Showing 24001 words to 27000 words out of 122467 words

Chapter 9 - Buzu Book 2 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

25

hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanunsa. Ta ajiye kofin kunun ta rasa abin yi. Kawai rungume shi, ta fashe da matsanancin kuka, sai da ta yi iya yin ta.
Sannan ta cika shi, ta share masa hawayensa.
Ta fara ?o?arin ba shi kunun, sai dai tana ba shi, ya haWiye wani kuma ya zubo.
Ta na yi tana goge masa wanda yake zubowa, ta gama ba shi, ta kama hannunsa su ka je waje, ta taimaka masa ya yi alwala. Ya dawo ya rama sallolin da ta gaya masa ana bin sa. Sai dai ba magana ga hannu a ma?ale, da ta kalle shi sai ta ji hawaye ya cika mata ido.
Ganin yana gyangyaWi a zaune, ya sanya ta saka masa pillow ya kwanta, ta saka hijjabi ta fita.

Tafiya mai nisa ta yi, ta je ta samu wani chemist, bayan sun gaisa ta ce "Dan Allah malam, idan babu damuwa, Bp nake son mu je ka gwadawa mijina a gida"

Ya kalle ta ya ce "A ina ne?"

"Cikin Budu ne, nan unguwar maharba"

"TaS gaskiya da nisa gurin nan ba kaWan ba, ba zan iya zuwa ba sai dai ki je ku zo tare a yi masa"

"Wallahi da zai yiwu, da ba zan zo na ro?e ka ba, yana kwance babu lafiya ka taimaka mini dan Allah"

Ya ce "Gaskiya kin san cajin zuwa gida ma ka yi wa mutum abu daban yake, sai dai idan za ki ba ni dubu biyu"

Nana ta ce "Eh na yarda mu je zan baka in sha Allah" Ya rufe chemist Win ya bi Nana.

Su na zuwa gidan, Nana ta shiga ta tarar da shi a zaune ya tashi, ta ce "Sayyid kar ka ga na fita ban gaya maka ba. Na je na samo wani ma'aikaci ne, ya zo ya duba jininka a gani, idan jinin ne ya hau ya sanya hannunka ya shanye, mu tafi Asibiti. Idan kuma ba shi ba ne, sai mu san abin yi." Bai ce komai ba, ta yi wa mai chemist magana, ya shigo ya gwada jininsa.
Ya gwada ya kalli Nana ya ce "Jininsa bai wani hau sosai ba, 140/90 ne" Ajiyar zuciya Nana ta yi. Ta ce "A ganinka wannan hawan zai iya sanya masa shanyewar hannu?.
Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba na tunanin haka, amma ban tabattar ba tun da ni ba likita ba ne ba. Amma a shekarunaa bana tunanin jinin 140 zai shanye masa wata gaSa a jikinsa, amma dai ku je Asibiti a ?ara bincikawa"
Nana ta ba shi kuWin sa, ta yi tai masa godiya. Ta koma Waki ta zauna ta yi shiru, tana tunanin ko Uwani za ta tambaya, idan akwai wani mai magani, ta raka su, sai dai ta fasa saboda akwai sauran SurSushin jahilci a tattare su, ba ta son surutu kuma tana tsoron a kai su gurin da ba shikenan ba.

****

Alhaji Fatuhu kuwa kamar yadda ya matsa, sai da aka sallame shi ya koma gida. Gidan nasa ma wani abokin kasuwancinsa ne ya saya, ya bar shi a ciki ya zauna ya bar masa aro.

Sagir yana kwance a kan gadonsa, yana kaWa ?afa ya ?ura wa screen Win wayarsa ido. Yusra ce zaune sanye da doguwar rigar material, kanta ko Wan kwali babu, dogon gashin kanta ya sha gyara. Tana ta zuba masa surutu.
Har mamaki yake yi, yadda Yusra ta zama mai Wan karen surutun tsiya, wanda da ba haka take ba.

"Ya ka yi shiru ne?" Ya wani lumshe ido ya ce "Ina jin ki ai".

"So talk, ka yi magana mana" ta yi maganar tana cika bakinta da guggurun hannunta.

