Showing 45001 words to 48000 words out of 122467 words

Chapter 16 - Buzu Book 2 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

48

nake ci ta zauna mu ci tare"

Ummi ta ce "Baba wayarta fa ba ta shiga, tun kafin na zo gidan nan, nake ta gwadawa, amma ba ta shiga."

"Ki sake kira ki ji dai"

Ummi ta karSi wayar ta kira Nana, amma aka ce wayar a kashe take.

Baba ya dasa faWa, Ummi a sanyaye ta ce "Dan Allah Baba kar ka yi mata baki, wallahi idan aka nustu Nana ba ta da laifi a cikin lamarin nan. Tin fil azal fa ba bincike aka yi ba, ba a san daga ina mutumin nan yake ba, ka aura mata shi, saboda kawai ka na tunanin su na aikata Sarna, alhalin babu cikakkiyar hujja da ta nuna hakan. Ba ta bujire maka ba ta yi biyayya, duk dan kar ta dawo gidan nan, kamar yadda ka gindaya mata cewar babu zawarci, ya sanya ta dage kai da fata, ta yi aiki tu?uru ta jure wahala da ?alubale take jinyar mutumin nan. Ka san Nana da gudun magana, duk tsoron abin da ka iya biyo baya ya sanya ta yanke wannan hukuncin, ka yi ha?uri a yi mata addu'a kamar yadda ta bu?ata "

"Amma Ummi, Nana ko yayyanka Naman jikinta zan yi na cinye dan ba'i ba gara ta dawo mini nan ba! Dan me za ta kama hanya ta tafi Nijar? Gurin uban wa za ta je?"

Jamila ma ta ce "Tun da dai ta riga ta tafi, dan Allah ka yi ha?uri"

Baba ya rasa abin da yake yi masa daWi, ya shuri takalmansa ya yi waje.

*****
Su na tafe a hanya, Nana tana addu'a, tana fatan Ubangiji Allah ya sau?a?a mata, ya ta?aita mata wahala. Ya haWa ta da Sayyid cikin aminci, tare da fatan duk inda Sayyid yake, ya kasance cikin aminci. Ta maimaita Hsbunallahu wa ni'imal wakil, babu adadi, tare da tawasalli da ayoyin Al?ur'ani a kan Allah ya shiga lamarin ta, ya sau?a?a mata wahala.
?arfe shida saura, Nana suka sauka a? MaraWi. Tun a Nigeria ta sai 'yan kayan ciye-ciye ta zuba a Jakarta.
Ta yi sallar la'asar ?asaru, sannan ta tsaya tana ?arewa tashar motar kallo, tana tunanin ma ta ina za ta fara. Ta ji ?afafuwanta kamar ba a jikinta suke ba, saboda nauyi, sun kumbura sun yi suntum, saboda azabar nauyi da gajiyar tafiya. Ga Wan cikinta ya yi jingim ko motsi ta ji ya daina yi saboda azabar wahalar tafiya, Bayanta da mararta suka ?ulle mata, saboda azabar wahala. Ga jikinta tamkar an sassara ta, saboda gajiya babu isasshen gurin mi?e ?afa.
Masu babur na ta tambayarta ina za ta je, amma ta yi musu shiru, ta Wauki bagcon kayanta, ta yi gaba. Tamkar ba ta jin jikinta, haka ta din ga jefa ?afa tana tafiya. Ta yi nisa sosai da tasha, ta fara hango unguwanni da gidaje.
Duhun magariba ya rufa, ta samu wani gida kawai ta shiga. Matar na tsugune tana tu?a tuwo Nana ta yi sallama.

Suka gaisa da Nana, matar ta tsaya tana kallon ta, ta ji abin da ya kawo ta.
Nana ta ce "Dan Allah baiwar Allah, ni ba?uwa ce, hanya ce ta biyo da ni, dan Allah salla nake son na yi, idan babu damuwa zan kama ruwa ne na yi alwala".
Matashiyar matar ta ce "To ba komai. Ga banWaki nan da buta a ciki"

Nana ta ajiye kayanta, ta shiga banWakin ta zubar da uban fitsarin da ya cika mata mara dam. Ta yi mi?a saboda gaSoSinta da suke yi mata ciwo.
Sannan ta yi alwala, bayan ta yi alwalar, ta tsaya ta Waga cikinta, tana Wan tattaSawa cike da damuwa, jin sa shiru bai dame ta da motsi ba.

