Showing 15001 words to 18000 words out of 59902 words

Chapter 6 - iznah Complete

juyawa yayi yabar 'dakin zuciyarsa takaicin zuwansa,,,,

Ko acikin marasa tarbiya da mutumci wannan uwarsu ce,,,

Hartanada bakin Kare 'dan shege agaban gwaggonta she'

s unbelievable......

Mota Yakoma saidata zayyan ya tsaya 6ata Masa lokaci kafin yafito suka tafi.

#vote

#comment

#share

*_EZNAH_*

🌹

_wattpad@mamuhgee_

*20*

Zama gwaggo tayi bayan fitar kamalu taga ananon tabi bayansa da wan

i mugun kallo tace,

Anano....

Na'am'''tace tana goge fuskarta inda Kamal ya taba cikin qunar Rai sbd jitake kamar tafasasshen barkono ne yata6ata.

Miqewa tsaye tayi ta nufi hanyar toilet din dakin tashige danta wanke fuskarta Kota rage zafin da zuci

yarta ke Mata akanta.

Tana fitowa Zama tayi a kujera tareda dibar abincin da gwaggo takawo tea ne Sai kwai soyayye da bread

Saidata bawa abdulshakur yaci ya qoshi kafin taci itama ta kimtsa Abdul din kafin ta tattara kayan ta kar6i kudi gurin gwaggo

ta fito tayo gida dantai wanka ta canza Kaya.

Kodata isa gida saidatayi wanka ta shirya kafin ta nufi sashensu mum asee,

Zaune take a Palo yakurah da Kamal na zaune tareda ita suna magana.

Kallon Kamal mum asee tayi tace,

Alhaji yaje kar6o taka

rdu wani guri Dan anjima zasui magana da saheeb Dan haka nasa su bullet su taresa a hanya su kar6emin takardun shikuma sukaisa gidansu dake can daji su rufemin shi cikin rizabuwar gidan harsai nagama hada takardun.....

Katseta Kamal yayi yace,

Mum ba

na tunanin wannan shawarar tayi sbd zai iya guduwa and wat do you think will happen idan yayi escaping bastard son dinsa yasan komai,,,,no I can't imagine spending the rest of my precious life in any army prison.....

Shut up stupid""""mum asee ta katses

a cikin takaicinsa he always think or say negative.

Ni kullum qarin baqin cikina akan saheeb shine yanda na haifi Mai tosashen Kai shikuma ya kasance Mai komai na yaron arziqi....

Tsuke fuska yayi sbd takaicin yanda kullum Sai mum takirasa da wani mu

gun suna.

Daria yakurah ta qunshe cikin ranta tace,

Slowly dai you two will become enemies and I will be morethan happy to see that.

Banda shegen rawar kanka daba yanxu Kaine Mai kulada dukiyar saheeb dinva tunda baida Mai kular Masa Amma ka kasa

nutsuwa duk wani mugun halin dabbancinka na neman Mata yasani...

Idan mukai Masa allurar yanxu uban waye zaisaka Mana hannu a sauran takardun kumama me kake tunani?

Shi saheeb din Wawa ne kamarka dabazai kaisa asibiti abincika agano allura akai masaba.

....

Mum please ya Isa nagaji da yanda kike insulting Dina ko yaushe akan wannan gud for nothing bastard step son din naki,

Idan kinsan ya fini maiyasa tun farko baki za6esaba akaina mitswww...

Miqewa yayi ya wuce a fusace Yana cewa,

I just hate th

at bastard like hell....

Karo yaji yayi da mutum da sauri taja baya jikinta na'dan rawa ganin irin kallon dayake Mata na zargin taji Mai suke fa'da saitayi saurin tattaro nutsuwa da murmushin yaqe tace,

Inazaka kake sauri haka?

Qura Mata ido yayi

batareda ya amsaba yanason karanto yanayinta sbd yaga rudewa atareda ita.

Ganin zai iya ganota yasa tasake washe Masa baki tana cewa,

Lafiya naganka haka?

Mum asee nanan kuwa?

Inason nagaisheta ne kafin nakoma asibiti.

Jin takira mum asee yayi t

saki tareda cewa,

Just get out of my way stupid.

Matsawa tayi ya wuce kamar zai tashi sama.

Ajiyar zuciya tasake tareda binsa da harara tana cewa,

Idiot'""""Nima na Rama mitswww.

Kodata shiga sama sama tagaida mum asee ta fito ta tafiyarta asi

biti tana cewa,

Ni da abdulshakur ma yaji sauqi tattarawa zamuyi mu tafiyarmu inda mukafi wayo Dan wlh Zama anan cikin makasa gangancine.

