Showing 57001 words to 59902 words out of 59902 words

Chapter 20 - iznah Complete

yafi 'daga mata hankali shine kamal dayazo ya sanar da ita duk watannin nan da

saheeb bayanan Ashe yana tareda matarsa..

Kallon yakura daketa faman cin gasashen kifi tayi taji ranta yayi mummunan 6aci

tananan tana tunanin masifar dake shirin 6allo musu shegun yaran ko ajikinsu..

Kasa hakuri tayi ta aika asabe kiran saheeb 'din a

mma kai tsaye sojoji suka koroto

Ta miqe da kanta taje suka sawa idonsu toka suka hanata ko isa qofar part din tadawo xuciyarta na tafasa lallai gwara su harhada abinda zasu sata su bar qasarma gaba 'daya kafin asirinsu yatonu dan tsaf wainnan sojojin za

su daddatseta su watsar shara...

Koda yadawo daga masallaci Samuel yakawo aiken dayayi masa ba dinner dayayi order

Daqyar yasamu ya lalla6ata taci kadan takoma ta kwanta jikinsa.

Washe gari ma duk yanda taso ganinsa bata samu ba

Sukam suna shirya

wa suka fito Samuel yayi gidansu zayyan dasu

Breakfast kawai sukayi suka kama hanyar zuwa qauye.

Sosai zazza6inta Keson dawowa sbd gajiyar tafiye tafiyen datai kwanakin ba Hutu.

Suna isa taji ta'dan wartsake tafito da saurinta ganin Abdul a qofar g

ida gurinsu jafar da baffa yana wasa hankalinsa kwance yaqara girma da wayo..

Yana ganinta ya taso aguje yana cewa,

Mommahna tadawo baffa...

Cikin tsananin farin ciki ta yunqura da sauri ya riqe hannunta batareda yadamu dasu baffa qasa qasa yace,

Easy ma'am,,,

Zame hannunta tayi tana harararsa tace,

Abinda ke hannuna shine nawa Wanda banganiba bazai hanani murnar ganin na hannunaba,

'Daukesa tayi sama tareda qanqamesa tanajin qaunarsa har cikin ranta.

Cikeda farin ciki jafar yataso shida

us man suka tarbi su saheeb 'din suka qarasa gurin baffa dake zaune yana gyarawa Abdul tsohuwar keken daya siyo masa a kasuwar dataci satin daya gabata.

Baffa baki har kunne yake kallon ananonsa cikin tsananin farin ciki Mara misali yana amsa gaisuwars

u..

Su Yusuf ma cike sukeda farin cikin ganin kwanciyar hankali tareda farin ciki atattareda qanwarsu.

Zama sukayi su saheeb itakuma tayi cikin gida tareda nabeela da Abdul dayaqi ko yarda ya sauka jikinta

Saheeb kuwa kasa 'dauke idonsa yayi kan ya

ron har suka shige

Jin zuciyarsa yake sayau sbd rashin damuwar komai da farin ciki.

Gwaggo na ganinsu farin cikin duniya yacikata musamman data qyallo qaruwa atareda dukkaninsu su biyun

Sun murje sai qyallin Hutu da kwanciyar hankali suke.

Inna m

adai bata 6oye farin cikintaba nan aka hau 'dawainiyar hidima dasu.

Baffa nashigowa tareda gaba 'dayansu bayan sunyi sallar azahar nan aka shimfida tabarma babba guda biyu kowa ya zazzauna takoma kusada baffanta sbd daga ita harshi sunyi tsananin kewar

juna.,

Abdul daya maqale mata takalla cikin kulawa tace,

Abdul baka gaida daddy zayyan ba ga kuma dadynka maza jeka gaishesu.

Qin tashi yayi daga jikinta kwance yace,

Daddy ina kwana.

Dariya kowa yayi banda saheeb daya qurawa abdul din ido z

uciyarsa da gangar jikinsa nason jinsa cikin jikinsa.

Abinci kowa yaci banda ita data kasacin komai sai fura datasha kadan

Ido ya kafeta dasu tasan meyake nufi ta marairaice fuska tareda 'daukar part 'daya na kaza takai bakinta,

Nabeela kuwa nik tayi

hankinta kwance musamman ma dambun dayaji zogala yayimata dadi sosai.

