Showing 45001 words to 48000 words out of 59902 words
na cikowa da hawaye ta aje tray din Kan bedside drower ta durqusa gabansa saitin fuskarsa.
Bu'de idanuwansa yayi ahankali ya kalli fuskarta
Ya qurawa hawayenta Ido nauyin zuciyarsa na qaruwa..
Hannu ya 'daga cikin sanyi ya share Mat
a hawayen,
Cikeda tsananin mamaki ta kallesa hawayenta na qara gangarowa.
Cikin sanyi da rawar murya tace,
Ga abinci.
Tray 'din ya kalla kafin ya maido da kallonsa kanta yaga yanda tai wani zuru zuru fuska akumbure jajir.
Ahankali ya tashi z
aune tareda nuna Mata kusadashi batareda yayi maganaba.
Tashi tayi ta tazauna kusada shi tareda jawo tray din ta 'dauki cup din tea ta miqa Masa tana kallon fuskarsa.
Kallon face dinta yayi kafin ya kar6i cup din tareda kaiwa bakinta
Ba musu ta bu'd
e Baki ta kur6a ahankali.,
Indomin ta 'dauka tareda debo kadan a spoon takai bakinsa ya girgixa Kai
Ta qyafta idanu hawaye suka gangaro
Ya bu'de Baki ya karba.
Ahankali suka ringa cin indomin suna Shan tea har suka cinye kusan duka duk da ba magana
r data shiga tsakaninsu saidai saqonnin idanu.
Suna gamawa ta fitarda kayan dagacan ta wuce bedroom 'dinta ta kwanta jiki amace zuciyarta cikeda damuwa da tausayinsa.
Daqyar bacci ya iya 'daukarta
Cikin Tsakiyar dare taji kamar motsi a Palo
gabant
a yayi mummunan fa'duwa ta miqe zaune tareda saukowa gadon ta fito palon ahankali saita jiyo kakarin amai bedroom dinsa
Tsinkewa gabanta yayi ta nufi bedroom din da sauri batareda takoma ta sanyo hijab ba.
Cikin toilet yake yanata yunqurin amai fuskars
a tayi jajir jikinsa ba inda baya rawa.
Da gudu ta qarasa tareda riqosa ya 'dora idanuwansa dasukai ja daqyar kanta.
Idanuwanta na taro hawaye ta kallesa kafin ta zuba Masa ruwa Yana wanke fuskarsa ahankali
Yana gamawa suka dawo bedroom ya kwanta ta
jawo duvet cover ta rufesa ta rage sanyin AC dakin tadawo bakin gadon ta zauna tareda qura Masa Ido tana qoqarin mayarda hawayenta ganin yanda jikinsa ke jijjiga sosai Yana fitarda wani hucin zafi.
Ganin yayi bacci yasa ta kamo hannunsa ahankali ta riqe
sonsa na qara karya zuciyarta.
Kyakkyawar farar fuskarsa ta qurawa idanu ganin ta fa'da sosai tayi jajir cikin kwana 'daya da yini da rasuwar abban.
Gab da asuba zazza6in ya'dan sakesa ya farka
Yana bu'de idanuwansa Sai Kan fuskarta data kwantar ba
kin pilonsa bacci ya 'dauketa
Da alama shitake kallo baccin ya 'dauketa sbd har numfashinsu Sosai yake ha'duwa.
Hannunsa ya motsa zai gyara Mata kwanciya sbd aqasa take zaune kantane kawai a gadon yaji hannunsa maqale da nata ta riqe Gam.
'dayan ha
nnun yakai ya shafo fuskarta ahankali sbd baida qarfin jiki.
Bu'de Ido tayi Sai kawai tasamu kanta dajin tsananin kunya ta rintse ido tareda qoqarin miqewa taji yaqara damqe hannunta da nasa yake ciki.
Sunkuyar dakai tayi tana qare damqe idanuwanta x
uciyarta na harbawa da sauri.
