Showing 3001 words to 6000 words out of 59902 words
an fixgota da qarfi a tsorace ta bu'de baki Anano tayi saurin rufe Mata baki t
areda sake janyo haki ta rufesu.
Rintse idanuwa nafeesat tayi tareda sakin Wani azababben kuka tana toshe baki sbd azabar datake tsananin ji cikin mararta musamman yanda takeji ruwa nabin qafafunta.
Cikin tsananin kuka da tausayi Anano ta riqe hannun
ta sbd ganin mummunan halinda take ciki Amma ba halin wani motsi.
Ganin kamar nafeesar zata iya rasa ranta sbd yanda tafara mimmiqewa tana wata irin jijjiga yasa ta leqo kanta bataji motsinsu ba ta fito tareda kamo nafeesar suka fara gudu duk da nafeesa
r Bata iyawa sosai.
Gasu can ku kamosu su duka akashesu.
Waigawa tayi cikin tashin hankali kafin ta sake matse hannun nafeesat suka fara gudu.
Binsu sukeyi ganin kamar zasuyi musu Nisa yasa ya tsaya tareda saita bindiga ya harba musu.
Wani irin
Nishi nafeesa tasaki sbd shigarta da bullet yayi ta fadi kife kan cikinta.
Kuka Anano tasaki cikin tashin hankalin dabata taba ganiba a rayuwarta ta sake kamo hannun nafeesar tanason tada ita.
Girgixa Mata Kai tayi cikin kukan azaba daqyar tace,
Ki tafi,kici gabada gudu karsu kamaki zasu kasheki kema.
Girgixa Kai Anano tayi cikin tsananin kuka tace,
Bazan iya tafiyaba.
Sake kamata tayi suna miqewa tsaye yasake harbowa still nafeesa yasamu tayi baya zata zube Anano tayi saurin riqo hannunt
a suka zube tare cikin rashin sa'a Ashe sun kawo kusada wani dogon cliff mai tsananin zurfi nan suka fara gangarawa suka fa'da.
Wani qaton dutsi kanta ya daka tasaki nishin azaba Mai qarfi Amma cikin dauriya ta daddafa ta tashi zaune ko gani sosai batay
i ga wani irin juyawa da kanta keyi.
Daqyar ta lalabo nafeesa cikin azaba ta juyo da ita daqyar sbd a kife ta fa'do ko motsawa batayiba.
Jijjigata tayi cikin tsananin tsoro da tashin hankali.
Wani irin mugun Nishi taji nafeesar tayi Wanda yayi mat
uqar Bata tsoro Sai kawai taji Abu a gabanta.
Baya tayi a tsorace jikinta na makyarkyata zuciyarta na bugawa kamar zata bar jikinta.
Cikin qarfin hali nafeesa da numfashi ke qoqarin barin qirjinta ta kamo hannunta ta saka Mata wani irin zobe tareda d
amqe hannunta cikin azababbiyar murya da Bata fita tace,
Dan allah mena Haifa?
Cikeda tsoro jiki na kyarma ta matso takai hannu na rawa ta tabo murya na rawa tace,
Namiji.
Wani wahallalen Nishi nafeesa tasaki tareda sake damqe hannun Anano mury
a a karye tace,
Dan Allah ga amana Nan Allah yabaki sbd zuwanki Nan ya nuna kina cikin wannan qaddarar kema,
Nice na haifesa Amma kece Zaki Zama uwarsa sbd wannan itace qaddararmu.
Cikin tsananin kuka da tsoro murya a shaqe Anano tace,
Dan Allah
ki daina magana kina bani tsoro..
Wasu hawaye ne suka gangaro gefen idon nafeesar murya na karyewa tace,
Nabaki shi halak malak matuqar Zaki iya riqesa sbd koya koma gidan mahaifinsa kashesa za'ayi kamar yanda aka kasheni hakama za'a kashe mahaifinsa
...
