Showing 9001 words to 12000 words out of 65624 words
tace
"hakanefa ai bazan taba barin hakan tafaruba, to yanzu kibari inta tafi kibi bayanta kiyi hayan kartan maza kuje dasu ku
kwashe kayansu tas ku cillasu titi, susan inda dare yamusu, "
"kai haka za aiyi kawata nagode sosae," da haka sukayi sallama farin ciki fal Hajiya fty,
**Nisha
tun safe haryanzu yamma lis amma sam babu alamar zaidawo, ga tunanin umma wani hali take ciki
, gawani hadari da ya lullube garin har ansuma yayyafi, dan haka ta tashi tafita, daga window mami tabi bayan Nisha da kallo tana dariya, mtswww yan wahala zaku gaji kubari, to atakaice dai wannan ciyo da yamatsan tawa umma da rashin ganin mijinta shiya ka
ita ga kwanciya asibiti har Allah yakarbi rayuwarta, wannan kenan
Cigaban labarin, seda tayi kukan ya isheta sannan ta mike ta wanko fiskarta, fitowa parlourn tayi itama nanma ba kowa parlourn kallon parlourn take gwanin shaawa, jin motsi cikin parlourn y
asa tajuya inda taji motsin, wata matace dagani tadan manyanta tafito daga kitchen hanunta dauke da filet din abinci tana jeresu a dining table ganin Nisha yasa matan tasaki murmushi tareda karisowa inda Nisha ke tsaye, tana fadin," yade yata akwai abunda
kikesone,? cikin tsoro Nisha tace," am ., banga kowa a parlourn bane, ko su fadeela kike nema,? cikin hanzari Nisha tace,"eh , suna part din Hajiya muje innuna miki inda suke, har bangaran Hajiyar ta rakata tabude mata kofar sannan tajuya, shiga Nisha tay
i hade da sallama, fadeela ne ta taso tana fadin," lah mundauka bacci zakiyi da kikayi wankan shiyasa muka fito muka baki guri kihuta, cikin wani irin murmushi nisha tace," nakwanta baccinne baizoba, murmushi Hajiya tayi tana adin," matsunan kizauna kusa d
ani yaranne se ahankali suntafi sunbarki kikade
murmushi nisha tayi tareda da matsawa inda Hajiya tamata nuni, hira suka cigaba da yayi suna janta da tadi amma sam bata wani sake sosae ba, hjy duk tana kula da yanayinta ba karamin tausayin yarinyar tak
eba, yarinyar irin wannan da rashin uwa bawani makusanci kusa da ita, itadae Nisha gaba daya hankalinta ya tattara ga aheel dake kwance yana bacci, kyakykyawa kamar bababsa haka kawai takejin yaron cikin ranta, kiran sallan magarib ne ya dakatar dasu daga
firan dasuke, duk suka mike toilet din hajja mama kowannesu ya nufa yayi alwala, itama tashi tayi tanufi toilet din tayi alwalan koda tafito bataga su fareedan ba, da alamu sun nufi part dinsu sallah, .
