Showing 3001 words to 6000 words out of 34383 words
yace"natafi Zuby sai watarana,Allah ya hada fuskokinmu da Alkairi karki manta dai har kullum nine me sonki da kaunarki muddin Rai,Ina Miki fatan Rayuwa me Albarka.
Ya juya yai gaba Yana me share hawaye Bai yadda ya waigo ba.
Kawai sai t
a kasa tafiya tana kallon bayanshi har ya qule.haidar Namijin gaske ne atsaye Inka kalleshi Yana da qirar Zaki jayint ne me faffadan Kirji ga kyau agunsa black beauty ne ga Ana yabon halayensa masu kyau karatu yakeyi bashida cikakkiyar Sana,a sai dinkin Ma
za da yakeyi idan ya dawo daga Sch.
Iyayansa ba masu shi bane,sunyi soyayya da zubaida tun batada wayo suke tare da girma yazo Mata Kuma ta fara juya Masa bay,a Dole take kulashi karshe ma da Allàh ya hadata da Alhaji sai ta juya Masa baya gaba daya,dakya
r take iya tsayawa dashi sau biyu a sati,da Alhaji yakawo kudin Aure ma sai tai Masa wuyar gani sai in ahanya ya ganta take tsaya Masa dakyar su gaisa,Abu daya ma da take tunawa yake cin Arzikinsa shine Ada shi yake ququtawa yai Mata kayan sallah wani zubi
n ma har uwani takan samu,kala daya ko biyun Nan dai takan tsira dashi,wani zubin kawun nasu yai musu biyu ko daya su hada abinsu.
Hawaye ta hau gogewa ta koma cikin Gida tana fadin"Ina Yi maka fatan Alkairi Haidar,Allah ya baka daidai Kai wacce zaka so a
gaba,Allah ka yafe min Dan ban zalinceshi ba,Kawai zabina na samu shiyasa.
Tana zuwa daki ta yage takardar jikin Abun, taga agogone da hotonta aciki Wanda ta taba bashi Ansaka *BEST WISHES* Acikin agogon sai cutcee Aliyu Haidar da aka rubuta.
Ta hau shaf
a Agogon tana murmushi Allah sarki Haidar tasan Dan ya faranta Mata ne,wani zobe tagani na Azurfa me jar danja yayi Mata kyau ta dauka ta saka a yatsanta na dama.
Tabbas alamu na nuni da bayaso ta manta dashi.
Taji kamar ta dauki waya ta kirashi Dan Yi M
asa godiya sai Kuma daya zuciyarta me sata girman Kai ta tahanata.
Kawai ta kunna data ta fara chrt Abinta tayi sa,a ma sugar dinta na online Nan suka hau chart cikin Nishadi.
*******
*******
Da safe wajen 9 ta Gama kintsawa ta gyara dakinta ta adana Ma
shayar shisha dinta can gefen katifa sbd kafin tayi bacci sai da Tasha Abinta ta qoshi
Gidan kawu zataje gun Matansa taji abinda yakamata ayiwa Yan kawo kayan lefe da zasu kawo yau.
Tun dare Alhajinta yace Mata Yau Abokin mahaifinsa da Dan uwan baban na
shi zasu kawo Kaya shiyasa ta tashi da Abun aranta,inba zuwa tayi taga Antsara musu Abin baka ba Hankalinta bazai kwantaba tafiso ayi musu harkar girma a soya kaji da snacks da lemuka tunda Suma kayan girma zasu kawo.
Ta Shiga Dakin Inna ta tararta tana S
hirin fita Bara.
Rai abace Zubaida tace"yanzu Inna ko karyawa bazaki tsaya kiyi ba yau?
Innar tace"zubaida yau Juma'a da wuri muke fita Kari Kuma ai Uwani ta dama Mana Koko munsha ta siyo Mana waina.
Zubaida tace"Akwai shayi a plask zance taje ta
debo muku asiyo biredi Ashe kun karya ma,to aishikenan Nima gidan kawu zanje insami Su Mama da Umman Nana inji Shirin abubuwan da za,ai na saukar Baki Yan kawo lefe xanbasu kudin da zasui musu Snacks asai kaji da lemuka.
Innar tace"kawun ki ma Yana da kok
ari da ace Yana dashi ba saikinyi,Amma dai kije kiji din,Nima da wuri Zan dawo yau kafin La,asar.
Zubaida tace"ai Inna ma yau Bai Kamata ace kin fita ba,ko Kuma ki dawo bayan masallaci.
