Showing 33001 words to 34383 words out of 34383 words
tana rantse rantse Wanda ita kanta mama DUK yanda take sonta da goya mata baya tag
a bakinta ayau.
Har fada tahauyi"rufa mana Baki Munafuka ai kinbani mamaki tunda bakya kaunar jinin Dan,uwanki ai shine bakya kauna,yaran me Suka tsare miki da har kikai kokarin wannan kisan Kai,ko ma ince kikai to
walh daga yau na cire hannu akanki ba r
uwana ko me zai wakana bazan sa Baki ba,gaki Kuma ga hukuma Dan kisan Kai dai kinsan hukuncinsa.
Zulaihat ta fashe da kuka Kuma Bata risina ba rantsuwar take Akan ba ita bace.
DUK yanda aka taru akanta bata tsorata ba har Alqur'ani baba yace zai bata ta
rantse tace ta yarda.
Karshe Haidar Yan sanda yakira yace atuhumeta da tsawatarwa sannan suyi mata hukunci shikam bazai bari ba inma da Saka hannun wasu akamosu.
Karshen wannan tirka tirka dai me Aikin Nan tasuce wato Mero ta fito ta fallasata Ashe taga
lokacin datake basu madarar ai kuwa Babu tsoro atare da Mero ta fito ta fesa tana amannar ita abata Alqur,anin zata rantse Akan lallai Zulaihat ce ta nemi kashe yaran da hannunta ta basu Madara Kuma taga lokacin datake zuba wani Abu daga kwalba cikin madar
ar.
Nan fa idon Zulaihat ya raina fata ta kasa cewa komai ta fara kuka tana neman yafiya wai tsautsayine.
Ai kuwa hankalin kowa ya dugunzuma Akan lamarin Kuma suka tsame hannunsu Akan ayi mata DUK hukuncin Daya dace Babu ruwansu.
Zuby Tasha kuka tana na
damar yadda da ita da tayi gashi har taci amanarta ta cutar da ita
Daga wannan Karan dai bazata Kara yarda da wani bawa ba har haka Azo acutar da ita,lallai Zulaihat tayi kyan Dan maciji agunta wato Ashe ba kaunarsu dama take yi Dan Allah ba akwai wata m
anufa aranta knn,gashi tagani tacita da yaki ta kashe mata Usaina abar sonta Wanda Banda Shima Hassan yanada tsawon kwana agaba da shikenan ta mata qurunqus ta rabata dasu duka, tabbas bazata taba yafe mata ba.
Haka kowa yanaji yana Gani aka tisa keyarta
Akai gaba da ita zuwa station ko ajikin Haidar bare Mama data ga ai hakanne ma daidai.
Ko da iyayanta sukaji Suma sunyi Ala wadai da halinta da Kuma tir da abinda ta aikata.
Kwananta uku a station aka tisata gidan yari.
Sai da tayi wata uku acan
cikin nadama da Dana Sani marar amfani Ashe tana da karamin ciki taita laulayi tana rashin lfy.
Alokacin kuma haidar dayaji yaje ya dubata tunda da Aurensu ba sakinta yai ba.
Yaji tausanta DUK ta rame ta canza kamar ba itaba.
Har kasa ta Durqusa neman y
afiya tana kuka tana ta tuba yataimaka ya fitarta anan ko Dan yaron cikinta ya tsira karta haifeshi ack. Wannan Kangin rayuwar da take ciki.
Tausayinta yasa yace mata to taci gaba da istigfari tana neman yafiyar Allah Amma shikam ya yafe mata.
Tace"nayi
nadamar bin rudin zcy da bin shawarar kawa Ruky ta cuceni Dan Allah kace Aunty Zubaida ta yafemin na tuba nabi Allah walh DUK randa na fito zan bita sau da kafa zan canza halayena daga munana zuwa kyawawa.
Ya bita da Ido yana gaskatata baice mata uffan ba
yace zai tafi Amma zai dawo kwana kusa,dama ba zuwa yake ba sai wannan Karan dayaji bata da lfy,Dan iyayanta na zuwar mata DUK wata agunsu mama taji ta sanar masan.
Dayazowa Zubaida da zancen sai ta taushi zcyrta tace ita kam ta yafe mata,yayi kokari ya
fito da ita tunda yana da dama kudi kawai zai cusa musu akashe case din.
Hakan Kuwa akai ya shiga ya fita saida yaga ya kashe bakin tsanyar ya fito da ita Amma da izinin mama Dan itama tace ya fito da itan sbd albarkacin iyayanta Amma kam sun raba gari ko
ta fito din.Ba ita ba sake shiga sabgar ta.
Data shaqi iskar 'yanci kuwa hamdala tayi me tattare da tarin nadama da burin canza Hali zuwa gyararre.
Kai tsaye gidan mama yakaita ahanya taita bashi hkr tana neman yfyrs yace ta wuce.
Mama ma ta nuna mata
ta wuce Amma inhar ta sake kwatanta hakan to kisane ta hanyar rataya Kai sbd Rai Rai ne bawai Dan yara bane za.a barta tasani tana son jikokinta fa.
