Showing 27001 words to 30000 words out of 34383 words

Chapter 10 - YAR GWAL COMPLETE

yasa ya kasheta Dif.

Yabar gdn Zubaida Rai abace ya nufi kasuwa Kuma sai ga Kiran Hajiya babba tana kuka tana sheda masa cewar Ankirata ana sanarta cewar Mahmud ya rasu.

Ce mata yayi to ai

yasani,taje ya bata izini tagano kawai.....

To fans muyi jiran wannan Abu Muji shin mahamud mutuwa yayi ko shine matuqin motar da akace Bai mutun ba,tabbas zamuso masa mutuwar ma

😁

*YAR GWAL*

( ~me kayan Dadi~)

_the sugar daddy story_

Na _Nabila

ncy love_

šŸ’˜

*Auntyn S and S*

______________________________

šŸŒˆšŸ‡°

AINUWA

šŸ‡¼

RITER'Sāœ

šŸ¼

*

šŸ‡¦

SSOCIATION

šŸ¤šŸ»

*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

_

_____________________________

Page 15

Kuka sosai Hajiya babba taringayi ganin Alhaji ya nuna mata rashin kulawa Akan lamarin,tasan shi dayake Namiji shi ya cancanci yaje ya Gano mata halin da mahmud ke ciki.

Taringa Adduar Allah yasa bashine ya mutuba

tanason taganshi don ya Nemi yafiyarta data Alhajin na abubuwan da yayi.

Dolenta ta shiryi tafiya Asibitin da aka gaya matan,Amma sai tasa Mansur agaba don su Tafi tare.

Mansur din ma yaji ba Dadi aransa don ko Banza Mahmud Dan,uwansa ne bazai

kyamaceshi ba tunda mahaifa Daya suka fito,Amma fa ya fita aransa yaji kishin abinda yaiwa mahaifinsu,dayaji cewar ma ba Uba Daya suke ba sai yaji dadin hakan,Amma don farin cikin mahaifiyarsa yasa Bai nuna wani abun ba ya dauketa suka nufi Asibitin.

Sunj

e bangaren Yan Accident sun duba Babu Mahmud aciki sai Wanda akace yarage yana can Rai kwakwai mutu kwakai suke tsammanin ko Mahmud dinne Akai musu jagora zuwa dakin da yake.

Awani Hali suka tararshi Mahmud din,fuskar ta kumbure da Baki kamanni sun sauya

ga idanunsa awarwaje ga ciwuka a jikinsa kafarsa ta dama ma ta karye bass!

Inka ganshi saika tausaya masa.

Yana ganin hajiyarsa da Mansur ya Kara rikicewa yana kuka yana cewa su yafe masa kar ya mutu da tarin zunubansu aka,Dan yasan sunji abinda ya aikat

awa Alhajin kunyar hakance tasa ya gudu.

Hajiya ta rufe masa Baki tana fadin"na yafe maka Mahmud,Allah ya baka lafiya ka Nemi yafiyar Alhajin.

Mansur yace"nima na yafe maka Allah yabaka lfy.

Ya tausaya masa ahalin dayake ciki kam.

Dayake lamarin na Aja

line ko kwana guda Bai Kara ba adaren dagashi sai Hajiya tana rike da hannunsa tana bashi labarin tarihinsa da yanda Alhajin yai masa Rikon gaskiya yana hawaye yanajin tarin nadama Ashe shi ba jinin gidan bane ba ma,lallai baikyautu abinda yaiwa Alhaji Ham

za ba,yayi sake da damarsa kam,yaci amanarsa ta kowanne bangaren,inama zai dawo kamar da Da ya Nemi yafiyarsu ya sauya Hali.

Yaita kuka tana bashi hakuri tana masa fatan zai warke.

Adaren a hannunta ya rasu Tasha kuka kuwa Dan bata zaci Mahmud zai mutu a

wannan Lokaci ba ganin yana maganarsa radau.

To Amma lamarin na Ubangiji ne,kwana ya kare.

Ahakan suka taho da gawarsa kano,dama sun Riga sun farfada awaya cewar mamhud fa yarasu ,Alhaji yai namijin kokari na danne abin aransa ya sanar a masallacin unguw

ar ko kasuwa Bai fita ba da safen kofar gidansa cike da Mutane ana jiran isowar gawar Mahmud Dan asallaceshi akaishi,ko kuka dai baiyiba Amma Mutane basu Gano ko me akwai ba,suna ta masa Ta,aziyya yana amsawa Ckn Damuwa.

