Showing 9001 words to 12000 words out of 59902 words
tana adduar Allah yasa ba anan gwaggon zata
zauna da itaba sbd Allah yagani arayuwarta ba abinda ta tsana take tsoro irin soldier.
Baffa ma Kam wani irin mugun yawu ya ha'diye na tsoro da tausayin ananon Dan shima Kam Yana tsoron kaki( kunsan Fulani da tsoron soja
😂😜
just kidding)
Usman dama
shi tuntuni atsure yake tunda suka iso yaga mutane sunyi Masa yawa Dan harwani jiri jiri yake gani Dan baita6a fitowa birni duk cikinsu jafar ne kawai Mai zuwa shima sbd visiting din ananon ne idan tana makaranta.
A darare suka Isa bakin gate din kusan
atare suka 'dan sauke ajiyar zuciya ganin ba soja ko 'daya days saura.
Cikin Yar fargaba jafar ya qwanqwasa qaramar qofar qatoton gate din dayake jabiru na kusa Yana hamdalar samun yancin aikinsa oga saheeb Yakoma da gayyar sojojinsa.
Bu'de qofar yay
i Yana ganinsu ya fito tareda jawo qofar Yana kallonsu a 'dage sbd daka gansu kaga fulanin qauye futuk ananon cema ta'dan banbanta ka'dan acikinsu.
Ganin irin kallon dayake musune yasa jafar jiki amace yace,
Dan Allah gwaggo hinde muke nema.
Sake
kallonsu yayi dakyau kafin yace,
Wa za'a cemata sunxo?
Kacemata baffa salisu ne yayanta daga qauye tareda Anano.
Juyawa yayi yashige tareda maqala sakata ya nufi babban part 'din oga saheeb.
Zagayawa yayi ta qofar baya inda 'dan qaramin boys qu
arter din part dinsa Wanda ke 'daukeda Palo 'daya da room daya Sai toilet.
Ta qofar kicin din part dinsa zaka it's fadawa direct palon gwaggon Wanda anyi hakan ne Dan aikinta basaita zagayo ta qofar paloba Kuma nafeesa ce tasa akai Mata hakan sbd tsanan
in qaunarta da gwaggon hakama shima saheeb sosai Allah yasa Masa qaunar gwaggon da ganin girmanta.
Qwanqwasa qofar palon zaiyi saigata ta fito zataje can 6angarensu mum asee.
Da mamaki take kallonsa tace,
Mal jabiru lafiya naganka nan....
Baqi
kikayi sunce baffa salisu da anono ne koma meye sunan na manta....
Da sauri ta nufi gate din cikin farin ciki dakuma fargabar Allah yasa lafiya wannan zuwa haka.
Shigo dasu tayi har cikin boys quarter palonta inda baffa daqyar ya zauna takawo musu ru
wa suka gaggaisa baffa yace,
Dagacan muke gidanki aka kawo mu Nan.
To hamma salisu Allah dai yasa lafiya.
Anano ya nuna Mata ta waigo Sai alokacin ta lurada 'da ahannunta.
Zaro idanuwa tayi tana sake kallawa danta gasgata idanuwanta tace,
Na
boni ni hindatu menene wannan ahannunki Anano.
Ba yanda kike tunani bane Nan dai yayi Mata bayanin komai ya 'dora dacewa,
Nakawota da kainane danta zauna agurinki idan komai ya lafa saita dawo.
Badan zuciyarta tagama aminta da zancen 'dan bana An
ano bane jiki amace tace,
To shikenan zanyi magana da Mai gidan idan ya amince saimu zauna anan idan bai aminceba zamu koma gida Dan dama jiya da'akai kwana bakwai da rasuwar Mai 'dakinsa naso tafiya yace nayi zamana anan harsai yace na tafi.
Ba yand
a bataiba dasu su tsaya suci abinci sukaqi musamman Usman da yake a firgice kamar ace qyat ya ruga da gudu.
Har titi suka rakasu suka tafi Anano da baffanta kamar karsu rabu musamman dayaga tana kuka ahankali.
Tundaga gida dama gwaggo ta kar6e 'dan t
agoyasa shiyasa Koda suka juyo ananon ke tafiya ahankali tana share hawaye jitake kamar karta koma gidan.
Suna shigowa direct part din mum asee suka nufa Dan Inna ta gabatarda ananon daidai zasu shiga Kamal shikuma yafito cikin sauri zai fita saiji yai
yayi karo da mutum ba zato.
