Showing 21001 words to 24000 words out of 65624 words

Chapter 8 - IG AJEEMAL BOOK1 COMPLETE

nisha tayi tana fadin,"har kungama firan , eh mungama anyi bake, cikin sauke numfashi Nish

a tace,"to yazanyi naso fitowa ayi hiran dani amma ciyo kan nan ya matsamin , oh sorry kinsha magani kuwa, fareeda ta tambaya," aa base nashaba nasuma jin sauki, aheel ne yazame daga bed din yana fadin," Aunty zanje gurin papana zan dawo anjima , to kawai

tace tareda bin bayansa da kallo har yafita,

Wani dugun numfashi tasauke tareda maida kallonta gasu fadeela da suka kwanta suna danna phones dinsu, ahankali tazame daga gadon tanufi hanyar fita, domin kuwa ta gaji

da kwanciyar, parlour tanufa tanemi kuje

ra daga gefe ta zauna tvn parlourn akunne yake dan haka tashiga kurawa tv ido,amma hakalin ta kwata kwata baya wajan , da alamar ta lula wani dunyar tunani,

Kamal ne yashigo parlourn hand dinsa daukeda hairbrush yana taje kansa, idonsa ne yasauka kan Nis

ha dake zaune takurawa tv ido, da alama batama sanda shigowar sa ba,

ahankali yamatsa tsakiyar parlourn yana karewa Nisha kallo da mamaki, kallonta kawai yake bakinsa tagagara furta komai,

ita kuwa jin kamar ana tsaye kanta yasa ta daga idonta kadan,

dantaga waye, daram gabanta yafadi kamal tagani tsaye kanta yana kallonta,

azabure tamike tayi baya tana kallon shi cikin zare ido, shima haryanzu kallonta yake," NEESHA kece,?:kml yafadi yana sake dubanta da kyau, ita kuwa baki se bari yake takasa cewa

komai, hakan yasa tajuya tareda watsawa da gudu tayi daki,

shikuwa baki bude yake binta da kallo harta shige dakin, abun yayi matukar bashi mamaki meye Nisha taxoyi gdnsu, to kodae gizo tamasa,

kaiwan nan ba gizo bane tabbas nisha ce yabawa kansa amsa,

yana cikin wannan tunanin ya tsinkayi muryan ammi dacewa,"

kai kumafa seyanzu, hanzarce ya kalli ammin tasu cikin sosa kai yana fadin," eh wlh , wani irin bacci kake haka, kayi break kuwa ammi ta tambaya, eh nayi Barka takaimin seda nayi ma nakoma bacci

n, okay to ae shikenan ammi tafada tareda take kokarin juyawa tayi kitchen, cikin hanzari kml yace,"

am bakowa mukayine, cikin tsareshi da ido tace," bakowa kuma aina ammi ta tambaya, eh yanzu naga tashiga bedroom dinsu fadeela, murmushi ammi tayi tana f

adin," kodae Nisha kagani,?

Eh to ina ganin ita dince kamal yabata amsa,

baku taba haduba se yau kenan, eh kawai kml yace yayinda yake kallonta yanaso karin bayani, okay yanzu ina dan saurine in nasamu time zan maka explain daga baya kajiko, okay yace

batareda yasake cewa komaiba, nan ammi tajuya tashiga kitchen abunta, ganin haka shima yajuya yafita daga parlourn,

Nisha kuwa tunda tashiga daki tanemigu ta kwanta, lokacin ta tarar su reeda duk sunyi bacci, nan ta nitsa kanta cikin pillow tana jin zuci

yar ta yanda yake mata dukan uku uku, yanzu ta tabbatar da zarginta dama shine ya kml dinda su fadeela suke fadi, atunanin ta wani kamal dine da ban ashe kamal din da tasanine,

tundaga wannan lokaci Nisha tasumu sara daga sungama breakfast sun koma parlo

ur Hira zata zame tayi daki tayi zamanta because kunyar hada ido da kamal takeji,

dukansu sun lura da hakan atunaninsu rashin sabu dasune wanda kuwa ba haka bane,

haduwa da kamal ne bata sonyi, wani lokaci ahar tunani take akan wace irin kaddarace ta k

awota gdnsu kml

inama bata biyusu Hajiya ba tayi wani wajan daban, duniya da fadi ae bazata rasa wajan fakewa ba,

aban garan kml kuwa tunda idanunsa sukayi tuzali dana Nisha yakeson sake ganinta but hakan yakasa samuwa because duk wani hanyar dazaisa su

hadu Nisha ta tusheshi ko haraba gdn ta daina fita, balle yazuba ido wajan shiga da fitar ta,