Tana Isa asibitin takasa samun sukuni sbd hakanan taji hankalinta yatashi da abinda za'ayiwa Abba Amma Kuma bata

san ya zatayi ba.

Har kusan maraice tana zaune takasa sukuni Sai Kai kawo take ta rasa mafita.

Kamar daga sama saiga zayyan da saheeb sun shigo saheeb fuskarnan a 'daure ko kallon gefenta baiyiba ya gaida Inna kamar bakinsa na ciwo.

Zayyan kuwa ts

okanarta ya'danyi saiyaga idanuwanta na zubda hawaye cikin kulawa yace,

Subhanallah maman abdul lafiya kuwa Naga kina hawaye.

Juyowa gwaggo tayi cikin mamaki ta kalleta tace,

Ke lafiyarki kuwa ni tunda kikaje gida Kika dawo Naga kin canza.

Sake

matso hawaye tayi gabanta na luguden tsoron qaryar dazata lafto Dan kuwa tunda akace tana kuka taga ya watso Mata shanyayun idanuwansa ya kafeta dasu.

Sosai zayyan ya damu yasake tambayarta taqi magana saima sautin kukan data fara fitarwa

Juyawa sahe

eb yayi zai fice Dan ya tsani kayan takaici

Ganin zai fice tayi saurin bu'de Baki da 'daga murya tace,

Dazan dawo asibiti dazu nataho ta gurin layi na hudu bayan na gida Naga kamar motar abban Kamal agurin wasu na qoqarin fitoda Abu direbansa suna qoqa

rin cusashi cikin wata mota kum......

Wat"""Taji yafada da qarfi tareda juyowa ya zuba Mata idanuwansa

Rawa jikinta ya 'dauka ta ha'diye yawu da qyar sbd tsoro Dan tasan ba baffa ka'dai zataciba idan yagano qarya take har innarta saitaci itadai fatart

a yayi saurin xuwa gurin da yaransa kafin Abba yabi gurin a daukesa.

Zaro idanuwa gwaggo tayi cikin salati tace,

Anano gskia kike fada kuwa kokuwa iskancin nakine ya mots....

Katse gwaggo tayi da sauri ganin zata 6allo Mata ruwa tasake sakin sabon

kuka tana cewa,

Da gske nake nagani da idona.

Juyawa yayi yabar 'dakin Yana Ciro wayarsa yakira office dinsa yabada umarnin motar soldiers biyar tazo ta samesa yanxu.

Kallonta zayyan yayi yace,

Just calm yourself and stop crying Bari muje muga

ni and I pray ba qarya idonki ya gane Miki ba...

Waro idanuwanta tayi akansa tareda qara ha'diye wani yawun tsoro kafin ta sunkuyar da kanta kukan gaske na zuwar Mata na tsoro Dan matuqar plan dinta baiciba ta ka'de.

Tunda suka fita takasa zaune taka

sa tsaye sai rawar qafa takeyi

Gwaggo Sai binta da Ido take cikin tsananin mamakin ikon Allah kafin takasa hakuri tace,

Wallahi wannan zazzaro idanuwan da kike bakida gskia Dan haka tun wuri ki sanardani meke faruwa.

Kallon gwaggon tayi cikin sauri

da tsoronta dayake qara bayyana tace,

Gwaggo nikawai ki tashi muje gida mu tattara kayanmu mu koma gurinsu baffa nidai nagaji da Nan 'din gaba 'daya.

Qura Mata ido gwaggo tayi har wani ciki ciki take da Ido sbd tasamu karanto ananon tsaf Dan duk ras

hin gaskiya ya bayyana atattareda ita

Tasan halin ananon tsaf da rashin ji da gajen hakuri ga shegen wuce wuri Amma tayi tunanin duk ta daina sbd wannan halinda tashiga na samuwar abdulshakur Amma ga alamu Nan sun nuna wani gagarumin abun tayi.

Qyaci

tayi tace,

Idanma baki fadaminba duk abin yabiyo baya ai naji Kuma idan ma wata maganar Kika jawo wlh daukarki zanyi muje nakaiki har qauye aliyu ya laka'da Miki mugun duka mudawo.

Itadai shiru tayi tana danasanin shiga abinda bai shafetaba Dan yanx

u batasan ya zata Kaya mataba.

Tunda Abba yafito office suka kamo hanyar gida yaga wata baqar mota nabinsu abaya da farko baiyi tunanin su motar kebiba saidayace Abu driver yayi parking bakin titi saiyaga Suma sun tsaya nesa ka'dan.

