Showing 30001 words to 33000 words out of 59902 words

Chapter 11 - iznah Complete

/>
🤨

Comment

Share

*_EZNAH_*

🌹



_wattpad@mamuhgee_

*27*

*Alhamdulillah banmasan ta yanda Zan gode mukuba Amma kusani mamuh taga qaunarku da kulawarku nagode matuqa,,,ku din nawane Nagani.. thank you so very much sweethearts more especially my wattpadians....*

*Mamuh  love yo

u guys*.

😍😍😍😍

Koda yabar palon direct motarsa ya nufa yabar gidan tareda kashe wayoyinsa gabaki 'daya.,

Zayyan Abba yakira yaqara yimasa bayanin inda zasu shida aminin NASA sbd yasani Sarai ba lallaine saheeb din yafada masaba.

Zayyan d

in nagama waya da Abba saheeb yakira Amma yaji suka wayoyinsa arufe

Dama yasan arina Kuma koba komai yasan zuwan saheeb din bamai yiyuwa bane yanxu

Dan haka Sai kawai yashirya shida Abu suka tafi batareda sanin abban bada saheeb suka tafiba...

Yau t

un safe baqin kauye dasuka iso suka qarasa cika gidan Sai hayaniyar biki suke

itadai amarya tana 'daki tareda qawayenta Sai firarsu suke cikin farin ciki da kwanciyar hankali

Lokaci lokaci idan ta tuno dawa zata aura Kuma gobene saitaji gabanta yayi mum

munan fa'duwa Dan 'yan kwanakin datayi agida jitake kamar karta koma tace tafasa

Sam yanxu batajin tsoron mum asee ko ka'dan bare na Kamal data gama rainasa kallon lusari ma take Masa Amma tsoron saheeb din acikin jininta Allah ya halitta Mata shi...

Kamar daga sama taji ana cewa ga angon Nan yazo gaisuwa

Ta lumshe idanu gabanta na tsinkewa Dan tasan saheeb bazai ta6a zuwaba Sai dai in Kamal n.....

Zumbur ta bu'de idanuwanta ta miqe Dan kuwa idan Kamal ne tonan asiri zaimusu anan kowa yagane kai d

a silar auren qilama har fiyeda hakan zaiyi.

Hijab ta dauko dogo tasaka tafito dakin su nusaiba suka bita da kallo

Tsakar gidan ma tana fitowa suka zubo Mata idanu ta Sosa Kai tareda waskewa ta 'dau buta ta nufi hanyar bayi tana satar kallon qofar shi

gowa

Cikin sa'a taga zayyan yaci ado cikin suturar alfarma yana shigowa tareda Yusuf da aliyu Dan harya gama ganinsu baffa yamusu bayanin aikine Mai qarfi yariqe saheeb shine ya wakilto shi kafin gobe suxo 'daurin aure..

Aje butar tayi tareda sakin aj

iyar zuciya takoma 'daki ahankali ta zauna tareda godewa Allah ma dayasa saheeb din baixo ba.

Kudi sosai da Kayan dazata saka gurin sha'anin bikin zayyan yabayar kafin ya juya kusan da yamma Kuma harya tafi Bai gantaba tana 'daki.

Da dare gwaggo da w

ata 'yar qanwar Inna suka kawo wani uban lalle daya yini a kwa6e sukace daura Mata zasuyi ta kwana dashi

Kallo daya tayiwa lallai ta kalli gwaggo tace,

Gwaggo wannan lallan idan na 'daura na kwana dashi ko kofin Dana riqe saheeb bazai sake kallaba bare

yaci abin hannuna...

Baki su gwaggon suka sake Amma ita gwaggon tasan saheeb din zai iya yanda ta fa'da 'din Amma Kam yaza'akai amarya ba lalle kitso ma tun safe aka kirawo maiyi Amma ta murje idanuwanta ba kunya tace saheeb din bayason kitso.

Zama

gwaggo tayi kusada ita tareda karbar robar lallen ta aje gabanta tace,

Anano Ina za'akai amarya ba lalle ba kitso saikace mugun aure..

Ki daure ko irin na 'yan gayune saiki 'daurashi kobai Kai safeba da tsakar dare saiki wanke Kinga fa kwana biyu zali

tayi tana yanka Miki wannan salatif din irin zanen Yan gayu..

Kallon salatif din tayi taga yanda aka yankashi kamar za'a daura a qafar mutum biyar ta karba tareda ajewa gefenta tace,

To Zan daura da kaina gwaggo.