Jawota yayi yakai fuskarsa daf da Tata zaiyi magana Bata Bari taji Mai zai fa'daba ta qwace ta Fice 'dakin da gudu.
Bayanta yabi da kallo da oily eyes dinsa dasukai mugun laushi suna lumshewa.
A daddafe yayi sallar as
uba yakoma ya kwanta yanaji zazza6insa na dawowa Dan yanda kansa ke Masa nauyi.
Tana Gama sallah ta fito ta nufi kicin ta ha'da Masa 'dan simple breakfast takoma 'daki Tai wanka ta fito ta 'dauka cikin qaramin tray ta nufi bedroom din.
Bacci yake Dan
haka saita aje abincin ta matso bakin gadon takai hannu ta ta6a goshinsa
Nan taji zafi sosai
Ta 6ata fuska kaman zatayi kuka ta fito takoma bedroom dinta ta dauki wayarta takira zayyan cikin tsananin damuwa tafada Masa halinda saheeb din yake ciki.
Ba'a 'dau lokaciba zayyan ya iso da Dr daqyar ya iya fitowa bedroom Dr yadubasa yayi Masa allurori tareda rubuta magunguna masu kyau ya wuce.
Abinci takawo Masa ta ajiye gabansa Kan table 'din dake tsakiyar palon tana qin kallonsa sbd lurada yanda yake
qureta da kallo Wanda tuntuni tagano hakan yafara zama 'dabi'arsa.
Zayyan dake kallon ikon Allah yayi gyaran murya tareda miqewa Yana cewa Bari naje daga can harabar gidan Sbd masu zuwa gaisuwa sunfara zuwa.
Yana fita takoma bedroom ta sanyo hijab'di
nta tabi ta kicin tai gurinsu gwaggo ta tararda gwaggon zata wuce gurinsu mum suka wuce tare tana riqeda hannun abdulshakur.
Kwana uku akai zaman gaisuwa aka watse Kuma tun lokacin take noqewa ganinsa saidai idan dare yayi ta lalla6a taganosa Wanda duk
zuwan datake idanuwansa biyu Amma Bata saniba.
Mum asee kuwa tunda taga yanda 'danta yakoma yakuma fa'da Mata abinda yafaru ta qara ninninka mugayen burikanta akan saheeb din wannan karon harda Anano Dan kuwa ta hangowa kanta masifa a idanuwan saheeb ga
meda Anano.
Tun bayan rasuwar rayuwarsa taqara canzawa miskilancinsa da shirunsa rashin son maganarsa ya qaru,
Gashi har lokacin lafiyarsa taqi dawowa gabaki 'daya.
Zayyan takira tayi Masa bayanin rashin lafiyar saheeb din Nan take yayi Masa booking
appointment na ganin doctor 'dinsa dake new York yafara nemar musu visa.
Ita kanta Bata saniba Sai abakin nabeela dake tsokanarta tana cewa,
Honeymoon 'dinnan fa Yana burgeni musamman yanxu danasan Sai ranarda muka ganku tunda dama saheeb sbd Abba n
e yake Zama anan.
Kallon rashin fahimta Anano tayi Mata tana cewa,
Honeymoon ana zaune qalau nida Zan fara zuwa makaranta tunda komai ya kammala registration kawai zanyi.
Miqewa nabeela tayi tana bu'de wardrobe dinta tace,
Kinyarda na qara shir
ya Miki kayan tafiya?
Da sauri ta taso tana cewa,
Aa banyardaba indai irin na wancen Karan ne.
Dariya tayi tace,
Amma dai koba komai na taimaka ko?
Harara ta watsa Mata tana cewa,
Eh ba laifi Amma dai kinsan ra'ayina.
Bata yarda da taf
iya zasuyiba Saida zayyan yakirata yasanarda ita washe gari zasu wuce.
Shirya kayanta tayi zuciyarta na Mata tunanin 'danta sbd har cikin ranta tana tsananin buqatarsa kusada ita saidai Kuma batason Yana kusantuwa sosai da saheeb yanxu tafison Sai komai
ya daidaita sbd tayi alqawarin insha Allah dasunje zata fadawa saheeb komai gameda su mum Asee
Saita fara ganin yanda zai kar6i zancen kafin ta sanar dashi maganar nafeesat da abdulshakur.