Innar tace"Ah,Ni da ba Ni Zan karbi lefen ba,Kuma ba anan Za,a karba
ba meye na saina dawo da wuri Dole,ai fitar mu ta yau akwai Alkairi Juma,a.
Hhhuumm kawai zubaida tace ta fice Abinta sbd Bata Isa ta Hana Innarta wannan bara data shiga ran taba,don ta Dade tanayi ko kawu yasha fama tace suyi hakuri bataso ta dorawa kow
a Nauyinta ne,da tana da Ido ma sai tayi Sana,ar cikin Gida ko Aikin wankau ko Aikin wanke wanken gidan masu kudi,to Amma tunda Allah ya hukunta Mata yin bara sai suyi hkr itama batasan zata yita arayuwaba sai da maraicin miji yazo Mata.
A gidan kawun kuw
a da taje ta tarar ya fita da wuri kasuwa.
Ta zauna da matansa a Babban falon gidan.
Mama uwar gidan tace"to ke Amarya maza ne zasu kawo kayan ko Mata? In Mata ne mu faffadawa makwabta in maza ne Kuma to kawunki zai sanarwa Aminansa na kusa ne da makwabc
insa.
Umman Nana Amarya tace"ya ma sanar musu fa don Daren jiya Muna daki naji Yana waya Yana sanarwa.
Zubaida tace"Ai nagaya Masa dama mazane zasu kawo,haka Alhajin yace.
Mama tace"to ga lemuka can ma katan biyar kawun ya kawo gidan yace abinda za,ai n
a soye soye sai in ya dawo bayan masallaci sai ayi tunda zuwan magriba zasui ko.?
Zubaida tace"gaskiya katan biyar yai kadan sbd ba kananun mutane bane,Kuma Kaya ba yn Nigeria bane ya kashe kudi muma Dole mukashe wajen fitar da kanmu kunya.
Mama ta
gyada Kai kawai.ita kuwa Umman kallo take binta dashi.
Zubaida ta zuge jaka ta fito da kudi ajaka ta Ciro kudade tahau qirgawa tana fadin akaro ruwa katan uku lemo katan biyu kunga goma kenan sai a siyo kaji guda goma a soya ayi cake da Donut
🍩
na kwano g
uda.
Umman Nana ta Kama Baki tace"abubuwan bazasui yawa ba kuwa.?
Zubaida tace"Harkar gima zamuyi Umman Nana tunda inada kudi Zan Kuma samu wasu awajansa karkuji komai.
Haka ta dire musu kudaden da akai lissafin abinda za.a kashe ta tafi.
Kama Baki suk
ai suka hau maganarta gani suke a lamarinta zallar karya ne da fafa Mama tace"Ai daga Dubai aka hado kayan fa.
Umman Nana tace"eh lallai zamuga Kaya Yan dubai yau.
Da magriba kawu ya hada mutanensa acikin gidansa.
Gidansa na Rabin filotine ba laifi Yana
da kyan fasali ba yabo ba fallasa.
Haka dakinsa ma dake da kofa ta waje sittin room yasha gyara kafet ne a malale da kujeru da kayan kallo an tsaftace Yana kamshin turare.
Ga kayan da aka tanadawa Baki a jibge agefe an nannadesu a foil paper me kyalli k
omai su mama da Umman Nana sunyi tsaf da fitar da Yar gidan tasu kunya.
Yan kawo Kaya sunzo akan lokaci motoci biyu sukai.
Kuma Kaya sunzo cikin Aminci da yardar Allah akwatina sunyi kyau da alamun tsadarsu Yan wajene Kam.
Anyi Abu cikin mutumci da girm
ama juna Dangin Alhaji Hamza sunkawo Kaya na gani na Fada Abu yayi ba kushe akwatina goma Sha biyu cike da Tsadaddun Kaya.
Su ma su kawu sunbisu da Sha Tara ta Arziki don dubu dari suka Dora akan akwatinan,haka kawu shima ya Dora musu dubu hamsin Akan lem
ukan da aka fita musu dashi dasu kajin da snacks.
Antsaida ranar biki sati uku me zuwa
Kawu da matansa sukaita jinjina kudi irin na Alh Hamza Dan ya kasosu ackn lefen Nan.
