Showing 93001 words to 96000 words out of 122467 words

Chapter 32 - Buzu Book 2 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

46

girkin Abinci da ni da ?awayena, da sauran aikace-aikacen gida.
Abu na farko dalilin da ya sanya na Waukko ki, ke ba ?abilarmu ba ce ba, ba na son saka ido, ba na son surutu
Duk wani abu da za ki ga na yi, ko ina yi babu ruwanki, aikin duk da na saka ki shikaWai za ki yi mini"
Nana ta yi shiru tana tunani, dama duk wannan abin ba wani branch Win za a kai ta aiki ba, wannan zu?a??iyar za ta yi wa bauta, shi ne har da ci mata mutuncin cewa an yi amfani da kuWi sai ta yi abin da ake so. Kuma me yasa ba ta zaSi kowa ba sai ita?.
"Ba kya ji na ne?"

"Na ji"

"Ban gane kin ji ba? Haka zan din ga yi miki magana ki na amsa mini, ke ni fa ba Hasna ba ce ba, dole ki yi mini biyayya ki yi duk abin da nake so".

Nana ji ta yi tamkar ta yi tsaki, ta ce "Amma yanzu fisabilillahi duk faWin ?asar nan ki rasa wanda za ki Waukko ya yi miki aikatau sai ni. Ni harkar dafa abinci nake yi, amma kin kawo ni nan in din ga yi miki girki da boyi-boyi ba tare da an yi mini bayanin haka ba, ni gaskiya ba a kyauta mini ba"

"Da hakan ki ka dace ai, ko kina ganin kin cancanci wani abin bayan bauta? Idan ba za ki zauna ba ga hanya nan za ki iya tafiya" Ta yi maganar tana mi?ewa tsaye.
Har ta yi gaba sai kuma ta tsaya ta ce "Duk wani abu da za ki bu?ata akwai shi a kitchen, kina iya dubawa, wanda babu kuma ki sanar mini, shi ma idan ba ki ga dama ba kar ki yi aikin" ta yi gaba ta bar Nana da ta gama ?ulewa.

*****

Gaba Waya Shukura ta burkicewa Sagir, ba Waga masa hankali ta yi da rigima ba, tattara shi ta yi ta watsar gaja Waya take harkokinta, da gaske take ?o?arin gano abin da mahaifinta yake Soyewa tsawon wannan lokacin da har ya hana Hajiya Amina bincike a kan lafiyarta.
Ga shirin tariyar Yusra Sagir na yi, ga damuwar rashin sakin jiki da shi da Shukura ta yi, ta tattara shi ta watsar.
?angarensa ya saka aka gyarawa Yusra, dama ba amfani yake yi da shi ba, aka ?ara gyara shi, aka haWa gidan gaba Waya aka sake yi masa fenti. Daga gaya mata batun dawo da Yusra zuwa gyaran gidan da kawo kayanta, ba a yi sati guda ba, gida ya Wau harama.
Duk yadda ya so ya lallaSa Shukura, ta saukko ta din ga saurararsa ta yi burus da shi.

Nana ta shafe sati guda tana gidan Asal, tana yi mata hidima, ta hantare ta ta kyare ta, dandazon ?awayen da take tarawa ma, su hana ta sukuni da aiki. Nana ta din ga iya ?o?arinta, gurin kai zuciyarta nesa, amma abin ya fara isarta.
Tana tsaka da nazarin yadda za ta Sullowa lamarin, da safe Asal za ta fita ta kalli Nana ta ce "Ki shirya nan da sati Waya zamu bar nan, zamu je asalin inda na Wauke ki ki yi mini aiki a gurin"

Nana ta ce "Ina kenan? Kuma aikin me?

"Idan mun je za ki gani" Ta ba wa Nana amsar a ta?aice.

*****
Jamila tana kwance tana chatting da Abba, bikinsa saura sati biyu.
Hajiya Sa'a tana ta zaginsa da yi masa bala'i, a kan yadda yarinyar take ta ?orafin ba ya kula ta, waya ma sai dai ita ta kira shi, babu abin da ya yi masa zafi da ita.
Yanzun ma kamar ya yi wa Jamila kuka.
Ita take ta rarrashinsa tana nuna masa babu komai ya yi aurensa kawai.

