Showing 21001 words to 24000 words out of 122467 words

Chapter 8 - Buzu Book 2 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

24

magungunan nan, babu yadda na iya ne nake shan na Asibitin ma, ni wahalar da ni suke yi"

"To ai wannan ba na Asibiti ne ba, dan Allah ka daure ka taimaka, ba dan ni ba"

Da ?yar ya yarda ya karSa, ya WanWana ya ji babu Waci, sannan ya ci gaba da sha, sai ma ya ji Wumin maganin ya yi masa daWi.
Bayan ya shanye, ta dafa masa shayi kuma, ya Wora dan duk wahalar ciwon da yake ciki, ba ya iya ha?ura da shan shayi.

Nana ta dage da bawa Sayyid, wannan ruwan maganin, tana addu'ar Ubangiji Allah ya taimake su, ya sanya ya karSe shi.
Cikin ikon Allah, sai kumburin da ya yi, ya fara sacewa a hankali, har yana iya cin Abinci sosai. Nana kamar ta zuba ruwa a ?asa ta sha.
Nana ta din ga murna, ganin ana samun ci gaba a yanayin jikinsa. Har banWaki yana iya zuwa, ba tare da ta kama shi ba, yana tafiya a hankali a hankali da kansa yana iya yi wa kansa Wasu abubuwan.

Yana zaune tsakar gida, yana shan shayi ta ce "Ashe maganin Sarkin baka yana yi"

Ya kalle ta, ta ce "Ka san Sarkin baka?" Ya Wan yi shiru yana kallon ta.

"Ranar da aka kai ni, kai na an kai ka, zaku tafi lokacin, ni kuma a lokacin na ji na fita daga hayyacina. Kai mun fa daWe muna haWuwa da kai."

Ya yi murmushi ya ce "Ruhina ne ya addabe ki, sai da ki ka nemo ni, ki ka aure ni ki ka nutsu"

Ta Sata fuska ta ce "Ba wani nan, kai ne ka din ga bi na dai, har ka aure ni".

Ya Wan sake zu?a shayin hannunsa ya ce "A'a. Har gidan da nake ki ka bi ni fa"

"Ni ba bin ka na yi ba, kuma ai kai ka ce a biya maka sadakin aurena"

Ya maze ya ce "Ai gani na yi kin li?e mini, har cikin Wakinmu na gadi ki ka bi ni, na ce kai yarinyar nan idan ban aureta ba, akwai matsala haka za ta yi ta bina saboda ruhinta da yake jikina. Kina ganina kuma ki ka rikice"

"Ni ba ina sane na shiga Wakinku ba, Jummai ce ta ce na ajiye muku Abinci, kawai na ji ana kirana a cikin Wakin, ban ma na san na shiga ba. Kuma ni da na shiga wannan tsohon na gani. Kuma ai kai ma idan ka ganni kallona ka ke yi"

"A'a faWi gaskiya dai, ni ki ka le?o ki gani, ranar ba ki ganni ba, sh... Kawai ya ga tana hawaye. A diririce ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Mene ne?" Ta yi masa shiru.

"Laifi na yi miki? Wasa fa nake yi" ta yi masa shiru, tana matse ?walla. Ba wai wasan da yake yi mata ne ya sanya ta kuka ba. Tuna yadda aka yi auren abin da Baba ya din ga faWa da wanda Mama ta din ga yamaWiWi da ita, abin ne kawai ya dawo mata.
Ji ta yi yana goge mata hawaye, fuskarsa Wauke da damuwa, ya ce "Ba zan sake ba" KwaSe baki ta yi cikin shagwaSa, wasu hawayen na ziraro mata.

"Na ce na daina fa, ki bari ?irjina ya fara nauyi" da sauri ta saka bayan hannunta, tana goge hawayen fuskarta.

"Yauwwa dama ina so mu yi wata magana, mai muhimmanci da ke"

Ta tattara hankalinta, gabanta na dukan uku-uku cike da wasi-wasin wace maganar zai yi da ita haka?.

Ayshercool
08081012143

57

Ya yi mata alama da hannunsa, a kan ta nutsu ta kwantar da hankalinta. Ta jinjina masa kai, duk da gabanta na ci gaba da faWuwa.