Suna fita ta jawo robar lallen ta

daura a yatsun qafafuwanta Dana hannuwanta tana tunanin yanda komai na aurenta yazamo wani iri

Harta gama ta kwanta zuciyarta na wani iri.

Washe gari.

Tunda ta tashi sallar asuba takasa komawa ta kwanta jikinta gabaki 'daya a mace yake gashi 'daurin

auren na safe ne qarfe goma..

Tun asuba gidan aka fara kaida kawon ayyuka har gari yayi haske lokacin 'daurin aure ya gabato su Yusuf da sauran samarin gidan suka shishirya tsaf

Tuni qofar gidan tafara cika da jama'ar daurin aure na qauyen.

Tunda s

uka hadu da Abba sallar asuba a masallaci abban cikin daurewar fuska yabasa umarnin shiri cikin lokaci daga haka ya tafiyarsa yabar saheeb din cikin wani irin yanayi...

Qarfe bakwai yamiqe yashiga toilet yayo wanka Yana cikin shiryawa zayyan tareda miqa

Masa Kaya.

Ko kallon gefensa baiyiba ya wuce closet dinsa ya 'dauko wasu kayan...

Dariya zayyan yayi yace,

Banifa naKar zomonba rataya aka bani.....

Cikin milk Australian gezna yashirya tareda fesa turarensa ya fito Yana daura agogo wayoyinsa

ya kwasa suka fito har lokacin fuskarsa a 'daure take..

Abba da sauran jama'arsa dama tuni suka wuce

Suna fitowa yaga motocin sojoji kusan goma ya sake 'daure fuska tareda watsawa zayyan wani mugun kallo suka shiga mota suka kwasa a guje suka dau hany

a...

Kamal daya fito da gudu daga part dinsa ya daki iska cikin tsananin baqin ciki da qunar zuciya sbd tun jiya ya shirya zarewa motocinsu saheeb din burki Amma wani mugun bacci ya 'daukesa bayan yasha drink gurin mum...

Qyaci yayi cikin zafin zuciy

a yace,

Zaku dawo gidan daka Kai har ita idiot din zanyi maganin kowa har useless dattijon Nan daya ha'da auren har mum asee sbd bazai ta6a yafe wannan cin amanarba,,,, you'll all gonna pay for this idiots...

Qarfe goma da saura mintuna goma Sha

biyu suka iso Nan qauye rikice da hayaniya sbd ganin sojoji mota mota kamar wa'inda sukazo kwantarda tarzoma...

Lokacinda saheeb din yafito yaqaraso ba baffa kawai yaji da'din ganin mijin Anano ba kaf su aliyu sunji Dadi Nan aka fara gudanar da 'daurin au

ren...

Tundata tayo wanka tazo ta shirya cikin doguwar Rigar wani tsadadden lace black Mai adon purple daya fitar da hasken fatarta matuqa Nan take tafito amaryarta ta shirya abdulshakur shima cikin adon sabbin kayansa da zayyan din yasako Masa shima.

Zaunawa tayi tareda 'daurasa Kan cinyarta tana basa sabuwar Madara da aka kawo Mata Tasha..

Kallonsu nusaiba tayi tace,

Anano kibani 'danki Mana kafin kugama cin amarci...

Murmushi tayi ta bu'de baki zatayi magana shigowar hamma Yusuf da goron

daurin aure cikin gidan Yana fa'dar andaura ne yasa bakinta nauyi gabanta yayi mummunan fa'duwa..

Rintse idanuwanta dasuka kawo ruwan hawaye tayi

Su ubaidah kuwa fita sukayi tsakar gidan Sbd cewa da akayi ga angon Nan shigowa ya gaida iyaye Mata.

S

ake rintse idanuwanta tayi lokacinda taji qamshin turarensa har cikin dakin ya shiga hancinta.,

Jiki a mace ta miqe daukeda abdulshakur ahannunta taje bakin window tana tsaya Yana qarasa shigowa tsakar gidan gabaki 'daya Kuma Kai tsaye cikin idanuwanta

nasa idanun suka fara sauka...

Saurin barin bakin windon tayi zuciyarta na bugawa da sauri takoma bakin gadon ta zauna da sauri.

Cikin qarfin hali ya gaggaisa dasu yafito sbd tsananin zafinda zuciyarsa ke Masa musamman ma yanxu daya ganta itada bastard

son dinta.

Sosai zayyan da Abba sukaita sakin kudi suna rabawa maroqa da Yan qauyen har aka watse suka juyo da niyar Sai washe gari za'a Aiko motar daukar amarya.

