Showing 21001 words to 24000 words out of 59902 words
Amma yaqi yarda ya amsa laifinda baimasan ta inda yafaroba.
Washe gari
Bayan anyi duk binciken daza'ayi dakuma bayanan Anano ankai ruwa Rana da wasu manyan dabasa son saheeb din kafin aka Kai qarshe aka
yarda dabashi yayiba aka sakesa tareda kar6e star dinsa biyu cikin hudu daga kanal major yadawo qasa major kawai....
Aiko Nan 'yan jarida da talabijin suka fara yadawa musamman da aka fito dashi Nan aka fara kakkaresa sbd Yan jarida gashi gabaki 'daya ko
tsayuwa sosai baya iyayi direct jirginsu aka shige dashi akayo gida dashi.
Motocinsu na sojoji suka daukesa aka nufi gida dashi cikin mugun gudu masu motoci da mashin Sai kaucewa suke Dan labarai sun gama yada ko'ina ansan yau sojojin yola kaf ransu a6a
ce yake anta6a kanal major saheeb Dan kuwa suna tsananin sonsa.
Tunda jabiru yajiyo jiniyarsu ya bu'de gate yabarsa bu'de Dan idan yayi wasa yau duka da tsallen kwado zaici Dan sun Saba horar dashi idan suka dawo agujen Nan yayi sanyar bu'de gate...
Abu kuwa dama Yana Jin yaune dawowarsu yayi sauri gyara parking motocin Abba yashigar dasu qurya danshima yaficin wahalarsu sbd shegen tsoronsa.
Tunda motocinsu suka shigo gidan Abba yafito cikin tsananin damuwa Dan kuwa tun jiyan yake cikin wani Hali n
a damuwar saheeb din.
Abba da zayyan ne suka kaisa har bedroom dinsa suka kwantar Nan zayyan yayi gaggawar Kiran Dr sbd saheeb din nabuqatar Dr sosai.
Mum asee datun safe da labarin sakin saheeb din yakusa sheqata lahira sbd baqin ciki ta fito tareda q
aqalo murmushi da farin cikin Dole na ku6utarsa nufi part dinsa.
Dr na zuwa ya dubasa yayi Masa allurori masu qarfi da magunguna kafin aka sallami kowa sbd baason kowa ya damesa for now.
Soldiers biyu sukaja suka tsaya bakin qofar part din duk Wanda
yazo basa barinsa shiga harsai oga saheeb din yatashi yabada umarnin abar mutane shiga.
Zayyan kuwa mota Yakoma ya aika jabiru yakira Masa Anano.
Zaune take tsakiyar dakin tanacin abinci kamar batasonci itada abdul Sai wasarsa yake idanuwanta sun bu
'de Amma a kumbure suke sumtum har wani nauyi suke Mata.
Gwaggo kuwa tana kicin tanata hidimar dafawa saheeb abinci.
Tunda taji dawowarsa gabanta ke fa'duwa zuciyarta na tsananin son ganinsa Koda daga nesa ne Amma batajin zata iya.
Sallamar jabiru c
e a qofa ta katseta ta amsa Masa cikin sanyin murya yafada Mata oga zayyan nakiranta tayi saurin kallon qofar Amma tuni jabirun ya wuce ta ha'diye yawu daqyar cikin tsoro tace,
Allah ka kawomin qarshen zamana Nan gidan konayi sauqaqaqiyar rayuwa kamar k
owa.
Miqewa tayi tareda 'daukar abdulshakur jiki a sanyaye taje kicin takaiwa gwaggo shi ta Goya sbd Sam Bata cika son fita dashiba sbd zagi da aibantashi da'ake.
Tunda ta hangosa jikinta yafara rawa ta daure ta qarasa tareda sunkuyar dakai tace,
Ina wuni?
Cikin kulawa ya amsa tareda tambayarta ya jiki.
Da sauki tace a sanyaye..
