Showing 6001 words to 9000 words out of 59902 words

Chapter 3 - iznah Complete

tace,

Baffa Dan Allah kayi hkr wlh ba abinda kuke tuna.....

Aliyu da tuni zuciyarsa tafara tafarfasa ya wurga Mata wani mugun kallo da jajayen idanuwansa a hasale yace,

Kifadi abinda ke hannunki

na waye aka tambaya ba tareda 6ata Mana lokaciba.

Yawun tashin hankali da tsoro ta ha'diye tareda sunkuyar da Kai tace,

Nawane Amma bani....

Wani gigitaccen mari Inna ta saukar Mata tana 'dauke hannu aliyu ya sauke Mata nasa harsaida tayi zaman Y

an bori.

Cikin tsananin hasala da zafin zuciya Yusuf ya karbi zancen Yana watsa Mata wani mugun kallo yace,

Dan ubanki Zaki bu'de baki kifa'da Mana 'dan uban waye ahannunki kosaina karya Miki wuya..

Kuka tasake saki tareda qara qanqame 'dan ta rar

rafa gaban baffa da tuni jiri yakusa zubar dashi Saida jafar ya taresa ta riqe qafarsa da hannu 'daya cikin hawaye tace,

Baffa Dan Allah ka....

Hannu baffan ya'daga Mata daqyar Dan tuni bakinsa ya mutu Dan har wani rawa yaji zuciyarsa nayi sbd fargab

a Dan har lokacin yakasa yarda da abinda ke Shirin tabbatuwa agabansa ya kalleta kalar tausayi murya a sanyaye yace,

Hassana..,

Rintse idanuwanta tayi zuciyarta na Kara karyewa Jin yau yakirata da ainihin sunanta.

Anano wannan yaron na hannunki na

keson kifadamin na waye dan ayi gaggawar mayar dashi tun kafin afara shigowa yi Mana barkar dawowarki agansa ayi Mana wani tunani Dan haka kiyi gaggawar fadar inda kika tsintoshi a mayar dashi Dan wallahi bazai zauna a gidan Nan ba...

A gigice ta 'dago

hankalinta na tsananta tashi tuni idanuwanta suka qafe jikinta ya'dau sabuwar rawa.

Wata razananniyar tsawa dabai ta6ayi arayuwarsaba yayi Mata cikin qufula yace,

Ki bude baki kiyi magana.

Rawar jikinta ce ta qaru sbd baffa da tuni tsananin 6acin

ransa ya bayyana

Kallon Yusuf baffa yayi Rai a6ace yace,

Kar6esa ka....

Cikin tsananin kuka ta qara qanqamesa tace,

Baffa dan Allah karka rabani dashi bazan iya rabuwa dashiba.....

Duka Inna da aliyu suka rufeta dashi lokaci guda Nan ta sak

e qanqame 'dan sbd Kar duka ya samesa abinda ya qara hasala kowa kenan Inna ta jawo icce tana cewa,

Gwarama mu kasheki cikin gida tun kafin ma wani yasanda abinda ke faruwa.

Riqe iccen Yusuf yayi yana kallon ananon yace,

'dan uban waye akace?

H

a'diye sabon kukan dayazo mata  tayi Kai tsaye tace,

Nawa ne.

Fixgota Inna tayi  tajata ta jefa 'daki batai wata wataba ta zare wandon makarantar dake jikinta wani razanannen salati tasaki tayi baya tana Kiran sunayen Allah jikinta tuni yayi sanyi ya

nxu Kam kukane ke Shirin qwace Mata ta fito kallo 'daya tayiwa baffa saita sauke Kai hawayen datake dannewa suka gangaro

Zuciya baffa ya dafe Sai kawai sukaga yayi baya ya zube Yana wata irin jijjiga jafar da Usman sukai kansa Yusuf kuwa waje ya nufa da

sauri Dan Kiran mande direba sukai baffan qauyen gabansu wurin sani Mai chemist Dan su shine likitansu.