Maman yara ma taji mutuwar haka Au

nty Amarya,cikin gidan Suma matane cike dam anata koke koke Yan unguwa haka da isowar gawar ma kowa ya Kara tsorata da lamarin.

Da aka gaskata,kowa tausan Hajiya babba yake,sbd sun san yanda take kaunar Mahmud.

Har Suma tayi da za,a tafi dashi

makabarta.

Maman yara ke rarrashjnta tana bata Baki.

Da labarin yajewa Zubaida ta tsorata matuqa ainun,ta Kara saduda da saddaqar da wannan rayuwa jikinta yai sanyi matuga gaya,Ashe Mahmud ba me dogon kwana bane,lallai kana taka ne Allah na nashi,taji ma

tuqar takaicin rayuwar da tayi dashi na fasiqanci da har ta biye masa sukaci amanar Alhaji,gashi shi yatafi gidan gaskiya Wanda ba,a dawowa,ita tana Nan da tarin zunubi akanta.

Tana ta neman mafita na yanda zata Nemi yafiyar Alhaji gashi tana bukatar saki

agareshi shikuma yace bazai sake ta ba haka zalika tana son ace ta Nemi yafiyarsa Amma ta wacce hanya? Ta gama zama dashi na Aure saidai tasan bazata iya fitowa fili tace masa tayi Rayuwar Ashsha!da Mahmud ba Dan ya yafe matan.

Allah Mai ikonsa ackn sati

n Kuma mahaifiyarta ta kwanta gajerar jinya ankwantarta a Asibiti Zubaida nata jigila akanta ta kashe kudi Amma Ashe jinyar bata tashi bace Inna ta rasu ta barsu da maraici sun zamo ba uwa ba Uba.

Zubaida ta koka sosai tsananin tausayin uwani takeyi yazam

o yanzu itace gatan uwanin.

Kawunsu yaita rausarsu yana basu hkr na su jure haka Allah ya kaddararta musu.

Ranar sadakar ukun inna saiga Alhaji yazo mata gaisuwa yaji labari.

Sun gaisa a sanyaye ta gaidashi,ya amsa cikin Yan mintina da zuwansa yakawo ku

di ya bata na sadaka ta karba tana Kara gode masa.

Abin mamaki Kuma yace mata zai Aiko mata da takardar sakin inhar har yanzun tana Nan kan bakanta na rabuwa dashi.

Ganin har ranta da gasken take yasa yaji gara ya bata takardar suyi rabuwar Arziki

Shi a

zatonsa tunda mahaifiyarta ta rasu ko zata rusuna ta bar maganar rabuwar.

Dan haka saki Daya ya iya rubuto mata sbd harga Allah yana sonta tijarar ta kawai yake Hange da yanda take nuna masa rashin kauna yanzun.

A ranar sadakar bakwai tana daga

cikin gida wajen gefin magriba akace ana sallama da ita

Tasan dai Alhaji sun rufe Babi ita da shi tunda ya Aiko mata da takardar saki,ta fita tana kokonton ko waye yazo mata haka.

Tasha mamakin ganin Haidar a kofar gidan a jikin motarsa.

Wani farin ciki ne ya mamayeta da annashuwa ta karasa gunsa

Tana sakin murmushi tana masa Sannu da zuwa

Ya gyara tsaiwa yana amsawa.

Yace"Ashe inna sa,i yayi?to Allah yajikanta da Rahama.

Tace"walh fa, Amin Ina godiya.

Yace"bana gari ne,Ashe har yau

bakwai

Tace"Eh walh Ina kaje ne,naso na Nemi nambarka Ckn abokanka ai.

Yace"nayi tafiya zuwa Dubai megidana ya Aikeni,sai daren jiya nadawo Kuma Ina dawowa naji labari,ya me gidan naki?

Tace"ai munrabu tuni yanzu kam banida Aure dashi Allah yahada Kum

a yaraba.

Ya zaro Ido"garin Yaya?haba Zubaida nasan kin sami mijin kere sa,a meyesa bazaki iya jurewa ba haba Zubaida ita rayuwa ai Yar hkr ce yakamata kiyi hkr ki koma indai da Dama.

Tace masa"Babu damar ai,Dan har kwaso kayana ma nayi fa,kawai na hkr d

ashi bazan iya da Auren saba,Dan tijarane ba na wasaba gashi yana neman mata ga yakaini cikin kishiyoyi manyan mata gaskiya bazan iyawa Auren sa ba,dama kaddarata kenan.