Shiru tayi tanason tambayarsa ya saheeb tana tsoro
kamar yasan metake tunani yace,
Saheeb na ciki Yana hutawa sbd yayi weak sosai sbd sanyin daya shiga qashinsa
sosai
Amma insha Allah he'll be fine idan yatashi.
Hmmnn nikam ai yanzu na tabbatarda bawanda yakai sojoji mugunta tunda Naga zahiran a idanuwana.
Katse mata tunani yayi ta hanyar cewa,
Idan bakya komai Zan kaiki gurin wani Dr ne yaduba idanuwan.
Girgixa Kai tayi tace,
Aa naji sauki tunda gashi Ina gani.
Murmushi yayi sbd ya hango tsoro qarara a idanuwanta Amma ai baiga laifintaba Danma tayi qoqari Sosai Dan tamatuqar burgesa.
Lalla6a yayi daqyar tabisa bayan taje tasanarda gwaggo.
Wani private asibiti yakaita aka dubata tareda Bata magani kafin suka baro.
Wani qaton shopping mall yabiya da ita shikadai yashiga yayo siyayya Mai yawa Suka nufo gida Yana 'dan janta da zance tana amsa Masa ahankali.
Suna shigowa harabar gidan Kama
l nafitowa daga part dinsa ya tsaya kallonsu cikin uban mamaki da 6acin Rai
Tana ganin haka tahau yaqewa zayyan baki tana amsa Masa zancensa cikin sakewar fuska.
Qwafa yayi ya wuce afusace Dan badan sojojin dake gurinba saiyazo ya 6alla musu rashin m
utunci Amma yasan Yana zuwa ubansa sojojin zasuci barema Daman idan saheeb na gida basa Bari atada hayaniya hardai yanxu da baida lafiya.
Please for godsake ku ringa sanin comment din dazakuyi karfa ku manta novel ne ba reality ba and fiction ne fa so m
eyesa kuke magana akan wannan is kaza,
Wannan is not kaza,,,,,gsk am not happy da yanda wasunku ke magana akan lallai Bai kamata ace anyi wannan ba,anyi wancan ba....
Please kufadi alkhairi ko kuyi shiru.
Anyways my wattpadian I love you guys so much
sbd Ina ganin kulawarku sosai but please kuyi voting kuyi sharing not only comment
😍
#vote
#comment
#share
*_EZNAH_*
🌹
_wattpad@mamuhgee_
*24*
Tana ganin ya shige ta kalli zayyan tace,
Nagode Zan shiga ciki.
Siyayyar dayayo
Mata ya fitar tareda miqa Mata manyan ledojin takallesa zatai magana yace,
Apologies and thank you......
Girgixa Masa Kai tayi zatai magana yarigata da cewa,
For Allah's sake karkiyi magana ki karba..
Kar6a tayi tareda godiya ta juya tabar guri
n yabita da kallo zuciyarsa na kar6ar abinda ke shigarsa akanta duk da dai yanason magana da ita sosai akan
abubuwan dasuka faru Amma yabari saita warware duk da dai zuciyarsa na hararo Masa wani alamari acikin zuciyarta gameda saheeb.
Washe gari Inna
da ciwon Kai Mai tsanani ta tashi tun Daren jiyanma take fama dashi..
Tana tashi ta Mike ta nufi hanyar fita Anano dake gyarawa abdul lullu6i takalleta tace,
Gwaggo Ina Kuma zakije?
Karin safiya Zan dorawa saheeb Kinga shima ba lafiyarne dashiba.
Keda bakida lafiya gwaggo kiyi zamanki zanyi Miki aikin.
Idanuwanta dabasu gama hucewaba gwaggo takalla zatayi magana takatseta....
Zan iya gwaggo zoki huta.
Miqewa tayi ta nufi kicin din gabanta na fa'duwa...
Cikin qanqanin lokaci ta ha'da Mas
a breakfast lafiyayye tarasa yazatayii tashiga palonsa takai masa.
