Showing 114001 words to 117000 words out of 122467 words

Chapter 39 - Buzu Book 2 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

40

dai wani abin ne daban.
Gyaran murya da ya yi da ?amshin turaren da ya cika gurin ne ya sanya ta farga ta waiwaya, sai ta ga a kan hanya ta tsaya.
Ta yi taku biyu ta ba shi guri, ya saci kallonta, zuciyarsa ta din ga raya masa son sanin wace ce ita, sanin na sosai ya yi mata tambayoyi game da wasu abubuwa.
Ya haWiye yawu ya zo zai gifta ta, wani irin daddaWan sanyi ya ratsa shi, sanyin da zai yi fatan dauwwama a cikin sa, saboda yadda ya saba da zafin jikinsa, wanda duk sanyin da yake guri, a cikin jikinsa yake jin wannan zafin.
Sai dai wannan sanyin da ya ratsa shi, har cikin ?ashinsa ya ji sanyin.
Ya sake waiwayawa ya kalli Nana, amma ya ga shi take kallo. Ji yake tamkar ya koma da baya ya ?ara samun kusanci da ita, sai ya fi jin sanyin sosai da sosai. Tun da Allah ya jarrabe shi da ciwon nan, bai taSa jin sanyi mai daWin wannan ya ratsa shi ba, kuma ya yi imani da Allah daga jikinta wannan sanyin yake, saboda sun samu kusanci sosai da sosai da zai gifta ta.
"Allah ya sa ba wani abin ake kuma shirya mini ko wani tarkon ake shirin yi mini da ke ba" Ya yi maganar a zuciyarsa.
Nana ta yi mamakin dalilin da ya sanya shi tsayawa haka.
Zuciyarsa ta din ga raya masa ya koma da baya, daf da Nana, ko zai fi kin sanyin yadda yake so.




AREWABOOKS

Nana ta ce "Sayyid ko wani abu ka ke bu?ata ne?"
Sai da ta yi maganar sannan ya farga, bai ce mata komai ba kawai ya fice ya bar gurin.
****
Shukura ce a zaune ta takure jikinta, tana kallon kwanon abincin da aka kawo mata, Abinci mai rai da lafiya sai dai ko sha'awar kai wa bakinta ba ta yi ba, duk da uwar yunwar da take ji, tamkar ta ci babu.
Shiru ta yi tana tuna yadda bayan fitowarta daga Asibiti suka yi karo da wani mai adaidaita sahu.
Ya fito yana jarabar sai ta biya shi, duk da shi ne da laifi, amma ta kasa fitowa daga motar, ta sauke gilas ta ce ya gaya mata dammage Win nawa ta yi masa ta biya shi. Daga sauke glass Win nan ba ta sake sanin inda kanta yake ba, sai farkawa da ta yi ta ganta a wannan Wakin, da sai dai a zuro mata abinci kawai.
Ba ta iya banbance adadin lokacin da ta kwashe a gurin ba, sai d????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ai ta kintaci lokacin salla ta yi.

Babu tsammani ta ji an buWe ?ofar Wakin, hakan ya sanya ta kalli ?ofar da sauri.
Sai dai hasken fitilar mai wayarya haske mata ido, ba ta iya gane waye ba.
Sannu a hankali ya jingine wayar hannunsa ya zura mata ido.
Duk da ta Wan razana amma abin bai wani ba ta mamaki sosai ba.

Ya zuba mata ido sannan ya ce "Kin yi mamaki ko?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba sosai ba"

"Ko me yasa?"

"Saboda jikina ya daWe da bani hakan"

"Ta yaya kenan?"

"Na daWe ina zarginka ne, sai dai ana ta dankwafe ni, an hanani"

"Gaskiya ne, ban so ki zurfafa ki takura da son sanin abin da bai kamata ki yi ta bibiya sai kin gano ba, amma ban san me ki ka gani ki ka dage kina bin diddigina ba"

"Zarginka nake yi da kai da doctor Sharif na kasa yadda Wa na mutuwa ya yi, saboda har yau ina ji a jikina, mafarkin da na yi gaskiya ne"

Alhaji Zailani ya ce "Haka ne, lokuta da dama mafarki ishara ne, duk da ban san abin da ki ka gani ba, amma zarginki gaskiya ne duk da na yi iya yi na a kan na Soye komai, sai dai kashi kin za?e Shukura, soyayyar da nake yi miki ba za ta hana ni Waukar matakin da ya dace a kan ki ba"

Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Da gaske ka na da masaniya a kan batun mahaifar Mami?"