"Amm na san kina ha?uri a kan abubuwan da suke faruwa, duk da kin ce mini ba kya so na din ga irin wannan maganganun, amma sun zama dole na yi. Ina ?ara yi miki godiya da nema miki yardar Allah, na san ba ni da abin da zan biya ki da shi a wannan Duniyar. Ke ce komai nawa da ki ka rage Asmy. Sannan Sangaren abin da ya shafi auratayyarmu, shi ma na san...

Ta katse sh6ta hanyar cewa "Amm ni dai a bar wannan zancen, bari na je na Wora wakena"

"A'a ki tsaya mu yi magana"

"A'a ba sai mun yi ba"

"To kar na sake jin kin bi dare ki na taSa ni" Kamar ta yi tsuntuwa ta Sace, saboda azabar kunya, ita a zatonta ma ya manta gaba Waya. Cikin azama ta mi?e ta Wauki robar wakenta, ta nufi inda take girki. Tana tashi ya kashingiWa yana dariya.

Nana tana ta fifita wuta, yana daga zaune yana kallonta. Wani irin abu ne yake yi masa yawo a jikinsa, a game da ita.
Yana jin zai iya yin komai, dan tabattar da ci gaba da zamanta mallakinsa, shikaWai.
Juriyarta, sadaukarwa da kuma tsananin tausayinta, ya sanya yake jin ina ma yana da wani abu da zai iya kamanta faranta mata rai, kamar yadda take ta wannan Wawainiyar da shi. Ya san in dai a wannan Duniyar ne ba shi da abin da zai biya ta. Duk da matsananciyar damuwar da ya kan shiga, da jin cewa ya zama silar nakasta rayuwarta, ta zama tana rayuwa ba tare da tunanin wani abu da take so ta cimma ba. Kullum tunaninta a kan sa ne kawai.
Tana Wagowa suka haWa ido, ta murguWa masa baki, ta ci gaba da fifitar wutar gabanta.
Ya tako zuwa gaban murhun ya tsuguna.

"Dan Allah ka tashi, saboda numfashinka fa"

"Kawo na yanka miki salak Win"

"A'a kar ka yanke hannu"

Ya ce "Ki kawo zan iya" Ta tsuke fuska ta kalle shi ta ce "Saboda sau?i ya samu, kana iya fitowa da kanka yanzu, shi ne za ka din ga damuna ko?"

Ya yi murmushi, ya zauna a gefe yana kallon ta, da ta Waga ido, sai su yi ido huWu da shi, sai ya yi mata murmushi.

Su na cikin cin abinci, ya ce "Ki na kiran Ummi?"

"Ba na samun ta, ita ma ta kira ni wayar ba na ji. Uwani ta ce haka garin nan yake babu network, sai a yi kira fiye da sau goma ba ka samu mutum ba.

"Idan na ?ara jin sau?i, zamu je mu gaishe ta, mu yi mata godiya"

Ta ce "Alhamdillah, lallai sau?i ya samu."

Ya ce "Eh, ina jin hakan a jikina nima. Mu je waje na Wan tattaka na ga gari"

Nana ta faWaWa murmushinta ta ce "Allah abin godiya, wallahi Sayyid da har na fara fitar da rai da kai, na karaya sosai wallahi" Cikin murna ta saka hijjabinta, suka fita. Su na tafe a hankali ta kalle shi ta ce "Gaskiya na yi mamaki, ashe da gaske magungunan sarkin Baka yana yi"

Ya tsuke fuska ya ce "Na gaji da jin zancen Sarkin Bakar nan"

Nana ma ta yamutsa fuska ta ce "Sayyid ka yi ha?uri, amma na yi farin cikin yadda maganin da na gani a gurinsa ya yi maka aiki. Ina yi masa fatan idan a kan daidai yake, Ubangiji Allah ya ?arfefe shi ya dafa masa, ko dan saboda yadda yake taimakon mutane. Idan kuma a kan kuskure yake Ubangiji Allah ya ganar da shi, ya ba shi ikon tuba kafin lokaci ya ?ure masa."

Sayyid ya yi mata banza, suka ci gaba da takawa a hankali su na zagayawa.

Wani irin sanyi ne ya fara ratsa Nana, ganin Sayyid ya durfafi wata hanya, ta kuma kasa ce masa uffan, balle ta hana shi. Su na tunkarar gurin, ?irjinta na bugawa da sauri da sauri.