"Ina ga zan shigo Abuja mu haWu very soon in sha Allah" wata irin zabura ta yi ta ce "Are You serious, dan Allah da gaske?"

"Da gaske nake, zan zo na ganki, amma ki na ganin babu matsala a zuwan nawa? Kar a yi miki faWa fa, ba zan ji daWi hakan ba"

Yusra ta ce "Babu wata matsala, ba za a yi mini faWa ba, ai ba na tare da su Mami, ina gidan Anty Sumayya. Dan Allah ka zo"

Sagir ya yi murmushi ya ce "Kin yi missing Wina ne?"

Ta gyaWa masa kai tana murmushi.

"Shikenan, i miss you too, ban taSa tunanin ma za ki neme ni ba, na za ta ki na jin haushina haryanzu, amma in sha Allah zan shigo, zan sanar miki lokacin da zan shigo na zo na ganki" ya yi maganar yana kashe mata ido.

Shukura ce ta turo ?ofar Wakin ta shigo, a burkice ya kif wayar yana kallon ta. ?arara yanayinsa ya nuna alamun rashin gaskiya, amma ta share shi, ta haye kan gadon ta ja bargo ta lulluSe jikinta.
Ya matsa kusa da ita yana Wan shafa ta ya ce "Sweetheart, ya na gan ki kamar a fusace ne? Lafiya dai ko?"

"Lafiya ?alau" ta amsa a ta?aice. ?an shiru ya yi yana tunanin ko dai ji wayar da yake yi ne? Amma a yadda ya santa da azababben kishi, da zargi da ta ji sai ta yi masa magana. Sai dai ya bar abin a haka bai matsa mata da tambayoyi ba gudun kar su yi faWa.

Tana ankare da take-taken Sagir, na rashin gaskiya. Sai dai ita yanzu ba wannan ne a gabanta ba, bin diddigin mutuwar Wanta take son yi. Dan haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da natural mutuwa ya yi. Domin haryanzu tana mafarke-mafarke marasa? daWi da mahaifinta da kuma Doctor Sharif.

****
Aka shiga sati na biyu, Sayyid yana cikin wannan yanayi na rashin lafiya, kuma hannunsa bai saki ba, yana nan a ma?ale.
Ga hauka da yake yi tuburan wasu lokutan, wasu lokutan idan ya burkice sai ya sha?e ta, ko ya hankaWe ta ?asa, sai dai ta yi ?o?arin kare cikinta. Ko kuma Ya ya ta watsi da duk abin da ya ci karo da shi, a Waki ko a tsakar gida. Wasu lokutan ma katangar Wakin yake duka da kansa. Ya ?i cin abinci ya ?i shan magani, ba salla, komai sai dai ta yi masa cikin rarrashi da ban ha?uri. Tun tana jin tsoron ya yi mata wani abin, har ta daina ji, ta zuba wa sarautar Allah ido.
Sannu a hankali ta rage yawan amai, sai dai zazzaSi da rashin son cin abinci da take yi, hakan ya sanya ta tabattar da cikin jikinta bai fita ba haryanzu. Sai dai ba ma ta cikin nutsuwar da za ta nemi inda Asibiti yake ta je, ta tabattar da halin da suke ciki ita da jaririn saboda tashin hankalin da take ciki.
Yanayin yadda uwani ta lura kamar Nana na Soye wani abu, ya sanya ta daina zuwa gidan,ta rage aika yara ma. Sai dai lokaci lokaci, ta kan aika mata da Abinci.
Haka sauran 'yan uwansu na garin ma, su kan aiko mata da sha tara ta arziki saboda su na tausayin Nana, sun san mijinta a kwance yake babu lafiya.
Yawon roro a gona kuwa yanzu Nana ta ?ware, ranar kasuwa ta je ta sayar da abin ta.
Kasancewar ranar Asbar kasuwar garin take ci, sai ta tashi ta yi fanke da sassafe, jikan Uwani Haladu, ya kai mata kasuwa. Ko ta dafa masa zoSo ta ?u??ula ya tafi da shi.
Idan ta gama komai kuma, ta bi yara gona roro.