Abunda yasani shine zasu hadu komai daran dadewa tunda gd daya suke dole wani dalili zai hadasu,

yau hutun so fareeda na makaranta yakare komai ya dawo mata

sabo kewa yasake dawo mata, domin kuwa su reeda sun koma makaranta,

dama hutu suke yanzu kuma hutu yakare,

shima kuma aheel mutumin ta yakuma school kuma wuni yake acan, gaba kidaya abokan surutun nata basa nan gd yakoma shiru, hatta itama ammin tana zu

wa office, dan haka intaji kewan yamata yawa, seta tattara takoma sashin Hajiya tazauna suita hiransu, har yamma kafin su fadeela sudawo,

bikin kml da nabeela se karatuwa yake yau bai wace saura month ba, gd se shirye shiryen biki ake kaikace next week n

e bikin, su fadeela har ankai dinki na event din bikin, duk da kamal yasheda musu shiba wani bidi'a zaiyi a bikinba,

atunanin shi wannan bawani bikin da za'ayi wani shagali bane because bikin bawani shiga heat dinsa yayi harcan ba,

nishane kwance bis

a gado yayinda idonta ke kallon sama kamar mai nazarin wani abu, phone dinta ne yashiga ringing akwai kamar jira take akirata dama, salmace kan laye, hanunta har bari yake wajan dagawa,

Karawa tayi akunne ta tareda yin sallma, salma bata amsa sallamar ta

ba tashiga watso mata tambaya, " wai nikam qlu kike kuwa, salma tafadi,cikin hanzari Nisha tace," mekika gani meyafaru,? tafada yayinda take kokarin gyara zama,

✍

️

Bansan meyake damunkiba, tunda nabar gdnku baki sake daukar waya ki kiraniba, kuma kince z

akizo gd shima kuma kin gagara, shine nace bari nakira naji har rayuwa tai miki dadinda zaki manta dani koh,

jikin Nisha ne yayi sanyi dan tasan bata kyauta ba , gaba daya tarasa meke damunta, cikin sanyin murya nisha tace,"

Nama rasa bakin magana amma

kiyi hakuri nasan ban keutaba, ke kwata ce kuma aminiyata aduniyar nan banida kawar datakaiki, hasalima in inada wata damuwa nakanzo nasanar dake ko ummata wani damuta bata sani kamar da ke kika sani , salma yanxu haka ina cikin damuwa amma maganar bazaiyi

yu awayaba, gashi gdn nan ba afita daga gd se mkrnt, kwata kwata ba afita salma,

naji ba afita amma yanzu dole kisamu hanyar fita domin kuwa ankawo kayan lefena, salma tafada tana tura baki duk da Nisha ba ganinta takeba,

cikin farin ciki nisha ta want

salo daga gadon tahau rawar murna kaikace ita aka kawo kayan, daga bisani tadan dakata da rawan tana fadin," amma kuma shine baki sanar daniba kafin akawo kayan,

dama nazuba miki idone inga ko zaki kirani, amma baki kiraba kirkinki yayi kadan, gashi nina

damu dake nakiraki, kuma na sanar dake, yanxu de sena jiki kuma ina zuba ido, to kawai Nisha tace daga bisani suka kayi sallama, salma takatse wayan, zama nisha tayi abakin gadon tareda zamewa ta kwanta farin ciki fal zuciyar ta, jitake kamar ta bace ta t

afi gdnsu salma,

aheel ne yashigo dagudu dakin tareda hawa bed yafada jikin nisha Yana washe baki yana fadin," Aunty

ta tsorata sosae ganin bata san da shigowar shiba, cikin tsoro tana zaro ido ta dago aheel tana fadin," amma kai wannan yaro koh tafada

tareda jan kumatun sa , gabani tsorofa,

washe mata baki yayi yana fadin, "Aunty wai tsorita kikayi, eh mn, waima mai ya hanaka zuwa school yau, Nisha ke tambayan sa,