Please ku ringa saurarawa kuga menene zai faru kafin ku ringa magana akan abinda yadace da Wanda bai daceba afterall karku manta novel ne is not reality so Dole wasu abubuwan zasu banbanta da reality so please take note
#no bad comments ko Kuma judgen abinda bakusan qarshensa ba Dan bakusan me writer ta shirya rubutawa agaba ba...
#vote
#comment
#share
*_EZNAH_*
🌹
_wattpad@mamuhgee_
*17*
Ja baya yayi da sauri cikin 'dan 6ata fuska Yana qare
musu kallo.
A 'dan ladafce gwaggo tace,
Yi hakuri kamalu Bata lura dakai bane baquwace duk a takure take shiyasa.
Kallon ananon yayi tundaga sama har qasa Nan take idanuwansa suka kyallo Masa kyanta da dirinta dazai fita matuqar tasamu kyakkyawar ra
yuwa musamman dogon hancinta daya qarawa fulani face 'dinta kyau da tsari.
Wani gajeran murmushin gefen baki yasaki tareda 'dan sakin fuska ya maido kallonsa kan gwaggon yace,
Baquwar waye cikin gidan?
Washe baki gwaggo tayi tace,
Eh wlh 'yata
ce 'yar gurin yayana da muke uwa 'daya uba 'daya tazo guri nane Zan kaita ta gaida hajiya babba.
Wucewa yayi da sauri sbd Kiran daya shigo wayarsa Yana cewa,
Ki shiga idan nadawo xan gaisa da ita.
Murmushi gwaggo tayi sbd Sam kamalu yafi yayansa s
aheeb sakewa dason mu'amala da mutane Kuma gidan kaf yafisu rashin qyamar mutane Ammafa kaf yafisu rashin imani da tausayi Dan komai na uwarsa mum asee bai baroba.
Itadai Wani yawu Anano ta ha'diye daqyar tareda saurin sauke kanta qasa sbd wani kallo da
ya jefeta dashi daya mugun fa'dar Mata da gaba.
Da sallama suka shiga palon Nan Anano taga kyau da tsari tareda uwar dukiya na aka narka a palon ta sake sauke kanta qasa sbd itadai zuwa lokacin jitake Sam Zama a hannun gwaggon yafita ranta sbd yanda tak
ejin fa'duwar gaba da wani irin tsoro irin yanda ta riqa ji lokacinda qaddarar samun abdulshakur zata sameta,.
Kicin gwaggo ta nufa gurin asabe suka gaisa tace,
Ga 'yata na kawo ta gaida hajiya
Anano matso gaida asabe itama aiki takeyi anan 'din.
Cikin sanyin murya tace,
Ina wuni.
Lafiya qlau ya Kika baro mutan gida?
Lafiya qlau'''"tace atakaice.
Saukowar mum asee ne daga sama yasa gwaggo fitowa ananon na biyeda ita kamar jela suka zauna qasan kafet gwaggo na sake gaisawa da mum asee '
din itama Anano murya na rawa ta gaidata Sai alokacin mum asee ta lura da ita ta tsaida kallonta akanta tsawon mintina ka'dan kafin ta 'dauke Kai zuwa kallon tv tace,
Gwaggo hinde wacece wannan Kuma?
Hajiya 'yatace tazo daga qauye sbd wata Yar matsal
a data samu acan shine nakeson koza'a Kira abdulshakur a sanar Masa zankoma gida.
Qaramin tsaki mum asee taja batareda tasake juyowa gurinsuba tace,
Basai ankirasaba sbd ba da'dewa zaiyi yadawoba kuje idan yadawo kinyi magana dashi koba komai Ina nem
an sabuwar Mai aikin dazata riqa kularmin da tsaftar Nan sbd asabe ayuka sun fara Mata yawa batamin yanda nakeso.
Hawayen takaici ne suka taru a idanun anano Jin Wai zatai aikatau agidan.
Gwaggo ma jiki asanyaye tace,
To shikenan hajiya Bari muje
ta'dan huta taci abinci zuwa gobe tafara aikin.
Bata kallosuba bare ta amsa taci gaba da abinda takeyi na qoqarin canza tashar DStv.
Jiki ba qwari suka miqe suka koma dakin gwaggo
Daqyar tasa ananon taci abinci tayi sallah tasakeyin wanka gwaggoma
tasauke abdulshakur tayi Masa Anano. Tabasa madararsa dasukazo da ita ta fulani.
Washe gari tunda safe mum Asee ta Aiko aka Kira Mata ananon jiki asanyaye ta tafi
A dining ta tarar da ita batareda zaune tareda wata kyakkyawar budurwa black beauty tana
waya,
Batareda takalli gefenda ananon take ba tace,
Asabe ki nuna Mata ayyukan dazata Kama Miki dasu Kuma ki tabbatarda kin koya Mata Dan kartamin 6anna dankifi kowa sanin bana 'daukar qaddara.