Bayan sungama ne zayyan ya zayyanewa su baffa komai nan mamaki da tsoron allah suka kamasu sosai

Tausayin ananonsu da saheeb din suka shigesu musamman idan suka tuno zargin dasuka r

unga binta dashi lokacinda tazoda abdul yana jinjiri.

Sai kusan magriba suka baro tareda gwaggo da abdul Wanda har lokacin baije gurin saheeb ba yana jikinta shikuwa bakinsa da jikinsa duk amace suke saidai ido dayake binta dasu duk motsinta itada abdul

.

Suna isa wanka kawai sukayi suka kwanta ya jawota jikinsa tareda sakin ajiyar zuciya.

Washe gari da kanta ta ha'da breakfast takoma tayo wanka suka fito Palo..

Bedroom takoma 'dauko wayarta daidai shigowar abdul da gudu.

Ahankali ya rankwafa

ya 'daukesa tareda yimasa kyakkyawar runguma zuciyarsa na tunano masa nafeesat.

Dawowa tayi daidai lokacinda ya ajesa kan cinyarsa yace,

I wish your mum is here to see how quick you grw.....

Kanta idanuwansa suka sauka yaga yanda yanayinta yaso ca

nzawa..

Dining ta nufa yayi saurin riqo hannunta zaiyi magana ta girgixa masa kai idanuwanta na cikowa tace,

Sorry.

Jawota yayi ya 'dora a cinyarsa 'daya yace,

You're the only one, and you'll forever be the only one..

Abdul dake kallonsu ta

kalla qasa qasa tace,

I know..

Breakfast sukayi a dining yau dole saidataci chips sosai sbd shida abdul suka data gaba sunata bata harsuka gama.

Hayaniya suka jiyo a harabar gidan ya miqe ya nufi qofa tana biyedashi riqeda abdul hankalinta na tashi.

Mum asee ce keta zubawa sojojin fada sbd dukan dasukaiwa kamal daga ta aikosa kiran saheeb

Sukuwa umarnin ogansu sukebi daya basu damar cin uwar duk Wanda ya 'daga musu murya agidan har mum 'din bai cireba.

Tana ganinsa ta qaraso gabansa cikin tsa

nanin 6acin rai tace,

Kaine kabawa wainnan umarnin hanani ganinka kome?

Rintse idnuwansa yayi ahankali sbd bayason 'daukar zafi ko fansa akanta sbd allah ne zai tsaya masa saidai ganinta na matuqar qona zuciyarsa da hakurinsa tareda tunku'do zuciyars

a gason 'daukar mataki.

Anano na ganin halinda yashiga tayi saurin matsowa ta riqe hannunsa

Ya bude ido yana ganinta yaji zuciyarsa ta sauka ya fiddo wayarsa zai sake kiran zayyan saigasu sun shigo harabar gidan shida Ahmed.

Komawa Kansu kallo yayi

suka qaraso gaban saheeb 'din

Ahmed ya miqa masa takardun dayasashi kawowa safiyar yau daya kirasa.

Kar6ar takardun yayi ya budesu 'daya bayan 'daya ya karanta kafin ya juyo gurin anano da duk jikinta ke sanyaye ya kamo hannunta tareda saka mata Biro

ciki ya'daga takardun yace mata,,

Sign..

Kallonsa tayi hankalinta na qara tashi ya tsuke fuska yakoma saheeb 'dinsa na da yace,

Sign..

Hannunta na rawa kamar yanda idanuwan mum da kamal ke rawar son ganin takardun meye..

Signing tayi a inda t

aga subayenta ta miqa masa biron.

Bin takardun yayi yai signing ko dubawa bayayi yana gama signing ya jawo hannunta har gaban mum ya 'daga takardun yasaka cikin hannun anano murya a karsashe yace,

Agaban lawyer na da aminnina tareda yarana ni saheeb

na mallakawa matata da 'dana jinina dukiyata da kadarorina gabaki 'daya kona mutu babu Wanda yakeda gado da ita....daga yanzu abinda zancigaba da mallaka sune nawa Dana 'yayana masu zuwa.

Kusan atare mum da ananon jiri yayi musu muguwar 'diba ya tareta

tareda kallonta yace,

Yes and ban amince kiyi ko kalma 'daya akan hkanba..

Mum kuwa yakurace tai saurin tareta sbd ganin yanda zufa ya yanko mata lokaci 'daya ya jiqata sbd masifar bala in da taji saheeb yafada,.

Kamal kuwa wani irin juyawa yaji k

ansa na masa tsabar baqin ciki nan take qwayar dayakesha tafara motsa masa cikin kai...