Sunan mahaifinsa ABDUL SHAKUR Amma ana kiransa da SAHEEB AB..... Bata qarasaba jini ya 6alle Mata daga mahaifarta Ba qaqqautawa,
Kuka Anano tasaki Mai qarfi lokacinda taga numfashinta ya fita Koda Bata San komai akan mutuwaba ta tababbatarda mutu
wace tayi Amma qwaqwalwarta takasa yarda da hakan jiki na rawa tafara
Jijjigata da qarfi cikin kuka Mai tsanani tace,
Meyasa Zaki mutu kibarmin 'danki alhalin bansan ya zanyi dashiba,
Meyasa qaddara ta raboni da abokanaina na taho na tararda wannan m
ummunar qaddarar.
Kuka takeyi sosai jikinta ba inda baya rawa.
Cikin sanyin jiki takai hannunta dake matuqar rawa ta 'dauki yaron Sai kawai ta fashe da wani sabon kukan sbd tsananin tausayin kanta da nasa daya shigeta Dan ko kuka baiyiba bare wani mo
tsi sbd azabar dayasha kafin a haifesa tasan Kuma ba lallaine Suma su samu tsira da ransuba daga hannun Yan daban.
Hijabinta ta zare tareda na'desa aciki ta kaisa qirjinta ta rungume ahankali Nan take taji tsananin qaunarsa na shiga jininta.
Cikin ku
ka tace,
Bansan dalilin dayasa Allah yakawoka rayuwata ba,
Wannan qaddaratace kaman yanda mahaifiyarka ta fa'da,
Na rungumi wannan qaddarar da hannu biyu nayi alqawarin riqeka tamkar Dan dazan Haifa,
Nayi alqawarin Zama jajirtacciyar uwar da bazan Ba
ri Akira da gurbataccen sunaba matuqar ina Raye Kuma nayi alqawarin jure komai zai biyo.,,
Kukantane yafara qara sauti tayi saurin cusa Kai cikin qafafuwanta sbd Kar sujiyo sautin kukan..
#vote
#comment
#and share
[9/12, 11:33 AM]
_wattpad@mamuhgee_
*13*
Kuka take sosai har jikinta na kakkarwa sbd rashin sanin takamaimai abinyi Dan kuwa batamasan ya zatayi ta fuskanci gagarumin mur'daden alamarin dake gabanta ba,
Miqewa tayi daqyar rungume da ja
ririn Sai alokacin taji jibiyarsa da ba'a yankeba tasaka hannunta dake rawa ta lalubo wani 'dan dutsi Mai tsini ta rintse ido ta yanke zuciyarta na tsinkewa sbd batasan taqamaimai adadin da ake yankewaba.
Gyarasa tayi ta sake shigardashi jikinta ta qanq
ame tafara laluban hanyar barin gurin cikin tsananin kuka tana waiwayen gawar nafeesa.
Duk inda tasamu ca6a qafarta takeyi cikin tashin hankali da fargaba take ko waiwaye batayi harsaida taga tayi Nisa da gurin ta 'dan waiwayo hawayen cikin
idanuwanta s
uka gangaro ta Rintse idanu cikin wani irin nauyin zuciya kafin tajuya tafacigaba da tafiya Dan lokacin gab ake da fara Kiran sallar asuba.
Tsayawa yayi tareda zubawa gawar Ido cikin tsananin takaici da baqin cikin mutuwar Tata batareda sunsamu yanda su
keso ba gashi dukkanin alamu sun nuna abinda ta Haifa Yana Raye sbd baya gurin antafi dashi.
Mitssw yaja qaramin tsaki zuciyarsa na tafasa jiyake kamar ya rufe gawar da duka.,
Cikin takaici yakalli Wanda ke kusadashi yace,
Ji9 Kira mum asee.
Wa
ya ya fiddo cikin wandonsa ya dannawa numbernta Kira duk da tsakiyar darene saigashi ta 'daga Dan ko gigin gifta fuskarta bacci baiyiba bare idanuwanta dake butse qyam da tsananin baqin ciki da 6acin Rai.