Gurinsu gwaggo tayi kusan Raba dare kafin tadawo tayi wanka T
ai Shirin kwanciya.
#vote
#comment
#share
#and follow.
[10/17, 7:00 PM]
_wattpad@mamuhgee_
*39*
Shirin kwanciya tayi harta kwanta Sai Kuma ta taso ta fito Palo ta nufi bedroom dinsa ahankali ta murda ha
ndle ta tura qofar tana kallon cikin 'dakin sbd duhu ko Ina.
Cikin san'da ta Isa gurin switch ta kunna wutar 'dakin
Zaro idanuwa cikin wata matsananciyar kunya biyu sbd ganinsa zaune a sofa idanuwansa qyar akanta
Dama yasan zatazo shiyasa,
Ciked
a kunya tayi qasa da kanta ai kawai saitaga kayan baccin dake jikinta a firgice ta 'dago takallesa taga oily eyes dinsa qur akanta da gudu tayi hanyar barin 'dakin cikin rashin sa'a ta bu'de qafarta da wardrobe tasaki qaramar qara tareda durqushewa cikin t
sananin zafi.
Akaro na farko dayayi murmushi bayan tsawon shekaru Wanda har nafeesat tayi rayuwa dashi ta rasu bata ta6a ganin murmushinsaba.
Sam baisan sanda murmushin ya kubce Masaba Dan ta matuqar basa dariyar yanda tashigo da yanda taji kunya.
Tasowa yayi ya qaraso gabanta saiyaga hawaye na gangaro Mata Sai kawai abin yaqara sashi murmushi
Duk da tana cikin azaba hakan Bai Hana tsantsar mamakinta bayyanowaba karo na farko arayuwarta dataga murmushinsa
Tasaki Baki tana kallonsa..
Hannu y
a miqa Mata daga tsayen
Ta Kama ta miqe har lokacin Bata daina kallonsa ba cikeda mamaki Dan har lokacin murmushin Bai gushe daga fuskarsa.
Bakin gado suka qarasa suka zauna tare ya juyo ya kalleta ganin takasa daina kallonsa.
Ahankali ya bu'de Bak
i murya akasance yace,
Kina mamaki ko?
Kai ta 'daga sbd bakinta ya mutu bazata iya maganaba.
I'm also surprised, after so many years I've found my smile again,.
Sunkuyar dakai tayi batareda tace qalaba sai qafarta datake tabawa gurinda ta buge
.
Kallon qafar yayi yakuma 'dauke Kai sbd ganin fararen santala santalan cinyoyinta a fili sbd rigarta iyakacinta kwatan cinyarta.
Lurada hakan yasa ta miqe ahankali cikin sanyin murya tace,
Saida safe.
Miqewa yayi tareda miqa Mata hannu ba mus
u ta miqa Masa suka fita tana 'dingisawa ya rakota har qofar bedroom'dinta ta shige ya juya Yana mamakin kansa.
Washe gari Sai qarfe takwas ta fito Palo taci adonta cikin Riga da skirt na turkie brown da lopas coffee brown ta nado gyalansu akanta Kar it
ama 'yar turkie dince.
Shida zayyan ta gani a palon suna maganar wasu takardu da ake buqatar saka hannunsa.
Gaisawa tayida zayyan yana tambayarta abdulshakur.
Mummunan fa'duwa gabanta yayi kusan atare suka saci kallon saheeb
Nantake taji hankal
inta ya tashi da yanayin dataga fuskarsa tayi sum sum tabar gurin tabita kicin tafada gurin gwaggo.
Rungume abdulshakur tayi ajikinta tanajin qaunarsa data mahaifinsa na qara shigarta.