Tunda asabe tafara nuna Mata ayyukan dazata yi taji ha
nkalinta yayi mummunan tashi Dan ita Koda take qauye Yar gatace Bata Saba da wahalaba Amma data tuno Dan abdulshakur dinta zatai saita fara qoqarin farawa.
Ahankali take aikin cikin nutsuwa sbd gudun banna kotai ba daidaiba.
Tana cikin mopping palon
Kamal yashigo yana waya ransa kamar a 6ace ba zato yaji sul6in ruwan data cika gurin mopping din ya jasa saura qiris ya Fadi yakurah data kawo gurin tai saurin taresa tana cewa,
Hey careful.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda juyowa ya qurawa fuskanta da
tuni tayi wani iri sbd fargaba murya a sanyaye tace,
Yi hkr bansan ya zanyi bane ruwan ya bushe da wuri.
Danne tsananin 6acin ransa yayi sbd qudirin daya qulla akanta tun jiya daya fara 'dora idanuwansa akanta yasaki murmushi yace,
Ba komai kawa
i dai ki kiyaye gaba Kuma ki Kira asabe ta qara Miki qarfin AC sbd ya bushe da wuri.
Kallonsa yakurah tayi dakyau cikin mamaki sbd tsaf tasan Kamal Dan iskane na qarshe matuqar baida wata manufa akan wannan yarinyar bazai sakar Mata wannan murmushin ba.
Anano kuwa suna wucewa tabi bayansa da kallo cikin mamakin sanyin halinsa.
Sai guraren azahar tabaro sashen tana shigowa ta fa'da toilet din gwaggo tayi wanka daidai Nan abdulshakur dake kwance a katifa ya tashi daga bacci tayi sauri ta shirya ta da
uko madararsa tabasa tasake yi Masa wanka duk da dai ba Sosai ta iyaba.
Wasa ta ringa Mai duk da dai jaririne baisan tanayiba saidai ya bu'de idanu kawai.
Sannu ahankali tafara sabawa da aikin gidan duk da iko da duk wani Shan qamshin mum asee tu
ni tafara sabawa dashi hakama yakurah Sam ba ruwanta da ita saidai idan zata sakata aiki takira shima tana gamawa take tafiyarta sbd ko kallon arziki Bata Mata.,
Ta 6angaren girki ma itada asabe ne sukeyi yanxu sbd tanason iya ayyuka da dama sbd agida can
qauye ko shara batayi bare ta iya wani aiki,
Sunyi sabo da asabe sosai duk da ta girmeta Amma tanajin da'din fira da ita musamman idan tana koya Mata aiki tana Bata labarin kyawawan halayen matar gidan data rasu.
Gwaggo kuwa sosai ta maida hankali g
urin taimakawa ananon gurin kulada abdulshakur sbd ganin ba laifi ta saki jiki tana 'dan Jin da'din aikin datakeyi duk da dai tuni abdulshakur din yadara wayo yafara gane itace uwarsa Dan kusan tsawon wata hudu kenan da zuwanta gidan Kuma har lokacin sahee
b baidawo ba Yana Lagos ayyuka sun Masa Dan yawa Kuma dama bason dawowar yakeba.
Ta 6angaren Kamal kuwa tuni wani irin sabo yafara shiga tsakaninsu Dan kuwa wata irin kulawa da mutumta yakeyi ga hidimar siyayyar Kaya dayake Mata kusan duk yafita.,
Haka
nne yasa ahankali batareda ankareba soyayyarsa Mai tsanani tashige zuciyarta Wanda tuni yagano hakan Dan dama hakan shine burinsa.
Yau bayan tagamo aikin girkin Rana tashigo 'dakinsu ta tube tayo wanka tana cikin saka Kaya Mai gadi yazo ya sanarda gwagg
o zuwan jafar da baffa Aida sauri tagama sako kayan tasa hijabi tafito itada kanta taje gate tashigo dasu jikinta har rawa yake sbd tsananin farin cikin ganin baffanta da hammanta jafar.
Baffa kasa rufe baki yayi sbd tsananin farin cikin ganin yanda ana
nonsa ta canxa hankalinta ya kwanta ga abdulshakur shima yayi wani irin girma gashi farine sosai shima Wanda hakan zaisa kace 'dantane.
Sunci abinci sunyi fira sosai kafin suka miqe suka fita sukayo sallar la'asar a masallacin gidan suka fara Shirin kom
awa gida.