Cikin nuna zallar takaicinsa yace,
Matar sahe
eb ta sheqa lahira....
Wani qaton Abu Mai kamada dutse ya danne maqoshinta tace,
Cikin jikinta fa?
Kallon gawar dake gabansa yayi yana yamutsa fuska yace,
Ta haifesa ba Rai sbd tun Yana ciki na harbesa.
Sai alokacin taji abinda ya tokare num
fashinta ya fa'da ta 'dan saki murya tace,
Good job bullet yanxu ku dauko gawar ku jefar qofar gidan Nan saiku gudu gawar abinda ta Haifa kuwa kusamu jeji ku wullar da shege.
Bullet na kashe wayar ya kalli yaransa yace,
Matuqar mum asee tasanda mu
n Bari abinda aka Haifa ya tsira to zamu samu matsala Dan itake biyanmu yanda mukeso a aiki Dan haka har abada karwanda yasan abinda ta Haifa na Raye.
Wucewa gaba yayi tareda cewa su biyosa da gawar.
Gudun tashin hankali suka dinga shararawa har suka
shigo cikin gari direct anguwar suka nufa daidai gate suka tsaya tareda aje gawar qofar gidan suka koma mota ji9 daya Sanya niqaf da dogon hijab ya qwanqwasa qaton gate din gidan maigadi dake zaune ya rafka uban tagumin tsoro da fargabar haduwarta da sahe
eb akan 6atan matarsa ya zaburo da sauri ya bu'de gate din cikin fargaba
Saura qiris yayi tuntu6e da gawar yayi saurin ja baya ya zube jiki na rawa daidai Nan ji9 ya shige mota da gudu sukabar gurin.
Hannu biyu Mai gadi ya 'dora akai Yana salatin dab
a Kai qarshensa yakeba da qarfi ba inda baya rawa ajikinsa....
Miqewa yayi ya kwasa cikin gida aguje bai tsaya komaiba yahau bubbuga musu qofa hankali atashe.
Abba dake qowarin fitowa sallar asuba yayi saurin qarasowa ya bu'de qofar cikin fargaba
Ya
na ganin jabiru Maigadi ya fito arikice Yana cewa,
Jabiru lafiya ku......
Gate ya nuna cikin tsananin tashin hankali yace,
Matar oga saheeb ce gatacan awaje wata Mata takawota ta gudu....
Ai abban bai jira sauran bayaninba ya nufi gate din daid
ai Nan Kamal ya fito da sauri Yana tambayar abba abinda ke faruwa cikin damuwa.
Murmushin gefen baki mum asee dake tsaye bakin windon bedroom dinta dake sama tasaki tareda cewa,
Not bad bullet.,,,
Sbd dabararsu ba laifi tayi Dan yanxu bamai ta6a tun
anin maza sukayi aikin za aita bincikene akan mace ce takasheta.
Hmmmnn and I will make sure nikuma Naga na qara lalata tunaninsa gurin binciken mitswww stupid bastard..
Juyawa tayi tabar bakin windon tareda fadawa toilet ta fiddo spray na pepper ta
fara fesawa cikin idanuwanta duk da tsananin azabar datakeji kamar zata shide Amma taurin Rai da qarfin baqar zuciyarta ya hanata dainawa
Cikin qanqanin lokaci idanuwanta sukai wani irin mugun kumbura sukai jajir Banda tsiyayar hawayen azaba ba abinda su
ke daqyar ta it's alwala ta fito hartayi sallah tagama idanuwanta Basu daina tsiyayar hawayenba.
Kodata idar jiki a sanyaye ta sauko Palo cikin hijab din anan ta tararda Abba da Kamal a tsattsaye sun saka gawar agaba jiki duk a mace ga jabiru gefe Sai s
ambatu yake sbd nafeesat mutuniyarsace sosai.