Atamfofi kala arba'in sai lesika kala Ashirin da material da shaddoji kala
Ashirin Suma dogayen riguna masu stone na ba sha'awa kala goma sai kananun Kaya da kayan bacci kala goma
Dangin jakankuna da takalma da mayafai kuwa ba,a magana Dan Babban akwati aka ciko dasu.kayan make up kuwa zatafi shekara bataga karshen su ba.
Kaya
fa sunyi komai Rabajau da safe Yan unguwa da ake zaman mutunci sun shishshigo sunga Kaya sun saka Albarka.
Saida sukai sati kayan Nan agidan Kawu kana yasa aka kaisu gidansu zubaidar saboda Kai dinki.
To itama Amarya ta Yaba kaya taji Dadi matuqa Alhaji
nta ya fiddata kunya ya nunawa duniya Yana sonta duk da Arzikinsa ne ya Nuna hakan,ta dauki hoton kayan ta Dora a status hade da anko sannan taita turawa kawaye da Dangi.
Sai da yabata kudin dayai Alkawarin ne ma dubu dari biyar na sauran shagulgulan da z
atai sannan mota yace Mata zata iso Nan gaba Amma sai in bayan ta tare.
Murna jitai kamar an Mata Albishir da Shiga Aljanna,Taji ta Kara sonshi Tabbas dace da miji dai tagama.
Da Abu ya qarato tare da Halimatu sukaje Kasuwar wambai sukai siyayyar kayan k
icin da Bata karasa siyaba ta hado labulaye masu kyau kalar kujerun data zaba,da zannuwan gado manya,dama dubu dari uku takaiwa kawu acikin kudin zai cika yayi Mata kayan gado da kujeru don katifa tuni ansiya da kudin gudummawar yan'uwan Inna da suka Aiko
daga kauye da Kuma Yan uwan kawun Mata su biyu da suke gidan Aure aka harhada aka sai Mata inci goma vitafoam me tsadar.
Sungama siyayya suka wuce gurin me gyaran jiki tayi booking sbd Ana saura sati biyu zata Fara zuwa ta Bata harda kudin turarikan wuta
da humra.
Ita kanta Halimatu ta kawo Mata gudummawarta na babbar cooler ta Abinci da plate plate da cokula na Yan gayu matuqar Jin dadi Zubaida taji daki guda take ajiyar kayayyakin kicin din, Gas cooker dinta babbbar ne komai ta siya sai godiya.
Mahaif
iyarta inna kayan abincin da za,aci agun biki ta sissiya Dan Dangi na kauye zasuzo tayi musu dinki itada uwani kana ta bada kudi aka hadowa zubaidar magungunan Mata
Kuma hakan datayi ya faranta ran zubaida sosai tunda Amfanin uwa dama ta fidda Yarta kuny
a ta Nan.
Ango ya ringa Nuna dokinsa ga Amarya kusan koyaushe suna tare.
Ranar da aka fara dinner tayi matuqar kyau ta kashewa kanta kudi kayan data saka yn ubansun material me tsada acikin kayan lefen ta dauka ta dinka ta hada komai macin da jaka ta
hannu da takalmi,ga madaurin Kai da na yafawa akafada iri daya ga mafici irin takalmin sarkarta me shegen kyau kamar gwal.
Ango dama baizo gurinba sunyi hakan tun farko baice zai iya zuwa gun ba haka tayi Abinta da kawayenta.
Amma anso ayi tarzoma agurin
Dan wasu Yammata ne sukazo su uku gurin Wai Auren ubansu akeyi dolene suzo suga Amaryar tayi ko batayiba.
Gaban Zubaida ya Fadi ganin manyan Yammata babbar tayita Wai duk Yaran Alh Hamza cindo ne.
Da Allah yasa itama ta gayyato tsageru gurin dinner din
sai 'yayan Alh hamzan basuci galaba ba sukai Yan fade faden maganganunsu suka tafi ganin matan gun sunyo kansu harda masu zaginsu.
Da fadin Basu da tarbiyya.
Sai da aka tashi a taro ta sanar Masa awaya tana kuka tana Nuna Masa yaransa sun bada ita agun.
Ya dafe kansa Yana fadin subhanallah!meyasa sukai Masa hakan,lallai yasan da laifin Hajiya Babba,yaita Bata hakuri yace zai tsawatar musu ko ma ya koresu agidan.
Tace"shiyasa ai naso ace ka wareni agefe ba acikin manyan matanka ba,ta yanda zamuci soyayya
ba takura.
Yace"kiyi hkr zaman Dan lokacine ke da nake Miki gininki a wani gurin daban ki Kara hkr *Yar gwal* Dina. Haba me kayan Dadi Bai Kamata ace Amarya ta Bata Rai Akan wani Abu kalilin ba sorry kinji my Baby.