Wata irin narkekiyar bishiyar kuka suka tarar a gurin mai ban tsoro. Yanayin yadda take Wauke da wasu irin murWaWWun rassa, da yadda murtuka-murtukan jijiyoyinta suka huda ?asa suka mamaye gurin. Ga wani irin ?aton kogo a jikinta, hakan ya nuna daWewar da bishiyar ta yi da wanzuwa a gurin.

"Asma'u" ya kira sunanta kai tsaye. Ta kalle shi cikin matsanancin mamakin yadda ya kira sunanta na yanka kai tsaye.
"Ji nake yi kamar na san gurin nan"

Jiki a sanyaye Nana ta ce "Nima haka, amma ni dai na san ban taSa zuwa gurin nan ba, amma ina jin kamar na san gurin, amma dai... Sai kuma ta yi shiru bayan da gurin ya gauraye da duhu aka yi wata irin wal?iyya, haske ya mamaye gurin. Tsohon nan ta gani a tsaye, ri?e da sandarsa ya zubo wa Nana idanunsa marasa kyan gani. Jikinta ne ya Wau kyarma, ta ?ara rikicewa bayan ganin a hankali wasu halittu da take kyautata zaton ire-iren su ?aisar ne su na bayyana a bayansa.
Tsohon ya kalle ta, ya buWe baki ya fara magana. "Ina sake yi miki barka da zuwa, garin da kakanin kakaninki su ka dur?usa suka haifo matsalar da har abada ba za ta daina bibiyar zuriyar su ba. Zan ci gaba da azabtar da rayuwarki, za ki ci gaba da biyan bashin nan, ko bayan ranki, muddin aka ci gaba da samun haihuwar masu irin tauraronki."

Yana rufe bakinsa, Waya daga cikinsu da Nana take kyautata zaton jininsin mace ce, saboda yanayin wani irin tsohon mayafi da ta yafa a kanta. Ta tunkaro Nana gadan-gadan.
Tana zuwa matar, ta hankaWa Nana ?asa, sauran suka rufu a kan Nana, su na zira hannunsu a mararta, su na ciro gudan jini.

"Ya hayyu ya ?ayyum ya Allah. Allah ka kawo mini Wauki, Sayyid, Sayyid, Sayyid ka tashi"? Ta yi maganar tana jijjiga Sayyid da yake kwance a gefen ta yana bacci.

Ya ja jikinsa ya tashi ya ce "Ma viee lafiya kuwa?"

"Sayyid marata ciwo take yi. Sayyid marata. Sayyid babyna. Ba na son na rasa jaririna a wannan karon, Dan Allah ka taimake ni"

Cikin rashin fahimta ya ce "Meyafaru ne?"

"Marata ce take ciwo, Sayyid ba na son cikina ya zube, ina son jaririna Sayyid ciwo marata take yi sosai" Ta yi maganar tana zubar da hawaye. Ya saka hannunsa a mararta, ta saka hannayenta ya dafe hannunsa tamkar hakan ne zai hana cikin zubewa.

Ya ce "Ki yi Addu'a" Kawai ta jinjina kai, amma Addu'a kam, ko Waya ba ta zo kanta ba, dan ta manta komai daga cikin kanta.

Cikin rauni Nana ta ce "Sayyid fitsari nake ji, ya matse ni"

Ya ce "To mu je ki yi"

Ta girgiza kai ta ce "A'a ba na son na je na ga jini ya zubo, cikin ne zai zube"

Ya ce "A'a ba za ki gani ba" . Ta mi?e ya kama hannunta, ya haska fitila har banWaki, su na zuwa a tsorace ta yi fitsarin, sai dai tana yi sai ga jini. Wani irin kuka ta fashewa da Sayyid. Ta mi?e jikinta yana rawa.

Ya rungume ta ya ce "Ki yi ha?uri, kin ga dare ne, ki daina kuka. Kuma idan za ki yi Sari, jinin da ki ke zubarwa ya fi wannan kin manta?"

"A'a idan jini ya fara zuba, shikenan ciki zai zube"

Ya ce "A'a, ba haka ba ne, ai bai zuba da yawa ba" Ya lallaSa ta da ?yar, ta gyara jikinta, ta Wauraye jikinta, da banWakin su ka koma Waki.