Aliyu kuwa dakin da anonon take tana fidda kuka Mara sauti hakama yaron tuni ya kara'de gidan da kuka ya nufa a zuciye yahau jibgarta baji ba gani I

nna ma zubewa tayi qofar 'dakin tana hawaye cikin mummunan tashin hankali da sanyin jiki.

#vote

#comment

#share

[9/12, 11:34 AM]

_wattpad@mamuhgee_

*15*

Jiki na rawa su Usman suka kwantarda baffa K

an tabarma suka hau you Masa firfita ahankali yafara rage jijjjigar numfashinta ya 'dan farawa rage zaburewar

dayayi ya lumshe idanuwansa yayi shiru Yana karanto sunayen Allah a zuciyarsa Dan yasamu nutsuwarsa ta daidaita ya fuskanci Anano Dan haryanxu shi

bai yarda da wannan shegen 'dan Mai kukan kwa'di ita ta haifesaba.

Usman ne ya miqe yashiga daki ya qwace Anano daga dukan da aliyu ke Mata cikin tsananin bacin Rai yace,

Wai Kai aliyu meyasa baka auna komai kayisa cikin mizanin hankalin cikakken 'd

an Adam ne?

Kana tunanin dukan dakake Mata zaisa ta fa'di gskia ne ko kuwa?

Mitssw''''yaja 'dan qaramin tsaki tareda riqo hannun Anano ya miqar da ita Amma Sam ko tashi Bata iyayi ya miqa hannu zai kar6i yaron tayi saurin 'dago kumburariyar fuskarta ta

kallesa saitaga fuskarsa a ha'de ba alamun wasa saita miqa masashi jikinta na rawa gabanta na fa'duwa.

Kwantarda yaron yayi yariqota ta fito tana tafiya daqyar ya kalli jafar da duk yayi zuru zuru yace ya debo Mata ruwa a bokiti tayi wanka.

Ta gefen

Inna ta wuce tana kallon yanda innar ke keta faman goge hawaye ta maida kallonta gurin baffa yanayin data gashi acikine yasa hankalinta tashi ta juya 'daki  duk suka bita da kallo

Jaririn ta 'dauko jiki a tsananin sanyaye ta nufi gurinda baffa yake Yus

uf yayi saurin daka Mata tsawa Rai a6ace.

Qin tsayawa tayi saidata Kai gaban baffa ta durqusa hawaye nabin fuskarta murya na rawa tace,

Baffa don Allah karka Bari zargi yasa ka cutatar da kanka,

Wallahi wallahi wallahi baffa ban ta6a aikata Zina ba,

Ban ta6a ra6ar ko wani Mai akatawaba,

Wannan jaririn nawa kamar yanda Wadda ta haifesa tabanishi kuma nafada muku da farko Amma wlh baffa bani na haifesa ba.....

Wani mugun kallo aliyu da Yusuf harma da Inna ke binta dashi sbd Jin abinda take fa'da W

ai an Bata kyautar jariri.

Baffa kuwa jajayen idanuwansa ya bu'de ahankali ya kafeta dasu cikin rawar murya kamar zaiyi kuka yace,

Anano Abu 'daya nakeson nasani akan jaririn Nan Wanda shika'dai ne damuwata Kuma daga kin fadamin gskia wlh zuciyata Za

ta iya 'daukar koma meye sauran bayanin

Anano jaririn Nan na waye?

Sabbin hawaye ne suka gangaro Mata ta share murya a dake tace,

taimakon uwarsa nayi lokacinda take naqudarsa Kuma tana haihuwarsa ta rasu.

Tsit sukayi jafar kuwa hambadala yasaki

a bayyane aliyu da Yusuf suka bisa da mugun kallo cikin takaici dansu Basu yardaba.

Baffa kuwa tsareta yayi da Ido tsawon lokaci kafin yace,

Anano gskia Kika fa'damin?