Taja ajiyar zcy tana fadin"shikenan my
Sugar ta wuce.gobe Yan jere zasuzo ka tabbatar ka tsawar wa matanka Dan Kar asami matsala fa.
Yace"za,ai hakan.
Sukai sallama ta kashe tare da Shiga tunanin rayuwar da zata shiga agaba fatanta dai Allah yasa ta iya zaman nan.dan Bata son tashin hankali
fa.
Angama biki cikin kwanciyar Hankali anyi komai tsaf.
Akazo Kai Amarya Alh Hamza ya turo motoci sunyi goma,kowa yasamu zuwa.
An Kai Amarya gidan Alh Hamza daya baiwa Yan Kai Amarya mamaki don wasu kujerun nata fa suna tsakar Gida agefe guda
Basu cinye asashin nataba.
Wato babu wani part part Daya fada mata agan,Babban gidane dai self contain kowacce Dakunanta na cikin babban falon,na yara suna gefe sai na mazan gidan daga tsakar Gida yk,Yan Kai Amarya sukaita rike Baki wato Namiji duk tsufan
sa sai yayi karya,shi da yace Mata kowa part dinsa daban,Ashe abinda su Umman Nana da mama suketa boye Mata knn Ashe akwai abinda suka gano shiyasa sukaita Bata hkr,to ita kuwa bazata taba hakurin Nan ba
Sai da Yan Kai Amarya suka kaita dakinta suka wats
e sai Halimatu kadai da take jiran saurayinta zaizo daukarta a mota ya mayarta Gida taita Bata hakuri tana cewa"Kinga abinda nake jiye Miki zaqewa Akan Namiji da cin buri uwa uba rashin bincike ga abinda son duniya yaja Miki kalli gidan Nan da yaci ace zam
an mace dayane ko biyu ne awadace,Amma Naga kamar ma ku hudu ne agunsa,Kuma naga ai ke ce maki ma yai matansa biyu kece ta uku to Amma Nagano ba Haka bane tunda Naga Mata uku Kuma da alamar kowacce matarsace da ake mik'aki amana gunsu Dan Anko sukayi ma.
Halima tayi shiru kana taja ajiyar zcy ta dafa hannun Zubaida tace"hakurin dai zanta Baki kiyi Masa lamfo kiyi Masa kwanton Bauna kiga iya gudun ruwansa karkice uffan dai nasan halinki da Rashin hkr.
Cikin dacin Rai Zubaida ta gyada Kai kawai tana share h
awaye Dan ta kasa magantuwa.
Ko da akazo daukar halima anan kukanta ya kubce ta riketa tana gunsheke halima jiki asanyaye tace"kiyi hakuri kawata Zan dawo jibi.
Nan suka rabu suna dagawa juna hannu.
Ita Kuma ta koma kan gadonta Dab'as ta Dora hannu aka
tana tambayar kanta"waima wa na Aura?!!wanene Alh Hamza!!?
To muje zuwa
Fans mujira ta samo amsar nan
😅
*YAR GWAL*
( ~me kayan Dadi~)
_the sugar daddy story_
Na _Nabilancy love_
💘
*Auntyn S and S*
______________________________
🌈🇰
AINUWA
🇼
RITER'S✍
🏼
*
🇦
SSOCIATION
🤝🏻
*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
______________________________
Page 04
Amarya Zubaida na kwance lumui akan katon gadon ta kamar mage ta shiga tunanin Duniya,lallai in har Matan Alhaji hudu sai ta Nuna Masa mugun bacin Rai Dan ta tsani karya,abinda ma yafi ci Mata tuwo a kwarya sai ganin yanda gidan Alhaji ya Bata hau
shi Sam gidan baiyi Mata ba don batai tsammanin fasalin gidansa na kananun mutane bane,a yanda yake fasalta Mata gidansa babba ne kowa part guda,sai gashi abin Bai kayatar da ita ba,don kowacce zataga motsin kowa tunda Katon Falo ne atsakiyar gidan kujeru
sunyi set biyu sai dakunan gadonsu wato bedroom acikin falon wanda cikin kowanne Daki akwai toilet acikinsa.