lah yaufa weekend kin manta ba school , oh haka na manta , suna cikin hiran tasu su f

areeda suka shigo daya nabin daya, suka karisu suka zauna, hanun fadeela dauke da chocolate suna sha, fadeela ne ta ajiyewa Nisha ledar acinyarta tana fadin," ga chocolate kisha, nan sha ta bude ledar tadauki daya tabare tasuma sha har wani lumshe ido take

aikin dadi, nisha na kaunar chocolate sosai,

Nan Nisha takalli aheel dake kallonta shima tana fadin," kaima kadauka kasha mana, nan yakai hanu zai dauka reeda tabuge hanunsa tana fadin," mai zakayi, Aunty nima sha zanyi yafada tareda marairaice fiska, f

adeela ne ta amshi maganar da cewa" saboda kaine mai bakin kwadayi koh,? to muma ya kml ne yasammana kaima kaje yabaka yanadashi dayawa,

cikin hanzari aheel kuwa yazame daga bed din yana fadin," nima bari naje yabani, yafada tareda yin waje dagudu,

Da

kinbarshi muma ba iya shanyewa zamuyiba, Nisha tafada tana kallon su reeda, ke kyaleshi yaje zamu iya shanyewa tunda muka dibo, Nisha bata kuma cewa komaiba sukaci gaba da hirarsu, wunin yau kam yamata dadi sosae because abokan hiran suna nan,

sede damu

warta dayane shine sanar da ammi batun fita, dan haka da batun takwana aranta,

Washe gari da suba suka tashi sukayi wanka tareda alwala suka yi sallah kamar yanda suka saba, su fareeda suka suma shirye shiryen tafiya skull domin kuwa 7 a mkrnt yake musu,

dan haka basu tsaya wani dugun breakfast ba coffee kawai sukasha suka wuce,

nisha kuwa tana kammala karatun Qur'an da tasaba ta koma takwanta, batayi wani wacci mai tsayiba sbd atunanin ta ammi 10 ma baya mata a gd,

wajan 8:45 Nisha tasamu daman fark

awa, dan haka ta sakko daga gadon tanufi hanyar parlour takoyi sa'a can dining ta hangi ammi na break dan haka tasamu daman karisawa dan su gaisa,

cikin fara'a da nuna kulawa ammi ke kallon nisha tana fadin,"har kin tashi, cikin murmushi nisha tace,"eh a

mmi natashi, ae na dauka se 10 kamar yanda kuka saba ammi tafadi tana dariya, murmushi nisha tayi batare da tace komaiba,

to maza kizauna kiyi break ammi tafadi tareda turawa Nisha kan abinci gabanta, hanu Nisha takai ta hada tea tafara sha, daga bisani

tadauki pancake tana ci tana mai satar kallon ammi yayinda take karyawa,

bari natashi nashirya karna makara ammi tafada yayinda take mikewa ta haura sama tanufi bedroom dinta,

Seda nisha tagama karyawa sannan ta tashi tareda komawa parlour tazauna tana

jiran sakkowan ammi, ba a wani dade ba , ammi ta sakko cikin shirinta mai kyau gwanin shaawa,

ido Nisha ta tsurawa ammi yayinda bakinta me bari tana kokarin cewa wani abu, ganin kallon da Nisha ta tsare ammi dashi yasa ammi fadin," lapia kuwa Nisha akw

ai abunda kikeson cewane ammi tafa yayinda take shafo gefen fiskar nisha,

kifadamin inkinda bukatan wani abu tafada cikin yanayi na kwarin gwiwa, dama kawata salma aka kawo kayan aure shine nakeson naje nagani nisha tafadi tareda sunnar da kanta kasa tan

a wasa da yan yaysunta,

murmushi ammi tayi na Fadi,"shine kuma baki fada tun jiyaba, gashi ina sauri da na ajiyeki, amma bakomai yanzu kiyi sauri kije kishirya sena saukeki, ammi bazansa ki makaraba, tafada tana kallo ammi, a no ba damuwa da sauran time