Koda suka koma tuni gyaran part dinsa yayi Nisa sbd fitar da komai da akayi akayo odar s

abo bedroom dinsa ne kawai ba'a ta6aba sbd gudun laifi hakama ba laifi mum asee ta Tara jama'arta anyi taro na musamman na auren 'danta..kaman yanda take fa'da.

Baidawo gidanba Sai dare Koda yadawo angama gyaran komai part din ya canxa sosai saidai hotu

nan nafeesat ko daya ba'a daukeba suna Nan maqale inda suke saima gogesu da'akayi aka mayar..

Bedroom ya wuce ya shige toilet yayo wanka yaxo ya kwanta...

Asuba nayi yayi wanka ya shirya ya nufi masallaci acan yasanarda Abba tafiyarsa qarfe bakwai na s

afen..

Cikin sakewa Abba yayi Masa adduar Allah ya tsare Dan dama shidai burinsa ayi auren yananan..

Yana komawa 'daki ya harhada abinda zai buqata ya sake shiryawa cikin qananun Kaya black da blue leather jacket yafito daidai isowar zayyan dazai kai

sa airport

Ya shiga mota suka wuce..

Jirginsa na tashi zayyan yadawo gida yahau Shirin zuwa 'dauko amarya sbd shine zaije.

Qarfe goma aka sata ta shirya baffa ya zaunarda ita yayi Mata nashiha shida gwaggo duk da da ita zasu koma

Hakama su Yusuf

kowa yayi Mata tasa kalar nasihar..

Sosai jikinta ya mutu da nasihar su baffa Dan ma basusan wane irin aurene ba tayi.

Babu abinda ta 'dauka Sai kayan da zayyan yakawo Mata

Qarfe biyu zayyan ya iso qarfe uku suka juyo daga ita Sai gwaggo da nusaiba

ubaida mijinta Bai bartaba Sai jafar dake gaba...

Tunda suka dau hanya jikinta ya qara saki tsoro da fargabar yanda zata ha'du da saheeb din take.

Gab da magriba suka iso Nan su mum asee da wasu baqinta suka tarbesu a aladance suka rakasu har part d

in saheeb har cikin bedroom din nafeesat dayake amatsayin nata yanxu..

Gwaggo 6angarenta ta nufa tareda nusaiba sbd basusan saheeb din baya gariba..

Bata tsaya wani dogon jiraba sbd tasan ba kamar kowane aurene wannanba dazata jira ango ta miqe jiki

asanyaye tana kallon tsari da haduwar kayan dakin da'aka canza tana qara mamakin inda aure yakawota harta fa'da toilet tayo wanka tazo ta bu'de akwatinta ta canza Kaya tayi sallar la'asar dabasuyiba da magriba..

Tana idarwa taji ana knocking qofar bedro

om din

Gabanta yayi mugun fa'duwa jikinta na saki ta miqe ta bu'de cikin fargaba.

Asabe tagani tareda wata sabuwar Mai aiki budurwa tasaki fuska suka gaisa asabe tace,

Abincine mum asee tace akawo..

Kallon kulolin hannunsu tayi kafin tace,

Su

aje dining

suna ajewa suka fice ta fito palon cikin fargaba ta nufi qofar kicin tabita qofar kicin din ta fa'da dakin gwaggo..

A zaune ta tarar dasu suna hutawa tazauna gefen nusaiba tareda gyarawa abdul kwanciyarsa tana  cewa,

Nusy ga abinci acan

kixo muje mudauko saimuci anan..

Muguwar harara gwaggo ta watsa Mata tana cewa,

Kedai wlh anyi gantalaliyar amarya Mara kunya,

Yanxu da ace saheeb din Yana gari haka Zaki taho kibarosa?

To Allah tsaya kiji matuqar kikace wannan zaryar gantalin Zaki

riqayi zuwa Nan kayana Zan ha'da nakoma gida tunda dama Dan kina ganinane,

Abinci mun Riga munci ki tashi maza ki koma 'dakinki..

Miqewa tayi jiki a salu6e ta duqa ta 'dauki abdulshakur ta sa6a akafada ta Fice gwaggo tabita da harara ko Abdul dinma Da

n taji asabe tace bayanan ne yasa tabarta ta tafi dashi.

Washe gari tunda safe nusaiba da jafar suka wuce Abu driver Abba yasa yamaidasu..

Bayan kwana biyu

Qarfe goma da rabi ta shiryo cikin wata dark blue atampar super exclusive batareda tayi kwal

liyar komaiba Amma duk da haka sosai tayi kyau cikin shigar ta fito ta riqeda hannun abdulshakur dake koyan tafiya ta nufi gurin gwaggo suka gaisa tabaro abdul din ta nufi part dinsu mum asee.