Wasu takardun Ahmed takuma miqo masa ya kar6a ya yaduba ya miqawa mum yace,

Wannan sune takardun gadonki keda 'danki wainda Alqali da lauyoyi suka raba

Nibazan

iya cin rahamba dan haka gasunan zaku iya tafiya sbd har hankalina bazai ta6a kwanciyaba idan kuna kusada iyalina.,

I cant ensure my family safety with you people around so please mum...

Qurawa abdul ido tayi zuciyarta na kumbura

Ganin irin kallon d

atakewa abdul ko qyaftawa da motsi takasayi zayyan ya matso yace,

Yes 'dansa da nafeesat ta Haifa tabari shiyake nufi......

Kawai ganin sukayi ta yanke jiki ta fadi asume

Ihu yakurah tana kiran sunanta cikin tashin hankali ita yanxu idan mum ta mut

u batada madafa tunda dai basu karbo dukiyarba bare tasamu.

Kamal kuwa takardun hannun anano ya damqo tareda kaimata mugun naushi aciki ya tureta baya da qarfi ta bugi qarfen rumfar motocin dake gurin da qarfi ta sulale ta zube gurin jini biyo doguwar r

igar jikinta.

Arikice Gwaggo da asabe sukai kanta suna salati,

Gate ya nufa da mugun gudu

Cikin zafin rai da qulewar zuciya saheeb ya kar6e bindigar hannun yaronsa 'daya kusan atare shida zayyan da samuel tareda soldier biyu suka sakar masa harbi a q

afa,

Bullet biyar suka shiga qafafunsa lokaci 'daya nan take ya zube agurin yana shure shure.

Arikice yayo kanta yana kiran sunanta daqyar ta bude idanuwanta ta mayar ta rufe jikinta yasaki.

Ruwa yakurah ta lemawa mum

Mum din na tashi taga kamal

cikin jini yana shure shure a haukace ta miqe tayi gurinsa tana ihu kamar mahaukaciya,

Dama akwai key hannun yakura suka ciccibesa suka saka mota aguje mum takar6i key tashiga ta tayar..

Gurinsu saheeb dake 'daukeda anano zai saka mota da abdul a ge

fe ta kalla taji zafin zuciyarta har abada bazai gusheba matuqar bata raba wainnan ukun da duniyaba.

Giya tasa tayi cikinsu a tsiyace da motar zayyan da Samuel ne suka turesu gefe harsaida goshin abdul ya fashe.

motar tayiwa rumfar aje motoci mugun bug

u saida rumfar ta karye qaton qarfe yafa'do kan motor ya sai cikin tsakiyar kan kamal ya rabe biyu.

Ihu tasaki tafito hartana faduwa tana dubawa taga kan kamal ya tarwatse sai kawai ta zube wasa Rabin jikinta ya shanye sai shure shure take.

Zaburowa

su Samuel sukayi zayyan ya 'daga musu hannu yace,

Kawai dai Ku fitar dasu ko jininsu karkubari saheeb yazo ya tarar Ku wanke.

Saheeb kuwa koda suka juyo tuni yayi asibiti da matarsa da 'dansa.

Kamar kayan wanki ba tausayi haka su Samuel suka kwash

esu harda gawar kamal suka kaisu bolar gefen tasha suka watsar suka tafiyarsu.

Zagayesu akai anata kallo wasu su tausaya musu wasu su tsine musu sbd sunsan abinda yasa akai musu haka ba qaramin mugun Abu bane.

Ganin yanda quda suka suka fara binsu ya

sa yakurah ta zari takardun gadon da saheeb yabayar ta lulale tabar mum nata wani irin shure shure har lokacin ta nufi hanya tana waiwayen mutanen dasuka fara biyota dan ganin meta Zara a jikin mum

Gurin waiwayensu tai titi wata babbar mota takawo aguje t

abi ta kanta ta wuce kuma drivern yaqi tsayawa

Takardun tareda jini da kwanyar kanta mota ta markade.

Ganin gawa biyu lokaci 'daya yasa mutanen gurin suka 'dauki gawarwakin suka kai daji suka zubar dan Dama duk gurin 'yan tasha ne,

Asibiti kuwa

suna isa aka kar6eta saidai cikin ikon allah da yardarsa cikin bai tsayaba ya 6are Wanda alamarin ba qaramin ta6a zuciyarsa yayiba matuqa dan saida su zayyan da Gwaggo suka tausaya masa.