, kije kishirya ammafa karki bata lokaci ammi ta fada yayinda tasamu gu tazauna,

cikin rawar jiki da murna Nisha tashiga daki dan shir yawa, kamal ne yashigo parlourn ya tarar da ammi zaune bisa kujera yayinda hanunta ke latsa wayarta, sallma yayi tareda

kokarin karisuwa kusa da ita,

nan ya zauna ya gaisheta ta amsa fiskarta daukeda murmushi, kallonsa tayi tana fadin," lapia kuwa naganka cikin jallabiya, ina shirin office din, ,? dan wani guntun tsaki yaja yana fadin," kai nifa ammi yau banajin zuwa offi

ce dinnan, why ammi ta tambaya, yau banajin dadin jikinane sosae shiyasa,

maganar ammi keda wuya Nisha tafito cikin shirnta mai kyau, fiskarta daukeda murmushi, amma ganin kamal murmushi da annashuwar dake fiskarta dip yadauke, gani fitowar nisha yasa am

mi tana fadin," yauwa kin fito ko to semu samu mutafi dan nakusa makara, ahankali neesha take daga kafarta sbd yanda taji kafarta yamata nauyi,

yayinda idon kamal kuwa ke kanta, ammi ina kuma zakuje nazaci office Zaki, kokema yau zaki hutane, kamal ya t

ambaya, no yanzu zan wuce nisha nakeso nasauke gdnsu friend dinta salma, cikin tare ammi da magana kamal yace,"

haba ammi keda zakitafi office maizai kaiki da wani biye biye, aiseki makara kisa driver yakaita mana, ko kibari nina sauketa, yafada yana sat

an kallon Nisha,

wow da kate makeni domin kuwa nakusa makaran please ka tai maka kasauke min ita , ni bari na wuce tana fadin haka tayiwa nisha sallama tayi fice warta,

Nisha kam kamar wacce aka dasa agun batayi gaba ba batayi bayaba, jitayi kamar tafa

sa fitan, har kamal yafita yakoma dakinsa yacanza kaya ya dawo Nisha na tsaye inda yabarta,

jin inuwar mutum kusa da ita yasa tadago takalleshi tareda dan zaro ido waje, kallonshi take sosae cikin shiri maikyau, yayi kyau dashi kamar kasaceshi kagudu,

kamarsu ya kara fitowa sosai da brothern shi AJMAL, sedan haske da AJMAL yafishi danshi yaynsu ba inda yabar mahaifinsu, mujeko abunda kamal yace kenan yana dan murmusawa juyawa yayi yafice, itama bayanshi tabi .

ahankali take tafiyan kamar wacce kwai yaf

ashewa aciki har ta karisu jikin motar, kamal duk yana kula da yanayinta, bude mata motar yayi ganin tashiga yasashi maida kofar motar yarufe, nan shima ya zagaya yashiga motar tareda sawa motar key,

tunda suka hau titi suka suma tafiya bawanda yacewa da

uwansa kala, kamalne ke sauraren sautin wakanda yakunna yana mai bin mamin din wakar, yana satar kallon Nisha wacce kanta ke gefe tana kallon hanya,

baki fadamin inda zakijeba, ko mucigaba datafiya se inda mai dinmu yakare, kamal ya watsawa Nisha tambay

a, dan jiyuwa nisha tayi tana fadin," nasarawa, bansan wajanba kamal yafada yana mai cigaba da kallon titi, zuro taimasa da ido ganin cewa komaiba still kuma tacigaba da tuki, tama kauda kai gefe tayi tana mai maganar zuci,"

dama kaida ba dan gariba taya

zatasan gari, shiru tayi tareda zubawa sarautar allah ido, amma ga mamakinta segasu a anguwar, yana tsaka da tukin ya dan jiyu yakalleta yana Fadin," sekuma ina zamuyi,

yo kuma kace bakasan unguwar ba yanzu waya kawomu ,?Nisha tafada cikin zuciyarta, kin

yi shiru kamal yafada yana mai kokarin tsaida motar,

dan tsuke fiska Nisha tayi daga bisani tashiga masa kwancen ida zasuyi har suka karisu kofar gdnsu salma,

daga gefe ya tsaida motar yayi parking, hakan yabawa Nisha daman fitowa daga motar, tafara ko

karin maida kofar tarufe, jin muryan kamal nafadin," karki bata time yasa taja tatsaya tana fadin," nifa zan kai yamma, aina kenan kamal ya tambaya, nan Nisha tafada tana mai tura baki,