Tana kaiwa qofar part din da Kamal tafaracin karo ya tsaya g

abanta Yana watsa Mata wani mugun kallo zuciyarsa na mugun tafasa...

Dauke Kai tayi tareda ra6asa zata wuce a zuciye ya fixgota tadawo baya

Bata tsaya Bata lokaciba ta yanka Masa wani lafiyayyan Marin dayasa su mum asee qarasowa cikin wani mugun yanay

i..

A zafafe ya 'daga hannu zai sakar Mata Marin yaji anriqe hannunsa ya juyo cikin zafi yaga zayyan tareda Ahmed zubair Barr Kuma PA na saheeb..

Kallonsa tayi cikin daure fuska tace,

Ka dawo hankalinka idanma gushe maka yayi kasan da matar babban

soldier kake

Ka gode Allah baya gari da baka qara marmarin ko kallon matarsaba bare ganganci ta6awa....

Ba Kamal kawaiba hatta mum asee da zayyan sunyi matuqar mamakinta bare Ahmed daya fito da idanuwa ganin matar saheeb din ta yanxu taci uban marigay

iya Dan nafeesat sanyi qalau take.....hmmm lallai akwai rigima tafe Amma Bari yagani...

Gyara tsayuwa yayi tareda kallon mum asee yace,

Mum asee dama maganar ku'din da ake bayarwane na duk wata na biyan ma'aikatan gidan da bills na gidan nakeson sani

n sabon lissafinku tunda oga yayi aure yanxu Dole lissafin zai qaru.

Kallonsa tayi a wulaqance tace,

Banda wannan lokacin kaje ka qara dubu 'dari asama......

Zaro idanuwa yayi tareda gyara zaman medical glass dinsa yabude baki zaice to cikin 'daur

e fuska Anano ta katsesa da cewa,

Wayene Mai biyan bills din?

Oga saheeb ne madam..

Nawane?

Dubu 'dari biyu ne duk wata madam....

Sake daure fuska tayi tareda satar kallon zayyan ya gyada Mata Kai a fakaici saita juyo ta kalli Ahmed din tace

,

Cancel wannan lissafin sbd nice matar saheeb nice Zan riqa bada duk wani lissafin abunda ake buqata matuqar daga dukiyar mijina zata fito daga yau kaje jibi zan nemeka idan nagama lissafin nakumayi magana baby anjima....

To yace tareda juyawa yabar

gurin Yana danne tsananin mamiknsa

Zayyan ma bayansa yabi Yana jinjina alamarin....

Hmmmnn su saheeb baby manya.

Suna barin gurin ta juya zata wuce mum asee ta riqo hannunta cikin wani irin mugun 6acin rai.

#vote

#comment

#share

*_EZNAH

_*

🌹

_wattpad@mamuhgee_

*28*

'dan fiddo da idanuwanta tayi tareda jujuyawa ko Ina tayi qasa da murya tace,

Mum yi ahankali Kar wani yagani cikin yaran saheeb su rainani inzo inason Basu umarni suna qin bi...

Wani mugun kallo mum

asee tasakar Mata Saida taji gabanta ya'dan Fadi ta ha'diye wani yawu tareda sakin murmushin qarfin zatayi magana mum asee ta katseta cikin wani irin yanayi tace,

Kibi ahankali fa karkibari rawar kanki tasaki wuce wurinki Dan kuwa bazaki Kai wani dogon

labariba,,,kisan dawa kike karkiyi gangaci da rayuwarki..

Sakinta tayi ta juya ta shige palonta Kamal da tuni yayi mutuwar tsaye sbd baqin ciki gashi baiji Mai suka tattaunaba yajuya yabar gurin Yana qissima wani mummunan nufi a zuciyarsa..

Sanyi taj

i jikinta na nemanyi sbd tabbas tasan waye mum asee tasan dawa take dealing amma itama dolece tunda ba wata hanya ko mafita yanzu idanba wannan dinba Kuma matuqar Bata fara da hakanba bazata samu su hada duk wata shaida dasuke soba ta tona su mum din

Dan

ko sunso tonasu yanxu basuda wata qwaqwaran shaidar gabatarwa...

Juyawa tayi ta jiki ba qwari takoma gurin gwaggo ta 'dau Abdul suka koma..

Abinci ta 'daura musu itada Abdul din sukaci suna gamawa yayi bacci takaisa 'daki kwantar bayan ta rage Masa

qarfin ac

Takoma kicin taci gaba da ayukanta

Ta gyare kicin din tadawo Palo tazauna tana kallon tashar cwtv.