Koda mum asee ta Aiko Kiran saheeb fuskewa yayi yace ace yariga y
a fita sbd yasan maganar Kamal ce zatai Masa wanda ita agurinta ba hakan bane wani mugun magani ne tasa aka kawo Mata daga nijar wanda zai ringa qone jininsa ahankali batareda kowa ya ganeba harsai yabi uwarsa da ubansa sbd yanxu shikadaine yayi saura Wand
a yayi Mata shamaki da samun cikar burinta.
Da gwaggo kawai tayi bankwana taqi zuwa gurin mum sbd zayyan yafada Mata mum batasanda tafiyarba sbd zata iya Hana saheeb tafiyar.
Tunda suka ha'du da safiyar fuskarsa ta canxa jiyake zuciyarsa da kansa kam
ar zasu tarwatse sbd maganar 'dan da zayyan yayi Mata.
Koda suka shiga jirgi harsuka Isa fuskarnan a tamke take ko alamar fara'a Babu.
Already zayyan yayi musu booking komai motar hotel dinsu tazo 'daukarsu takaisu hotel din.
Lafiyayyan honeymoon
suite aka Basu
Shiyafara yin wanka yayi sallolinsa yasaka kayan Shan iska ya kwashi wayoyinsa ya fice zuwa ganin Dr sbd a Daren ne yakeda appointment dashi.
Wanka tayi itama jiki asanyaye tareda yin sallah tasaka rigar baccinta ta kwanta Nan take bacc
in gajiya ya 'dauketa.
Bai dawoba Sai tsakar dare 'daukeda ledojin snacks da pizza daya siyo musu.
Jikinsa yaji ya mutu dayaga yanda tayi bacci atakure fuskarta na bayyana damuwar data kwanta da ita.
Ajewa yayi tareda qarasowa Bakin gadon ya shafa
fuskarta ahankali.
Bu'de idanuwanta tayi cikin nutsuwa ta 'dorasu akansa suna cikowa da 'kwalla.
Tayarda it's zaune yayi Yana kallon cikin idonta ta rintse idanun
Ya jawo pizza ya bu'de tareda Ciro 'daya yakai bakinta.
Ba musu ta ringa ci haida
ida taci slice uku kafin ta girgixa Masa Kai ya Bata ruwa tasha.
Tana zaune tana kallonsa yaci uku shima yatashi yaje yasako wanka da brush
Yana fitowa Tai saurin rufe idanuwanta.
Yana Gama shirinsa ya hawo gadon ya kwanta Yana kallon idanuwanta da
ke rufe dogayen eyelashe dinta daya kwanta.
Ahankali wani irin sabo da shaquwa yafara shiga tsakaninsu musamman yanda ta sake take kula dashi sosai
Nan take rayuwarsa tafara canxawa sbd yanxu ko abinci sukeci sunyi sabon ciyarda juna,
Gurin kwanciy
ama tun ana kwana kowa gefensa Amma su farka sukagansu maqale da juna harsun fara sabawa.,
Abu 'daya data lura yafiso shine tsananin kulawa da riritawa tareda son rayuwar yanci kamar turawa kotace yatashi ciki yanason rayuwar
Saita tattara ta lalace g
urin riritashi da basa wata irin kulawa ta musamman
Ga yawo da kullum suke fita yi idan ka gansu zaka dauka masoyan asaline..
Haryanxu baisawa zuciyarsa Wai sone yayi Masa mummunan kamuba sbd baitaba Jin wannan feelings din akan kowaba.,
Abu 'daya yas
ani zuciyarsa ta yarda da ita,
So da dama tanason sanar dashi komai sai Kuma taji batason 6ata Masa 'dan farin cikin dayake ciki zata Bari Sai sun dawo Nigeria...
A Nigeria kuwa tunda mum asee Kamal yasanarda ita tafiyarsu saheeb da ananon bindigewa
ne kawai zuciyarta bataiba sbd baqin ciki da tsananin 6acin rai Wanda tayi alqawarin magance komai lokaci 'daya dasun dawo.