ina tunanin baki da labarin gdn ALH ABUBAKAR MODIBBO BATURE ba afit

a yawo balle asa ran za awuni kuma kema yanzu kina daya daga cikinmu, dan haka ki hanzarta inajira yafada tareda maida kansa ga wayarsa,

jiki ba kwari tamaida kofar motar tarufe tajuya tashiga gdnsu salma, da sallama tashiga cikin gdn tana dan wul wul ga

ido,

salma ce tafito daga dakin, ganin Nisha tsaye cikin gdnsu yasa tazura da gudu tayi kan Nisha ta rungume ta, cike da murna da zumudi, yar halak ashe kina tafe, tafada tana washe baki,

bakowa gdnne ina ummyn naji gidan shiru, ummy bata nan faruk ku

ma yana makaranta tareda tareda jan hanun Nisha suka shiga ciki,

daga nakin gadon salma nisha tasamu tazauna tana kallon salma wacce itama Nisha take kallo, kawata kinga yanda kika kara kyau kike glowing har wani kumatu kikayifa, salma tafada tana jan ku

matun nisha

Murmushi nisha keyi yayinda take kallon salma tana fadin," amaryanmuba mrs bello to akawomin lefen nima nabawa idona abinci, ko anrufe gani, Nisha tafada cikin tsokana, yo ko anrufe gani dole abude kigani tafada tareda jan hanun Nisha suka fit

a daga dakin,

dakin ummynsu takai nisha domin adakin ummy kan suke, nan salma tashiga nunawa nisha kayan arzikin da abun kaunar ta, ya aiko mata, masha Allah kawata kaya sunyi kyau sosai kawata tayi gishi nisha tafa tana zungorin goshin salma,

to yaush

ene bikin ko ba asa ranaba nisha ta tambaya, ba asa ranaba tukun kin kin matsu akaini koh, gsky kam namatsu shima kansa uban gayyan amatse yake Nisha tafada tana tabe baki, salma ce takaiwa nisha bugu tana fadin," kefa bakida m to karya akayine nisha tafad

a tana dariya,

.

sun dau dugun lokaci suna fira daga bisani Nisha tamike tsulum tana dan zazzare ido, sam ta manta da kamal dake jiranta awaje, salma bari naje gd ba kowa muku ana jirana awaje, salma tace," dawuri hk nadauka wuni zamuyi, zan sake dawowa

nisha tafada cikin hanzari,

to bari na tattara kayan nan nazo na rakaki, to kawai Nisha tace tashiga tayata suka maida kayan, mayafi salma tadauka suka nufi hanyar fita,

fitowar su keda wuya gaban Nisha yafadi, ganin ba motar akofar gdn, wul wul ga ido

tashigayi nan ta hangi motan daga can gefe yayi parking,

nanfa Nisha taja wani goron numfashi tareda kokarin yiwa salma sallama, to to ina motar da take jiran nakin salma ta tambaya, da hannu Nisha tayiwa salma nunin inda motar take a pake, yo inbanda

abun driver meyena kai motar can kuma salon yasaki tafiya, dariya Nisha tayi tana fadin,"

maybe ya gyara parkine bari naje se munyi waya, to kawata nagode kigaida su Hajiya dasu reeda nima zanzo inna samu time insha allahu, to shikenan senaganki nan suka

yi sallama sannan salma tajuya tashiga gdnsu, hakan yabawa Nisha daman barin kofar gdnsu salma tanufi inda ta hangi motan kamal,

tana karisawa tasa hanu tabude murfin kofar tashiga tamaida kofar yarufe, akife ta sameshi ya kife kansa kan siterin motar da

alama bacci yafara daukansa,

jin motsin shigowarta Nisha yasashi daga kai yana binta da kallo da rinannun idanunsa da sukayi jawur dasu, harara ya watsa mata yana mai hade gira wanda yasa Nisha sunkuyar da kai kasa,

baicemata Kala ba yaja motar da wani

irin gudu kamar mai shirin tashi sama, wanda hakan bakaramin bawa Nisha tsoro yayiba,

✍

️

🥀🥀

IG AJEEMAL

🥀🥀

Story and writing by Oum AmReesh

♥

️

tunda suka hau titi suka suma tafiya bawanda yacewa da dan uwansa kala, har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login