Lokacinda ta farka taga halinda yake ciki tasan cikin ya 6are said

ai ta sakawa kanta juriya sbd karta qara masa damuwa saidai daga baya tayi kuka kamar me

Lokacinda yazo da safe yana kallonta yasan tayi kuka ya qarasa kusada ita ya zauna tareda riqo hannuwanta ya damqe cikin nasa

Batasan sanda kukan yadawo mataba ta

fada jikinsa ya rungumeta yana shafa kanta danshima zuciyarsa na cikin zogin rasa gudan jininsa.

Kwananta 'daya aka sallemesu suna dawowa su baffa da inna dasu Yusuf gabaki 'daya na isowa Samuel yaje yadaukosu umarnin ogansa.

Cikeda tausayawa suke ma

ta sannu da ya jiki

Nan su asabe da nabeela suka girka abibci kala kala.

Ganin yanda kowa yadamu yasa ta 'dan sake tanuna tacire damuwar komai.

Aranar su baffa sukaso komawa saheeb ya hana sbd Dama niyarsa sune zasu dawo nan gidan suci gaba da zama s

hikam da matarsa da 'dansa sabon gida zasu koma inda bazai ringa ganin komai yana tunasu mum ba.

Daqyar su baffa suka amince shidinma saida anano tace yannanta ta za6a su kular mata da dukiyarta.

Tafiyar sati biyu yayi kafin yadawo su tare gidansu.

Tun bayan tafiyarsa mummyn nabeela da Gwaggo harma da nabeela suka duqufa gyarata nan take takoma shar Lamar budurwar larabawa.

Ranar dazai dawo tana sane ta gudu gidan nabeela daga aje abdul school.

Bajewa sukayi suna fira a palo sai qyalqyala dar

iya suke hankali kwance..

Tun a airport zayyan yafada masa anano na gidansa dan haka kai tsaye can suka nufa.

Zayyan ne yashigo yashige bedroom 'dinsa tareda kiran nabeela aka barta ita 'daya ta fiddo wayarta akaro na ba adadi dan duba ko misscall di

nsa amma still babu ta turo baki tana gyada kai.

Tsayawa yayi daga nesa tareda qura mata idanu yana qare mata kallo

Sonta na qara karya kuxarinsa.

Juyowa tayi da niyar kallon agogo idanuwansu suka hadu da juna wani irin sanyi da farin ciki ya ratsa

ta amma saita 'dauke kai tana qowarin miqewa.

Gyara murya yayi yace,

Da zarar kin bar palon nan ba abinda zai hanani komawa inda na fito.

Shagwa6e fuska tayi tana kallonsa tace,

You know this is not fair right?

Murmushi yayi tareda nuna mata q

irjinsa ta nufesa tana jujjuya ido tun bata qarasoba ya fixgota ya rungume suka saki ajiyar zuciya kusan tare ta qara shigewa jikinsa tana qara qanqamesa.

Dago fuskarta yayi yace,

Lets go home missty..

Murmushi tayi tace,.

Yes baby.

Batareda k

o masu gidan sun saniba tabi mijinta suka wuce warsu a motarta.

Sabon gidansu direct ya nufa da ita takallesa zatai magana ya 'Dora hannu a bakinsa yana kallon cikin idonta yace,

You're my wife i can take you anywhere anytime i want OK?

Da kansa ya

bude mata mota ya riqo hannunta suna shiga ga mamakinta taga asabe nata aikin kaida kawon Girki koina sai qamshi da sanyin ac ke tashi.

Bedroom dinsa suka yada zango yana shiga wanka ta sulale ta fito sbd hayaniyar abdul da'aka kawo data jiyo.

Qaton

lafiyayyen 'dakinsa dayaji adon komai na yara takaisa ta cire masa uniform tai masa wanka ta sako masa kayan shan iska suka fito Palo daidai fitowarsa da gudu yayi gurinsa yana tambayarsa yaushe yadawo suka nufi dining suka ci abinci,

Suna gamawa tayi mas

a shirin islamiyya Abu yatafi kaisa ita kuma tayi sallah suka fara shirya abincin dare.

Kwanan mum asee biyu agurin wani 'dan qwaya yazo da qaramin baronsa ya kwasheta yasaka ciki ya dinga bara da ita yana samun kudi

Id an dare yayi duk inda yasamu y

a zubeta nan saida safe yazo yakuma 'daukarta sbd yunwa da wahala ga shanyewar jiki da dau'da ta nanna'de takoma kamar wani tsumma.