"Haba yaron kirki, ka motsa mana ko na ji daWi, haba Wan Baba. Nana na cikin damuwa dan Allah ka motsa" ta yi maganar a hankali cikin tsoro da damuwa, dan ta ji ana cewa idan Wa ba ya motsi, to mutuwa ya yi. Har ta fitar da ran Wan nan zai motsa, ta tsorata idonta ya fara cika da hawaye, kawai ta ji ya motsa a hankali, sai kuma ya ci gaba da motsawa.
Wata irin ajiyar zuciya ta yi, ta shafa cikin ta ce "Alhamdillah, Allah ya bayyana mana Sayyid Winmu cikin aminci" Gaba Waya ta manta a banWaki take.
Ta fito matar ta ba ta dadduma a Waki, ta shiga ta tayar da salla. Bayan ta idar da sallar, ta zauna a kan sallaya, ta din ga tasbihi tana gaya wa Allah damuwarta, har aka yi sallar isha'i.
Nan ma ta tayar da salla ta yi, tana cikin addu'a matar ta shigo da kwanuka, ta ajiye.
Nana ta shafa Addu'ar ta kalli matar ta ce "'yar uwa Na gode sosai da sosai, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi na gode ?warai da gaske"

"A'a babu komai, musulmi ai Wan uwan musulmi ne, ki ci abinci kafin ki tafi dan Allah"

Nana ta ce "A'a, na ?oshi Alhamdillah, Allah ya saka da alkhairi, ya biya miki bu?atunki na alkhairi"

Matar ta ce "A'a daga gani daga tafiya ki ke, ga juna biyu, ai sai wahala, dan Allah ki ci ko kaWan ne kafin ki tafi" Nana ta dage matar ma ta dage. Da ?yar Nana ta amince ta Wan ci Abincin kaWan sai dai babu abin da take tunani, sai yadda za ta yi da gurin kwana.
Ta rufe sauran Abincin ta ce "Na gode sosai da sosai 'yar uwa, Allah ya saka da alkhairi"
Matar ta amsa da "Amin, Allah ya kiyaye hanya"

Nana ta amsa da Amin, ta Wauki jakar kayanta ta yi waje.

*****
Babar Nana wuni ta yi sukuku, gaba Waya hankalinta a tashe, sai koke-koke take yi. Baban su Walida kuma ya yi burus da ita.
Ganin kuka da damuwa ba zai fishshe ta ba, ya sanya ta yi alwala ta hau kan sallaya, ta gabatar da salatul haja, sallar neman biyan bu?ata a gurin Allah.
Ta Waga hannayenta tana kuka, take yi wa Allah kirari da magiya.
"Allah kai ne Allah, Allah kai ne ka halicce ni ka kuma halicci Nana, ka rayata ta girma cikin ikonka da kulawarka. Ya rabbil arshil azim duk inda yarinyar nan take, Ubangiji Allah ka kai mata Wauki, da ita da abin da yake cikinta. Allah ka kare ta daga dukkanin sharrin abin ?i, Allah ka zama gatanta ka tsare mini ita. Ya hayyu ya ?ayyum domin kyawawan sunayenka maWaukaka masu girma, Ubangiji Allah ka kai wa Nana Wauki, ta inda ba ta zata ba" ko abinci ba ta iya ci ranar ba, gaba Waya addu'ar wunin ranar, Nana kawai take yi wa.

Can gida Baban su Nana ma, an ba shi Abincin dare, amma ya gagara ci sai uban tagumi da ya rafka. Lissafinsa kawai gidan uban wa za ta ga je a Nijar? Hannun wa za ta faWa kuma a ina za ta kwana?
Nasiru kuwa tun da ya samu labari shi ma abin duniya ya dame shi, kuma ya Wora alhakin hakan a kan mahaifin su.

Mama ta ce "Wai baban Jamila ba za ka ci Abincin ba sai ya sandare?"

"Wai wane Abinci zan iya ci? Wanan shashashar yarinyar, tana can babu uban da ya san a yaya za ta kwana? Kai Nana muguwar sokuwa ce. Kin ga Wauke Abincin nan, gurin Malamin Almajiran can zan je na gaya masa, ko kiranye ne a yi mata ta dawo gida dan ubanta".