To tun daga Nan dai Hali ya canzu ga Zulaihat don rabuwa ma tayi da Ruky Kuma wani gidan Yakama yasakata k
afin yaga yanda zaman nata zai yi inta canza sai yasai karamin gida yasata Dan Wanda yakaita ma kwatane Yakama haya Nan nashi dai yafi karfinta don zuby tace ba ita ba ita,bata ma kaunar sake ganin ta.
Kuma itama kunyar idonta yasa bazata iya zuwa
neman yafiyar ta ba saidai Aike.
Ahakan dai tana lallabashi tana nuna ta shiryu har cikinta ya isa haihuwa yakaita garinsu kamar yanda ta nema Dan ta haihu acan tunda anan tazama mujiya Babu me yin ta Tata.
Alokacin kuma Zuby ta yaye Hassan Dan cikine da
ita yakusa isa haihu ma dole aka yaye shi Dan yasha ciki ma.
Zulaihat ta haihu tahaifi 'ya mace saidai ba lfy ta kwanta jinya Dan batasan suwaye akantaba
Har Ana gobe suna da jikinta ya rikice Kuma batasan inda kanta yakeba Aka kira mata Haidar Dan nema
n magana dashi da take Kuma cikon Allah abin Bai yiwuba Dan kafin ma yazo garin Kaduna har Rai yai halinsa Zulaihat ta rasu tabar baby.
Daya karaso yaji ba Dadi aransa ahannunsa yarike babyn yana zubda hawaye na tausayinta zata taso Ckn maraici Kuma dole
rikonta ahannun zuby zai taso shiyasa akeso akoyaushe ka Aikata khairan Dan bakasan gawar fari ba.
Yan kano sunaji akayo ayari zuwa gidan gaisuwa har Zubaida ta biyosu hankali atashe.
DUK da tana kan gaba cikinta ya isa haihuwa yau ko gobe Amma tabiyo su
inna.
Sunji abin har cikin Ransu Kuma sun tausayawa jaririya,Tun aranar ahannun Zubaida ta wuni babyn, tana me tausaya mata Kuma Tasha Alwashin rikonta bisa gaskiya da Amana sbd dole ne tazamo me son DUK wani jinin Haidar bare jinin yarantace babyn, baza
ta taba duba abinda mahaifiyarta tayi mata ba ta ajiye komai agefe ta Kuma yafe mata.
Tabbas hakan akeson DUK wani mumini yayi,Kuma wannan koyi ne da halin ma,Aikin Allah Ubangiji ya jikan Zulaihat dai.
Sai da Akai sadakar uku suka dawo kano Kuma sun tah
o da babyn Wanda aka fara da bata Madara
Tausayinta suke ji sosai gata kamarta futuk da margayyar.
Haidar yanajin dadin yanda Zubaida ke ririta babyn Kuma da suna yazagayo aka rada mata sunan Zulaihat ake ce mata Little ko baby.
Ana radin suna da kwana
biyu saiga Nakuda ganga gangan taxowa zuby Kuma cikin iKon Allah ba daukar Lokaci ta haihu ma agida wata nurse dai tazo kanta a arear tasu take ta haifi mace kyakykyawa da ita.
Ai fa sai tazamo me twins dayake tayi biyun abaya sai abin Bai bata
wahala ba ga Kuma Yar Aiki na tayata renonsu ta hadesu tana basu nono baby ma ta kama nono Tasha aranar.
Ita dai zuby hankalinta kwance yake da mijinta ga Iyayan mijinta yanzun sun karkato da kaunarsu kanta baya ma inna datake nuna mata so agaban kowa ga
Rikon little datake Ckn so da kulawa yasa maman tana nuna mata so itama.
Ba Taron suna Akai ba sai Yan uwa da suka zozzo tayata murna.
Alokacin ma sai ga uwani ta haihu namiji bayan sunan Zubaida Wanda ita Zubaida sunan innarta aka Saka aka cewa babyn mo
mee,ita Kuma uwani sunan mahaifinsu akasaka mata.
To hankalin Zubaida dai akwance yake ta koina ga mijinta na sonta,ga dangin miji na kaunarta ga yaranta sun taso gwanin sha.awa Business dinta na samun cigaba yana habbaka Allah yasaka Albarka,ga rufin asiri da take ciki mijinta Arziki na k'aruwa
Tana zu
munci dasu Hajiya babba dasu maman yara da Aunty Amarya Dan har suna sunzo mata Abin nasu kamar Yan uwa dai.
Ita har bata son ta tuno rayuwar da tayi abaya da Mahmud takan roki Allah akullum Akan ya yafe mata.
To Allah ya yafe mana Baki Daya,TAMMAT BI HA
MDALLAH anan mukazo karshen labarin YAR GWAL me kayan Dadi Allah ya sake hadamu ackn Wani sabon da zai Fi wannan Dadi da fadakarwa Amin.