Tsaye take gaban mirror tana qoqarin 'daure gashinta da band ya riqe hannun yana qarewa rigar baccin jikinta kallo taciki

n madubin sbd da ita da babu duk 'daya

Ya birkitota idanuwansa na sauyawa murya a shaqe yace,

This dress is making me loose my mind,,,

Shafo wuyanta yayi tareda zura hannunsa 'daya cikin rigar

Taja wani irin numfashi tareda kamo fuskarsa ta hade

bakinsu tana lalubo harshensa

Shikuma ya cirata ya kwantar agado yabita.

Washe gari daqyar ta iya fitowa ta shirya abdul ya wuce school sbd taji jiki matuqa kamar Daren farkont.

Koda abdul ya wuce tana dawowa suka sake lulawa soyayyarsu hankalinsu k

wance...

Da daddare sukaje gida ya gaidasu baffa itadai kasa sakewama tayi sbd kun ya.

Cikin qanqanin lokaci tasamu wani cikin Wanda yafi na farko laulayi sosai qarshedai saida suka dangana da barin qadar yakaita ganin Dr a madina daganan sukai zaman

so suna shan love sbd cikin maitar ubansa aka saka masa kullum suna maqale abinsu.

Watansu biyu acan nabeela ta haifi baby girl 'dinta suka dawo dole yarinya taci sunan Fatima wato mum 'din zayyan.

Tunda cikinta itama ya tsufa taso takoma gurinsu Gwa

ggo kai tsaye yaqi dole sai gwaggonce tadawo gidansu.

Zuwan Gwaggo da sati 'daya ta haihu a asibiti bayan uwar wuyar datasha itadashi sbd kasawa yayi ya tsare kamar zaiyi hauka shima sbd ganin halinda tashiga kodata haihu ita sharkab da gumi shima shark

af.

Baby boy tasamu Wanda yayi saheeb Zak bai bar komaiba.

Ranar suna yaro yaci sunan Abba suna kiransa da saheeb junior.

ALHAMDULILLAH.

Nan nakawo qarshen labarina na eznah Wanda yayi nuni da shi aikin alkhairi kokuwa sharri binka yake basai W

anda aka cuta yadau fansaba,,

Arayuwa karkazamo mai sonkai da qyashi tareda zalama dan kuwa sune suka kai mum asee da tawagarta ga wannan mummunan qarshen,,

Su nuratu da bullet kuwa koba'a fada qarshensuba kunsan bamai kyau bace sbd shi mugun abu shuka

ce girbarsa ake dan haka allah yasa muyi aiki da darasin dake ciki kuma mu watsarda illar dake ciki....amin.

Kurakuren ciki allah ya yafe mana dani Dana rubuta daku masu karantawa.

Karku ce bai kamataba ace novel yaqare anan sbd banga amfanin jansaba

bay an Riga an isarda saqonda akeson isarwa jansa ba abinda zai qarar sai rage dadinsa.

Godiya ta musamman ga dukkanin groups danake ciki dan bazan iya lissafosuba amma kadan daga ciki sune,

Mamuhgee's novella,

Mamuhgeee fans grp 2 to 3

Masoya

n mamuhgeee

Zauren biebie isa

Biebiedee fans grp

Khadijatus crew

Ummu subay'a fans grp

Realhausa Fulani

Duniyar marubuta

Zama na Amana 2

Hausa novels palava

Faeamgnovels

Sophy novels,

Members na kundin qaddarata fans grp

Musan kanmu marubuta,

Aysha sada machika fans grp,

Aufana fans grp,

Lubbies crew

Meesharh lurv fans

Dokin karfe association

Dandalin raheenat

Kai im really sorry I can't name all amma dai ngd duka har wainda ban zayyanoba.,

*Thank you my wattpadians i love you guys

morethan you guys can imagine...*

Thank you,

My momy Aysha hassan

My zinnie,

Balkeey shuwarh

Aunty sis

Ummumaryam

Splendid

Ag

💞💞💞💞💞

Anfa

Sisin mama

Real maidambu

Mum subay'a

Biebiedee

Raheenat Niamey

Faeamg

Dadah

Sameera ilyas

U

hhhmm im sorry nanma i cant name them all

Thank you all allah yabar qauna saikun jini gaba.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login