Dare ya tsala, amma Nana tana zaune tunkurkur, wuni Sayyid ya yi yana wani irin nishi, ga wannan azababben zafin jiki da yake fama da dhi.
Tana zaune tana tunani, t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ana jin yadda mararta take motsi, cikin jikinta yake motsawa.
Ba ta da sauran wanda za ta kai kukanta bayan Ubangiji. Ta fara tunanin ?o?arin tara musu kuWin mota, su tafi Nijar, neman danginsa, sai dai idan sun je Nijar Win ina za su nufa? Babu tsammani ta ji Sayyid Win ya laluba cinyarta, ya kwantar da kansa.
Ta shafa gashinsa ta ce "Sayyid" bai amsa ba, sai dai ya ri?e hannunta. Hakan ya tabattar mata da ya dawo hayyacinsa ne. Haka ta tashi a cikin daren ta tsiyayo ruwan zafi, ta ba shi shayi ta yi masa wanka suka kwanta, ta lulluSe su da bargo.
Sheshshe?ar kukansa ta ji, duk da yadda ta san ya daWe yana dauriya, da son Soye gazawarsa, sai dai ta ga hakan a idanunsa.

"Sayyid idan ka na kuka, ni kuma ya zan yi kenan? Dan Allah ka daina" ta yi maganar muryarta na rawa. Ta din ga shafa bayansa a hankali, har ya yi shiru, bacci ya Wauke shi.
Sai dai tun daga wannan, haka aka sake shafe kwanaki biyu, bai sha ko ruwa ba. Dama rashin maganarsa ya daina damunta.
Ga shi yau abin ya tashi sosai, haukan yake yi da gaske. Ta rufe shi a gidan, ta je ta samo gasara a gidan Uwani, ta dawo ta dama masa kunu. Ta nufi Wakin cike da fargaba tare da fatan ya samu ya sha ko kaWan ne.
Sai dai ta ji wata irin guguwa ta taso mai ?arfi.

Jin yadda guguwar ta taso da ?arfinta, take fatali da duk abin da ta ci karo da shi a tsakar gida, ya sanya ta tashi da azama, ta fara ?o?arin rufe ?ofar katakon da take Wakin. Sai dai tana danna ?ofar guguwar ma na danno ?ofar.

A take ta fara karanto "A'uzubillah, Allahumma inni as'aluka khairiha wa a'uzubika min sharriha. Allahumma inni as'aluka khairiha wa khairi ma fihi, wa khairi ma ursulat bihi, wa a'uzubika min sharriha wa sharri ma fiha, wa sharri ma urisilat biha" take ta ji nauyin da ?ofar ta yi ya ragu, ta samu ta rufe ta, ta juya da sauri ta nufin gurin da yake.

Da fari yana zaune a guri Waya ne, amma yanzu Jifa yake da kayan Wakin da hannu Waya, da sauri ta fara? bi tana tattarewa, cike da damuwa.
Cikin siriryar muryarta ta ce "Sayyid za ka ji wa kan ka ciwo, ka saurara ka saurari muryar matarka, ni ce a gare ka, ni ce fa, Husnan ka ce fa" Ta ?arasa maganar a raunane, duk yadda take ?o?arin tare shi ta kasa, domin ta gama firgita da lamarinsa. Tun safe take fama da shi, ya ?i cin komai, kuma ta kasa sarrafa shi duk rarrashin da ta yi a banza.
Cikin matsananciyar damuwa, hawaye na bin kuncinta ta ce "Ubangiji ka dubi mijin Nana, ka cire masa zafi da raWaWin da yake ji, ka saita masa tunani da ?wa?walwarsa, ya yi rayuwa mai cike da nutsuwa da farin ciki irin na sauran mutane" sai kuma ya tsaya cak, ya juyo yana kallonta.
Ta ?arasa gurinsa, ba tare da fargaba ba ta? ri?o hannunsa cikin nata jikinsa zafi sosai. Ta kalli cikin idanunsa sai taga yana birkice mata yana rikiWewa kamar ba Sayyid Win ta ba, idanunsa har wani haya?i yake fitarwa, gaba Waya kaminsa sun sauya.
Ta lallaSa ta zaunar da shi, Ta yun?ura zata tashi, domin ta Waukko kununsa ta sake jarraba ba shi, ta ji ya cafko ta yana wani irin sambatu bakinsa na kumfa da dalalar da yawu, da alama magana yake son ya yi mata. Rashin ?arfin jiki ya sanya ta faWa jikinsa. Ya ?an?ame ta sosai, saboda zafin da yake ji, ita kuma jikinta sanyi ?alau. Ita ma jikinta ya Wauki rawa, ta lafe a jikinsa ta kwantar da kanta a ?irjinsa tsawon mintuna, jin ya Wan nutsu jikinsa ya rage zafin ya sanya ta zare jikinta a hankali.