Yau watansu 'daya a qasar
Dukkaninsu sun sauya matuqa musamman mashi dahar wata lafiyayyar qasumba ya aje data qarawa lafiyayya
r farar fuskarsa kyau da aji ga wani haske sosai daya qara.
Ita kuwa girma da cikowa ta qara tareda qarin wayewa tazamo mace Mai cikakken class musamman hips 'dinta dasuka baje daidai.
Tsaye take gaban mirror 'daure da towel fari tana waya da nabeela
tana combing dogon gashinta Dan handsfree tasaka wayar ta aje gaban mirror.
Suna cikin wayar ne yashigo 'dakin sanyeda jallabiya fara qal da hular larabawa dawowarsa kenan daga sallar isha'i.
Kallonta yake Yana qarasowa gaban mirrorn.
'daukar way
ar tayi tareda cire handsfree ta 'dora a kunne tace,
Nabeela gobe zankiraki.
Aje wayar tayi ta 'dauki comb zata cigaba ya riqe hannun Yana kallon cikin idanuwanta ta cikin mirror.
Sunkuyar dakai tayi sbd yau tun safe take ganin sauyi ataredashi Wa
nda hakan ba qaramin tayar Mata da hankali yakeba,
Har cikin ranta batason wani Abu yashiga tsakaninta da saheeb Dan zai gano Bata ta6a sanin wani 'da namijiba kenan Dole zai tsareta saita fa'da Masa abdulshakur 'dan waye.
Zame hannunta tayi tareda miq
ewa zata nufi wardrobe ya birkitota tareda matsota Yana jifanta da wani irin kallo daya karya dukkanin garkuwar jikinta.
Rufe idanuwanta tayi ahankali numfashinta na fita da sauri qirjinta na sama Yana komawa.
Qirjin nata ya qurawa Ido Nan take yaji
abinda baita6a jiba na yawo cikin jininsa
Yakai hannunsa 'daya ya dafe Mata qirjin 'dayan hannun kuwa ya riqo qugunta yaqarasa matso da ita cikin jikinsa
Still idanuwansa dasukai wani laushi suna kanta
Ta qara rintse idanuwanta tana jan 'dauke numfash
i.
#vote
#comment
#share
#and follow.
_*EZNAH*_
🌹
_wattpad@mamuhgee_
*40*
Idanuwanta data rintse ya kalla tareda shafa dogayen eyelash nata Dan suna matuqar burgesa da 'daukar hankalinsa.,
Gangaro da hannunsa yayi zuwa lips dinta d
asuke qyallin lipbalm ya lumshe ido ya bu'de cikin nutsuwa sbd nauyin dasuka fara Masa na rikidewar dasuke Dan kuwa zai iya cewa baita6a Jin wannan lafiyayyar sha'awarba.,
Ahankali yakai fuskarsa daf da tata tareda riqo Tata fuskar hancinsu na gogar jun
a ya qurawa idanuwanta dake rufe nasa idanun dasuka canza,
Ahankali ta bu'de idanuwanta dasuka fara canzawa itama
Idanuwansu suka shiga cikin na juna cikin sanyi ya 'dora bakinsa Kan nata Yana kallon cikin idanuwanta
Tanajin bakinsa cikin nata ta ruf
e idanuwanta ahankali sbd wani yanayi daya shigeta karo na farko arayuwarta.
Sam saheeb baya komai da zafi arayuwarsa
Cikin nutsuwa yaje komai shiyasa yake kissing 'din bakin nata ahankali yana zame towel 'dinta da hannunsa 'daya,
Jin saukar towel
'dinta a qasa yasa hawaye gangarowa daga idanuwanta dasuke rufe taja wani mugun dogon numfashi sbd numfashin dataji Yana qoqarin barin qirjinta sbd wani lafiyayyan ta6i daya kaiwa qirjinta
Ta zame ahankali tareda durqushewa qasa
Binta yayi qasa cikin nu
tsuwa ya 'dauketa
Tayi saurin qanqamesa tana qara rintse idanuwanta sbd kunyar batada komai ajikinta,,
Ahankali ya kwantarda ita a gadon Yana kallon face 'dinta ya zura hannu ya rage hasken wutar 'dakin sosai..