Rintse idanuwa tayi tareda sauke numfashi ta dauka ta bu'de qofar palon ahankali tashigo.
Tsaye yake bakin fridge na dining area din ya Ciro Power horse zaisha kayan baccine black aji
kinsa Sai suka qara fito da hasken fatarsa sosai....
Cak ta tsaya jikinta na'dan rawa sbd Sam batayi tsammanin ganinsaba kallo daya tamasa tayi saurin 'dauke idanuwanta cikin nasa tareda saurin qarasowa ta aje zata juya suka qara hada ido ya dauke Kai t
areda tsuke fuska
Komawa tayi ta 'dauko sauran abincin tadawo wannan karon yabar gurin Yakoma tsakiyar palon ya zauna Kan kujera.
Sake hada idanu sukayi murya na rawa tace,
Ina kwana?
'daga power horse din hannunsa yayi yakai baki baiko kalli i
nda takeba bare ya amsa.
Harara ta watsa Masa tareda turo baki Aiko Sai Akan idonsa
Wani kallo yasako Mata zai dako Mata tsawa tun kafin maganar ta fito ta fice da sauri tana cewa,
Ni kullum da masifaffi Allah ke hadani hunnn.
Tun safen kamalu keso
n ganinta ta lafe cikin daki raqi fitowa yayita Aiko asabe tayi biris taqi zuwa
Sai Da yamma zayyan yazo ya Aiko kiranta tafito cikin doguwar Rigar blue atampa da qaramin hijab.
Kallonta yayi cikin kulawa suka gaisa tareda Yar fira sama sama ya wuce
part 'din saheeb.
Part din mum asee ta wuce Dan dubo asabe dataita zaryar dubata kwana biyun.
Tana shiga taji an fixgota da qarfi tareda jefota tsakiyar palon saidata bugi centr table gefen bakinta ya fashe ta 'dago da sauri taga Kamal yana wani irin
huci kamar zai buga ya sake damqo gashinta dake cikin hijab da qarfi cikin 6acin Rai yace,
You ingreat bitch so nawa Zan fa'da Miki Babu shegen dazaki kula bayan ni Amma kinqi ji
Bakisan rufa Miki asiri ne zanyiba na taimaka muku keda that bastard th
ing you called son
Ke bandama qaddara mezanyi dake da bastard son dinki.....
Cikin baqin ciki da hasala ta katsesa tareda miqewa tsaye tace,
Karka qara Kiran yarona da shege sbd ba shege bane Dan haka ka janye tausayi da taimakonmu dazakayi ka rufa
Mana asiri sbd har abada bana buqatar taimako ko tausayawa daga gareka afterall Mena sama yaci bare yaba na qasa,,,
Karka Kuma Kiran sunansa sbd inason abuna ahaka duk da Yana shege Zan iyayin komai akansa Dan kuwa dakasan yanda nasamesa naci wuya akansa
na yafe gatana sunana mutumcina da iyayena akansa nazo Nan nasan zaka tabbatarda idan nace maka Zan iya komai akansa zaka yarda Dan haka karka Kuma shiga rayuwata da yarona bakasan wacece Anano ba
Yaron dakake Kira bastard yafika Dan kuwa Bai dauko halay
en shegunba ko 'daya saima Kaine kakeda kaf halayensu harma.......
Hannu ya 'daga a zafafe zai wanketa da Mari mum asee ta riqe hannunsa tanabin Anano da wani irin kallo Dan dama tana palon zaune itada Kamal kafin ananon tashigo....
Lallai dama ance
'dan iska na qauye...ta fa'da cikin zuciyarta
Taji zafin maganganun ananon sosai Amma qarfin zuciyarta da iya fitsararta tareda son datace tanayiwa shegen 'danta zatai komai dominsa su zatayi amfani dasu tayi amfani da ananon ta jefi tsuntsu biyu da duts
i daya,,,ta cimma burinta,,ta wargaza ananon bayan ta sheqa shegen danta lahira..