hajja mama ce daga gefe kan sallaya tana gabatar da
sallah hakan yabawa Nisha daman matsawa inda taga an ajiye mata lufaya da sallaya, gefe da hajja mama nisha ta shimfida sallayan tashiga gabatar da nata sallan, bayan kammalawar hajja mama tashiga lazimi tana jan jarbi, yayinda idonta kekan Nisha dake gaba
tar da sallah cikeda nitsuwa murmushi Hajiya tayi yayinda tamai hankalinta ga abunda takeyi, bayan idarwa nisha tajima tanayiwa umma addu'a da ftn alkhari da samun rahama ga ubangijinta, tareda mahaifin nata dan shima ako ina yake yana bukatar addu'an ta
gareshi, tana kammalawa tamike tareda ninke sallayan , mike hajja mma tayi daga zaman da take tana fadin,
" bari naje na dubo baba Barka ko ta kammala dinner dan yuwa nakeji sosae gyada mata kai kawai Nisha tayi hakan yabawa hajja mma Daman ficewa, aheel
dake kwance saman capet anmasa matashi da pillow Nisha takurawa ido tana kallonsa, sam bata gajiya da kallonsa, yaro so beautiful wani dan larabawa, gsky family din Allah yabasu kyau masha Allah, murza idonshi yashigayi alamar farkawa daga bisani yabude id
on gaba 2 , ya saukeshi akan Nisha da ta kura masa ido kamar zata hadiyeshi, kallon rashin sani yafara mata, cikin wara ido da tsoro yake fadin,' who.., who are you yafada cikin muryan bacci, Nisha kasa mayarmasa da amsa tayi dan ita kanta ba san mezata ce
masa ba, maryan shi tasakeji yana fadin
"Zansha ruwa "
zamuwa tayi daga kujeran da take tasa hanu ta dauki ruwan dake gefensa tareda cup din tashiga tsiyaya masa ruwan ta mika masa , ganin ya miko mata hanun hagu because dayan hanunsa da matsala hakan
yasa ta tallafo shi tashiga bashi da hanunta , karba yayi yasuma sha seda ta tabbatar ya koshi ta zame cup din daga bakinsa tareda sakar masa marshi, shima washe mata baki yayi yana fadin,
" thanks you" baki Nisha tabude da nufin magana jin shigowar fadee
la ya tahadiye talk dinta, ganin su zaune saman capet sunyi zuru suna kallota hakan yabata daman karisuwa inda suke, murmushi tasakar musu tareda mayar da kallonta,
" my little baby katashine " gyada mata kai yayi yana fadin',
" aunty I'm feeling hungry
,
"okay don't worry zan turo baba Barka tazo tayi feeding dinka kajiko to kawai yace nan tamaida kallonta ga Nisha tareda jan hanunta tana fadin,
" muje muci abinci dama ke nazo kira , sunkuyar dakai nisha tayi tareda cewa,
" bana jin yunwa, cikin han
zari fadeela tace,
" Allah baki isaba taya zakice bakya jin yunwa, dagaske kwata kwata babu yunwa atare dani, kodae bakyason cin abincin damune, mudakefa munriga munzama daya fadeela tafada tareda jan hanun Nisha harsun kai kofa Nisha taja ta tsaya taka
lli dayayi abun tausayi yana binsu da kallo sekuma takalli fadeela tace,
" please to kikawomin nan semu zauna tareda shi kar abarshi shikadai,
" nafahimci kifi bukatan Zama nan , alright bari na turo muku Barka, " tafada tareda juyawa tafita, murmushi ta
bi bayan fadeela dashi, gefe kuma tamaida kallonta ga aheel, kumawa tayi tamatsa kusa dashi tazauna, tana maibinsa da murmushi jin yaron take sosae ajikinta, sekace wanda suka fito ciki daya, Nisha uwar yaya tana mutukar son yara dan koda suke gd faruk ka
nin salma tare suke wuni tana manne dashi darene kawai ke maidashi gdnsu, ita kade Allah yabawa mahaifanta batada yaya ko kani, shiyasa Allah yadaura mata jaraban son yaya, shima aheel din murmushi yaketa zuba mata kamar gonar auduga, yaron akwai fara' a s
osae shiyasa yakeda shiga rai,
ba adadeba Barka tashigo hanunta dauke da tiredin abinci zubawa Nisha tayi afilet tamika mata, tuwone miyan egusi yaji kifi da nama kaca kaca , aheel kuwa irish da akwai aka suya mishi nan baba Barka tazana tana kokarin fee