Kai ta 'dago ahankali tace eh hawaye na sake gangaro Mata.

Yusuf da Usman ya

kalla yace,

Suje inda tafada subi hanyar adubo gawar azoda ita.

Kanta ya maido kallonsa Nan take yaji zuciyarsa ta yarda da ita 'dari bisa 'dari ya riqo hannunta cikin nutsuwa yace,

Anano na yarda dake tako wanne 6angare Kuma natabbatarda bazaki

aikata Koda makamancin hakanba Dan haka kiyi qoqarin ganin konan gaba baki rusa yardataba.

Kai ta 'daga ahankali gabanta na fa'duwar wane hukunci baffan zai yanke akan yaron.

Inna ya kalla Koda Bata fa'daba fuskarta ta nuna tashin hankalinta ya 'dan

ragu saidai itama kamarsu Yusuf hankalinta bai kwantaba sosai da zancen ananon.

Cikin nutsuwa yace,

Ki tashi ki 'dora ruwa Anano tayi wanka.

Badan tasoba ta miqe ta nufi madafarsu tafara ha'da itace.

Anano kuwa har ruwan yayi zafi tana durqushe

agurin Saida jafar ya cika Mata bokiti ya sirka yakai Mata qofar bayi takuna ta miqe jiki a sanyaye ta shiga 'daki ta tube ta fito sum sum tashige bayin.

Duk da tana cikin tashin hankali da damuwar makomar jaririn sosai taji da'din wankan Dan Nan take

taji ta'dan warware ajikinta.

Tana gama wankan kafin takai ga fitowa yaron yatashi Nan take ya kara'de gidan da kuka cikin sauri ta janyo zaninta ta 'daura ta fito

Turus tayi jikinta na saki sbd ganin ba Wanda ya motsa cikinsu kamar basusan da acikin

gidan ake kukanba.

Sanyi qalau jikinta yayi Dan kuwa taga tabbas ko barinsa ya zauna gidan baffa yayi bamai qaunarsa.

'dakin tashige bayan ta aje bokitin hannunta ta zauna kusada yaron Nan itama tafara nata hawayen Dan kuwa tasan daga ita harshi suna

tsaka.

Saidataji kukan harya fara sanyashi laushi takai hannu ahankali ta 'dauke tareda qura Masa Ido Dan Sai alokacin tafara kallon fuskarsa.

Farine sosai Kuma da gani ba lallaine yayi baqi ba duk da dai bazata iya cewa ga fuskar mahaifiyarsa ba sb

d komai yafarune cikin duhu..

Numfashi ta sauke ahankali cikin zuciyarta tace,

Allah yasa su hamma su gano gawarta asuturta kodan jaririn.

Sallama aka fara kwadowa a qofar gidan baffa ya kalli qofar da sauri zuciyarsa na 'dan tsinkewa ya miqe daq

yar tareda tattaro 'yar nutsuwa ya nufi qofar aliyu nabin bayansa.

Murmushin qarfin hali yasaki lokacin dayaga Mal Garba maqwafcinsa yace,

Aa Mal Garba Kaine da safennan.

Cikin 'yar damuwa yace,

Nine Mal salisu an gari lafiya?

Lafiya qlau Ma

l Garba ya iyalin?

Alhamdulillah nace ko anji want bayani akan Anano kuwa?

Washe baki baffa yayi cikin qarfin hali yace,

Eh kaga shaf na manta na sanar maka tun a Daren jiyan tadawo Wai Ashe ita da qafa ta qaraso daga can rugar nuhu shiyasa ta iso

dare sosai.

Masha Allah Abu yayi kyau dama dai nace ne nazo naji halinda ake ciki Kan 6atan nata Allah ya tsare gaba.

Amin Amin Mal Garba nagode.