Murmushi tasakarwa ananon bayan ta sauke hannun Kamal tareda cewa,
Bakada hankaline zaka daki mace
Kai kullum cikin zafin Rai da rashin hakuri..fice kaban guri mutumi
n banxa kawai.
Kallon mamaki yabi mum din dashi tamasa alamar ya wuce
Ya wuce Yana qwafa kamar zai tashi sama.
Kamo hannun ananon tayi suka zauna a kujera ta kalleta tace,
Karki saka alamarin Kamal arai haka yake kamar Mai shaqar cocaine.
Mama
kine yakama Anano ganin yanda mum asee ta sakar Mata tasan akwai abunda zata qulla
koma meyene zatabita yanda takeso.
Murmushim yaqe tayi tana goge gefen bakinta da tissue dinta mum asee din ta miqo Mata tace,
Bakomai aina Saba da halinshi zuwa yan
xu.
Mamakin Anano mum asee tasakeyi ganin yanda take Kai tsaye tayi murmushin mugunta tace shege baqauye...kafin ta fuskanci ananon dakyau tace,
Kince kinason 'danki,,,bakyayi Masa sha'awar kyakkyawar rayuwar hutu da ingantaccen ilmi da Jin da'din ra
yuwa..
Kallon mamaki Anano tayiwa mum asee
Mum asee tace,
Eh sbd naji kince zakiyi komai akansa..
Ina Masa addua da fatar hakan...
To idan nace Miki ga damafa Wadda zakiyi arziki 'danki yayi sunan Mai arziki hakama akiraki da uwar 'dan Mai arz
iki
'danki yayi kyakkyawar rayuwa yasamu ingantaccen ilmi...
Zaro idanuwa Anano tayi
mum asee tasaki wani shi'umin murmushi tana cewa,
Yes idan har Zaki iya tsayawa kice saheeb shine uban 'dan shegenki,
Ki tsaya kice shine yamiki cikinsa Kika haif
esa.....
Miqewa tsaye tayi da sauri tsoronta na fitowa qarara Dan Bata ta6a kawo wannan shine abinda mum asee zata fa'daba..
Zaunar da ita mum asee tayi tace,
Kar kiji tsoron kowa idanhar Zaki iya nizan tsaya Miki akomai.
Tana kallon tsakiyar i
danuwan mum asee 'din cikin tsananin mamaki tace,
Meyasa zance 'dana 'dansa ne...?
Sbd samun cikakken iko akan dukiyarsa...
To ai a musulunce 'dan shege baida gadon ubansa...
Ba wannan Zaki dubaba yanxu cigaban 'danki da naki Zaki Duba.
'dan
a bazai ta6a samun iko daga dukiyarsa ba Dan ance 'dansane tunda ba aurene atsakaninmu ba..
Aurenki zaiyi.....
Miqewa tasake yi cikin tsananin mamaki da fa'duwar gaba da zancen yasata.
Muryarta na rawa tace,
Ta Yaya?
Ta nice Zan saka ubansa
yasashi aurenki Dole sbd yayi Miki ciki kin haihu...
Cikin 'daga murya takatseta da cewa,
Duk menene dalilin dazaisa ayi hakan.
Murmushi tasaki tareda miqewa tana kallon ananon da tuni zufa yafara jiqata sbd tashin hankali tace,
Dalilin hakan s
hine Ina buqatar takardu ahannunsa Kuma bazan ta6a samunsuba Dole saita hanyar matarsa.....
Girgixa Kai Anano tayi idanuwanta na cikowa da hawaye murya na rawa tace,
Bazan iya ba..
Zaki iya.
Bazan iyaba ki aura Masa yakurah.
Dole Sai kece za
kiyi sbd 'dankine zai Zama dalilin auren.
Bazan iyaba"""ta fa'da hawayen idanuwanta na gangarowa sbd mum asee tafara wuce tunaninta.