Dariya yai yace"na fuskanci dai akwai tsagoran kishi dayake tattare Dake,to

Allah ya zaba mk Mafi Alkairi.

Batasan lokacin da tace masa"Amin kamar kai dai.

Yace"har yanzun Ina sonki Zubaida Amma Ina Jin shakku araina akanki,don abaya kin daina so na,yanzun kuwa ko kindawo kince kina Sona na San ba gaske bane.

Ta zaro Ido " kam

ar yaya! Haba Haidar munyi soyayya abaya wacce Ba zata misaltuba,kawai sharrin shaidan ne da rabon sai naje na Auri Alhaji yasa muka rabun,Amma walh har yanzu da sonka araina Haidar.

Ya qura mata idanu yana fadin"serious? Zubaida are you sure?!

Ta gyada

Kai

Yace"inama abaya na samu wannan damar,bansan kin rabu da mijin ki ba da tuni na dawo gareki,gashi Lokaci ya qure min Antsaida Ranar Aure na da wata cousin sister Dina a Kaduna take saura wata uku bikin,Asalima ita yarinyar ke Sona nikam zan Auretane k

awai sbd iyaye na so.

Ta hade Rai ta daina fara'ar tana matsa yatsun hannunta takaici fal cikinta na Jin bazata sami Haidar ba.

Ganin kamar ta canza da damuwa kan fuskarta sai ya gyara tsaiwa yana fadin"Zubaida ke ba karamar yarinya bace da za,ace bazaki

fahimci rayuwa ba,ayanzun ke abar tausayice sbd maraicin Dake kanki,da ace zaki hakura ki ajiye komai aranki ki nunamin kauna kamar yanda nake kaunarki da sai in Hadaku duka in Aura tunda Allah ya horemin arziki daidai gwargwado.

Wani Hasken annuri ne ya

mamaye mata arai tayi saurin sakin fuskarta tace"Na Amince Haidar,walh inhar iyayenka zasu bari kayi hakan,to ashirye nake da na zauna da kishiya inhar bazaka nunan banbanci ba tunda ita yar'uwar ka ce.

Ya jinjina Kai yace"Ai Zubaida saidai ita taga banb

ancin tunda kece first love Dina,ita ke Sona ni Kuma ke zcy ta ke so,tabbas inhar kin aminta zansan ta hanyar da zan biyowa iyayena don su yarda in Aureki.

Tayi saurin gyada Kai tana furta ta aminta.

Gani tayi ai dama ce Allah yabata,ya Kuma kawo mata ag

aji Akan Haidar din,don dama burinta kenan agaba ta mallakeshi ko ta halin ka'ka ne.

Kafin yatafi ya bata kudi rafar Yan dubu na dubu ashirin kana yace mata zai dawo Nan da kwana uku,Akan maganar yanda aka yanke zataji.

Sukai sallama suna mararin

juna tabbas soyayya bala'i ce don tsagwaron so Haidar na Mata Kuma ta aminta cewar shine me son ta da gaskiya Gashi itama ayanzun son ya dawo mata sabo.

Dama tasan son kudi ne ya rufe mata Ido har ta gujeshi ta zabi Alhaji Wanda Auren ma ta kirashi da Aur

en kaddara, Auren Nadama,ta karu dai da shagon data bude da Kuma Yar motar hawanta Amma kam son gaskiya tagano Aliyu Haidar takewa.

Kwana da wuni take tunanin Haidar gashi basui canjin nambar ba Amma tana qirgen kwanakin da yace zai dawo saboda so take ta

ji inda aka kwana ita dashi.

Gabanta kan fadi in ta tuno cewar akwai wacce aka bashi qila ma suqi yarda da itan,tunda acan baya ita taqishi.

Ta shiryi damarar Auren Aliyu ko ta wane haline,zata Kuma Kara da kowacce mace akansa,bata da d'ar aranta ko shak

ku na zama da wata mace a turba Daya,bare tana da tabbacin Haidar na son ta.

Kawun su na kawo kafa gidan Dan dubasu,yaso ma su koma gidansa da zama ita da uwanin to Amma sai ta nuna masa gara su zauna anan su biyun idan Aure yazo mata sai uwanin ta koma g

abansa.

To ganin yanda ta kame kanta bata yin rashin ji ma,ana ta ringa yawo ko shigar Banza yasa kawun ya barta suke zaune su biyu agidan.

Tana kula da kanwarta uwani bata zuwa koina sbd ita,gara ma in zataje boutique dinta takan dauki uwanin su Tafi ta

re,shagon Kuma yana Kara samun Ciniki Allah yasaka nasibi Akai.