ding din shi, lah da kimbarshi zan tayaki bashi kije ki huta kema, nisha tafada yayinda take kokarin dakatarda ita, aa yata karki damu bawani hutawan da zanyi aheel mutuminane gwara na sallameshi, daker Nisha ta lallabeta ta tashi tafita, filet din abincin
ta ta ture gefe ta kamo na aheel tasuma bashi, seda ta tabbatar da yaci sosae ya koshi sannan ta kyaleshi ta tsaya tana kallonshi ko abinci takasa ci, kwata kwata abinci baya ranta, muryan aheel taji yana fadin,
" aunty ke bakici abincin nakiba, am. banaj
in yunwane, to aunty kici kokadan because baba Barka ta iya abinci kema nasan zai miki Dadi, gyada masa kai tayi yayinda taja filet din abinci gabanta, nan tafara tsikaran abinci tanaci ba dan tana jin dadinsaba, sam bata ma gane dadinsaba, nan tunanin umm
a yafado mata nanfa hawaye yashiga wanke mata fiska jitake kamar ta fashe da ihu, sunnar da kanta tayi kasa dan kar aheel yagane halinda take ciki, guge hawayen tareda sake kasa da kanta tana cigaba da tsikaran abincin,
," aunty meye sunanki , da guwa ta
yi tana kallon aheel dayayi mata tambayar, murmushi yasakar masa tana fadin
" NEESHA Aunty nisha? yafada yana kallonta gyada masa kai , ina Zaki zauna damu anan koh kuma baza kitafiba tunda mummy na bata sun zama dani kezaki dinga feeling dina kimin wan
ka kishiryani cikin uniform natafi school? yafada yana washe baki, yaron akwai surutu balaifi kallonsa take yaro irin wannan da bai wuce 7 year's ba amma se surutai wani radio, a ido inka ganshi bazakace yana da surutu hakaba, koda yake Aunty's din nasama
ba bayaba wajan magana, karka damu muna tare duk abunda kakeso zan maka kajiko tafada tareda da ture filet din abincin gefe, tareda yiwa aheel matashi da cinyarta, aheel hira tacigaba da yimata kamar dama can yasanta, kodama can aheel na saurin sabo da m
utane, labarin papansa yashiga yimata, irin sonsa da yakeyi da kayan wasan da yake siyo masa , da wajan wasa da yake kaishi,
itadae Nisha kallon yaron take yayinda yaketa zuba makar fanfon da ya lalace, hira yake sekaceba majin yaciba, sam bakinsa bai mu
tuba, jin motsin shigowarsu hajja mma ne yasa
Nisha daguwa suna binsu da kallo yayinda suke karisuwa , fareeda ne takariso wajansu tana fadin,
" yauwa yanata zuba sutun nasa daya saba ko wani labarin yake baki naketa jiyo sautin muryan sa daga waje ,
"l
allai baki yabude sauki yasamu, washewa sukayi da dariya dukansu nanfa hira ya farke aka cigaba da tadi, tadi suke sosae wanda sundau tsawon lokaci suna yinsa , yanzu kam Nisha ta dan sake sosae anyi firan da ita, hajja mma data fahimci hakan ba karamin da
di tajiba, Hajiya bata wani dadi sosae ba wajan hiran ta mike taimusu seda safe domin kuwa bakaramin gajiya tayiba zaman asibiti ga ba bacci mai Dadi, gakuma dawainiyar aheel, sallama sukayi ta tafi tayi kwanciyarta, ba adadeba fareeda ma tamike saka mak
on wayanta dake ringing itama seda safe taimusu ta tafi, sunyi tadi sosai da fadeela sewajan karfe 10:30 lokacin bacci yafara cinye idon fadeela itama mikewa tayi tana fadin,
" Nisha kitashi muje mukwanta wlh bacci nakeji sosae, aheel baiyi bacci ba karmu
tafi mubarshi shikadai, rabu dashi papanshi zezo ya daukeshi ae ,
" aa kije kawai zan biyoki dan nima banajin baccin yanzu zamu danyi hira kadan, murmushi fadeela tayi tana fadin,
"naga kamar zama da aheel yana miki Dadi koh,
"hmm zaki gajima inde yaro
n nane surutain sama kadae ya isheki,
"aa nikam bawani isata dazaiyi, alright se kinshigo to, tafada tareda juyawa tafita, maida kallonta ga aheel tayi da ya tsura mata ido dan bayason ta tafi tabarshi,
"Aunty zanyi fitsari kikaini toilet , taimaka mis
