Showing 12001 words to 15000 words out of 59902 words

Chapter 5 - iznah Complete

musamman ma kayan aikin.

Tuwon semon da gwaggo ke tuqawa ta kar6a tana cewa,

Gwaggo kawo nayi kije ki huta.

Kallonta gwaggo tayi tace,

Barmin aikina jeki kiji da naki ai...

Qarar fashewar Abu acikin palon ya katse zancen gwag

gon a tare suka Kai kallonsu gurinda ta aje abdulshakur sukaga baya Nan Aida sauri tasakarwa gwaggo tuqin ta shiga palon.

Barbaza idanu tashiga yi tana neman inda yake sbd girman palon.

Zaro idanuwa tayi da qarfin Jin yasaki wata irin qara tareda kuk

a..

Da gudu ta qarasa gaban kayan kallon dake palon

Jini tagani ahannuwansa,

Frame din dake gurin ajiye da hoton nafeesa yajawo ya fasa kwalbar Kuma ta yankesa sosai.

Hoton takalla taji gabanta yayi mummunan fa'duwa ta 'dauke kanta da sauri tared

a duqawa ta 'daukesa tana 'dagowa Yana shigowa palon idanuwanta suka shiga cikin nasa saura qiris Abdul ya kubce Mata tayi saurin tarosa jikinta Sai rawa take sbd kukanda Abdul din yakeyi dakuma idanuwan da saheeb ya kafeta dasu.

Ahankali yakai kallonsa

ga 6arnarda akai Masa yamaido kallonsa kan Abdul dake kuka sosai gashi takasa motsawa ya 'dauke Kai tareda nufar hanyar stairs ya haye.

Kicin ta nufa da 'dan sauri tahau wankewa Abdul hannuwansa Sai qara kuka yakeyi.

Daqyar tasamu jinin yafara tsaya

wa ta saka tissue data gani akicin din ta na'de Masa hannuwa tareda goyasa ta 'dau tsintsiya da mopper takoma palon ta tattara gurin tareda cire hoton batareda tasake kallonsaba ta aje Kan receiver tafito.

Koda dare yayi wani zazzafan zazza6i yarufe Abd

ul Nan hankalinta yayi mummunan tashi sbd har wani irin zabura yake tayi kuka harta gode Allah,

Agogo takalla taga qarfe goma Sha biyu da minti ashirin miqawa gwaggo shi tayi cikin dashashiyar murya tace,

Bari naje nafadawa Kamal saimuje asibiti.

Hijabi ta 'dora Kan doguwar rigarta ta barci ta fito ta nufi part din Kamal din dake facing na saheeb.

Knocking qofar tashiga yi ahankali.

Sake knocking tayi Amma still bai budeba saita qara qarfin knocking 'din sbd yaji.

Motsi taji daga bayanta t

ai saurin juyawa cikin tsananin tsoro..

Ido hudu sukayi dashi ya bu'de qofar palonsa zai fito.

Saurin 'dauke kanta tayi gabanta naci gaba da fa'duwa tanaji ya wuce ta 'dan juyo tabisa da kallo yaje motarsa 'daya ya bu'de ya 'dauko wasu takardu yadawo

.

Sauri sunkuyar dakai tayi ganin ya dawo daidainan Kamal ya bu'de qofarsa Yana ganin itace yayi saurin sa hannu ya jawota ciki idanuwanta suka sauka cikin na saheeb daya dawo kafin ta sauke idanuwanta Kamal ya tura qofar ya rufe.

Kallonsa tayi cikin

tsananin damuwa hawaye na zuwa idanuwanta tace,

Abdulshakur ne ba lafiya sosai Dan Allah asibiti nakeson nakaisa ko chemist.

Kallonta yayi tareda zubewa Kan kujera Yana watsa Mata kallon banxa yace,

Dama sbd wannan ne Kika tadani bacci.?