"Ina da ita, haka zalika ina da masaniya a kan jaririnki ma da ki ke ta zargina da Sharif a kai, duk da ban san me ki ka gani a mafarkin ba"
Shukura ta yi masa wani irin kallo, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri.

"Tabbas mafarkinki ishara ne. Amma kafin na yi miki wannan bayanin ina son ki sani, talauci bala'i ne Shukura, babu yadda ban yi a kan na yi ya?i da shi ba, amma abu ya gagara. Na faWi na tashi na yi iya yi na amma na kasa nasara a rayuwata. Burina ya gaza cika na mallakar manyan motoci da gidaje da tara manyan kuWaWe yadda zan yi nesa da talauci.
'yar makarantar da nake ta?ama da ita, abubuwa suka nemi ?wace mini, bayan faWuwa a jarrabbawa. A ta?aice dai a makaranta na samu ?ungiyar asiri na shiga, cike da burin na gama makaranta cikin sa'a da fatan cikar burikana na yin arziki mai yawan gaske ta hanya mai matu?ar sau?i.
Bayan na auri mahaifiyarku, ta haifi Sadik, ?ungiya ta fara neman jini a gurina. Na bayar da babban Wa na Sadik, na kaWu na shiga tashin hankali, sai dai hakan ne zai ba ni damar taka babban matsayi a ?ungiyar, duk da na bayar da waWanda ba jinina ba a ?ungiyar amma na ji zafin bayar da Sadik. Aka haifi Yusuf, aka haife ki, ba a sake neman kowa ba, sai da wata bu?ata ta sake taso mini, wadda biyan bu?atar na bu?atar na ?ara taka wani matsayi a ?ungiyar.
Haka na bayar da matata ta fari, Hafsat da tsohon ciki, na saka mata ?yallen jini a ?asan shimfiWarta ta tashi da ciwon na?uda ta mutu a gurin haihuwa.
Hakan ya sanya dukiyata ?ara haSaka, na yi kuWi na yi suna. Duk fafutukar kasuwanci da muke yi tare da Fatuhu, shikaWai yake abin sa, ni fakewa kawai nake yi da kasuwanci amma ta ?ungiyar asiri nake samun kuWina.
Duk da ina samu ta kasuwancin ma, amma ga mamakina Fatuhu da baya ?ungiyar asiri, ya fi ni samun kuWi, kuma duk inda muka je an fi son sa.
Bayan na auri Amina, aka bu?aci duk wani Wa da za ta haifa, zan din ga ba wa dodon ?ungiya. Lamarin ya yi mini nauyi, saboda ina jin Wacin rabuwa da iyalina. Na nemi sassauci, sai aka dasa wa Amina wani jaririn aljani a cikin mahaifarta, duk cikin da ta samu ba ma ta sani yake cinyewa. Sai dai kawai ta wayi gari tana zubar da jini, babu ?a??autawa. Karo shida na shidan saura ?iris ta rasa ranta, saboda jini take zubarwa ba kaWan ba, sai dai a yi ta saka mata jini.
Ba a taSa gane Sari take yi ba, an zata larura ce kawai,? Asibiti aka kasa gane abin da yake damunta, na kuma hana a yi mata na hausa, tana zaune lafiya kawai sai ta hau zubar da jini babu ?a??autawa.
Ta damu ta damu da matsalar rashin haihuwa, amma na hana ta zuwa Asibiti ta ci gaba da bibiyar lafiyarta.
Ni kaina na damu da wahalar da take sha, sai aka nemi na sadaukar da mahaifarta gaba Waya ga wannan jaririn aljani, yadda ba sai ta ci gaba da samun ciki ba, cinyewar da yake tana azabtar da ita ba.
Haka na amince, cikin dare ta farka tana ihu da buge-bige, ina kunna fitila na haska, na ganmu a cikin jini male-male.
Na rirri?e ta, amma ta fita daga hayyacinta, ihu kawai take tana ri?e mararta, a dole? na Wauke ta muka yi Asibiti, ganin za ta rasa ranta saboda zubar jinin nan. Ta fi kwana uku ba ta hayyacinta, jini kawai ake saka mata.
Aka tura mu scanic, domin a gano musababbin zubar jinin.
Na takurawa mai scanic Win ya gaya mini me ya gani. Ya sanar da ni babu mahaifa ma a jikinta gaba Waya, dan haka bai ma gano daga inda bleeding Win yake ba a scanic Win, sai dai a ci gaba da bincike.
Abin ya bani mamaki, duk da a cikin ?ungiyar asiri nake, ban taSa tunanin za a ga abin a zahiri a yi scan a ga babu mahaifa ba.
Na biya mai scannnic kuWi, ya rubuta sakamakon da ba daidai ba.
Muka koma gurin likita, aka din ga bincike ba a gane komai ba. Ita kuwa sai da ta shafe kwana goma ba ta tantance wanda yake kanta, har an fitar da rai da ita sai kuma ta warke.
Na daWe ina tunanin abin da na yi mata saboda son da nake yi mata. Muka tattauna da malamina, da mamakin yadda a scanic Win aka gane bata da mahaifa ma zata a zahiri bs a za a gane ba.
Sai ya ce mini idan na ce haka na ?aryata kungiyar asiri gaskiya ce kenan, amma ya aka yi na yadda da kuWin da nake samu a cikinta, har nake kashe su a zahiri? Ya ce mini dole na san duk yadda zan yi na ci gaba da rufe mata ba ta da mahaifa, dan kar ta ce za ta bi diddigi duk da ko ta bi diddigin babu abin da za ta iya ganowa.
Wannan aljani haryanzu yana rayuwa a cikin Amina, gurbin da mahaifarta take, kan addabe ta da ciwo wasu lokutan, sannan wannan aljani shi ne yake saka ta zubar da jini lokaci zuwa lokaci da take tunanin Al'ada take yi. Wasu lokutan ta zubar da jini fiye da kima wanda take tunanin duk su ne dalilin rashin haihuwarta."