hi tayi takaishi yayi fitsarin, ta dawo dashi tagyara masa kwanciyar tamasa matashi da cinyarta, suka cigaba da hirarsu wajen karfe 11: lokacin sunyi laushi daga shi har Nishan, domin kuwa bacci yafara cinye idon su, tuni aheel yasuma baccinsa nanfa itama
tafara gyan gyadawa,
Motarsace ta kunno kai gdn , jin hon yasa mai gadi yaye geat din gdn, nan ya tako motar ya kariso haraban gdn yayinda yayi parking, mitowa yayi yayi da mai gadi yakarisu da hanzari yana mai kwasan gaisuwa, amsawa yayi tareda tafiya
yakarisa ga part dinsa , nan yatura kofar yashiga back din hanusa yacillar kan kujeran, direct bedroom dinshi yanufa kokarin cire kayan jikinsa yasuma yi seda yacire yarege daga shi se dan short dress daga bisani ya dauke lallausan towel dinsa yanufi toile
t, wanka yashiga yi sosae dan yau ba karamin gajiya yayiba , fitowa yayi jikinsa daure da towel iya gwiwa, kallon inda mai yake bai kalleba because wani kasala yakeji gakuma gajiya gaba daya yagama yin laushi, jallabiyarsa yazura tareda fitowa yanufi kitch
en tareda hadu coffee yasamu gu daga dining yasamu waje yazauna yana sha, seda ya kammala yamike ya koma bedroom domin kwanciya ya hutawa ransa, kashe wutan dakin yayi tareda kwanciya saman bed din hade da janyo blanket yarufu, wayarsace tayi kara hakan ya
bashi daman lalubu phone din dan yaga waye meshirin shiga hakinsa acikin night haka, dago phone din yayi yana kallon screen din wayan , matarsace raheela ke tafaman kiransa komai zatace masa oho, wani tsaki yaja da kamar bai daukaba sekuma ya daga batareda
yace komai ba,
" hey my baby yau nayi dare sosae gashi but ina ta missing dinka gakuma wani accident din da aka kawo yanzu, so bazan samu dawowa ba se zuwa tommorow, baijira takarisa maganar ba yakatse wayar tareda cillata gefe namaijan tsaki,
" stupid
dama yau kika saba kwana hospital koba wani issue zakice akwai meye problem dina da hakan yafada tareda sake lullube jikinsa hade da rufe ido yana maida numfashi slowly, firgit yatashi yazauna se yanzu ya tunada aheel, gaba daya gajiya tasa ya mata dashi,
da sauri yatashi yanufi hanyar waje, bangaran Hajiya yanufa tareda murda handle din kofar yajita abude take yakutsa kai, dauke da sallama, turus yayi yayinda yakarisa shigowa ciki, binsu yayi da kallo duk sunyi bacci Nisha ma baccin barawo yasaceta, kan ah
eel na cinyar ta , itakuwa ta jingina bayanta da jikin kujera, tanata sheka bacci, haunsu cikin najuna, Nisha tareke hanunshi gam, wani abu yaji yatukare masa makoshi , gaba daya haushin yarinyar yagama kamashi , datasan haushita dayakeji bata fara gigin
kusantu dansaba, matsawa yayi ahankali yafara kokarin jan hanun aheel tareda cire hanunsa acikin na Nisha,
cikin bacci Nisha taji aheel na kokarin zare hanunsa hakan yasa takara rike hanun gam , kamar wani zai kwaceshi, gaba daya jiyayi ransa yafara bacc
i gani irin rikon da tayiwa dansa, hunsa yasa akan na Nisha yana yamutsa fiska, daya hanun kuma ana aheel yana kokarin raba han nayensu, jin tarike gam yasa afusace yafincike da karfi wanda yasa aheel mutsawa yana fadin,
" ah. Aunty hanuna yafada cikin n
an nauyan bacci, yacigaba da bacci yana surutai, itakuwa jin aheel ya janya hanunsa yasa tasake jayo hanunsa ta rungume akirji, waro ido yayi yana bin hanusa da takamu takai kirji tanamai cigaba da baccinta, nanfa yafara kokarin jaye hanunsa jin haka yasa
Nisha kokarin bude ido dayan hanunta tasa tana murza idonta, karfa idonta ya sauka akansa dake kokarin kwace hanusa daga nata kyansa ta zubawa ido wanda ta gagara dauke idon akansa, lumshe ido tayi tabude still tana rike da hand dinsa taki sakewa, ,
" he
y madam samu dama kisakarmin hand na dauki dana yafada tareda hade gira, cikin hanzari takalli hand dinshi da tarike Gam sakuma tasake dasauri tana fadin,