Gwaggo Hindu Mai Taya nafeesar Zama tuni ta zube qasa Banda kuka ba abinda takeyi hakama fadime da Deborah masu aiki Suma hawayen suke Dan kuwa suna tsananin qaunarta Dan itace kawai Mai mutumta mutane agida
n.
Baya mum asee tayi cikin tsananin tashin hankali tareda sakin saririn kuka tana Kiran sunayen Allah yakurah data fito bedroom dinta tayi saurin tareda cikin damuwa itama.
Waya Abba yafitar tareda barin palon yafara Kiran uwayenta ya sanar musu kaf
in yakira saheeb Amma Sam wayarsa Bata shiga nandai yakira duk yanuwa da jamaarsa yasanar musu da rasuwar.
Qarfe Tara da rabi na safe suna airport ten jirginsu zai tashi jin sauran thirty minutes din yake kamar basa tafiya.
Wayarsa dake kashe tun
jiya ya fiddo tareda kunnawa kamar jira ake saiga Kiran Kamal yashigo wayar
Kallo 'daya yayiwa screen din ya mayar da wayar sbd badashi yake buqatar wayaba yanxu.
Yana kallo Saida Kamal yayi Masa Kira bakwai kafin ya daina kiran,
Nemo number Abba yay
i ya Kira Sai yajisa line busy sai kawai ya sake kashe wayar tareda miqewa riqeda black smiones leather jacket dinsa da iPad da wayarsa dakuma passport dinsa tareda ticket zayyan na gefensa shima Amma waya tunda sukazo yake waya Sai time din ya kashe Yana
saka wayar a aljihu tareda gyara zaman jacket dinsa Mai zanen sojoji.
Tunda suka shiga jirgi ya kwantarda kansa tareda rufe idanuwansa Dan he's having this feeling something is not right.
Zayyan datun a airport Abba yakira yasanardashi jikinsa yake
a sanyaye sosai rasuwar ta daki zuciyarsa Dan kuwa yasan tabbas amininsa yayi rashi babba Dan har abada bayasa ran zai Kuma samun maisonsa kamar nafeesat Dan kuwa ta soshi ta qaunaceshi ayanda yake da rayuwarsa da Babu farin ciki ko ka'dan.
Yayita yunq
urin sanardashi saiya fasa sbd baimasan ta inda zai fara sanar Masa rasuwarba musamman yanda suka fara ganin haske yafara shigowa duhun rayuwarsa ta sanadin nafeesat da cikinta Amma gashi lokaci 'daya Allah ya karbi baiwarsa.
Koda jirginsu ya sauka su
ka fito mota biyu ce tazo 'daukarsu 'dayar sojoji ne acike Sai 'dayar driver ne kawai Kuma shima soldier ne dukkaninsu cikin uniform dinsu suke suna ganinsa suka saurin sunkuyar da kawunansu cikin girmamawa sukace,
Wellcome sir.
Da Kai ya amsa musu t
areda shigewa mota Nan take suka bar airport din a guje Dan dama yanada wuya kaga soldiers ba gudu sukeba.
Jabiru dake zaune bakin gate daga waje tareda wasu daga cikin masu gadin kusa dasu dasuka zo gaisuwa Yana hango wutar motocinsu duk da da Rana n
e Amma
yasan motocin soldiers din oga saheeb kullum akoda Rana a kunne suke ya miqe da sauri yayi ciki ya bu'de gate 'din gabansa na tsananta fa'duwa.
Lumshe fararen manyan oily eyes dinsa yayi lokacinda yaga harabar gidan da mutane duk da ma tuni wa
su suka tafi
Wani sabon nauyi yaji ya qaru a zuciyarsa Akan Wanda yakedashi ya fito ya nufi gurinsu Abba dake jiran qarasowarsa yayi qasa dakai lokacinda wasu Yan uwan nafeesat maza ke Masa gaisuwa.