Cigaba suka

yi da tafiya motarma tabiyosu cikin mamaki yace,

Abu ka lurada motar bayanmu mu takebi kuwa?

Kallon mirror Abu yayi yace,

Alhaji tunda muka fito office take biyedamu banfada maka bane Dan Kar hankalinka ya tashi.

Wat to ai hankalina Kam yagama

tashi Dan kuwa ba tantama kidnappers ne.

Qarawa motar gudu Abu yayi cikin rawar jiki Jin abban yakira kidnappers hankali tashe Dan kuwa gani yake gara alhajin daukarsa kawai zasuyi shikuwa shegen duka zasuyi Masa subarsa kwance qilama Sai anmasa sakiya

kozai dawo daidai.

Atake Suma su bullet suka qarawa motarsu gudu

Aikuwa Abu naganin haka hankalinsa yaqara mugun tashi ya Kuma bawa motar wuta jikinsa na rawa musamman ma dayaga Abba hankalinsa yayi mugun tashi ga tsoro qarara ataredashi

suna shiga la

yin farko na anguwar motocin soldiers din saheeb na shigowa Aida wani mugun ribas motarsu bullet suka bar layin motar sojojin na Mara musu baya Amma Basu samesuba haka suka dawo.

Abu na ganin motocinsu saheeb yayi wani mugun parking a tsakiyar layi ko m

otar Bai tsaya kashewaba dashi da abban sukai rige rigen fita motar Dan hankalinsu ba qaramin tashi yayiba.

Abu cikin sojojin yayi a guje jikinsa ba inda baya rawa Dan duniya Allah yayisa da shegen tsoro musamman ma na 6arayi Dan tsaf zasu yankaka kosu

harbeka.

Abba motar saheeb daya fito cikin tashin hankali ya nufa Yana zare babbar rigarsa Dan wani mugun zafi yakeji.

Bu'de Masa mota saheeb yayi yashiga ya rufe Masa ya juyo ya kalli yaransa ya Basu umarni kafin ya kalli Abu dake zare idanuwa jikin

sa baibar rawaba yace,

Kashiga motar kaja ka qarasa gida da ita...

Zaro idanuwa yayi zaiyi magana wani soldier ya daka Masa wata gigitacciyar tsawar data sashi nufar motar haryana tuntu6e jikinsa na qara karbar rawa.

Shigewa motocinsu sukai sukaba

r gurin abu ma a mugun gujen ya Mara musu baya Yana kallon bayansa ta cikin mirror.

#vote

#comment

#share

[9/20, 3:43 PM]

_wattpad@mamuhgee_

*21*

_*Thank you so very much habibtis coz gskia jiya naqar

a tabbatarda eznah nada masoya*_

*_inasonku Ina qaunarku kamar yanda kuke yina_*

*_Musamman yanda Nima kuka sakani dariyar Abu da Abba ajiyan Dan kuwa comments dinku yasa nasake karantawa Nima nayi dariya sosai ammafa karkuga laifinsu kowa wuya yake gu

du yanxu a rayuwarnan sbd duniyar ta lalace..._* *_Allah ya karemu ya tsaremu..._*

_*Mamuh love you guys more*_

😍

_*Aysha agamcy and faiza amg this one is for you guys*_

😍

Suna shigowa gidan zayyan ya bu'dewa Abba dake hada gumi still duk

da ac motar ya fito riqeda babbar rigarsa ya miqawa saheeb jakar takardun hannunsa ya nufi Palo yashige direct sama ya haye yashige bedroom yasaka key tareda zubewa bakin gado Sai lokacin yakejin kansa safe..

Abu ma jiki na rawa ya fito motar ya nufi '

dakin jabiru Maigadi da sauri ya fa'da toilet dinsa Dan a buqace yake da bayin.

Kallon yaransa yayi fuska a 'daure yabasu umarnin tsaron lafiyar Abba daga yau din harsai yagama bincikensa.

Part dinsa suka nufa shida zayyan kowannensu da abinda zuciya

rsa ke saqa masa..

Zama yayi akujera tareda rintse idanu kansa nason 'daukar zafi akan alamarin Dan kuwa ba tantama yasan dasaka hannun wannan ill mannered girl din....

Zayyan ma tunanin ananon yake sbd da saninta Dan kuwa Dole tasan da hakan zatafar

u to Amma idan dasaka hannunta meyasa zata turasu Kuma in a indirect way kenan bazata iya fa'da musu Kai tsayeba wani Abu zai faru idan hakane then watake karewa kokuma 6oyewa....I have to find out komai akanta coz something is definitely fishy...