Janyota tayi da qarfi tareda cewa,
Dolene kiyi idanba hakaba Zaki 'dauki gawar shegen 'danki da gwaggonki a hannun
ki Dan bazakiji sirrina abanza ba.....ta bu'de qofa ta hankadata waje da qarfi ta kife a qasa.
Qafafun mutum tagani agabanta ta 'dago da sauri gabanta na fa'duwa tayi Ido biyu da zayyan fuskarsa ta ka'da tayi jajir..
Miqewa tayi jiki asanyaye tareda su
nkuyar dakai zata wuce ya sha gabanta tareda nuna Mata hanyar gym room 'din saheeb da hannu fuska.
Ganin yanayinsa ba sauqi yasa ta nufi inda yake nuna Mata Dan tsoron karta Kuma Shan azabar dazata sakata rasa idanuwanta.
Suna shiga ya rufe qofar tar
eda zaunawa Kan wani machine ya dafe kansa idanuwansa na qara canzawa...
Rakubewa tayi cikin tsoro duk da itama tana cikin tashin hankalin.
'dagowa yayi ya kalleta ciki wani irin yanayi yace,
Me saheeb yayi muku arayuwa dakuka za6i Zama masu farau
tar dukiyarsa da rayuwarsa....
Girgixa Masa kai tayi cikin sanyin murya tace,
Qaddaratace takawoni Nan Kuma nasan qaddara zata daukeni daga Nan din sbd na fado cikin mutanen daban ta6a ganiba arayuwa,,,,,
Qaddarar taimako ita tarabani da komai naw
a harna kasance cikin wannan mummunan halin...
Kuka tasaki ahankali tana cewa,
Tabbas zasu kashe gwaggo da abdul matuqar banyi abinda sukaceba sbd nasan zasu iya fiyeda hakan Dan sunsha yi.
Kallonta yayi tereda matsowa ya fuskanceta yace,
Tabba
s tun farko nayi zargin cikin gidannan basa qaunar saheeb sbd abubuwa da dama Amma bantaba tunanin hakanba...
Cikin qureta da Ido yace,
Waye yasa abisu Abba last time?
Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta Dan batason shiga wata masifar bayan Wadda
take ciki yanxu
Yanda ya tsareta da jajayen idanuwansa yasa ta bu'de baki ahankali murya na rawa tafara zayyano Masa komai ta 'dora da fa'din ,
Sun kashe matar saheeb da Mai aikinsu hakama Abba na cikin layi nasan zasu iya kashe gwaggo da abdul bazan i
ya zamaba tafiya zamuyi..
Dafe kansa yayi Yana karanto innalillahi sbd zancen ya girgixasa matuqa musamman mutuwar nafeesa.
Cikin rawar murya yace,
Idan tabbas nafeesa kasheta akayi da ciki ajikinta shima sun cire..
Dagowa tayi takallesa gabant
a na tsananta fa'duwa.
Bazaki je ko'ina sbd duk inda kikaje zasu biki.
A tsorace ta 'dago hawayenta na qara gudu tana girgixa Kai tareda ficewa da sauri tana sakin sabon kuka.
Vote
Comment
Share
*_EZNAH_*
🌹
_wattpad@mamuhgee_
*25*
Zuciyarta taji tana sake kar6ar komai ta bu'de idanuwanta ahankali tareda kallon zayyan tayi shiru batareda tayi maganaba....
Shima ita yake kallon yace,
Trust me Anano I will never let anyone hurt you,,,,
I will never let any harm cme to
you insha Allah....
Saheeb is my only family my only friend...
Muna secondary School na rasa both mum Dina da dad,
Saheeb shine yaci gaba da daukar nauyin karatunmu harmuka gama muka shiga military school.....
Saheeb has always been there for me harn
akawo matsayin danake dashi yanxu nazamo wani.