Gashinta daya barbazu ya shafo tareda
Kai hancinsa ya shaqo qamshinsa ya lumshe idanu buqatarsa na qara tsanantuwa
Ya jawo ya 'dora Kan jikinsa idanuwansa qyar akan qirjinta farare tas
Ahankali yakai hannuwansa da bakinsa lokaci Yana fidda numfashi ahankali jikinsa na fara rawa
Nan take
komai ya kunce Masa yafara 'daukar zafi zafi da al'amarin
Dan kuwa tun tana qoqarin dannewa harta kasa yayi mugun fitarda ita nutsuwarta tana Jan numfashi
Tanajin alamarin yayi zafi jikinta ya'dau rawa tafara qoqarin zamewa tana kuka ahankali
Shikuwa
Sam jiyake bazai iya dakatawaba...
Qarar ringing na wayarsane yafara tashi
Harta katse Baima saniba
Nan take aka cigaba da danno Kiran
Cikin qarfin hali tasamu ta qwace tareda juyawa ta shige cikin bargo tana fidda numfashi da sauri tareda qoqarin
daidaita numfashin.
Dafe kansa yayi Yana daidaita nasa numfashin shima kafin ya Kai hannu daqyar ya 'dauki wayar ya Duba...
Tashi zaune yayi Yana 'dan wartsakewa sbd ganin ogansu ne gabaki 'daya ke Kira.
Gyara muryarsa yayi ya 'daga wayar tareda
gaishesa cikin nutsuwa da girmamawa,,
Dafe goshinsa yayi Yana karanto innalillahi cikin zuciyarsa sbd Jin abinda umarnin gaggawa dayake basa na ana nemansa a gaggauce qasar Romania gobe.
Yana aje wayar ya rintse idanuwansa dasuka qanqance sukai ja sb
d urged,,
Ahankali ya miqe ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwan 'dumi..
Hawayene sabbi masu 'dumi suka gangaro Mata sbd taji wayarsa.
Koda yafito yitayi kamar tana bacci ya shirya cikin kayan bacci yazo ya kwanta bayan yayi booking flight 'dinda
zaibi goben ta wayarsa ya kashe wayar tareda jawota jikinsa Yana sauke ajiyar zuciya har bacci ya 'daukesu.
Tunda sukai sallar asuba ta shirya Masa kayansa ta shirya nata sbd itama jirgin ranar zatabi takoma gida.
Jikinta duk a sanyaye takeyin aikin
Yana lure da ita
Tana gamawa ya jawota jikinsa tareda zaunar da ita Kan qafafunsa ya riqo fuskarta Yana kallon cikin idonta yace,
Zaki bini?
Girgixa Kai tayi hawayen datake dannewa na gangaro Mata.
Hawayen ya kalla sbd Shi kullum yaga hawaye mama
kinsu yake yanda shi basa fito Masa koda zai ringa rage ra'dadi da quncin zuciyarsa
Amma ita nata mamakin zafinsu yakeji sbd itace ke fitar dasu shikuma shine Mai Jin zafinsu cikin qirjinsa.
Hannu yasa yana goge Mata ta sunkuyar dakai tareda shigewa ci
kin jikinsa ta kwanta tareda zura hannayenta ta zagayosa ta rungume.
Ajiyar zuciya yasaki tareda sake shigewa da ita jikinta Yana rufe idanuwansa.
Wanka sukayi sukai Breakfast daqyar suka ciyar da juna suka shirya mota takaisu airport.
Zama sukayi
jiran kowa Akira flight 'dinsa tana kwance cikin jikinsa hakanan dukkaninsu bamai farin ciki,,
Jirginsa aka fara Kira ta 'dago ta kallesa taga kamar baida niyar tashi ta 'dago daga jikinsa tareda miqa Masa hannunta ya kama suka tashi tsaye ya juyoda it
a suka fuskanci juna Yana jifanta da wani irin kallo daya qara karya