Bayan tafiyarsa baffa ya Jima tsaye Yana tunani kafin suka juya suka koma cikin gidan Kai tsaye inna

ya kalla yace,

Ki kimtsa yaron ki goyesa duk tsanani Kar kibari agane da akwaisa acikin gidannan.

To tace badan ranta yasoba saidan Bata qetare umarninsa ta miqe ta sake 'dora wasu ruwan.

Cikin qanqanin lokaci Inna tayi Masa wanka ta gasashi sosa

i ta 'debi sabuwar madarar shanu tabasa yasa sosai Nan take yayi luf bacci Mai da'di ya daukesa takuwa goyesa bayanta tasaka hijab bazaka taba cewa akwai 'da a bayanta ba.

Sai alokacin Anano ta'danji sanyi aranta take Kuma mamakin yanda takejin yaron ha

r tsakiyar ranta.

Kamar jira ake Inna ta goyesa Nan take jama'a suka fara zaryar zuwa barka da dawowarta dakuma ganinta da'akayi.

Su ubaidah sunxo Nan suka hauta da fadan tafiyarta datayi Bata tsaya musu ba.

Itadai murmushin yaqe kawai take musu

Koda suka tambayi kumburin fuskarta da Jan idonta cemusu tayi batai bacciba ahanya qunama ta cijeta.

Sosai suka tausaya Mata duk da sun fahimci kaman Bata cikin walwala hakanan suka qarashi firarsu suka tafi.

Su Yusuf kuwa duk iya bincikensu Basu ga

wata gawaba haka suka dawo suka sanarwasu baffa qarshe dai aka tattara zancen aka aje Sai bayan kwana biyu tukuna a yanke shawarar abinyi.

Tunda tadawo kusan komai ya canxa Mata ba kamar da ba da kowa gidan keji da ita kamar su lasheta Amma yanxu kaf ya

yunta iyakacinsu da ita ta gaidasu idansunga dama su amsa idan basuga damaba su qyaleta baffa da jafar ne kawai ke kulawa da ita Sai Usman idan yaga dama shima,

Inna kuwa kadaran kadahan ga baffa dayasata kulada jaririn Dole badan tasoba.

Sosai hanka

lin ananon hankalinta yafara 'dan kwantawa sbd ganin anbar zancen saigashi Randa sukai sati 'daya kwatsam zancen yafara fita Wai akwai jariri agidan Nan maganganu suka fara yawo hankalin baffa yafara tashi musamman da zancen yafara yaduwa Wai 'dan na Anano

ne tunda dai ba Wanda zai haihu a gidan.

Zaune suke a tsakar gida yau duk sunyi jugum jugum bamai magana Sai Inna daketa aikin Kai kawon girkin dare datakeyi Anano kuwa tana zaune tana yiwa Inna wanke wanke jiki a sanyaye sbd tun Daren jiya taji hirar

Inna dake bawa baffa shawarar akai yaron gidan Mai gari ace tsintarsa akayi.

Cikin sanyin murya baffa yace,

Idan muka kaisa mukace tsintarsa mukayi kenan mun bada damar daza'a yarda da zargin da ake Mana sbd zaaga meya Hana tun farko mukaisa Saida ak

a ganomu,

Kawai dai na yanke shawarar aikasa can binni gidan marayu kamar yanda Yusuf yace tun farko.

Da wannan tunanin ta kwana ta tashi sosai taji hankalinta yatashi sbd tausayinsa dakuma qaunarsa dake maqale aranta.

#vote

#comment

#shar

e

[9/12, 11:34 AM]

_wattpad@mamuhgee_

*16*

Ahankali baffa ya 'dago ya kalli yanda take aikin cikin sanyin jiki duk saiyaji qaunar yarsa da tausayinta Dana yaron ya qara shigarsa ya bu'de baki ahankali ya

ce,

Zo Nan Anano.