Kallo

nsa tayi idanuwanta na kawo hawaye tace,

Dan Allah kayi hakuri bazan sake 6ata maka Raiba yanxu muje akaisa...

Qaramin kuka tasaki Dan dama Yana kusa.

Tsaki yaja da qarfi tareda miqewa ya wuce bedroom dinsa ya canzo Kaya yafito riqeda key din mota

yazo yakama hannunta suka fito.

Kallonsa tayi cikin farin ciki da tsantsar sonsa tace,

Ngd.

Not to soon sbd idan Kika cigaba da rainamin hankali zakisha mamakina stupid village girl kawai.

Kallonsa tayi saima kawai taji yaqara shiga ranta taje

da karbo Abdul da sauri tazo suka nufi wani babban pharmacy yasiya Masa magani suka dawo.

Koda gari ya waye lafiya qalau Abdul din yatashi ba wani zazza6i saidai kawai rashin qarfin jiki sosai.

Wanka tayi Masa tabasa abinci da magani kafin tabarwa g

waggo shi ta nufi gurin aikinta.

A hanya shiga Palo ta ha'du da Kamal wani lafiyayyan murmushi tasakar Masa ya 'dauke gira daya Yana qare Mata kallo harsaidatazo daf dashi ya riqo qugunta Yana qoqarin hadata da jikinsa tayi saurin qwacewa takaici yasash

i tureta da mugun qarfin tayi baya da qarfi Sai ajikinsa duk da haka hannunta Saida ya bugu da bangon gurin.

'dago idanuwa tayi cike taf da hawaye suka ha'da Ido ta miqe ahankali tareda shigewa palon tana share hawayenta.

Fasa shiga palon yayi yajuya

warsa ya nufi mota yabar gidan.

Tsaki Kamal yaja tareda fiddo sigarinsa ya kunna yayi Mata mugun ja ya huro hayaqinta waje Yana cewa,

Stupid soldier man,,ka gama Jan ajinka da taqamarka hell is coming Cox nakusa kammala shirina akan tarwatsaka in and

out you'll be in worse than a hell for the rest of your miserable life,,,,

And for this stupid village idiot she and her bastard son sune zanyi amfani dasu na cimma burina and then fewwwww send them to heaven...

Dafasa yaji anyi da sauri ya juyo

Aj

iyar zuciya yafara saukewa ganin mum asee tareda yakurah cikin Shirin zuwa gurin saheeb.

Sake Jan sigarinsa yayi tareda 'dauke Kai yace,

The bastard just left ko minti biyar baiyiba so just keep all the pretendings aside mum asee and tell me ya muke

ciki sbd haqurina fa yafara qarewa,

Zaman Nigeria Nan is fuckin killing me...kullum muna Abu daya akan samun dukiyarnan Amma mun kasa samu idan nace mu kashe monkey fool 'din this stupid yeye girl din tace tanason ta auresa batason ya mutu yanxu and you m

um is like all the evil ideas naki sun 6ace...

Gyara tsayuwa yakurah tayi cikin tsananin takaici itama sbd tanason saheeb Amma tafi son dukiyarsa dashi

mum asee ta 'daukota riqo daga gidan marayu tun tanada qananun shekaru sbd kawai su cimma burinsu ak

an hakan Amma saheeb ya tsallaketa ya auri nafeesa sun kashe nafeesar Amma haryanxu ba wani biyan buqata itama dai Kam tafara Kai maqura.

Cikin baqin ciki tace,

Burina nacin dukiyarsa Yafi na banxar soyayyar danake Masa girma matuqar kirsa da emotion

al blackmail din mum asee baiyi Mana aikiba to Nima banga dalilin barinsa da raiba damacan nasone naji how good he is in bed....