Yaran data dora masu Amana ne suna kokari sosai wajen kula mata da dukiyarta,ranar lissafi kawai take zuwa.

Aranar da Aliyu yace mata zai dawo ta tanadeshi don har girki tayi masa kala biyu

dasu snacks harda fruit salad

Gashi ta tashi da wani farin ciki da Annashuwa tasan alamune wannan na samun Nasara

Fatan ta Allah yasa Aliyun dai yazo mata da batu Mai kyau Akan Aurensu.

Inko iyayansa suka Hana sun cuceta Dan yanzun zuciyarta naga Aliyu

kaunarsa take sosai,a yanzun me rabasu ai sai Allah.

*YAR GWAL*

( ~me kayan Dadi~)

_the sugar daddy story_

Na _Nabilancy love_

šŸ’˜

*Auntyn S and S*

______________________________

šŸŒˆšŸ‡°

AINUWA

šŸ‡¼

RITER'Sāœ

šŸ¼

*

šŸ‡¦

SSOCIATION

šŸ¤šŸ»

*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

______________________________

Page 16

A can bangaren Amarya zuby kuwa ta rike angonta da

kanaynaya taringa kissa tana nuna masa so.

Nunawa take zatai kewarsa idan yatafi dakin Zulaihat tabbas dakyar inzata iya baccin kirki.

Ya janyota jikinsa yana fadin"kiyi hakuri my Hubby kinsan tunda da ita aka fara daura Auren kafin ke dole itace amatsay

in uwar gida,gara nabi komai Ckn tsari kar ashiga hakkinta,banason kisa damuwar Nan aranki.

Tace"nasani Amma bakin cikina,kar ka fara dandanar Dadinta kaki dokin nawa dadin.

Ya shafo habarta yana fadin"my first love ke ai nasan ta musamman ce,nayi amanna

Babu wata 'ya da zata shigo gabana tafiki akomai,na yarda Dake kinfita zakka a Ckn mata.

Taji ddin wannan yabo matuqa ta lumshe Ido ta budesu ahankali akansa tana fadin"nagode mijina.

Bai bar dakinba sai da yaciyar da ita Naman kazar da yashigar

mata dashi Tasha fresh milk din ta qoshi kana ya tafi.

Dakyar suka rabu har kofar daki ta rakoshi tana masa bye bye kamar Wanda zaiyi doguwar tafiya zuwa wani garin.

Auren bazawara da Auren budurwa akwai banbanci tabbas.

Zuby dayake ta taba Aure shiyasa

baiga laifinta Akan wani Abu datayi ba.

Na ajiye kunyar daren farko ta dire gyalen kan nata kana ta ringa nuna masa kaunar tsararo da rakiyar datai masa

Idan Zulaihat tai hakan sai an DiGa mata ayar tambaya.

Dakyar ta iya rintsawa Dan tsabar kishi Gani

take yana can yana baiwa Zulaihat dadin soyayya ita na Nan kwance gaho.

Da ace ita aka fara daurawa Aure dashi da sunanan atare Akan gadon.

Ta shafa kan makeken gadon nata na uban kudade dayawa Dan sabo ta sake ba na gdn Alhaji bane.

Tayi juyi bari gud

a tana qanqame da filo bisa kirjinta tana tuno fuskar mijinta

Mahaifiyarsa ita tayi dolen sai an fara daura Aurensa da Zulaihat inhar zasu yarda a Daura Auren zuby inba haka ba saidai afara kam,bazai yiwu ace ga duka ga tsinka jaka ba,a hakan ba,a son ra

nsa ba ya hkr Akai hakan

To ita anata bangaren Zulaihat zcyrta Babu komai sai kaunar mijinta Amma tana da kishi nunawa ne Dai Bata isa tayi ba sbd gudun bacin ransa.

Kwana biyun dayai mata kuwa Bai kusanceta ba ya Saka aransa sai yafara dandanar Ni,imar

zuby tunda sukai masa dolen Auren Zulaihat din a farko Shima zai fara Jin zuby a farko a wannan fannin.

Hakan kuwa dayai ba karamin gigita yayi ba Daya dawo dakin zubyn Dan ta tanadeshi sosai

Ta fannin sex rikitashi tayi sbd tayi gyaran can din

Magunguna nasha Dana tsarki na matsi Dana karin Ni,I'ma da saukar da ruwa lutsu lutsu ba,a magana fa.

Ga iya salo salon kwanciyar data nuna masa kwarewarta.

Wani abun dama shi bako ne a wannan fannin.