'dauraye hannayenta tayi ta taso ahankali ta zauna kusadashi ya kalleta dakyau yace,

Anano bazamu bar yaron nanba a gidan Nan sbd mumaganganun dake yawo zasu Bata Miki suna su Bata Mana zuria shiyasa na yanke shawarar Yusuf da Us

man zasu kaisa binni gidan marayu.....

Kaka tasake ahankali batareda yakai qarshen zancen nasaba.

Shiru yayi Yana sauraron kukan nata ganin batada niyar dainawa yasa ya dafa kanta yakira sunanta.

Bata 'dagoba saidai tadan tsagaida da kukan.

Cik

in tsananin qaunarta dake rinjayarsa kowane lokaci yace,

Anano wlh da inada wani zabin bayan wannan da bazan rabaki da 'dannan ba sbd koba komai mun taimakesa Kuma bamusan baiwar da Allah 6oye cikin alamarinba saidai vanida wani zabin kodan gudun lalace

war sunanki.

Cikin kuka ahankali tace,

Baffa Dan Allah karka biyewa maganar mutane ka fasa abinda kayi niyya na taimakawa marayan Allah dabaisan kansaba.

A qule Yusuf yace,

Ke dallah ki rufe Mana shegen bakinki badan shegen iyayinki da rawar ka

nki ba da duk haka Bata faruba,

Wannan yaron yagama barin gidannan Dan wlh bazai zaunaba.

Cikin takaici Aliyu ya kar6e zancen da cewa,

Wama yasani ko shegene uwar tasa ta Haifa.

Katsesu baffa yayi da cewa,

Koma dai meyene shi yaron bayada laif

i tako Ina Kuma kamar yanda Anano tace munyi niyar taimakawa sabida Allah Kuma zamuyi.

Tunda suka fara magana Inna ko inda suke Bata kallaba sai lokacin takallesa cikeda mamakinsa tace,

To yanxu abinda takeson shi kake nufin za'ayi kome?

Eh'''yafa

da Kai tsaye tareda kallon jafar da tuni jaririn ke hannunsa Yana 'dan jijjigasa sbd dagashi Sai Anano ke saukarsa a gidan Sai Inna idan zatai Masa wanka Amma ko baffa Sam bai ta6a daukarsaba iyakaci dai Yana tausayinsa shima sbd ananonsa nasonsane kawai.

Cikin sakewar fuska yace,

Jafar meye shawararka akan hakan?

Kallon yaron yayi yakuma kalli Anano datai zuru cikin hawaye Sai yaji tausanta da 'dan yakalli baffa yace,

Baffa shawarata 'dayace

Komai zakayi kayisane domin Allah badan waniba kokum

a badan abinda wani zai fa'daba..

Murmushin qarfin hali baffa yasaki cikin jinjina Kai yace,

Usman da jafar ku shirya zuwa jibi zamukai Anano gurin gwaggwonta tareda yaron zuwa wani lokaci idan komai ya lafa saita dawo.

Ajiyar zuciya Inna ta sauke

duk dai bahaka tasoba tasone su yarda qwallon mangwaro su huta da quda Amma ko ahakan da sauki sbd itadai dama damuwarta zaman yaron ne agidan bataso ga ananon da shegen taurin Kan tsiya sbd samun daurin gindi daga baffan.

Yusuf da aliyu kuwa miqewa su

kai suka ficewarsu sbd takaicin hukuncin da baffan yanke na barin yaron.

Anano kuwa jikinta ne yayi sanyi ta matsa ta riqo hannun baffan ta kallesa hawaye na gangaro Mata tace,

Baffa Allah zai saka maka da mafificin abinda kayi Koda a bayan ranka ne.

Shafa kanta yayi yace,

Allah yabiyani ta hanyar kawo farin ciki da haske Mai dorewa a rayuwarki ananona.

Jafar ne ya katse yanayin nasu na shaukin uba da 'ya ta hanyar cewa,

Yaron haryanxu bashida suna..

Fuskar Anano baffa ya kalla yace,

Anano za6ar Masa suna.