"?anwata ko na yi aure hankalina ba zai kwanta ba, kar ki manta da Sarnar da ta faru tsakanina da ke, ya zan yi da shi"

Ta ce "Na san kai mutumin kirki ne yayana, hakan ne ya sanya ka ke jin damuwa a kan abin da ya faru, amma ka yi ha?uri ka yi aurenka kawai, ina ro?on Ubangiji Allah ya kawo mini wani mijin"

"A'a ki daina faWa mini haka, zuciyata tana sosuwa, baki da wani miji sai ni in sha Allah" haka suka kasance tana ?arfafa masa gwiwa, shi kuma yana rarrashinta.
Ta gama wayar ta ajiye, ta ga Suwaiba ta ?uro mata ido tamkar ba ta taSa ganinta ba.

"Meye ki ke kallona, lafiya?" Suwaiba ta yi shiru ba ta bata amsa ba, kuma ba ta yi magana ba.

Jamila ta ja tsaki, tana ?o?arin kwanciya, Suwaiba ta ce "Jamila"

"Na'am mene ne?"

"Ki Wauki sa?onki mana"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wane sa?on?"

"Na cikin jakarki"

"Cikin jakata kuma? Mene ne a jakar tawa? Wato bincike ki ke yi mini a jakar ko?"

"A'a ni tuni kawai nake yi miki da sa?onki na cikin jakar"

Jamila ta tashi zaune ta ce "Wai wani sa?on? Mi?o mini jakar dai na gani"

Suwaiba ta ce "A'a ba zan taSa miki jaka ba"

Jamila ta janyo jakar ta fara buWewa ta ga abin da Suwaibabta dame ta a kai. Cin karo ta yi da wannan 'yar tsanar da ta riga ta jefar. Saura ?iris ta kurma ihu, ta rikice gaba Waya jikinta ya hau rawa, a tunaninta tun da ta yar shikenan ta rabu da ita.
Suwaiba kuwa ta tuntsure da wata irin mahaukaciyar dariya, ta din ga yi tana ?ya?yatawa tana kallon Jamila. Gaba Waya Jamila ta kiWime ta rasa abin da yake yi mata daWi, gaba Waya jikinta ya hau rawa tamkar ta kurma ihu, sannu a hankali kanta ya fara juyawa ta fara gani dishi-dishi, dole ta rufe jakar ta nemi guri ta kwanta.

*****

Alhaji Zailani ya kwana biyu bai je gidan Alhaji Fatuhu ba sai yau. Sai dai ya sha mamakin ganinsa a harabar gidan da sanda yana dogarawa yana tattakawa a hankali, yana tsaye a kan ?afafuwansa yana kallon yadda Muhsin yake ta gudu a harabar gidan.
Sai da ya aro jarumta sannan ya iya danne abin da ya ji ya taso masa na tashin hankali da mummunan ba?in ciki.
Da ?yar ya iya washe baki ya ce "Ikon Allah, Abokina kai ne haka nake gani?"

Alhaji Fatuhu ya yi murmushi ya ce "Ka ga ikon Allah ko? Sannu da zuwa Bismillah" ya yi maganar yana nuna masa Waya daga kujerun da ke ajiye a gurin.
Alhaji Zailani ya zauna suka ?ara gaisawa

"Bani labari, ya aka yi sau?i ya samu haka, wani Asibitin ka je ne?"

Alhaji Fatuhu ya ce "A'a na ga an yi na Asibitin ne babu wani ci gaba, Fadila ta zauna ta din ga yi mini bayani, na amince muka fara gwada na islamic, cikin ikon Allah sannu a hankali wannan Waurewa da nake ji a jikina ya yi mini sau?i, wannan gigicewar da nake na ji kamar zan yi hauka shi ma Alhamdillah ina daWewa ban ji ba, wannan warin ma da nake ji ya ragux

"Amma Fatuhu ya za a yi ka biye wa mace da shirmen ta, ga na Asibiti ana yi kawai ta saka ka fara wani na shirme, sai ka je ka yi abin da za ka kauce wa hanya tukuna?"