Washe gari da safe zayyan zo tareda takardunta dayasa aka kar6o Mata na gama makaranta..

Drinks din data kawo Masa ta aje tareda Zama cik

in sanyin murya tace,

Mum asee tafara tambayata akan nafara gaggawar aikata abinda yasa akayi auren.

Wayarsa dake ringing ya fitar Yana cewa,

Karki damu da wannan kicigaba da yanda Kika fara dinnan sbd rashin hakuri da zafin zuciyar Kamal agurin m

um ya gado abinsa coz Sam itama batada hakuri.,

Idan Kika cigaba da kunnasu cikin qanqanin lokaci zasu fara fiddo da halayensu,

Yanxu dai kishirya gobe Ahmed zaizo yakaiki siyayyar Kaya da duk wani abun buqatarki saikuma maganar jamb dinki yau za'a cik

a komai insha Allah..

Miqewa yayi tareda miqa Mata kwalin wayar iPhoneX yace,

Bari natafi baby saheeb ne ke kirana Kar ya hasala kinsan halinsa...

Sunkuyar dakai tayi tana dariya cikin kunya sbd tasan tsokanar zancenta na jiya ne yakeyi.

Yana f

ita ta fiddo wayar ta kunna tayita dube dubenta kafin ta maqala charging Dan Sam Bata iya wayarba.

Da marairaice gurin gwaggo takai abdulshakur tasamu tagama aikinta sabuwar Mai aikin da mum takawo Mata tana tayata duk da tana zargin sbd saka Ido aka ka

wo Mata ita.

Washe gari Ahmed yazo Koda yakirawo wayarta da zayyan yabasa number yasanar Mata ya iso

Ta shirya ta fito riqeda wayarta ta nufi part dinsu mum sbd taga motar Abba Kuma ta tabbatarda Yana gida.

Cikin sa'a kuwa ta tararda dukkaninsu a

palon ta sunkuyar dakai ta gaida abban cikin girmamawa

Fuska cikeda walwala ya amsa tareda tambayarta Abdul.

Sunkuyar dakai tayi cikin ladabi tace,

Mum Ina wuni.?

Baki mum asee da yakurah suka  saki cikeda mamakin mugun ladabin data nuna,

Cikin

sanyin murya tasake bu'de Baki tace,

Mum fita nakeson nayi Zanje asibiti shine saheeb yace karna kuskura nahau adaidaita....

Katseta Abba yayi da cewa,

Dama Kam ai baza'a Bari kihau napep ba ga motocin mijinki Nan aje acikin gida..

Kallon mum

yayi yace,

Kwaso Mata gabaki 'daya mukullan motocin saheeb kibata ta ajiye ahannunta tunda dai yanxu itace matarsa duk lokacinda zata fita ta 'dauka drivernsa nanan.

Wani qululun baqin cikine ya danne zuciyar mum har wani 'daci 'daci ta ringa ji ta m

iqe taje takwasosu ta miqawa Ananon

Cikin sanyin murya tace,

Aa Abba abarsu 'dayama ya Isa..

Aa ki kar6a duka ki adana Masa sauran ai dama sbd rashin iyali ne wasu abubuwan suke Zama ahannun mu iyayensa ai tunda ya aje iyali yanxu Kam aimuma saimu

huta..

Hannu biyu tasa ta kar6a tareda kallon fuskar mum asee dake turnuqe zuciyarta kuwa suya take matuqa.

Ficewa palon tayi Kai tsaye tareda zuba mukullan cikin handbag 'dinta tana sakin murmushi..

Nabeela itace budurwar zayyan dazai aura,

Kyak

kyawar matashiyar datake gab da kammala karatunta a jami'a,

Nabeela ta waye sosai Amma ba irin lalatacciyar wayeba,

Hakama she's very fashionable Dan haka zayyan yasameta yasanarda ita so yake ta kusanci Anano amaryar saheeb sosai sbd so suke tazama fash

ion and classy ta waye sosai ta yanda zataji da'din tsula tsiya agidan.

Dan haka suna fitowa cikin wata fitinanniyar motar saheeb din black suka nufi gidansu nabeela

Tarba Mai kyau tayi Mata cikin sakewa suka gaisa da mummynta  kafin suka fito suka nu

fi gurin shopping.

Ahmed ne agaba da driver itada nabeela suna bayan motar harsuka iso wani qaton mall suka shiga.

Siyayya sosai sukayi Wanda duk nabeelarce Mai zaba Dan kuwa Nanda Nan ta ha'da Mata wani irin lefe guda musamman mayuka masu tsadar gsk

e da Arabian ouds masu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login