Karatun Alkur'ani ya kunna a waya, ya ajiye a gefen katifar da suke kai, kamar yadda ya ga tana yi, a duk lokacin da su ka shiga yanayi na tsoro.

Suka kwanta yana Wan shafa ta, cikin sigar rarrashi.

A hankali ta ce "Sayyid"

"Na'am"

"Da gaske mun fita Wazu ko?"

"Eh mun fita"

"Mun je can bayan gari, har ka ce mini kamar ka san gurin?"

"Eh haka aka yi, mun je"

Ta sake cewa "To daga nan meyafaru?"

"FaWuwa ki ka yi, na ri?e ki muka dawo gida. Tun da muka dawo kuma ki ke bacci"

Ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba, ta ?ara lafewa a jikinsa cikin tsoro. Yau ma kwana suka yi, tana gane-gane da jin abubuwa daban-daban masu razanarwa.
Wannan bafulatanar matar ce, ta ?ara zuwa ta tsaya a saitin tagat Nana tana kiran ta, a kan lallai sai ta fito ta ga yadda suke gudanar da bikin girka. Nana ta ?ara rintse idanunta tare da ?an?ame Sayyid.

Da safe ta tashi da wani irin nauyin jiki, ga sanyi da ta kasa daina ji. Ta duba ta ga ba ta kuma ganin jinin nan ba. Ta yi wanka ta rama sallolinta, sai dai Sayyid bai tashi ba. Da ?yar ta samu ya yi alwala ya yi salla.

Ta gaishe shi, amma bai yi magana ba sai kallonta da yake yi. Hakan ya sanya ta fuskanci maganar ta Wauke.
Ta tambaye shi za ta fita, amma bai ko Waga kai ya kalle ta ba. Ta saka hijjabi ta fita ta bi 'yan matan gidan Uwani gona roron gyaWa a gona.

Allah ya taimake ta, ta samo da yawa ta zo tsakar gida ta baje ta domin ta sha iska.

Ta Wora musu Abinci, ta kammala ta fara dafa masa maganinsa, kawai ta ga ya fito daga cikin Wakin. A zaton ta, ko banWaki zai shiga, ta tashi da nufin kai masa ruwa, kawai ta ga ya nufi fita waje.

Da sauri ta bi shi tana faWin "Sayyid ina za ka je ne haka?" Ya yi mata shiru yana ?o?arin buWe ?ofar. Ta ri?o hannunsa, amma ya waiwayo fuskarsa a Waura kamar bai taSa dariya ba, saka hannu ya hankaWe ta, ta faWi a gurin, ya saka kai ya fice daga gidan. Da gudu ta shiga Waki, ta Waukko hijjabi, ko takalmi ba ta saka ba, ta bi bayan sa. Ga yamma ta yi li?is, hanya babu kowa, ta ga ya nufi hanyar inda wannan bishiyar ta kuka take.

"Sayyid dan Allah, dan Allah kar ka koma gurin nan. Me za ka je ka yi?" Sai dai tamkar ba mara lafiya ba, saboda yadda yake sauri.

Sai da ta Wan haWa da gudu, Saboda saurin da yake yi, amma ta ji gefen mararta ya ?ulle. Ta daure ta cim masa.

Babu tsammani ta furta "Bismillah wa hifzan min kulli shaiWanin marid." Aya ta bakwai cikin suratul saffat, kamar yadda Malam Auwal ya taSa cewa ta yawaita nanata ayar. Gaba Waya ta shafe a cikin kanta, sai da ta faWo mata yanzu. Tana karanta ayar, ta ri?e hannunsa ya ja ya tsaya ya yi shiru ya sunkuyar da kai.

"Mu koma gida" ta yi maganar tana jan hannunsa, tamkar ra?umi da akala, ya bi ta suka koma gida. Allah ya taimake ta, babu wanda ya gan su har su ka isa gida. Ta rufe ?ofar.

Su ka shiga Waki, ta kunna fitila ta kalli Sayyid cikin damuwa ta ce "Sayyid me yasa ka fita? Me za ka je ka yi a wajen da?" Ya yi shiru ya sunkuyar da kansa ?asa fuskarsa babu annuri a ciki.

Ba ta sake ce masa komai ba, ta fita banWaki ta yi alwala, ta dawo ta yi salla, amma ta ga ba shi da niyyar tashi ya yi.