"A'a nima na jaddada mata, ta kuma tabattar mini da babu kauce hanya a ciki, kuma nima shaida ne, shi ya sanya ma nake amfani da magungunan kuma ana samun ci gaba"

Alhaji Zailani ya mi?e ya ce "Haka ne, to bari na je dama ina da gurin da zan je na biyo, sauri nake yi"

"Ba zaka tsaya ku gaisa da mutanen gidan ba?"

"Sauri nake yi zan sake dawowa"ya yi maganar yana yin gaba cikin ?unar rai, ji yake yi tamkar ya kashe Alhaji Fatuhu ya huta, dan shi bai taSa zaton zai kawo yanzu bai mutu ba.

*****

Al Hussain ne a tsaye ya tsare Hasna da ido, yana yi mata faWa cikin matsanancin Sacin rai.
"A kan me za ki yi haka? Dan me za ku yi mata dole, ai ba Waukar ta aiki muka yi saboda bu?atar mutum guda ba. Abin da yake cikin yarjejeniya shi ne ta yi wa gidan Abincinmu aiki, idan ma canza gurin aikin ne, wani reshen zamu mayar da ita, amma dan me za ku haWa kai ku yi mata haka wannan wula?anci ne da cin zarafi, kuma ga shi bama 'yar ?asarmu ba"

"Ni fa Al Hussain na kasa gane maka, ko son yarinyar nan ka ke yi ne? To bari na tuna maka kai Buzu ne, buzun ma farin buzu ka san abin da nake nufi ai, kuma matar aure ce ko bazawara dan ta ce mana tana da Wa ma"
"Ni ba wannan na tambaye ki ba, dan me Asal za ta yi amfani da ?arfi da kuWi ta tursasa mata yin abin da ba ta so, ai ba haka ake rayuwa ba"

"Ai na san za a yi haka, babu bayanin da ban yi mata ba ta?i yadda, ga shi ni yanzu ka zo ka saka ni a gaba da jaraba, sai ka je ka dawo da ita ni ba zan iya ba"

"Ke dai da ki ka yi hakan ki je ki dawo da ita, idan ba haka ba daga ke har ita na rubuta masa abin da ku ka aikata, daida yake da ku"

Ta kwaSe baki ta ce "Wa ya san ma inda yake, mutumin da ake tunanin ya Sata babu wanda ya san ma yana raye ko yana mace?"

"Hakan ya baku damar cin karenku babu babbaka daga ke har Asal ko? Yayi muku kyau" Hasna ta fice tana jin haushin masifar da Al Hussain yake ta yi mata, duk yadda ta yi ?o?arin hana Asal Waukar Nana.

*****

Ana gobe su Nana za su bar wannan gidan, Asal ta sanar da Nana ta shirya washegari za su bar nan.
Ita dai Nana ta sanya wa sarautar Allah ido, rayuwarta ta zama tamkar tamaula daga nan zuwa can, ba ma ta da 'yancin tambayar ko sanin inda za a kaita sai dai inda ta tsinci kanta kawai.
Ta sha aiki ta gama, ta Wan zauna a falo tana hutawa, sai ga Waya daga gayyar ?awayen Asal ta saukko ta kalli Nana ta ce "Dan Allah ina son shayi"
Nana ta ce "Akwai a kayan Abincin da na girka"
"Shayin kanumfari kawai nake so bana son Shan na girfa"

"Ga gurin dafawar can, idan ki ka je akwai komai, ki dafa ki sha idan kin matsu"

"Ke, kin san wace ce ni ki ke gaya mini haka?"

"Ban san wace ce ke ba, kuma ba na bu?atar sani"

Asal ta saukko tana tambayar lafiya.

Ta gaya mata abin da ya faru, ta kalli Nana ta ce "Wai ke me yasa ba ki da mutunci, ban gaya miki dole ki girmama ba?ina ba, mene ne a cikin dafa shayi mintinan nawa ne kin yi kin gama?"

Ta kalli Asal ta ce "Ki yi ha?uri, wallahi ko cokali ba zan iya sake Wauka ba, yau na bautu a gidan nan ke kin sani, kuma ban taSa yi miki ?orafi ba, amma yanzu dai na gaji gaskiya"

Suka juya yare suka yi magana, ba ta san me suka ce ba, ta ga sun koma kan bene.