Har titi Anano ta rakasu jafar na riqeda abdulshakur Yana Masa wasa Sai dariya yakeyi kamar dama can yasansa.
A gabansu motar Kamal ta tsaya ya sauke glass Yana kallonta tasaki murmushi tareda yin qasa dakai tace,
Su baffanane sukazo.
Saurin fitowa yayi ya gaida baffa harda 'yar rusunawa kafin ya miqawa jafar hannu suka gaisa Sai alokacin idanuwansa suka sauka kan abdulshakur dake hannun jafar yaji gabansa yayi mummunan fa'duwa sbd hakanan saiyaga kamar idanuwansa na nuna Masa kamar ya
ron da kusan mutum uku na farko kamar nafeesat sbd Dan qaramin bakinsa da fa'din fuskarsa,
Saiyaga kamar Kuma saheeb sbd dogon hancinsa da manyan idanuwansa masu maiqo aciki Sai kuma Anano da kalar fatarsu take iri daya har yellow yellon.
Fa'duwa gaban
ta ya'dan yi sbd ganin yanda yake kallon abdulshakur Dan haryau ba Wanda yasan da akwai 'da agidan.
Cikin sakewar fuska yace,
Muje na sauke ku Tasha Mana.
Aa baffa yace Yana tsayarda Mai adaidaita dayaxo wucewa.
Shiga sukayi jafar ya miqo Mata
Abdul suka wuce.
Kallon kallo suka shigayi tsakaninta dashi ya daure yace,
Yaron waye....
Sunkuyar dakai tayi cikin sanyin murya tace,
Dashi nazo.
Wat"""yafada Yana kallon yaron yace,
Yaron nanfa na hannunki nake magana..
'daga Masa Ka
i tayi tace,
Eh dashi nazo dama tunfarko.
Shiru yayi baisake cewa komaiba ya wuce yashiga motarsa ya nufi gida.
Itama wucewa tayi na nufi gidan jiki a sanyaye.
Washe gari da safe suna cikin breakfast ya dago ya Kalli mum asee yace,
Mum Anano
nada 'da Wanda ta Haifa..
Ruwan tea ta kurba tareda Kai plantain bakinta tace,
Toni meye hadina da wannan zancen.
Yakurah tace,
Dama tun farko Mai kake tunanin zaisa atattarota akawo wani gurin idanba samun shegeba.
Cikin 'danjin haushi yac
e,
Ba haka nasoba Amma ko ahakan ba matsala Zan canxa tsari.
Tundaga lokacin ya canxa tsari ta hanyar nuna tsananin kulawa da qaunarsa ga abdulshakur Dan kuwa har Kaya yake siyo Masa Nan take kuwa yaqara samun kyakkyawan mazauni a zuciyarta ta yanda
takejin zata iyayi Masa komai matuqar bai kaucewa addiniba.
Yau tana fitowa da safe Dan zuwa aikinta taga sojoji kusan guda biyar a harabar gidan da Kuma sabbin motoci guda biyu.
Yawu ta ha'diye da cikin fa'duwar gaba tareda dauke Kai Dan itadai
tana matuqar tsoron soja
Da sauri ta qarasa ta shige palon tareda sauke ajiyar zuciya.
Kicin ta nufa ta ha'da breakfast sbd yau asabe ce zatai shara da mopping.
Tana gama hada komai ta jera a dining mum asee ce tafito cikin sanyin jiki fuska duk a
kumbure ga idanuwanta dasukai wani laushi sbd rashin bacci data Hana kantayi sbd mugun nufinta.
Kallon Anano tayi da qyar tana Zama a kujerar palon tace,
Bani black coffee Mai zafi yanxu.
To tace tareda komawa kicin din.
Cikin nutsuwa da wani i
rin kwarjinin ya shigo palon Kamal na biyedashi Yana Masa bayanin rashin lafiyar mum asee da rashin cin abinci datake na damuwar rasuwar da haryanxu takasa cirewa aranta.
Wandon uniform dinsa ne ajikinsa Sai farar shirt shade na warby parker da wristwat
ch na yazole,
Nan take qamshinsa turarensa na signature da clinic for men spray yacika palon.
Kamshin nashiga hancin mum asee ta lumshe idanu wani irin duhu da mugun tirir na shiga zuciyarta sbd tsanarsa da baqin cikin ganinsa.
Gurinta ya nufo direc
t sbd sauri yake zashi wani taro Kuma shine wakiltacce dazai wakilci soldiers Kuma shine babban baqo.