"Sayyid, ba ka yi salla ba fa" Nan ma bai kula ta ba, dan haka ba ta sake magana ba, ta zubo masa Abinci ta zo gaban sa ta ajiye. Ta tashi ta ninke hijjabinta, tana waiwayowa, ta ga ya kifar da Abincin ya tarwatse a tsakar Wakin, yana wani irin huci.

"Sayyid wai meye haka ne? Idan ba ka cin abincin sai ka zubar mini a ?asa?" Sai dai tana rufe baki, ya wulwula kwanon ya yi jifa da shi guri Waya. Ya mi?e ya fara fatali da kayan Wakin. Take Nana ta fuskanci ba lafiya ba. Jiki a sanyaye ta rakuSe tana kallon sa.
Tana tunanin yanzu kuma abin har ya kai ga haka? Ba ta yi yin?urin hana shi ba, ya yi kaca-kaca da Wakin, ya fita tsakar gida ya nemi guri ya kwanta a dandaryar ?asa.
Inda ta yi wa Allah godiya ba su da ma?wabta, da kowa sai ya san abin da ya faru. Haka ta dur?usa ta hau aikin gyaran Wakin, ta kintsa abin da za ta iya kintsawa. Ta dawo tsakar gida inda yake kwance. Ta dur?usa a kan sa, ta dafa shi ta ce "Tashi mu je ka kwanta a Waki, nan akwai sauro kuma ?wari za su cije ka"

Da ?yar ya tashi, suka koma Waki, ya nemi guri ya kwanta a ?asa. Kawai Nana ta zauna ta zura masa ido, cikin matsananciyar damuwa, duba da yadda take maganin ?aba amma kai na daWa kumbura.
A haka dare ya tsala, ta gaji ta kwanta a gefen sa, zuciyarta fal da damuwa. Bacci na ?o?arin Waukar ta, ta ji tasowar guguwa ta buWe idonta, ta gan su kwance a cikin sahara, ga yashin saharar na wani irin han?oro iska za ta mamaye su. Ta saka hannu ta rungume shi saboda guguwar saharar. Sautin tsohon nan ta ji yana wata irin dariya. Ji ta yi an hankaWa ta, sai da ta wuntsula Wakin gauraye da duhu, amma ta ga alamun Sayyid ne zaune a kan katifa shi ne ya hankaWa ta. Ya tashi ya koma bakin ?ofa ya yi zamansa.
Da kyar ta sake lallaSa shi, ya koma ya kwanta. Ita ba ta sake komawa bacci ba, ta yi alwala ta zauna tana tasbihi har aka yi sallar asuba. Sai dai fafur ya yi salla ya ?i yi. Ya nemi guri ya zauna ?yam yana kallon ta.

Ta dama masa kunu, ta soya fanke, ta zo Waki ta zauna a gaban sa. Ta ce "Ga kunu ka sha, amma dan Allah kar ka zubar Sayyid ka ji?" Ta yi maganar tana mi?a masa kofin kunun. Sai ya mi?o hannun hagu zai karSa. Ta janye kofin ta ce "Hannun dama dai, wannan hannun za ka bani" Ta yi maganar tana nuna hannun damansa, amma bai mi?o mata ba, ya zura mata ido.

Ta kai hannu ta janyo hannun nasa, dan ta dam?a masa kofin kunun, amma ta ji hannun a ?ame ?am. Ta sake ?o?arin janyowa, amma ta ji tamkar tana jan itace.

Ta kalli hannun sosai, sai ta ga shanyewa ya yi.

Gabanta ya yi wata irin mummunar faWuwa, ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Sayyid me ya same ka haka? Me ya samu hannunka? Ya Allah!" Ta yi maganar tana kuma ?o?arin ganin ta mi?ar da hannun nasa, amma hannun yana ma?ale, kamar an tsotse shi.

Ya sunkuyar da kai ya yi shiru, fuskarsa Wauke da damuwa. Ta aro jarumta, ta matsa daf da shi, ta Webo kunun ta kai bakinsa. Amma ya tsaya yana kallonta, bai buWe bakinsa ba.

"BuWe baninka na baka" Ta yi maganar tana ?o?arin danne hawayen da ke ?o?arin ?wace mata.

A hankali ya buWe bakin, sai ta ga shi ma bakin ya karkace, yawu na ?o?arin zubowa. Kawai ya rufe bakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login