Ta Waukko kofin kunun da cokali, sai wani Wan ?aramin tsumma, ta zauna a gabansa ta Webo kunun a cokali ta kai bakinsa, sai dai ya tsaya yana bin ta da ido, kamar ya ga ba?uwar halitta, ta buWe nata bakin, ya kalleta shi ma ya buWe nasa.
Ta fara zuba kunun a bakinta ta haWiye, sannan ta zuba masa a bakinsa shi ma. Ya haWiye sai dai wani na biyo gefen bakinsa, bai haWiye duka ba. Tana bashi tana goge masa wanda yake? zubowa. Sai da ta tabattar ya ?oshi, sannan ta goge masa bakinsa. Ta Wauki kofin ta nufi ?ofa ta buWe a hankali ta ga an daina iskar, ta fita da kofin ta ajiye, ta tattara abin da guguwar ta watsa sannan ta dawo Wakin.

Jiki a sanyaye, ta zauna a gabansa tana ?are wa kyakyawar fuskarsa kallo. Da ?yar yake jan numfashi yana saukewa.? Ta sanya hannayenta biyu, ta gyara masa gashinsa, da ya rufe masa gefen idonsa, ta saka idonta a cikin nasa, cikin rauni da karaya, idanunta na zubar da hawaye ta motsa bakinta, ta fara magana

"Sayyid, dan Allah ka yi magana ko na ji daWi, wannan karon ka daWe ba ka ce mini komai ba. Da na sanya ran ka fara samun? lafiya, amma kullum lamarin nan gaba yake yi. Ka gaya mini wane ne kai? Daga ina ka ke? Ina zan samu danginka da 'yan uwanka, wata?ila kai naka dangin ba za su guje mu ba, za su karSe mu, tare da sar?ar da ta haWa ?addarorinmu wuri guda, duk da ban kasance Waya daga cikinku ba, ni fatana a nema maka magani ka samu lafiya, ba na son ganin ka cikin wannan mummunan yanayin, idan na ci gaba da ganain ka a haka, zuciyata za ta iya bugawa. Dan Allah ka yi magana" Ta yi maganar wasu hawayen na zirarowa daga cikin idanunta.

Ayshercool
08081012143

58
Ya haWiye wani irin yawu, da yake yi masa zafi a ?irjinsa, yayi ?o?arin Wago hannunsa na dama, sai ya tuna ya riga ya shanye, ba ya iya komai da shi. Ya buWe baki da nufin ya kira sunanta, saboda tasiri da kuma ciwon da kukanta yake yi masa a zuciyarsa, amma ya gaza bakin ya karkace yawu ya fara zubowa daga bakin nasa, maimakon kiran sunanta da ya yi yin?urin yi.
Tana kuka, ta sanya tsumman da tayi amfani da shi wurin ba shi abinci, ta goge masa bakinsa. Ba shi da zaSin da ya wuce, ba wa hawayen da yake ma?ale a cikin idanunsa damar zubowa, ko shi ma ya samu sassauci abin da yake ji.
A hankali ya hura mata iskar bakinsa a fuskarta, a take ta silale ta faWi a jikinsa.
Ya sanya hannunsa mai lafiya, ya rungume ta, ya ci gaba da kuka. Jikinta gaba Waya ya saki.

?aisar ta gani a gurin haWe-haWen magungunan sa, yana ta haWa wani abu a cikin kwalba. Zuciyarta ce take ta azalzalarta, da ?o?arin ingizata, sai dai ba ta yi magana ba.