"Kiranye kuma?"

"Eh mana, tun da dai shi mijin nata mutumin banza ne, bai san abin da ya dace ba, ya tafi ya bar ta, ai sai ta dawo gida, tun da ba ?anin ubanta ba ne"

Jamila ta ce "Kayya! Ba na tunanin wani kiranye zai yi wa Nana tasiri, ka san tana da ha?uri amma akwai taurin kai"

"Aikuwa wannan karon, dole ya kama ta, duk gidan uban da ta tafi, sai ta dawo"
ya yi maganar a fusace ya fice fuuuuu.

Sagir yana tsaka da bacci, ya buWe idonsa ya ga Shukura a zaune. "Sweetheart lafiya kuwa? Ya na gan ki a zaune?" Ji ta yi tamkar ta kifa masa mari, amma ta maze ta ce "Ba na jin daWi ne"
?an rikicewa ya yi, ya tashi ya matsa kusa da ita. Da gaske jikinta da zafi.

"Ya salam, bari na duba miki pcm" ya tashi ya kunna fitila, ya kawo mata ruwa da magani. A dole ta karSa ta sha. Ya kashe fitilar ya zauna a kusa da ita, ya ri?e hannunta yana Wan murzawa a hankali.
"Sannu"

"Yauwwa" ta amsa a ta?aice.
"Beb anya ba wani cikin ba ne?"

"Ahha haba dai, ba wani ciki maybe malaria ce"

Sagir ya ce "Ban yadda ba, gobe in Allah ya kaimu zan kai ki Asibiti a sake duba mini ke. Ubangiji Allah ya sa cikin ne" shiru ta yi ba ta amsa masa ba, shi kum hakan bai dame shi ba. Duk haushin Sagir da take ji, yana da halayen da duk ?iyayyarka da shi, muddin za ka yi masa adalci dole ka kira shi mutumin kirki. Yana da matu?ar tausayi, duk faWan da za su yi, da ya ganta a yanayi na rashin lafiya, zai rikice gaba Waya. Haka ya lallaSa ta ta kwanta, sai dai da ya fara bacci sai ya farka, ya taSa goshinta da wuyanta. Ita kuma idonta biyu duk abin da yake yi tana jin sa.

****
Sai da Nana ta tabattar da sawu ya Wauke, sannan ta Wauki jakarta, ta koma gidan da ta shiga ta yi salla. An kulle ?ofar gidan, amma ?ofar rilar gidan a buWe.
Ta shiga rilar, ta ciro daddumarta ta shimfiWa, ta Waukko zani a kayanta ta yi kwanciyar ta.
Har a wannan lokacin, da take shirin kwana a waje haka, ba ta ji ta yi nadamar tahowarta Nijar ba. Sai ma ji da take yi ta zo inda babu wanda ya santa, balle a din ga gudunta, a din ga ganin da ta rabu mutum sai wata masifar ta afka masa.
Ta saka hannu ta tallafo cikinta, da ita ma take jin nauyinsa, ya wuce adadin watannin da take tunani.
Tana jin yadda yake motsi, wanda motsin nasa kaWai, wani irin farinciki da nishaWi yake sanya ta.
Sai kuma damuwa ta biyo bayan farincikin nata, bayan da ta tuno Sayyid, da kuma rashin sanin halin da yake ciki. Da haka bacci nannauya ya yi awon gaba da ita a gurin.

Ko da dare yayi, Maijidda bacci gagarar idanunta ya yi, ta tattara Iliyasu ta watsa a gefe, addu'a kawai take yi Ubangiji Allah ya sanya Nana ta kasance cikin aminci da kwanciyar hankali.
Tana zaune a kan gado, ta yi shiru abin duniya ya ishe ta. Ji ta yi yana lalubata, wani irin ba?in ciki ya turnu?o zuciyarta.
?o?arin janyo ta yake yi, ta buge hannunsa a fusace, saboda ko ?aunar ganinsa ba ta son yi.
Ya ce "Mai Jidda meye haka ne wai?"

"Dan Allah ni ka rabu da ni, wallahi ko ?aunar ganin ka ba na yi. Ni dan zatin Allah ka sake ni, gara na yi zaman 'ya'yana kawai, da na ci gaba da zama da mutumin da ba ya ?aunata, na yi kuskure tun farko da na biye wa son zuciyarka na banzatar da 'ya'yana" Ta yi maganar tana kuka mai ?unar zuciya.