Washegari da wuri suka Wau hanya, sai dai ga mammakin Nana, har da rakiyar jami'an tsaro, kuma a wannan karon shigar Shadda Asal ta yi, an yi wa shaddar aiki tun daga sama har ?asa.
Mota Waya suka hau, ta ce Nana ta hau gaba, ita kuma ta hau baya.
Sai da aka kuma wata tafiyar mai nisa, sannan ta ga sun tunkari wani? irin ginin ?asa tamkar ginin ganuwar Kano.
Ginin ya ?ayatar da Nana sosai da sosai.
Jami'an tsaro ne suke gadin ?atuwar ?ofar gurin, da wasu Buzaye farare tas sanye da rawani.
Nana kamar ta ce a tsaya, ta duba buzayen nan Waya bayan Waya ko za ta ga Sayyid Win ta cikinsu. Sai da motar su ta tsaya, suka sauke glass Win motar.
Da Hausa suka gaisa, suka yi mata sannu da zuwa, Waya daga cikin su ya kalli Nana ya ce "Wannan fa?"

"Ba?uwata ce" ta ba shi amsa, ya jinjina kai motar ta shige.
Su na shiga Nana ta ga ai gari ne guda a cikin ganuwar nan.
Sun Wan yi tafiya kafin su shiga wani ?aton gida.
Nana ta tsaya tana ganin yadda aka yi wa ginin ?asa wani irin ado mai ?ayatarwa.
Tun da suka doshi shiga gidan, ake gaida Asal cikin girmamawa, ita kuma ta yi fuska sai taku take cike da ?asaita, kamar ba ita ce suke rashin hankali da ?awayenta a wancan gidan ba.
Wannan gidan saSanin wancan da mutane a ciki, kuma da alama duk a ?ar?ashin Asal suke.
"Wace ce ita?" Nana ta tambayi kanta. Sai da suka ?arasa wani falo, sannan ta yi wa wata dattijuwar magana da yaren su.
Matar ta kalli Nana ta ce "Bahaushiya ce ke ko? Zo mu je na kai ki masauki"
Babu musu Nana ta bi ta, matar ta kai ta wani daki ta ce nan ne Wakinta.
Sai da Nana ta kwana biyu a gidan, ba ta sake ganin Asal ba, ba kuma ta aikin fari ba ta na ba?i kawai tana zaune, sai dai za a kawo mata Abincin safe, rana da dare sau uku a rana. Sai dai babban abin da ya dame ta, tun da ta shigo gidan, network Win wayar ya sauka gaba daya, ko ta kira Nene ba ta shiga sam.

A kwana na huWu, da daddare dattijuwar matar nan ta zo ta kira Nana. Babu musu Nana ta tashi ta bi bayanta.
Sun yi 'yar tafiya su na ratsa faluka masu kyau da ado, sannan suka bi wata ?ofa. Sanyin A.C ya daki Nana, ga wani irin haWaWWan ?amshi. Asal ta hahakimce a kan kujera kaWa ?afa.
Ta kalli dattijuwar ta ce ta jira a waje. Daga ?asa wata matar ce a zauna a kan carfet, ta gurfana kamar tana jiran Asal Win ta gafarta mata.

Nana ta yi turus tana tunanin a ina za ta zauna, sama ko ?asa.
Matar ta kalli Nana cikin zare ido ta ce "Ke ki rage tsawon ki, kin tsaya mata a ka"
Nana ta ja guri ta zauna a kan carfet Win ita ma.
Asal kamar ba za ta yi magana ba, sai da ta gama iyayinta ta sauke ?afarta ?asa ta dubi Nana ta?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? ce "Amm na saka an kirawo mini ke, saboda ki san abin da na kawo ki gidan nan ki yi. Ke dai da ganin gidan nan kin san ba gurin da za a yi wasa ne ko shirirta ba, babban gida ne na mulki.
Saboda dalilin girki da kuma wani dalili na ?ashin kaina, ya sanya na kawo ki gidan nan. Ba a Waukko bare wanda yake ba jinin gidan nan ba, ko ?abilarmu ba ya yi mana aiki, amma na ga wasu abubuwa a tattare da ke da ya sanya na kawo ki cikin gidan nan.
Kamar yadda na gaya miki, ina ?ara jaddada miki, zaman ki a gidan nan dole ki yi taka tsantsan, babu ruwanki da shishshigi, saka ido, gulma ko kuma shiga abin da babu ruwanki.
Sannan kar ki kuskura wani ya ce zai haWa kai da ke a yi wani abu, rayuwarki za ta iya salwanta ba tare da kowa ma ya sani ba, dan haka sai ki san irin zaman da za ki yi."