Saheeb tun Yana yaro yataso cikin wata irin rayuwar kadaici da Rashin farin ciki sbd tsawon rayuwata da saheeb banta6a ganinsa cikin farin cikiba,,,,,
He was living a loneliness life,,,
A with no one to c
are or been there for him,
Tun muna yara Sam shi ko wasa bayayi sbd that witch woman tariga ta kashe Masa rayuwa and Abba is always busy he has no time for him,
Baisan damuwarsa ba,baisan buwatarsa ba,baisan ciwonsaba baisan farin cikinsa ba..
Nafeesa
t in his life was the only first good thing that happens to him sbd yafara hangowa kansa sauyin rayuwa,rayuwar farin ciki da iyalansa sbd samun cikinta changes alot Amma saigashi lokaci 'daya sun rabasa da wannan farin cikin, again he lost all hope haryana
tunanin baya cikin masu rayuwar farin ciki a duniyar nan....
Anano Insha Allah kece hasken rayuwar saheeb daya Dade baizoba,
Kallonsa tayi idanuwanta na bushewa Jin irin rayuwar da saheeb ya 'debo shekaru yanayi haryanxu..
Share hawayenta tayi ci
kin wata irin murya tace,
Kamar yanda tafada Zan tabbatarmada gaskiyar hakan datace lallai 'dan iska na qauye..
Kallonta yayi ganin yanda tayi maganar koba komai tafara soye zuciyarta Wanda Dole saita cire duk wani tsoro ta qeqashe zuciyarta kozata i
ya hakan
Hakama Dole zata cigaba da karatu sbd samun cikakken ilimin dazata iya kane kane da dukiyar tahana kowa iko da ita sbd har Abba Dole zai shiga layi coz idan ba haka mum asee zata riqa amfani dashine tana samun yanda takeso...
Kodata suka rab
uda zayyan tadawo 'daki ta 'dauki abdulshakur dake wasa ta rungume jikinta tareda lumshe idanu tanajin sabuwar qaunar yaron nashigarta sbd taqara tabbatarda shine qaddararta tunda samunshi shine mafarin komai...
Kallo 'daya gwaggo tayi Mata ta 'dauke K
ai sbd ita alamarin Ananon yadaina Bata mamaki.
Da daddare harta kwanta Amma takasa bacci
Zuciyarta takasa samun sukuni Sai azalzalarta takeyi akan tunda tana zargin zamowar Abdul 'dan nafeesat to tabbas idan batai bincike ta tabbatarba to Sam baymtay
iwa Abdul adalciba..,
Meyasa tasawa Abdul suna abdulshakur sbd mahaifiyarsa ta fa'da Mata sunan mahaifinsa ne....
Tashi tayi zaune gabanta na tsananta fa'duwa tareda saukowa ta nufi akwatin kayanta ta bu'de ta fiddo komai kafin taciro wani qyalle ta wa
rware zobenda uwarsa tabata ya bayyana..
Qurawa zoben idanuwa tayi tanajin fargaba nacigaba da shigarta ta rintse idanuwa tareda miqewa ta fito dakin ahankali...
Qurawa qofar kicin dinsa idanuwa tayi na tsawon mintuna tana qara qame zoben dunqule aha
nnunta..
Cikin fargaba da wasi wasi ta nufi qofar ahankali takama handle din ta bu'de tareda shigewa....
Kamal da dawowarsa kenan daga yawonsa a buge yake Amma duk da haka saidaya zagayo da niyyar nemanta cikin Daren danya lallasheta Sai kawai yaga s
higewarta qofar kicin din part din saheeb na bayan....
Ransane yayi mummunan 6aci zuciya ta ciyosa ya juyo Yakoma part dinsu mum asee yaci sa'a palon ba'a saka key taciki ba...
Kicin ya nufa direct yafara 6arin Kaya gurin neman wuqa Dan ya'dau alwash
in kashe saheeb yau kowama ya huta....
Yakurah cikin bacci taji 6arin Kaya ta zabura zaune