Tsaki mum asee taja cikin tsananin takaici da baqin ciki

Ba qaramin Kai zuciyarta qarshe take ta danneba sbd mugun girman K

ai da miskilancin saheeb,

Cikin qara takaici Kamal yace,

Believe it or not mum wannan bastard soldier step son 'din naki ya daina sonki idan ba hakaba idan uwarsace shegen zai fitane baizo ya gaidataba hakama jiya wannan crazy carrot village girl din

ta zuba Masa coffee ya wuce batareda yatsaya ko gaidaki yayiba hakama yau the psychopath 'din fell on him and the gorilla decided to left without coming to see you again,

To ahaka shekara nawa kike tunanin zamu 6atar gurin jiran burinmu yacika.

Tabbas

saheeb yanason ya canza sbd mutuwar nafeesat Amma Kuma wlh bazan yardaba,

Tun Ina budurwa nakeda burin mallakar wannan dukiyar ta Nan gidan Amma yayata damuke uwa 'daya uba 'daya tamin shigar sauri ta auri alhaji sbd ita ya nuna yanaso tun farko,,,

Tund

a nake arayuwata bantaba son Abu na rasaba bazan iya kallo anty sakeena ta samu rayuwar da ni nake burin samuba shiyasa saheeb nada shekara biyar a duniya na zuba Mata madarar 6era a juice Ina zaune Ina kallonta tana roqona nakira alhaji ko iyayenmu Amma n

aqi ba kalar roqon dabataiminba Ina kallonta hartagama aman jinin 'yayan hanjinta ta mutu nasamu daqyar na auri alhaji,

Yanxu saheeb yayi dukiyar datafi ta ubansa burina ya ninku matarsa taso kawon wargi nasa su bullet suka kaita dajin wani qauye suka cil

lata lahira tsohuwar Mai aikinmu tagano ainihin niyarmu yakurah ta taketa da mota ankaita asibiti acan muka biya Dr ya qarasa cillata lahira to duk wannan wahalar tanason tazama abanza wlh bazan yardaba dolene nasamu yanda nakeso Koda kuwa kowa nawa zai ra

sa ransa..

Kallonta Kamal yayi da manyan idanuwansa dasukai ja sbd 6acin Rai yace,

Yanda kikeji mum haka nakeji nama fiki Dan Nima Zan iya kawar da kowa akan hanyata when I said everybody I mean everyone...harma da Abba.

Kallonsa mum asee tayi cik

in Dan takaici tace,

Dama kana tunanin idan Yana Raye zamu samu yanda mukeso ne?

Hmmm nayo Masa odar allura ta musamman dazata sa Yakoma gwara gawa dashi Dan idan muka kashesa saheeb yatafi ba sake waiwayarmu zaiyiba bare asamu biyan buqata shiyasa kaw

ai Zan nakasashi Dan saheeb din ya dawo gaba daya ko yariga zuwa akai akai.

Murmushin Jin da'di yakurah tasaki sbd ganin komai zai tafiyar Mata ayanda takeso,

Bayan sun gama wahalar mallakar dukiyar zata aikasu indasuka iya aika mutane wato lahira.

Wani Abu Mai 'dumi taji nabin qafafuwanta da sauri takalla taga fitsari ne ya kufce Mata sbd mugun abunda kunnuwanta suka jiye Mata su mum asee na fa'da.

Barin gurin tayi jikinta na tsananin rawa har qafafuwanta na hardewa sbd tsananin ki'dima da firgic

e..

#vote

#comment

#share.

*_EZNAH_*

🌹

_wattpad@mamuhgee_

*19*

'dakin asabe ta fa'da Kai tsaye ta shige toilet ta rufo qofar tareda jingina jikin kofa tana sauke numfashi da qarfi.

Yawu ta ha'diye daqyar akaro na ba adadi kaf

in tafara tattaro 'yar nutsuwa ta cusawa kanta...

Jikinta tafara 'daurayewa kafin ta fito ta zauna bakin gadon asabe tana tunani.

Meyene manufar Kamal akanta da 'danta dayake fa'da?