Kallo

n saheeb yayi yaga yanayin dayake ciki ya dafasa yace,

Don't stress your self man tunda Allah yasa ba abinda yafaru....

Wani mugun kallo ya watsa Masa yace,

Like seriously,,,wannan crazy yarinyar tayi magana Kan Abba thank God we arrived at the ri

ght time idan badan hakaba wat do you think will happen?.....

She has to explain her self coz koma meyene tana sa hannu da masaniya aciki..

Miqewa yayi ya nufi hanyar bedroom dinsa ya shige yabar zayyan din a zaune cikin dogon tunanin alamarin kafin da

ga baya shima ya miqe ya tafi.

Tunda su bullet suka Kira mum asee suka fa'da Mata abinda yafaru taji wani mummunan baqin ciki yarufeta sbd rashin samun nasara Amma ba komai zata canza salonda ba saheeb da shegun sojojinsaba ko uwarsa dake kabari tayi fa

talwa bazata ku6utar dashiba.

Qarfe bakwai na dare suka shigo asibitin shida zayyan kallo 'daya zakai Masa ya burgeka sbd kwarjininsa da izzarsa saidai fuskarsa dake ha'de kamar ko yaushe.

Ita kadaice a 'dakin zaune bakin gadon Abdul daya gama rigi

ma yayi  bacci

gwaggo taje gida ta 'dauko musu wasu abubuwan Dan itama anan zata kwana taredasu.

Sam ba'a cikin cikakkiyar nutsuwarta takeba Dan har lokacin Bata daina fargaba ba.

Tanajin anbude qofar 'dakin tayi zumbur ta miqe tsaye gabanta na fa'd

uwa musamman dayake shine agaba zayyan na bayansa.

Yawu ta ha'diye da qarfi tareda qura Masa fararen idanuwanta dake cike taf da tsoro da fargaba.

Wani mugun kallo ya watso Mata zaiyi magana zayyan yayi saurin Shan gabansa Yana kallonta cikin 'yar sa

kewar fuska yace,

Ya jikin Abdul?

Jijjiga Masa Kai tayi sbd bazata iya magana ba still idanuwanta nakan saheeb daya gama burkuta gaba 'daya nutsuwarta da hankalinta da kallonsa...

Kallonta yayi yakalli saheeb din ganin duk ta firgice yace,

Ok k

i nutsu tambayarki zanyi and i don want any lies..

Ya akayi kikasan abinda zaifaru dasu Abba?

Muqut ta ha'diye wasu yawu tana Dana sanin abinda tayi sbd yanzu Kam batada ikon fa'da musu komai Kuma idan taqi fa'da suka tsananta bincike mum asee zataji

itace ta rusa Mata plan kenan tasan komai gameda sirrinsu Kuma hakan na nufin mutuwarta kota Abdul dinta.

Wata gigitacciyar tsawa saheeb ya daka Mata yanacewa,

Will you talk or saina sa ansaki kinyi magana....

Baya taja da sauri tareda tsuke fusk

a tace,

Niban saniba kawai gskia na fa'da Naga kaman motarsu ne shiyasa na....

Shut up....ya daka Mata wata tsawar Yana matsota a zuciye tareda 'daga hannu zai wanka Mata lafiyayyan Mari aka turo qofar dakin......

Atare dukaninsu suka juya tana ga

nin Kamal tace,

Oh God I'm dead....

Kallon mamaki Kamal yakebin dukkaninsu dashi tareda tsayarda kallonsa kan hannun saheeb daya 'daga da niyar marinta.

Cikin sauri tayi shahada tareda riqo hannun saheeb din da sauri ta sauke tareda samin wahallal

en murmushin qarfin hali take,

Ok Yaya saheeb Sai da safe nagode da kulawa Allah yabiya ya saka muku da alkhairi.....

'dauke Kai tayi tana ha'diye wani busasshen yawu tana qara qaqaro murmushin Dole ta kalli zayyan da yayi kusan mutuwar tsaye sbd tsa

nanin mamakin qarfin halinta da rashin sanin dalilinta nayin hakan Amma koma dai meyene ya fahimta batason Kamal yasani...

Shima hakanan yasamu kansa da sakin murmushin yaqe na Dole Yana cewa,

Ok Allah ya qaro sauqi.

Kallon saheeb da zuciya tagama

kashesa yayi ta gefen Ido yaga yanda kafeta da idanuwansa dasukai mugun kadawa sabd 6acin Rai yayi saurin dafasa cikin qasa qasa da murya yace,

Please danne 6acin ranka and Let's go from here sbd wannan qanin naka karya fahimci wani Abu sbd inaga bai k

amata wani yasan komaiba gameda wannan alamarin harsai mun gama bincike mun San komai.