Shiru yayi batareda ya 'dagoba har Saida Abba ya daf
asa cikin tsananin tausayawa yace,
Allah yaji qanta ya kawo maka sassauci Abdul.
Har magriba ta gabato Yana zaune kusada Abba kansa a sunkuye still
Ba Wanda baiyi mamaki da jinjinawa jarumta da qarfin hali irin nasaba Dan ko magana bayayi duk Wanda
yai Masa gaisuwa Kai kawai yake 'dagawa idanuwansa sun rine Sai jijiyoyin kansa dasuka firfito ahaka har akai magriba kafin yashiga cikin gida inda ya tararda mum asee ba lafiya sosai Nan dai Dole yasa Kamal Kiran Dr sbd antabbatar Masa da ko ruwa taqi Sh
a tunda akai rasuwar Nan take tsananin qaunarta da tausayinta yaqara shigarsa Dan kuwa dan yasan soyayyarta garesa cikin jininta take.
Ana fitowa sallar asuba tafara hango qauyensu maimakon taji sassauci a zuciyarta saitaji hankalinta ya qara
tashi gabanta ya tsananta fa'duwa ta tsaya cak tareda 'dago fuskar jaririn ta kalla hawayen idonta ya gangaro ya sauka har kan fuskarsa ta maidasa jikinta ta rungume ta nufi cikin garin zuwa lokacin gari yafara haske daqyar takai kanta qofar gidansu sbd y
anda qafafuwanta sukai Mata nauyi suna hardewa ta tsaya bakin qofar gidan zuciyarta na bugawa da tsanani cikin fargaba da tashin hankali ta cira qafarta daqyar tasa cikin gidan.
Vote
Comment
And share
[9/12, 11:33 AM]
_wattpad@mamuhgee_
*14*
Zaune baffa yake kan tabarma yayi zuru dawowarsa masallaci kenan
Jafar na gefensa zaune shima cikin rashin da'din Rai Sai aliyu dake tsaye gefe shima dai ran ba da'di
Hamma Yusuf da Usman kuwa daga masa
llaci gidan mande direba suka nufa suka sanar dashi zasu bisa idan zai koma da safen sbd su dubo can din koza'a dace Dan Sam Babu Wanda ya rintsa a gidan tunda motar daliban ta iso aka nemi Anano ba'a gantaba Nan hankali yayi tsananin tashi gasu ubaidah da
nusaiba Koda aka tambayesu Sai kuka suke su kansu basusan Ina Ina zasuce takeba mande direba kuwa kusan hankalinsa yafi na kowa tashi musamman dasu Yusuf sukace ga hukuma zasu miqasa matuqar ba'a gantaba ko Kuma wani Abu ya sameta.
Inna data fito 'daki
sanye da hijabin datayi sallah dashi ta gaida baffan bai amsa mataba sbd takaicinta dayakeji na yanda take qoqarin nuna ko inkula kan 6atan na Anano Wai ita kawaici,
kicin ta nufa tafara qoqarin hura wuta.
Harara baffa yabita da ita Rai a tsananin 6
ace cikin hasala yakira sunanta ta qaraso gabansa daidai Nan idonta ya sauka kan Anano dake tsaye qofar shigowa.
Jafar ne yafara ganinta bayan inna yayi saurin miqewa cikin farin ciki tareda hamdala yakira sunanta da 'dan qarfi.
Da sauri baffa ya juy
a batareda ya balbale Inna da fadan da yayi niyya ba ya miqe Yana cewa,
Alhamdulillah ya Allah,,,,
Qarasa shigowa cikin tsakar gidan tayi ahankali qafafuwanta na hardewa kamar Wadda kwai ya fashewa aciki tazo gaban baffa ta tsaya tareda sunkuyar da k
anta qasa sabbin hawayen fargaba da tsoro na gangaro Mata.
Cikin tsananin kulawa da farin ciki baffa ya riqo hannunta 'daya ya nufi tabarmar daya taso Yana cewa,
Ananon baffa me.....