Bedroom din nata babba ne don duk kayanta ya dauke Amma duk da hakan fa an maida Mata wasu kujerun Gida Dan 3siter Bata samu matsuguni
ba,kayan kicin dinta ma wasu a ckn lokar sif akasakasu,don kicin dayane dasu Kato agidan Wanda Babban Gas ke ciki kowacce Nan take shiga girki,itama da alamar Nan din zata shiga taringayi kenan.
Ranta inyai dubu ya baci don Abinda Bata zata bane,Kuma zata
nunawa Alhaji bacin Ranta saidai in ya mayarta Gida ko ya nema Mata wani gidan.
Sai wajen goman dare ya shigo Mata dakin,duk da tun Tara taji dirin mota da hargowar yara suna Masa oyoyo da masu sannu da zuwa.
Duk sallamar da yake Mata qin amsawa tayi,sa
i da yazo kusa da ita ya zauna adaf da itan Yana fadin"Amarya kinsha qamshi.
Jin tayi Masa funfurus sai ya Kara matsowa jikinta Yana yaye mayafin Yana shafa qunshin hannunta Yana fadin"me yafaru da amaryata ne.?
Ta fashe da kuka,Wanda ya taba zuciyarsa t
ana fadin"Ni me zaka ce min insake yarda dakai Kuma,walh kabani mamaki Alhaji,dama Ashe matanka uku shine kace su biyune,lallai Ashe maza ko Kun manyanta bakwa kame kanku da karya,yanzu dubi gidannan da ka kawo Ni a matse zamu zauna da qunci Ni dasu to wal
h bazan zauna ba,Dole ne ka Nemo min mafita ko Kuma arabu har...."kakkk!!Kash!!!meyasa Zaki Fadi hakan bayan kinsan Ina Miki mugun so my Zuby,haba amaryar Alhajinta tashi matso Miji meye damuwar in magance Miki ita.
Tayi kasa da murya tana
fadin"bazan iya Zama acikin gidan Nan ba,mutane sunyi yawa,bana son hayaniya.
Cikin rage murya da iya yaudara yace"Ayya ai na Dan lokacine baby, ai ginin da nake Miki kalar kine da zarar angama Zaki koma,gidane gari guda me kyau da kyan fasali zankaiki Na
n gaba kadan kigano,Ina sane na kawo ki Nan saboda wani nufina agaba Zaki sani, Kuma zancen matana uku ba Haka bane,su biyu ne jal,dayar matar dan'uwana ne komai dai tare sukeyi da matana har Kaya iri daya inayi musu Dan baya gari zamanta acikin gidan Nan
ma na Dan lokaci ne,kiyi hakuri karki tada jijiyoyin wuya Akan wannan kinji my baby.
Ta saki Ranta tace"to naji Amma walh bazan dauki wulakanci da sa Ido agun matanka ba abinda Raina yakeso shi zanyi tun wuri ma ka gaya musu su dauke idonsu akaina,sannan
bazan iya yin girkin mutane dayawa acikin gidan ba Dan ba jaka bace Ni,banzo danyin wahala ba ato.
Yahau gyada ka Yana fadin"naji!naji!Amma kiyi komai Dan Ni tawan,kitaimaka ki kyautata sbd a yabeki kinji sbd Naga kina da kyan Hali.
Nan yaita yabonta da
yaudareta cikin salon iya kalaminsa har ta saki jiki ta bada Kai bori ya hau,gashi Alhajin nata hariji kafin safe yayi sex sau biyar Dan ma yasameta cikakkiyar budurwa gashi Ni'imarta tayi Masa itanma ta gamsar dashi ta daurewa jarabarsa ta bashi hadin Kai
ackn sauki.
Da safe Bata iya tabuka komai ba dakyar ma ta iya yin Kari ankawo Mata bread da kwai soyayye da shayi a flask.
Su kuwa matan suna tare a falon suna karyawa da dumamen tuwo sai yara da sukasha Koko da kosai,itama sunso tura Mata Koko da kosan
ya Nuna musu bacin Ransa tare da Yi musu kashedin Kar asake abata wannan cimar ita ta dabance.
Yana barin gurin Aunty Amarya tace"ahayye zanso Inga karshen film dinnan don Dole za,Azo gurin ai,abinda mukecin baya Mana illa a aciki itama Dole taci Nan gab
a.
Murmushi Hajiya Babba tayi tace"ke Kam Amarya akwai Keta walh,gaki da rashin hakuri kardai ki tanka Masa walh ba raga Miki zaiyi ba kinsan dai dukansa Ba ji ba gani ki kiyaye.
Maman yara tace"ai Amarya taqamarta akullum