Amma fa ya Gane cewar zaiji dadinsa anan

Zai more

rayuwarsa zai Sha Nishadi

Kafin safiya yayi sau uku Kuma kowanne Ckn Nishadi da gamsuwa.

Tabbas yasha sambatu yana kiranta da me kayan Dadi.

Takanji dadin Kalmar Nan sosai sbd DUK macen da batada Dadi to sorrynta,Dadi shine mace don namiji na son yaji

Dadi ajikin matarsa takan fita daban ackn mata.

Da safe ma hada magungunanta tayi na Mata ta cika Kofi ta shanye don tana son adaren yau yakara sanin akwai banbanci

Gashi ta wuni Shan fruit salad hadin murtuka yasha Madara da dandanon Zuma.

Da dare kuwa

ta sallo wanka ta feshe jikinta da turarika 'yn ubansu,duk inda tayi kamsasawa take.

Gashi bangaren nata ya dau kamshin turaren wuta.

Bandakinta kuwa kamshin Air freshener yake yasha wanki tiles na kyalli

Acan kan dinning table kuwa ta cikashi da cima

danginsu mietpie da dambun kaza da cake sai drinks kala biyu datai har da kunun Aya.

Yaji matuqar dadin wannan kulawa da take nuna masa.

Tun anan yafara ganin banbancin inda zai ringa Jin dadinsa da walwala..

Daya dawo gida ya fara shiga sashin

mara girki Zulaihat

Ta tarbeshi da sannu da zuwa da gaisuwa

Dayake yashigo mata da leda ahannunsa nama ne da malt ta gwangwani ya mika mata nata.

Ta karba a durqushe tana godiya.

Daya fita ya nufi bangaren madam dinsa

Tun daga kasan benen babban falon

kenan da zaka hau bene kamshin turaren data hada ya sauko yana dukan hancin majiyinsa

Yana shiga dakin nata ta taso aguje ta tarbeshi da runguma tana manna masa kiss na welcoming

Sararo ya tsaya yana kallonta taci kananan kaya Riga da wando sun dameta k

oina na jikinta amatse dama ga kirjin acike.

Ta karbi ledar hannunsa taja hannunsa sukai gaba zuwa kan kujera ta zaunarshi.

Takai ledar kan dining

Kana ta dawo gareshi Ckn karairaya ta rage masa kayan jikinsa tana fadin"muje in fara maka wanka sai ka

dawo kan dinning.

Ta hada ruwan wankan ackn kwami da turarika na kamsasa ruwa wani gishirin wanka na kamshi kadai data zuba cikin ruwan ya wadatar ace inkai wankan ba saika fesa turare ajikin ka ba Dan kamshinsa da zaunawa ajiki Amma sai da ta kawo wani t

uraren na ruwa me masifar kamshi ta zuba.

Shi dai Haidar yana ganin abubuwa agun Zuby na burgewa tabbas dole Duk Wanda yake tare da ita ya sota,ga kyautatawa ga kyau ga iya girki ga iya kwanciyar Aure ga mu,amala ga Rikon miji ga dadin dandanon da

take dashi,ta wajen biyayya ma ta iya hadata da kissa

Tai masa wanka ta salloshi kana suka dawo daki ta zaba masa wata sabuwar jallabiya me gajeran hannu ta bashi yasaka suka dawo kan dining Nan ma ciyarshi tayi komai na gun bata barshi ya wahalar da kans

a wajen ci da kansaba.

Haidar yace mata ta shiryi zuwa gaida mahaifiyarsa gobe zai kaisu ita da Zulaihat can gidan nasu.

Gabanta sai da yafadi don tana gudun taje taga an nuna mata banbanci fa.

Ta amsa masa da To kawai ba yanda ta iya tunda iyaye iyayen

e intaqi bazai ji Dadi ba ko yai mata fassara ta wani abun, da sai ta zille masa zuwan.

Washe garin Daya fita a dakinta ne Daya dawo da yamma ya daukesu takaisu gidansu.

Dayake mahaifiyar tashi tana da kishiya agun kishiyar tata kawai taga fuska

Amma m

aman Haidar bata sakarwa zuby fuska ba

Data gaidata dai agaban Haidar ta Amma fuska asake

Amma Daya fita zuwa waje sai take ta Jan Zulaihat da hira

Sukai ta hirarsu Banda zubyn wacce tai shiru a gefe guda.

Da suka fito tsakar gida yin Alwalar magriba

.

Zubyn na yin Alwalar ta shige dakin inna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login