" I'm sorry ta fad'i tareda mikewa tsaye , kauda kai yayi tareda daukan aheel yadaurashi saman shoul
der dinsa suka nufi part dinsu, bayansa tabi da kallo jikinta se mazari yake sekace wanda taga wani dodo, cikin hantsari tabi bayanshi ta nufi bangaran su itama, tana shiga ta samu su fareeda duk sunyi nisa da bacci itama samun waje tayi takwanta dan idont
a tuni yamata nauyi,**********
washe gari da asuba suka tashi sukayi sallah su farida suka koma bacci abunsu, qur'an Nisha ta dauka tasuma karatu kasa kasa take gudun karta shiga hakkinsu suna bacci ta dade tana karatu daga bisani ta dakata, addu'a tashi
gayi wa mahaifanta ita kanta sannan tashafa takoma tayi kwanciyar ta,
,sewajan karfe9:40 Nisha tafarka ganin babu kowa ita kade aka bari tanata sharar baccinta hakan yasa ta sakko daga bed din ahankali takarisa sakkowa, itama waje tanufa a parlour ta isk
esu suna zaune, ahankali takarisa inda hajja mma take hadeda gaisheta amsawa tayi cike da fara'a tana fadin ,
"anishatu harkin koshi da baccinne tafada tareda kokarin dagata daga durkusawan datayi , cikin tsukuna fareeda tace,
" oh mubaza akulamuba hajja
mma kawai aka sani, bude baki tayi daniyar magana nanfa hajja mma tace da ala kyalesu zumuje muci abinci ke muke jira daman tafada tareda jan hanun Nisha suka nufi dining table, time din baba Barka takammala komai ta ajiye inda yadace, fareeda ne ta bude
abincin tashiga zubamusu, seda ta zubawa ko sannan ta koma tazauna domin fara ci, kuwa yashiga cin nasa banda Nisha datasa plate agaba tana juya spoon, tanason sake sa aheel aidonta, hajja mma duk tana duk tana kallon abunda take, yade nisha tunanin mekike
,? cikin hanzari Nisha tadagu tana fadin,
" bakomai tana fadan haka tashiga tsikaran abincin tana ci, wayan fareeda ne yayi kara ta dauka cikin hanzari ganin mekiran , karawa tayi akunne tareda fadin,
" hello ammi ina kwana, daga daya ban garan ammi ta a
msa da lapia, ya gd yasu Hajiya, qlu suke sede gd ba dadi muna miss dinki gsky fareeda tafada cike da shagwaba, fisge wayar fadeela tayi takara akunne tana fadin,
" ammi yaushe zaku dawo , ina daddy ,? kibashi wayan , daddyn ku baya kusa don't worry nand
a 2 days zamu dawo, ammi tafa cikin sigan lallashi, yau to kuyi suri kidawo kiga new baby girl da muka miki fareeda ne ta kwace wayar dacewa,
" kuma ammi so beautiful inkika ganta zakiyi happy, ammi batayi mamakin maganar suba domin ta dade da jin labari
n gurin Hajiya daga ita har Daddy sunsan zancen, to shikenan se mundawo din, daga Nisha har hajja mma kallonsu suke suna murmushi, sunyi fira sosai da amminsu daga bisani sukayi sallama yakatse wayar farin ciki fal zuciyoyinsu, suna kammala cin abincin suk
a koma cikin parlourn suka cigaba da firansu, sundau time suna hirarn daga bisani hajja mma takatse kiran dacewa,
" kun fasa fita shopping dine ko se rana tayi? cikin hanzari fadeela tace,"lah mun mance fira tayi dadi, lallai kam hira tayi dadi kutashi mu
je mushirya mutafi cewar fareeda duk suka mike, ganin ba alamar mikewar nisha yasa reeda taja hanunta tana fadin,
" dake zamu ae tashi mutafi tafada tareda jan hanunta izuwa ciki, hajja mma kam kallo kawai tabi bayansu dashi tareda mikewa tanufi bangaran
ta , ba adadeba suka fito cikin shirinsu mekyau but koda suka fito basu tararda hajja mma a parlourn ba, hakan yasa suka bi bayanta domin yimata sallama, Nisha kam bata samu daman bin bayansuba daga waje tatsaya tana bin part din dataga AJEEMAL ya nufa da
aheel tana karewa benen kallo , juyawa tayi danufin shiga part din Hajiya jin muryan aheel yasata dakatawa, da sauri ta daga kai takalli inda take jiyo muryan aheel, daga saman benan yake kwala mata Kira, Aunty see me