kake ba to kuwa inhar ka koreshi to ni ka kora.
Ya nunata da yatsa yana fadin"ke har kina da bakin magana to kisani inhar kika goya masa baya nikuma zan hukuntaki da Kuma baiyana sirrin da nake tayaki boyewar.
Ta fashe da kuka kawai.
Duk wani Abu na binkice ya hattama an tabbatar dai Mahmud shine yasaka ayi wannan Aikin na sace Alhaji,Kuma an dubashi baya koina acikin Kano ba,a ganshiba,Amma wani abokinsa yace yai tafiya.
Duka ya tara matansa yana jaddada mu
su cewar ayau ya cire Mahmud daga cikin yaransa sannan zai kwace komai Daya mallaka masa daga gida zuwa mota da sauransu,sannan su sani ayau yana me ajiye sirrin Daya dade yana boyewa na Mahmud dayake ba amatsayin Dan Daya Haifa acikinsa ba.
Sunkui da Kai
hajiya babba tayi tana zubda hawaye tabbas Mahmud shi yaja domin da Bai aikata hakan ba da ba a masa wannan terere ba yanzu shikenan kowa yasan ba Alhajine ya haifeshiba.
Aunty amarya tace azcyrta to dama Dan riko ne kenan.?
Maman Yara itama axuciyarta
tambaya take Ashe dama agola ne?
Ita kuwa zubaida cewa tayi aranta"haba no wonder mana yake hanqoron kashe Alhaji Ashe ba shi ya haifeshi ba to Dan shegene ko Dan halak zasuso suji fa.
Alhaji yai gyaran murya yana dubin hajiya babba yace"Mahmud yana cikin jarabawarki tunda akansa muka Sha samun matsala har ajiyeki nayi agefe duk akan wannan matsalar to Amma tunda yaimin hakan na gaji na Kuma hakura kowa ya kama gabansa ni dashi.ke Kuma i
nkinso zaki iya ci gaba da zama Dani,in Kuma danki zaki bi to sai ki nemeshi kibishi kutafi tare Amma da takardar sallamarki
Duka matan ita suke kallo takasa magantuwa.
Shi kuwa Alhaji cewa yayi"munyi Aure dake alokacin bansan kina da ciki ba sai da kik
a shigo gidan da wata biyar kika haihu na karbi lamarin amatsayin nawa ne,Alhalin ba nawa bane kin boyemin ne Nima sbd tausayinki karki wulakanta na boyewa mutane nakuma ci gaba da zama dake,Kinga kuwa tunda yaimin hakan zanbarshi kada gaba yakasheni,Kuma
Ina me sanar dake cewa indai kika sameshi kiyi gaggawar sanar masa ni ba mahaifinsa bane ya cire rai da samun arzikina idan na mutu Dan bashida gado.
Kuka sosai hajiya babba keyi kishiyoyinta nata kallonta suna jujjuya wannan lamari...
To Muma bari mu ju
ya lamarin kafin mudawo.