Tana gama hado coffee din ta zubo a cup ta fito..
Batareda ta luraba ta Dora qafarta inda asabe ta mopping Nan take santsin sauran ruwan mopping d
in dabai busheba ya jata kafin tayi wani yunkurin tuni cup din yayi sama Sai akan farar shirt dinsa.
Ba Kamal da asabe ba kawai ko mum asee saidata miqe tsaye cikin tsinkewar zuciya.
#vote
#comment
#share
*_EZNAH_*
🌹
_wattpad@mamuh
gee_
*18*
Cak ya tsaya tareda kallon rigarsa ahankali batareda yadamu da zafin da coffee din yakedashiba.
Mum asee ta qaraso da sauri cikin kulawa ta riqo rigar ta juyo cikin fa'da tace,
Anano meyasa Sam haryanxu qauyanci da hankali tareda nuts
uwa sun kasa shiga cikin tosashen kanki?
Matsowa Kamal yayi ya riqo hannunta dake rawa sbd tsoro da fargaba ya kalli mum asee kafin ya maida kallonsa kan saheeb din yace,
Kayi hakuri natabbatarda batai da ganganciba tsautsayine.
A hannun Kamal din
dake riqeda nata yafara sauke idanuwansa kafin ya dago ya Kalli fuskarta
Nan take kallonsa yasa jikinta ya qara daukar rawa Sai kawai tasamu kanta da saurin janye hannunta daga na Kamal din tanayin qasa da kanta.
'dauke Kai yayi tareda juyawa yabar p
alon batareda yacewa kowannensu qalaba.
Da muguwar harara mum asee tabisa zuciyarta na qara quluwa cikin baqin ciki tace,
Gobe idan Zaki zuba Masa wani abu ki tabbatarda tafasasshe ne Kuma a zuciya ko fuska Zaki zuba Masa.
Cikin tsananin tsoro da
mamaki ta 'dago takalli mum asee din saitaga har cikin zuciyarta zancen yafito sbd tsananin tsana da qiyayyar data gani Yana tashi a fuskarta.
Tsaki tasaki tareda barin gurin yakurah nabin bayanta da sauri Kamal kuwa sake riqo hannunta yayi zaiyi magana
ta zame tareda barin gurin da sauri sbd wani irin a jagule takejin zuciyarta.
Tana fama gyare gurin tafito da sauri zata koma tayi wanka daidai takusa Isa part dinsu Kamal daya biyota yayi saurin riqo hannunta tareda juyo da ita sauran ka'dan ta fa'da
Masa daidai Nan shikuma ya canzo kayansa yafito idanuwanta suka sauka cikin nasa tayi saurin qwace jikinta daga Kamal tana 'dauke Kai.
'dauke Kai yayi shima tareda fadawa mota suka bar gidan a guje.
Kallonta Kamal yayi tareda 'daure fuska sosai zaiyi
magana Sai kawai ya fasa tareda juyawa zai bar gurin tai saurin Shan gabansa murya a karye tace,
Dan Allah karkayi fushi Dani.
Sake 'daure fuska yayi tareda tureta gefe ya wuce Yana cewa,
Stupid village monkey.
Binsa da kallo tayi cikin sanyin
jiki sbd taji abinda yace Amma zuciyarta takasa Jin zafin hakan saima haushin kanta dataji na 6atawa masoyinta Rai duk da dai ta lura yanxu yafara canza Mata sbd yanda yake yawan ta6ata dakuma tsawa dayake yawan yi Mata ga uwa uba zagi.
Juyawa tayi ta
wuce tana shiga 'daki a qofa taci karo da abdulshakur ya rarrafo Yana wasa.
'daukarsa tayi cikin sanyin jiki ta qarasa ciki dashi sbd Inna na kicin tana aikin abincin ranan saheeb.
Zubewa tayi a katifa tareda 'dora Abdul saman cikinta ta lumshe idanu
Abu biyu na yawo akanta,
Maganar mum asee dakuma canxawar kamal.
Har gwaggo tagama tashigo tana kwance abdulshakur ma tuni bacci ya 'daukesa ahaka.
Jin Kiran sallar la'asar yasa ta miqe tareda kwantarda Abdul ta tube tashige toilet tayo wanka tared
a alwala.
Shiryawa tayi cikin doguwar Riga baqa tareda yafa gyalen rigar ta 'dauko Abdul suka nufi qofar baya ta kicin din part din saheeb da gwaggo ke aikin yimasa abincin dare duk da kona ranar baidawoba bare yaci.
Kallon kicin din tayi sbd yafi na
su mum asee komai