Babu tsammanni, ta ji ya fara magana "ZaSi Waya ya rage miki, a halin yanzu, ko dai ki yadda da abin da na zo miki da shi, ki rungumi ?addararki, ko ki na kallo Buzun nan zai mutu, domin ba zai taSa tuna waye shi ba har abada, muddin Giyaz yana tare da shi. Dan ba na tunanin akwai wanda zai iya raba shi da shi. Idan har bai iya tuna waye shi ba, shikenan kin ga ba ki da wata makoma. Abu Waya zai sanya a wannan karon na bar miki abin da yake cikinki, duk da ba ni da tabbacin zai zama mai cikakkiyar lafiya ko akasin haka, Giyaz da mu?arrabansa sun riga sun fara taSa shi a cikin ki. Kin san meyasa ban ?arasa lalata wannan cikin ba?" Bai jira ta ba shi amsa ba ya ce "Saboda zan so na ga yadda za ki yi, a lokacin da Wan zai amsa sunan shege, kuma ba za ki iya hanawa ba, domin ba ki da hujjar kare kanki. Idan Buzun nan ya rayu bai san waye shi ba, ga kuma nakasa. Idan kuma ya mutu suwaye dangin baban Wan ki? Daga ina yake? Suwaye ahalinsa? Kin san ku a jinsinku na bil'adam da uba ake ado ba riga ba. Babu wanda zai damu da wacece ta haifi mutum, amma za a damu da waye ubansa meye nasabarsa? Tun da ki ka zo garin nan, zuriyarmu suke alwashin yadda fansar su za ta kasance a kan ki. Kafin zuwa wannan ?adamin babu abin da ban gaya miki ba, na gargaWi. Dan haka dabara ta rage ga mai shiga rijiya"

Cikin kuka Nana ta hau girgiza kai ta ce "Ba zan yi bori ba ?aisar, ba zan yi shirka da Allah ba. Babu tsanani ko wahalar da za ta sanya na rabu da imanina. Amma na rasa gaba na rasa baya, ba dan ina neman taimakon ka ba, ko ka kawo mini Wauki ba. Na san Ubangiji Allah shi zai taimake ni.
Amma dan zatin Allah idan ka na da hannu a ciwon Sayyid, ka yi mini rai ka rabu da shi, shi ne kaWai duniyata. Ina matu?ar tausayin sa, ban damu da jinya da nake yi ba, wahalar da yake sha ta isa haka. Idan kuma laifikan zuriyarmu ne suke shafar sa, dan Allah ku yi ha?uri ki ?yale shi haka"

Cikin sautin muryarsa mai ban tsoro, da ya kan yi amfani da ita, idan ya so razana ta, ko yi mata magana mai muhimmanci? ya ce "Na sha gaya miki na maimaita miki, daga lokacin da ki ka fara bani umarni, kin yadda kin amince da bu?ata ta ne. Ba ni da hannu a ciwon mijinki, kuma bai ya cikin zuriyar ku, sai dai ?addara mai ?arfin gaske, ta haWa ku tarayya guri guda. Amma muddin ki na son ya warke daga wannan rashin lafiya, ba ma iya haka ba, ya tuna waye shi, sai kin karSi ?addararki.".

Nana ta sake marairaicewa ta ce "Ba zan iya shirka ba, ba zan iya zama 'yar bori ba. Zan jure jarrabawata komai zafinta amma ba zan yadda rasa imanina ba"

?aisar ya ce "A cikin biyu dole abu Waya ya faru, tunda kakaninki su suka ?yan?yashi wannan matsalar. Na yi iya ?o?arina gurin dakatar da ita a wancan lokacin, amma ta sake tasowa a wannan karon. Dole a cikinku Waya zai warke ya rayu Waya ya mutu a haka, dan babu alamar Giyaz zai sassauta wannan mummunan ?udirin nasa a kan zuriyar ku. Gefe ga aikin da ya karSa yake yi a akan mijinki, ko dai ki ci gaba da rayuwa da shi, laifukan ku na shafar sa, ko kuma ki yarda ki karSe ni a matsayin hadiminki ki yi abin da nake so, ni kuma na san yadda zan yi da Giyaz, na baki maganin da mijinki zai warke"

"Ta yaya? Me yasa sai ni? Me yasa ni zan biya zunubin da lokacin da aka aikata shi ba na nan, zunubin da zamanin da aka aikata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login