*YAR GWAL*
( ~me kayan Dadi~)
_the sugar daddy story_
Na _Nabilancy love_
š
*Auntyn S and S*
______________________________
šš°
AINUWA
š¼
RITER'Sā
š¼
*
š¦
SSOCIATION
š¤š»
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
______________________________
Page 14
Alh Hamza ya Mike yana me Shirin fita A gidan Amma da sauri
Hajiya babba ta mike Tasha gabansa ta Durqusa ta dafa kafafunsa idonta cike da hawaye tana fadin"Alh ka yafe mana ni da Mahmud Ina me neman afuwarka,gara ka hukuntamu da kanka,Dan Allah karka bari maganar Nan ta bazu ko su Yan sandan su dau Mataki da hannu
nsu abin bazai dadiba,insha Allahu nima zan hukuntashi....ya daga mata hannu yana fadin"ni kam ke bakiyi min komai ba,tun afarin da kika haifeshi tausayinki ma nakeji Akan hakan,tunda ba da saninki kikai cikin sa ba,hakan yazo a kaddararki to Ashe ni makas
hina na kawo cikin gida,tabbas bazan yafe masa ba,na Riga na Baki zabi,inkinga kina son ci gaba da zama Dani amatsayin miji to Babu batun saki atsakaninmu DUK da sauranmu Daya,Kuma dama akansa sauran biyun suka wakana,Amma kisani Mahmud bazai sake zamarmin
agidaba ko da yadawo,sannan Jami'an tsaro bazan hanasu aikata hukunci akansaba,don in Aka barshi hakan to kisani agaba ko ni ko ke zai kashe,Dan haka indai kina son zama ackn gidan Nan to daga Rana irin ta yau kar nasake Jin an ambaci sunanshi,Kuma kisani
ko gidan yari suka turashi bazaki je gareshi ba sai dai in Babu Aurena akanki,dama darajar zubaida kikaci abaya na maidaki dakinki da muka rabu Kuma naji tausan Baki da gurin zuwa kiji dadin zama inba Nan cikin manyan yarankiba shiyasa na barki kikai zama
n 'ya'yanki.
Yana gama fadin ya wuce ta gefenta ya fita.
Ta fashe da kuka.
Aunty Amarya taso ace taji labarin Hajiya babba na yanda Akai mahmud ya zama shege.
Hajiya babba ta mike ahankali taje ta kamo ta ta zaunarta acknsu kan 3 siter akusa da Zubaid
a tana fadin"kiyi shiru Hajiya kada yara su shigo ki kwantar da hankalinki komai zai wuce,Kuma ki cire damuwar Mahmud aranki kada kizo ki kamu da babbar cuta,zanso Kuma kiyi biyayya ga Alhaji sbd dauwamar Aurenku.
Zubaida ta matso ta dafata tana hawaye ta
ce"tabbas Hajiya tun da nashigo gidan Nan afarko nayi miki rashin kyautawar rashin Sani,Amma daga baya da nasan kece uwar 'ya'yan Alhaji na gyara,Kuma na shiryaku Dan haka Ina me Baki shawarar da ki zauna da Alhaji sbd yaranki Kuma kinyi girman da yaci ace
kin wuce zaman gida,bazamuso Aurenku ya girgiza ba,tunda yace sauran Daya,Kuma wannan Karan yana me ikirarin barinki gidan Nan,Dan haka Dan Allah ki danni zuciyarki.
Hajiya babba ta dago ta kallesu tana share hawaye tace"tabbas naji na gamsu Kuma nagode
muku sannan Mahmud na barshi yaje yashiga duniyar nasan zata koya masa Hankali ne.kuma yanzu zan baku labarin yanda Akai na samu cikinsa nashigo gidan Nan da ciki.
Nan ta gyara zama ta fara da fadin"Alokacin Ina budurwa Mahaifina yayi rashen kudi Kuma ni
kadai ya haifa yanaji Dani sannan mahaifiyata ta rasu kafin na gama secondary sai Babana yayi Aure matarsa Yar bauci ce Kuma tana min Rikon Amana da gaskiya batada matsala,tazo har tsahon wasu shekaru bata haihu ba.
Awani dare 'yan fashi suka shigo gdn m
ahaifina fashi.
Sun kwashi kudi sosai sannan sukai min Aika Aika n fyade.
Su biyar ne Amma mutum biyu suka haikemin manyansu kenan Amma babbansu shine ya fara Kuma sau biyu yana min Wanda naita ihu nafita haiyacina don yana kaina na Suma.
Sai da aka ka
ini Asibiti, Alhaji Hamza shine babban yaron Babana na sirri shi kadai yasan wannan labari Kuma ya tausaya min sbd dama anata Shirin idan nayi candy a Dauramin Aure dashi DUK da ba soyayya muke ba wannan Alkawarine na iyaye.
Wannan Abu Daya Faru Dani yasa
Babana awani Hali na damuwa da rashin lfy ga dukiyarsa tayi kasa.