"Maijidda da ba na sonki, ke kin san ba za ki je ki yi wani auren ki fito na aure ki ba. Ni kishinki nake yi, kuma na gaya miki tsanar da na yi wa mijinki ne ya shafi 'ya'yansa"

"Ka na ?aunata, ina cikin wannan mawuyacin halin, da kai ne sila, za ka zo ka na nani?ata bu?atarka ce kawai a gabanka? Wallahi ba ka ?auna ta. Kuma ha?urina ya riga ya ?are, ka sauwwa?e mini kawai, ni zan tafi neman 'ya ta. Allah kaWai ya san a yaya za ta kwana a ?asar da ba ta san kowa ba, ga tsohon ciki"
Kasancewar bu?atarsa a gabansa, ya sanya ya kwantar da murya, kamar yadda ya saba ba ya tashi kalailaye ta, da kwantar da murya sai a irin wannan lokacin.
"Wata?ila ma fa ba Niger Win ta tafi ba, ai ba yarinya ce ?arama ba, na san gidan babanta ta koma, ki ke ta Waga hankalinki"
"Da akwai damar zama a gurin Baban nata, ka na ganin za ta zo inda nake ne? Nana ba za ta ajiye mini wannan rubutun ta koma gidan babanta ba, ni ka riga ka cuce ni" Ta yi maganar tana sauka daga kan gadon. Ya bi bayan ta yana lallaSa ta, amma ta wuce ko saurarasa ba ta yi ba ta bar Wakin, abin da ba ta taSa yi masa ba a tsawon zaman su.

Baba ma abin Duniya ya dame shi, ya fito ?ofar gida yana takaicin abin da Nana ta yi, sai ga kiran Uwani.
Kamar ya share sai kuma ya Waga, suka gaisa Uwani ta ce "Isa kiran ka na yi na ja maka kunne, tun jiya da su Ummi suka taho nake son na kira ka na ja maka kunne, kar ka kuskura ka kira yarinyar nan ka ce za yi mata faWa, ko ka kira uwatta ka yi musu jaraba, saboda Nana ta tafi can, ita ma mafitarta take nema, tuntuni da ka kama 'yar ka ka ri?e, babu yadda za a yi ta tafi Bauchi gurin babarta. Kuma ga halin da take ciki an nemi miji an rasa, ba a san kowa nasa ba, yarinyar nan na cikin wani hali, dan haka kar ka ce za ka yi mata faWa tun da kai ne ummul aba'isin duk wannan lamarin. Da ka binciki dangin mutumin nan kafin ka aura mata shi, da duk haka ba ta faru ba".

"Uwani"

"Na'am"

"Nana fa ba ta Nigeria ma gaba Waya, mijin Babarta ya kore ta, ta rubuta wa Ummi sa?o ta tafi Niger neman mijinta"

"Me? Ta tafi Nijar ta san a inda za ta gan shi ne?"

"Oho ina san mata ma, na samu wani malami, na ba shi abin sadaka ya yi mata kiranye, gaba Waya yarinyar nan ba ta da lissafi"

"A'a ai duk kai ka janyo, amma Nana ba ta yi dabara ba, wallahi da na san abin da zai faru kenan, da ban bari ta tafi ba"

"Sai anjima bari na koma gurin malamin na gode " ya kashe wayar dan ita kanta Uwanin haushinta yake ji.
Yana shirin yin gaba, sai ga wata mota ta tsaya a gaban Baba.
Har Baba zai wuce, sai kuma ya tsaya. Wani matashin saurayi ne ya fito Baba ya din ga yi masa kallon sani.
Matashin ya ?araso su ka gaisa. Matashin ya ce "Baba dama, Mamanmu ce ta aiko ni, can gidan da Nana ta yi aikin rainon yaro. To wai Hajiya ce kwana biyu suna ta kiran wayarta, ba ta shiga sam, kuma an je can gidan da suke gadi, amma ba sa nan, shi ne ta ce na zo gida na tambaya ko lafiya, ko kuma a bani lambarta da take shiga na kai mata"

Baba ya kwaSe fuska ya ce "Kai ne ta auri Buzun yaron nan a gidanku kenan?"