Cak ya tsaya Jin Bata motsa daga inda takeba yayi saurin juyowa
Sai alokacin ya lura da Inna da aliyu dasuka kasa motsi sun qurawa ananon Ido cikin wani irin yanayi
Maida kallonsa yayi ga ananon saiyaga tuni sautin kukanta yafara fita ahankali.
Sakin hannunta yayi tareda fuskantarta cikin damuwa da kulawa zaiyi m
agana idonsa ya lurada abinda ke hannunta dunqule cikin farin hijab 'dinta.
Kallonta yafarayi tun daga samanta zuwa qasa,
Gabaki 'daya jini ne a uniform dinta ga fuskarta datai jajir ta kumbura...
Daqyar ya tattaro yawu ya ha'diye suka wuce maqoshi
nsa daqyar kamar zasu yankesa yakalli ananon cikin son yaqar wani tunanin dakeson shigarsa idonsa qyar akan hannuwanta yace,
Ananon baffa meya sameki Kuma menene wannan a hannunki?
Inna da tuni tafara mantawa da kawaici cikin tsananin fargaba ta mats
o tareda Kai hannunta dake rawa zata bu'de baffa yayi saurin riqe hannunta still idanuwansa nakan Anano yace,
Anano meya sameki?
Kafadamin idan ba wanine yayi Miki mummunan illa ba....
Kuka tasake fashewa dashi Mai qarfi daidai shigowarsu Yusuf suka
qaraso da sauri saidai suna qarewa kayan jikin Anano kallo gabansu yayi mummunan fa'duwa sbd sun saddaqarda fyade akayiwa 'yar qanwar tasu
Bango Yusuf ya dafe Yana karanto innalillahi cikin tsananin tashin hankali.
Usman ma cikin tashin hankalin ya su
lale qasa zaune jafar dayake da tsananin sanyi da karyayiyar zuciya tuni yafara hawayen tausayin 'yar qanwarsu da aka 6atawa rayuwa aliyu kuwa baffa yayi saurin riqewa ganin zai iya zubewa qasa sbd halinda yashiga.
Cikin zafin nama da takaici inna ta fu
zge hijabin Saida jaririn yakusa fa'duwa cikin wani mugun sauri Anano tayi saurin zubewa qasa ta taresa tareda qanqamesa da sauri jikinta na rawa shikuwa jaririn Sai alokacin yasaki wani irin kukan jarirai Wanda tunda yafado Sai alokacin yayi kuka.
Yusu
f,Usman,aliyu da baffa kusan dukaninsu atare suka zabura sunakai kallonsu ga jaririn Dan sai alokacin suka sanda akwai wani Abu acikin hijabin Anano din.
Inna ma ta razana matuqa da ganin jaririn duk da dama tayi zargin akwai wani Abu a hijabin Amma Bat
a ta6a kawo zataga jariri ba.
Qurawa yaron idanuwa sukayi cikin tsananin fargaba jafar kuwa jiki na rawa haryana tuntu6e yayi saurin Isa qofar gidan ya rufe harda maqala sakata Dan karma ajiyosu ko wani yashigo gidan.
Cikin rawar hannu baffa ya nuna
jaririn Yana kallon usman dake kusa dashi yace,
Usman dubamin meye wannan kamar jariri nake gani....
Jiki a mace usamn yayi qasa da kai murya a sanyaye yace,
Baffa jariri ne a hannunta Kuma me Rai ba matacceba sabuwar haihuwa ma.
Anano''''' Baf
fa yakira sunanta cikin kammalalliyar murya.
Kasa 'dagowa tayi saima wani kukan data fashe dashi.
Sake Kiran sunanta baffa yayi ta rintse kumburarun idanuwanta da sukaci kuka harsuka gaji ta girgixa Kanta da yayi mugun nauyi sbd kukan datasha dakuma
ciwon dayake Mata ta bu'de baki daqyar murya a dashe