Dama tun farko ba son gskia yakeminba kenan,

Idan sunason su kashe

saheeb Dan suci dukiyarsa to ita meyene nata da 'danta,,,,,

Tabbas idan sukasan naji Nima kasheni zasuyi kamar yanda sukace sun kashe maman saheeb ta hanyar Bata guba da Mai aikin gidan itama ta hanyar ka'deta hakama matar gidan sun kaita daji sun kashet

a........

Miqewa tsaye tayi gabanta yayi muguwar yankewa sbd wani irin tunani daya shiga zuciyarta..

Fitowa tayi jikinta na qara karbar rawa tabi ta qofar kicin tabar sashen ta Isa gurin gwaggo gabanta na tsananta fa'duwa.

Tattaro 'yar nutsuwa tay

i Dan tanason ta fahimci amsar tambayar dazatayi wa gwaggon.

A darare ta zauna tareda bawa gwaggon baya Dan batason ta fahimci halinda take ciki murya a sarqe tace,

Gwaggo..

Abinci gwggo kebawa abdulshakur batareda ta juyoba tace,

Ya akayi?

Ku

n sake fa'dan ne keda kamalu tunda ke bakida aiki Sai saiyiwa wahalalliyar soyayya kuka.

Batama damu da abinda gwaggon taceba tace,

Yaushene matar gidannan ta rasu?

Watanni bakwai kenan yanxu.

Mummunan bugawa gabanta yasakeyi sbd watanni bakwai

kenan da faruwar komai na haihuwar abdulshakur.

Meyene sunan saheeb na gaskiya?

Abdulshakur..... gwaggo tabata amsa Kai tsaye..

Yani irin yawu ta ha'diye tareda miqewa tana girgixa Kai Dan Sam Bata fatar banxan tunaninta yazamo gskia sbd ganin irin

mugayen mutane marasa imani dasuke shirye da kawar da kowa akan abun duniya takosan abdulshakur dinta Dan qaramin alhakine gurin kashewa.

Daki ta shige da sauri tareda kawar da tunin cikin ranta Dan batamason yinsa.

Kaya ta canxa ta fito tareda 'dau

kar abdulshakur suka fito ta kar6i kudi gurin gwaggo suka fito siyan pad.

A layin bayansu taje siyan pad din sbd can ne kawai da shago tasiyo sun juyo kenan motar sojojin saheeb ta shigo layin da mugun gudu kafin ta Ankara sunyi sama da ita.

Abdulsha

kur dake hannunta saidayayi sama ya daki saman motar kafin ya fa'do qasa cikin jini.

Qara ta qwalla ganin ko numfashi bayayi duk da itama taji ciwo a hannu da gefen fuska haka ta miqe jikinta na rawa tayo kansa tana Kiran sunansa da qarfi.

Rintse ida

nu yayi cikin wani irin yanayi kafin ya fito motar sbd shine yake tuqi da kansa Sai  zayyan dake gefensa tukuna motar sojojinsa a bayansu.

Zayyan ma fitowa yayi ya qarasa gabanta da sauri tareda durqusawa yana ganin halinda yaron ke ciki ya 'dago da sau

ri yakalli saheeb dayake tsaye yace,

We need to take him to hospital now...

Tanajin haka ta miqe da sauri tana qoqarin 'daukarsa Amma batasan sanda tasaki qaraba tareda sabbin hawaye sbd azabar dataji ahannunta.

Jawota taji anyi da qarfi tareda ju

yo da ita taga kamal,

Cikin hasala yace,

So nawa Zan fa'da Miki ki daina fita da wannan bastard son din naki sbd badluck ne agareki Amma kinqi

Gashi kin karya hannunki sbd shi and still kinason 'daukarsa sbd hannun ya qarasa karyewa let me tell you so

mething karkiga Ina sonki duk da nasan kin haifi shege kiyi tunanin idan kin karye ko kin nakasa Zan cigaba da sonki sbd Sam bazan yarda ki 6atamin shirina.....