"Eh ni ne Baba"

"To ai 'yan uwansa ne suka fara guduwa, ya yi ta rashin lafiya, to yanzu dai shi ma ya gudu, ta tafi can Nijar neman sa".
Yusuf ya yi sororo cikin rashin fahimta ya ce? "Ya gudu ta tafi nemansa kuma?"

"Eh kamar dai yadda ka ji na gaya maka"

Ganin kamar Baba a fusace yake, ya sanya Yusuf cewa "To shikenan Baba, Allah ya kyauta, ya bayyana su cikin aminci" Ya koma ya shiga motarsa ya tafi.

*****

Sanyin iskar sahara ce ta din ga ratsa Nana, har ta fara karkarwa saboda sanyin.
Ta Waga kai, ta ga sararin samaniya ta yi tarwai, sai hasken farin wata da ya haska cikin saharar.
Wani irin ?ugi ta ji saharar tana yi, da alamun tasowar iska. Ta kalli gabas ta ga iskar sahara daga nesa, tana wani irin han?oro da alama iskar tana da ?arfi.
Sauke Numfashin Sayyid ta din ga ji a cikin saharar. Waige-waige ta fara tana neman ina za ta gan shi.
"Sayyid, ka na ta ina ban ganka ba"

"Ma viee"

"Na'am Sayyid, ka na ina ne?"

"Za su kashe ni, dan Allah ki zo mu koma gida, na fi son rayuwata da ke, na nufi nutsuwa"

Cikin rauni ta ce "Sayyid ba na ganin ka, ka na gurin ina?"

"Husna" ta sake jin muryarsa yana ajiyar zuciya. Gadan-gadan Nana ta nufi inda ?urar Saharar nan take tasowa, saboda daga nan take jin sautin muryarsa.
A Wan razane ta farka, saboda taSa ?ofar gidan da aka yi. Tana kwance a cikin duhu, ta hangi mai gidan ya fito, da alama masallaci ya tafi.
Ta tashi da ?yar, ta buWe kayan ta, ta Wauki ruwa pure water, ta kama ruwa ta yi alwala. Tana jin yadda magidanta suke buWe gidaje, su na tafiya masallaci. Ita ma ta tayar da salla.
Kusan mintuna Arba'in mai gidan ya dawo, sai da ya tsorata kasancewar gari ya fara haske. Ya ga mace tana salla a kan dadduma a cikin rilar gidan. Nana ta Waga kai ta kalle shi, ta mayar ta sunkuyar ta ci gaba da tasbihi. Sai dai duk iya ?o?arinsa a kan ya yi mata magana, ya kasa kamar an saka masa sakata a bakinsa.
Ya lallaSa ya buWe ?ofa ya shiga gidansa, ya tarar da matarsa tana bacci, kasancewar Al'ada take yi, ba ta salla. Kamar ya tashe ta ya gaya mata batun matar da ya gani, amma ya kasa, ya ha?ura ya ?yale ta.

****
Jamila bata taSa sanin ta damu da Nana har haka ba, duk da takun sa?a da sukan yi wasu lokutan, saboda ?uruciya da sakunta, wasu lokutan kuma saboda zigar Mama. Amma ta damu sosai da halin da Nanan ke ciki. Jikinta ya yi sanyi sosai da sosai, da Ummi ta ba ta labarin wahalar da ta yi ta faman yi, ga miji ga laulayin ciki. Yanzu mai Wungurungun ta tafi inda babu mataimaki sai Allah.
"Amm Jamila"
"Na'am Mummy"

"Kwana biyu na Waga miki ?afa da batun Nana, saboda ki samu ki ?ara sakin jikinki, yanzu dai ki na ganin yadda al'amuran ?ungiya suke wakana, kuma na ga kin saki jikinki yanzu.
Dole fa ki yi ?o?ari a wannan karon, ki samo mana jinin Nana, saboda ba ?aramin alkhairi ne a tattare da taurarinta ba. Tun da dai kin ga Uba ku ka haWa kawai da ita."
Jamila ta yi murmushi cike da takaici, amma a zahiri ta danne ta ce "To ai Nana mijinta ya Wauke ta, ya tafi da ita can ?asar su Nijar a can ma ina ga za ta haihu"

"What? Jamila

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login