Nana ta yi shiru ta gama sauraren ta, sai dai har a lokacin ba ta ji dalilin da ya sanya Asal kawo ta gidan ba, dafa abinci kowa ma zai iya mai yasa sai ita.

Wannan matar da ta tarar a zaune, ta tafi da ita, ta kai ta gurin da ake girke-girken abinci, da gaya mata yadda jadawalin girke-girken gidan yake. Ta Waukko kayan ds Asal ta bayar a ba ta, na kayan shafe-shafe da mayukan wanka zuwa kayan sakawa.
Da Nana ta koma Wakinta, ta kalli kayan ta fara tunanin Allah ya sa ba kwance Asal ba ne, dan gara ta saka kwancen Ashura da ta saka na Asal, da ba ta da mutunci.
A washegari Nana ta fara aiki a wannan madafa, sai dai madafar daban-daban ce. Akwai wadda ake girkin da ma'aikatan gidan ne suke ci, akwai wadda na ba?in da suke zuwa ne, sai kuma masu girka wa Asal abinci daban, dan haka Nana na cikin masu yi wa Asal girki.
Sosai matar nan ta ?ara jan kunnen Nana, a kan ta kula da kanta, dan muddin aka samu matsala ba za ta sha ba.
Nana a ranta ta ce "Ji wata jaraba, da wannan wahalar mutum ya girka abin da zai ci mana da kansa."

Kwana huWu da fara aikinta, ranar Alhamis da daddare, tana shirin kwanciya, aka ?wan?wasa ?ofar Wakinta.
Ta tashi ta buWe, ta ga shugabar girke-girke ta gidan, kamar yadda aka gabatar mata da ita a baya.

"Ki sako hijjabinki, ki biyo ni"

Nana ta saka hijjabinta ta fito tana tunanin ko lafiya.

Harabar gidan matar ta yi, Nana ta bi bayanta, ta nuna mata mota. Nana ta kalli dare ya yi kuma an zo da mota an ce a tafi da ita.
Cike da mamaki Nana ta shiga motar, sai ta ga mutum uku, da su ma duk tare suke aikin girkin a gidan a cikin motar.

Ta shiga ta zauna, ita ma shugabar ta su ta shiga. Nana ta gaza ha?uri ta ce "Dan Allah ina za mu je ne?"

"Za ki gani"

"Eh amma na ga dare ne fa"

"Idan mun je za ki ji dalilin fitar" Nana ta yi shiru tana tunani, ita ba ma wannan ba, hankalinta ya koma kan rashin samun damar kiran waya da ba ta iya yi, kuma ba a kiranta ya shigo. Dan sai da ta tambayi Waya daga cikin masu aikin, ko matsalar daga wayarta ne, ta ce mata kar ta kuskura ta bari ma a san tana da waya, dan sai an ?wace ta.

Tana ta zancen zuci, har suka isa inda aka tsaya suka sauka, aka shiga da su.

Asal ce a tsaye, tare da dattijuwar matar da ta saka ta raka Nana masauki. Suna tsaye a cikin Wakin Nanan.

Asal ta ce "Zazzage mini kayanta, ki Waga mini komai Waya bayan Waya"

Ayshercool
Ku tura mini hakkina kan ku karanta 0069685771
Aisha Adam stanbic.
73

?aya bayan Waya, aka din ga zazzage kayan Nana. Aka zazzage su tsaf aka Azzage jakar da ta zuba kayan turarukanta da mayukan shafawa, duk ba ta ga wani abu ba, sai jakar gurin sarkin baka.
Ta nuna jakar ta ce "Mene wannan?"

Ta Wago jakar ta ce "Jaka ce"

"BuWe ta ki zazzage na gani" Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login