Fixgewa tayi da qarfi hawaye na ciko idanunta sbd baqin ciki da kunya daya sata Dan kuwa tun

i zayyan ya waro idanuwansa Yana sake kallonta Jin ankira abdulshakur da 'danta shege Mara uba.

Saheeb kallo 'daya yama yaransa suka koma mota da gudu suna sorry sir yashige motarsa tareda janta cikin wani mugun speed yabar gurin motar sojojin ta Mara M

asa baya Dan idan da akwai abinda yafi tsana da qyama to zinace saigashi wannan yarinyar Ashe bayan ganin dayake yimata da Kamal cikin wani irin yanayi har lasisin iskanci ne da ita tunda ta haife shaida....wata tsanar yarinyar da qyamarta yaji tana shigar

sa harma da 'dan yaja qaramin tsaki Dan kuwa badan yana ganin qimar gwaggo ba da har ita har shegen 'danta bazasu qara kwana cikin gidanba.

Hawayen dasuka gangaro matane yasa Kamal Jan tsaki tareda riqo hannunta ta qwace zatabar gurin taga zayyan dauked

a abdulshakur cikin sanyi yace Mata,

Muje akaisa asibitin.

A Motar Kamal suka nufi asibitin zuciyarta Sai tsananin quna take da abinda Kamal yayi Mata Kuma ga halinda Abdul 'dinta yake ciki.

Suna Isa akai gaggawar kar6arsa emergency itama daqyar t

a yarda Kamal yakaita akai dressing din hannunta tareda gefen fuskarta da aka shafa mata ointment.

Ganin yanda ranta yayi tsananin 6acine yasa yafara lallashinta Yana Bata hkr Dan wani 6angare na zuciyarsa na tsananin sonta Amma burinsa nason dukiyane y

ake danne hakan.

Kallonsa tayi idanuwanta na kawo hawaye zuciyarta na karyewa sbd maganar gaskiya har lokacin akwai sonsa maqale aranta saidai zata biyar dashi ta yanda yakeso harsaita gano manufarsa akanta.

Cikin sanyin murya tace,

Ya wuce Amma k

arka sake.

Murmushi yasaki tareda riqo hannunta Yana cewa,

Bazan sakeba my love.

Zame hannunta tayi tareda kallon gefenda zayyan yake zaune Yana waya.

Zayyan baibar asibitinba Saida aka gama komai aka kwantarda abdulshakur din a aminity,.

Ma

gungunan da'aka rubuta dakomai ya biya kafin ya kalleta cikin sakewar fuska yace,

Tom Zan tafi tunda komai yafara daidaita zuwa gobe insha Allah zamu zo tareda saheeb saimu qara dubasa Allah ya basa lafiya yakuma tsare gaba.

Amin nagode....tafada cik

in sanyin murya.

Kallon Kamal yayi yace,

Kamal kozaka saukeni gida tunda kaga yanda mukazo.

Kallonta Kamal yayi tareda sakar Mata murmushi yace,

Ok baby Zan dawo zuwa goben Nima ok?

Kai ta 'daga Masa ya wuce Yana murmushin mugunta itama bins

a tayi da wani mugun kallo aranta tana cewa,

Zakai mamakin halinda zaka tsinci kanka kaida 'yar ta'addar uwarka ranar Dana gama sanin manufarku na  wargaza muku komai.

Koda Kamal ya sanarda gwaggo abinda yafaru hankali ya tashi da daddare haka ta shi

rya ta nufi babban  palon saheeb cikin sallama.

News yake kallo Amma Rabin hankalinsa nakan wayarsa da mum asee keta Kira.

Amsa sallamar yayi cikin maqoshi tareda yiwa gwaggon kallo 'daya ya 'dauke.