Rintse idanuwa yayi cikin wani irin zafin zuciya kafin ya bu'de ya saukesu akanta

Ta qaqalo wani hadadden murmushi ta sakar Masa gabanta na dagargajewa cikin zuciyar

ta tana cewa,

Anano kin mutu...

Juyawa yayi yabar room 'din zayyan yabi bayansa Dan kuwa tagama kwashesu da mugun mamaki...

Suna fita ta juyo ta kalli Kamal ta juya zata shige toilet Dan tattaro nutsuwa kozata samu ta iya fuskantar Kamal din shima

taji ya fixgota da qarfi ahasale tareda jefata gado saura qiris ta fa'da Kan abdul tayi saurin 'dagowa ta kallesa cikin zafin zuciya ya nunata da yatsa cikin tsananin masifa yace,

What was that bastard trying to do.....

Bansaniba"""""ta fa'da da qar

fi ya shaqota da qarfi Yana cewa,

Ohhh wato har idonki ya bu'de kinfara mayarmin da magana you ingreat bitch,

Tell me what is going on between you two idiots,

Are you having a secret affa....

Qwacewa tayi da qarfi tana shafa wuyanta tana tari sbd b

a qaramar shaqa yayi mataba.

Wani mugun kallo take binsa dashi na tsana da takaici tace,

He is far morethan you tako Ina Dan haka ba laifi bane Dan nayi mu'amala dashiba sbd yafika sanin darajar mace.....

Kanta yayo tayi saurin kaucewa zata gudu y

a damqo gashinta dake cikin 'dankwali cikin azaba tafara qoqarin qwacewa tana cewa,

Kaga babban kalar banbancinka dashi sbd he will never hurt a woman and....

Shut up bitch,,,,barima nafada Miki wani Abu dabaki saniba

Babu shegen daya Isa yasoki ida

n baniba Dan kuwa duk Wanda yayi gangancin hakan wallahi sainayi Masa mummunan illarda harke saita shafa,

Ke tawace nikadai

Bazaki so kowaba saini

Duk Wanda kikayi gangancin so saikinyi Dana sani...when I said kowa

I mean kowa ciki harda kwartonki sahe

eb...

Wurgi yayi da ita yafice afusace kamar zai daki iska..

Wani irin kuka tasaki ahankali zuciyarta na tsananin quna,

Kuka take sosai Dan kuwa tasan tana cikin masifar dabatasan yazata fidda kantaba daga taimako Abu yazamar Mata qaddara mummuna

Dan kuwa dayanzu tana tareda iyayenta tana cigaba da karatu Amma qadda ta jefota cikin wa'innan mutanen Daba imani ko tausayi a zuciyarsu ga Kamal nason zamar Mata wani bala'in na musamman.

Adaren kwana tayi kukan tausayin rayuwarta data juye ta yamutse

Mata takeyi Dan kuwa shawarar guduwa takeyi Amma abin mamakinta 6angare 'daya na zuciyarta jitake bazata iya tafiyaba su Kamal su cutatar da saheeb Dan kuwa jitake zuciyarta kamar bazata iya daukar hakanba...

Guraren asuba ta farka a firgice sbd mafark

in datayi da mahaifiyar abdulshakur duk da har cikin mafarkin bataga fuskarta Abu 'daya ta ringa maimaita Mata,,,,

Ke haske ce arayuwar masoyana abdulshakurs,,,,

Ina roqonki daki tsaya aduk inda kike ki Hana cuta kamar yanda Kika Hana a hallakani da ci

kina har Allah yabani ikon haihuwarsa,,,,,

Anano ke haskece kizamo jaruma Mai tsayawa akan maqiyanki.........

Dafe goshinta tayi gabanta na fa'duwa sbd kanta gabaki daya a qulle yake musamman Yanzu datayi wannan mafarkin...

Toilet tashiga tayo alwal

a tazo tayi sallah ta roqi Allah yabata sa'a da qwarin gwiwa akan wannan yaqin dazata fara Dan kuwa tayanke shawarar tsaya tsayin daka akan bazata ta6a Bari su mum asee su ta6a saheeb ba to Amma why all the risks..?ta tambayi kanta tana qara daga hannu sam

a tace,

Ya Allah karka Bari zuciyata takamu dason.....shiru tayi sbd tsananta fa'duwa da gabanta yayi Dan kuwa kaman she's too late..

Qarfe goma na safe aka sallamesu suka shigo napep suka dawo gida tun a gate tasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login