Sunkuyar dakai tayi cikin fargaba tace,

Abdulshakur..

Su Inna sunaji suna gani baffa yasa jafar ya Kama rago 'daya ya yanke aka ra'dawa yaron suna abinma Sai ya daina Basu takaici sbd ganin yanxu Kam su baffa kawai wahalar

ta fasha sukam sun cire hannunsu musamman aliyu daya tsani Koda ganin yaron.

Kafin jibi ranar tafiyar tayi gata da kulawa sosai baffa da jafar suka shiga nuna Mata harma da Usman yanxu da ananon ke basa tausayin ganin Allah ya 'dauki son abinda batada a

laqa dashi yasa Mata kamar jininta saiyake ganin hakan da wani 6oyayyan sirri daga Allah.

Ranar dazasu tafi sosai tayi kuka kamar ta tafi kenan musamman dataga Inna na farin ciki da tafiyar tasu Dan har Allah Allah take su wuce.

Basu shiga motar mand

eba sbd gudun tsegumi Kai tsaye doguwar tafiya sukai da qafa har bakin babban titi kafin suka shiga motar shiga yola.

Tunda suka iso taji hankalinta yafara tashi Dan hakanan takejin fa'duwar gaba.

Direct wata qaramar unguwar talakawa suka nufa cikin

adaidaita jafar dayasan gidan Yana nunawa Mai napep 'din inda zaibi.

Har bakin kwanar layin gidan aka ajesu Nan baffa ya biyasa suka gangara suka shige lungun.

Ba wata tafiya sukaiba suka iso gidan jafar ne agaba Yana kwada sallama suna shiga Dan qar

amin tsakar gidan asiya matar qanin mijin gwaggon daya rasu ta fito 'dakinta tana Sanya hijab tana ganin jafar ta washe baki tana musu sannu da zuwa tareda 'dauko musu tabarma tana cewa,

Gashi kuwa gwaggon batanan tanacan gidan datake aiki rasuwa akai m

usu matar gidance ta rasu gurin haihuwa.

Allah sarki Allah yaji qanta....cewar jafar dake qoqarin juyawa waje yafadawa baffa da Usman gwaggon batanan.

Kallon hijabin anano asiya tayi ganin Sai muqu muqu take batason asan meyene aciki tace,

Ananon

gwaggo bazaki zaunaba.

Qoqarin zaman take jafar yasake shigowa Yana kallon asiya yace,

To Wai zamu samu Wanda yasan can gidan da gwaggon take Sai akaimu?

Eh Bari nakira Bello yananan waje saiya kaiku yasan gidan.

Qofar gidan ta nufa saidata gai

sadasu baffa kafin ta kirawo bellon a gidan maqwaftansu inda suke kallon qwallo 'dakin abokinsu.

Sallama sukai Mata suka nufi titi Bello Kam Yana tare Mai adaidaita kwatancen gidan yayi Masa Dan shikam baiso ya rasa kallon qwallonsa Dan yau wasar na zaf

i sosai.

Yana fara kwatancen Mai adaidaita yace ya gane sbd gidan ba wani a boye yakeba idan kaje anguwar danma masu adaidaita da mashin Sam basa shiga layin Dan mugayen soldiers din dakecin uwarsu na gadin gidan.

Nesa ka'dan da gidan ya tsaya ya nun

a musu gidan da hannu suka biyasa ya juya suka nufi gidan kowannensu gabansa na 'dan tsinkewa sbd ganin gidan da akace nanne ga sojoji dasuke hangowa tun daga nesa.

Wangale qaton gate din sukaga anyi wasu jibga jibgan motoci suka fito aguje kamar zasu t

ashi sama ta qarshen ita ta tsaya sauran sojojin dake qofar gidan suka fa'da ciki aka figa da qarfi harsaida su baffa suka daka wani mugun tsalle suka ra6e gabansu na qarasa tsinkewa Dan Anano tuni taji ta tsinke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login