Yazo ya kwanta jinya kadarorinsa suka shiga ciki Dan sai dasu Akai Babu abinda ya ragu sai gidan da muke ciki Kuma Daya rasu ma sai aka sai dashi aka bawa Hajiya lami matarsa
tumulin takaba ta koma garinsu Bauchi nikuma kudin gadona yana hannun Alhaji yana juyawa har aka dauran Aure dashi yasai min kayan daki dasu sauran Kuma na mallaka masa Shima ya dora da Yin business Wanda Allah yasa masa Nasibin da har dukiyarsa ta bunkasa
, Alhaji yana Sona Bai nunamin komai ba Kuma iyayansa alokacin kafin su rasu suna Sona su ma Dan dama agunsu na zauna kafin aurenmu da babana yarasu sbd babana bashida kowa anan Dan zamfara ne sai daga bayane ma wani yayansa yazo Nan yafara kasuwanci da iy
alansa.
Karshen labarin dai Ashe akwai ciki ajikina bamu saniba,Saida ya fito tunda ba wani hankali yacikaniba,Nasha kuka sosai Dana Gano ba nashi bane,don nasan wannan Ogan Yan fashin sune sukaimin ayanda qirgen watannin ya kama don ciki wata shida Aure
Wata biyu.
Alokacin iyayansa sun rasu Dan ma ba wani dangi yacika anan ba Alhajin. Shiyasa Asirina ya rufu shi kadai ne yasan ba cikinsa bane shiyasa ya rufan Asiri muka reni cikin tare,sbd naso azubar shi ya Hana ya nunan cewar tunda ciki ya nuna zansha
wahala ko na rasa Raina tunda dole saidai a burgeshi wajen fitar dashi.
A lokacin Mahmud na ciki tsanar cikin Nayi Amma da yazo duniya sai Allah yasamun son cikin Kuma yazo kyakkyawa dashi kunsan dai Dan shege da kyau Wanda aka haifa ba Aure.
Lokacin da
nayi haihuwa ta biyu na haifi Mansur ba wata tazara dayawa ta shekaru don Mahmud Bai cika shekara ta biyu ba Mansur yazo duniya Kuma sai suka danyo kama tunda DUK sun daukoni sannan Alhaji yafi murna da doki na zuwan Mansur kam ban nuna damuwata ba don hak
an ba laifi bane,sannan yanda uba kewa D'ansa komai na haihuwa tundaga kayan jarirai da hakika Alhaji yayiwa Mahmud,haka Kuma da suka taso suka fara girma komai tare yake musu.
Sai da nayi haihuwa biyu na Mata Wanda suke gidan miji alokacin ne Alhaji ya A
uro ke Maman yara nagodewa Allah na godewa Alhaji Dan Bai gayawa kowa wannan siriin ba sai kawo yau da wannan lamarin yai sanadin da kukaji.
Kuma alokacin da wata rigima ta hadamu Wanda Babu Wanda yasan dalilin dayasa Alhaji Bai sanarwa da Habiba da Zubai
da ni matarsa bace da zai Aurosu har da sukazo gdn Nan suke hanani Abincin wannan ma a sanadin Mahmud ne.
Don mukam samu yin sa'insa Akan sai naturashi karatu wata kasar shikuma yace ba haka ba,yafisonsu anan sbd ya koya musu kasuwanci yafi sonsu akusa da
shi
Tabbas akoyaushe Alhaji yafini gaskiya ban Kuma San shi me Sona da kaunata da yaro na bane Saida yasai musu gida da abin hawa atare Babu banbanci shiyasa Nagano nice ma nake masa butulci Amma ayau nagane na zubda komai zanbi Allah zanbi Alhaji sbd s
hi din mijin Asiri ne,yasan darajar matar fari yasan darajar Rikon marainiya,gashi asanadin Mahmud yaron Babban Dan fashi zamu samu sabani.....