Cikin jimami tai Masa maganar tanason yasa akait

a asibitin sbd Anano bazata iya da sha'anin yaro ita kadaiba musamman da akace taji rauni itama a hannu.

Tsuke fuska yayi batareda yakalli gwaggon ba yace,

Bazata iya 'dawainiyarsaba ta haifesa

Kije kiyi kwanciyarki idanma bazata iya 'dawainiyarsa d

a wahalarsaba ta koya yanxu ko ta nemi ubansa ta miqa masashi.

Kallonsa tayi taga yanda fuskarsa take a ha'de saita miqe takoma daki ta zauna cikeda tausayin ananon Dan kuwa tasan raguwa ce sosai ta wannan fannin.

Har dare yayi Anano bataga gwaggo ba

hankalinta yaso tashi Amma ganin har lokacin abdulshakur bai farkaba saita maida hankalinta kansa har bacci ya dauketa a zaune.

Da safe gwaggo tayi musu abin Kari tasa a kwando ta shirya Dan niyarta Yana fita aiki tabi Kamal ta tafi asibitin.

Qarfe

goma saura yafito cikin shirinsa na qananun Kaya black trouser da dark blue shirt Sai black shade na warby parker dayayi matuqar yiwa farar fuskarsa kyau ya nufi palon mum asee.

Tana ganinsa wani Abu ya danne numfashinta daqyar ta tattaro numfashinta ta

sakar Masa murmushi tana cewa,

Gud morning my son.

Morning mum''''yace Yana Zama kusada ita tareda gaida Abba daya shigo palon lokacin.

Kallonsa Abba yayi yace,

Anjima idan kadawo inason ganinka akan wasu takardu danakeson kasa hannu.

Ok ins

ha Allah Zan dawo around 6.

Wani 'dadi mum asee taji Dan kuwa tasan yau Abba zai fito da duk takardun kadarorinsu kafin saheeb din yadawo abban ya tashi aiki ta 6oye takardun.

Miqewa yayi ya fice a bakin motarsa ya tararda gwaggo zayyan dayazo yasa a

nkirata.

Shiga yayi suka bar gidan Yana ganin sun 'dau hanyar asibitin ya qara tsuke fuska zaytan na luredashi yasaki murmushi kawai.

Sbd gwaggo ya fito motar suka shiga.

Zaune take bakin gadon da Abdul yake kwance Kamal na zaune gabanta Yana shaf

a Mata ointment a gefen fuskarta Sai murmushin yaudara take sakar Masa shikuwa ji yake kamar yacire Mata ciwon.

Ji sukai anbude qofa atare suka kalli qofar cikin idanuwansa idonta yafara sauka tayi saurin 'dauke Kai gabanta na fa'duwa da mugun kallon ts

ana da qyama dataga ya jefota dashi.

Kallon hannun Kamal dake fuskarta tayi tai saurin janyewa tareda miqewa tana gaida zayyan da gwaggo Dan shi ko fuskar gaidasa Bata ganiba Dan ba qaramar qyamarta ta hango a idanunsa ba.

Cikin sakewa zayyan ya mats

o Yana duba Abdul din daya tashi lokacin Yana cewa,

Lallai yaron Nan soldier ne Dan gashinan yatashi da qarfinsa.

Dariya gwaggo tayi tace,

Ina wani soja anan gashinan kwana daya duk yasa ananota ramewa qilama kwana tayi tana kuka.

Murmushi Anan

o tasaki tace,

Kai gwaggo duk ciwon Nan dayake ciki bazaki raga masaba jifa Yan.......

Ha'diye sauran maganar tayi sbd idanuwansu dasuka shiga cikin na juna taga yanda fuskarsa ke qara tsuke saita waske tareda miqewa tashige toilet kamar munafuka Dan

dai itakam Sam Bata iya Zama indai Yana guri sbd zuciyarta ke bugawa da qarfi.

Shima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login