Rufe mata Baki maman yara tayi tace"kada ki sake fadin hakan,Dan Allah kada ki dawo yi masa kallon D'an babban
d'an dashi hakan bazai yiwu ba Akwai kannensa da bazamuso suji waye shi ba,kowa da tashi kaddarar shi take kenan,kema taki kenan,haka Alhajin ma tashi kenan akansa,ki godewa Allah da hakan yazo miki asauki,anjarabceki Kuma kinci jarabawa Dan haka ki karasa
ahakan,muma zamuci gaba da rufa wannan asirin. Ta dubi habiba da Zubaida tace"kubamu hadin Kai Dan Allah Kuma kunji.
Habiba ta gyada Kai cikin sanyin jiki da tausayi.
Zubaida da take hawaye ta share tana me fadin"insha Allahu kuwa,Kuma Ina me Baki shaw
ara Hajiya da kiyi ta masa Adduar Allah ya shiryashi kawai.
Hajiya babba ta gyada Kai tana me murmushi Jin dadin samun abokan zama na gari.
Kwana biyu da faruwar hakan anata neman Mahmud guri gurin ackn jahar Nan Amma Babu labarinsa,hatta gurin Aikinsa d
a akaga bayanan sun tsananta bincike don sunyi zaton ko kidnapping dinsa Akai,Amma da sukaji abinda yayi abakin Jami'an tsaro sai suka rubuta masa takardar korar Aiki in anganshin.
Aranar da Alhaji nagidan Zubaida rigima ce ta balle atsakaninsu sbd ya Gan
o tana Shan maganin planning sannan yazo mata da maganar zai karo Aure da gasken gaske Kuma wacce zai Auro 'yar masu kudi ce tasanta don yarinyar fitacciyace tana tictok
Samun hanyar ficewa agdn yasa ta bijire masa ta tada ballin bazata zaunaba sbd karuwa zai Auro bazata zauna da NiNa Sim card ba haka ne sunanta
Alhaji ya murmusa yace "to nikuma gashi bana saki ya kenan.?
Ta mike tsaye tana masa wani banzan kallo tace"a
i shiyasa bana son na haihu dakai Alhaji sbd me ake da Namiji me Aure Aure,walh da cikin Nan ma Bai zube ba tabbas da zubarshi zanyi.
Yace mata"Ke ma nasan sbd kudina kika Aure ni Ai,sannan Kuma ki godewa Allah kinci naci gashi Nan kin canza ko haka na Au
roki?
Taji wani malolon haushi cikin ranta tace "ba haka ka Auroni ba K'aruna,shiyasa nake so ai kasakeni na koma wahala tunda awahalce ka Auronin.
Wayar da aka kirashi ne ya Hana ya karasa maganar Daya bude Baki da niyyar yi mata,ita Kuma taje ga sif ta
janyo akwati tana loda kaya tana fadin bazata Kara kwana agidan ba tabar Aurenshi, idan ta makashi akotu ai dole ya saketa.
Ficewa daga gidan yayi yana amsa wayar da aka kirashin wanda bakuwar nambace Kuma sanar masa akeyi Akan anyi wani hadari gagarumi
Wanda mutanen cikin motar suka mutu sai drivern kawai An mika mutanen Asibiti Shima Wanda Bai mutum ba yana asibitin ankwantar dashi awani Hali yake,an tsinci wayoyinsu ana Kiran nambobin iyaye da suzo su ga waye nasu aciki.
Alhaji yace"eh to gaskiya babu
ni acikin iyayensu sbd babban Yarona yana tare Dani Mansur domin yana ksw ma yanzu haka.
Daga bangaren da ake kira akace"da dai kazo Alhaji sbd anga Fa me wayar yasaka My father Akan nambar.
Alhaji yahau fada yana fadin"To nagaya muku ni bansan shiba kad
a ku Kara kira na.
Me wayar yace"sunan me wayar Nan Mahmud Amma bamu da tabbacin yana cikin matattun ne ko shine me ran tunda ahanyarsu abin yafaru mu taimaka musu mukai muka kawosu asibitin.
DUK da gabanshi ya fadi Amma sai ya Dake yace"bani da D'a me i
rin wannan sunan.
Ya kashe wayar.karsu dameshi ma