Cikin matu?ar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buWe ido a duniya ba ta taSa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba.

Cikin matu?ar tsoro da matsanancin mamakin yadda ya zauna ya wassafa mata wannan mummunan labarin da tun da ta buWe ido a duniya ba ta taSa jin labari mai razanarwa da tashin hankali ba.
Da ?yar ta harhaWo kalmomin da ta ce "Kai ka kashe Mummy, kuma ka bayar da mahaifar Mami? Da..da.dama aljani duk zai iya yin irin wannan abin?"

Yayi dariya ya ce "Ki na mamaki ne? Kodayake mutane duk abin da ba a kanmu ya faru ba, bamu fiye yarda ba, nima da fari kasa yarda na yi, abin ya Waure mini kai. Sai dai idan ki ka duba, ba a taSa yi wa Amina aiki ba, kuma babu alamar tabo na tiyata a jikinta, dan haka ta yaya za ta rasa mahaifarta? Aljani muddin za ka yi masa biyayya, ka yi abin da yake so, to zai zama mai biya maka dukkanin bu?atunka. Da su ake sihiri, da su ake jifa, neman shugabanci, Waukaka kungiyoyin asiri da makamantansu. Duk wani siddabaru da za a ce miki sun yi ba abin mamaki ba ne ba" Ya yi maganar yana wata 'yar guntuwar dariya.
Shukura ta ?ara rikicewa ta kiWime. Ta ce "Yanzu Daddy, duk son da mahaifiyarmu ta yi maka kai ka kashe ta? Ga amanarmu da Mami ta ri?e ta kula da mu, ashe dama rashin haihuwarta da ciwon nan na zubar da jini da take yi babu gaira babu dalili, kai ne sila? Kai ka haddassa mata? Yanzu tayaya zaka nemi yafiyar su? Ka rasa imaninka saboda abin Duniya? Kai fa ka kashe su"

Ya ce "No in ji wa? Ai ban rasa imanina ba, ai annabi ya ce duk wanda ya ce La'ila ha illalahu zai shiga aljanna"

Cikin kuka ta ce "La'ila ha illalahu ba ta fatar baki ba Daddy, tayaya za ka shiga aljanna bayan ka kai bu?atarka gurin wanin Allah da ya bu?aci ka saSa wa mahaliccinka dan ya biya maka bu?ata. Me yasa ka ga bu?atar ka ta yi girman da ta gagari Ubangijinka ka dangana ga waninsa"

"Wannan wa'azin naki kin riga kin makara Shukura. Ina da ya?inin zan tuba kan na mutu, kuma Allah zai yafe mini"

"Wa ya baka garantin ganin nan da awa Waya ma?" Ta yi maganar tana kuka mai tsuma zuciya.

"Ina da shi, dan ko ciwon kai sai na shekara ban yi ba"
Ya mi?e tsaye yana faWin "Ki mayar da hankali ki din ga cin abinci, saboda ke da abin cikinki nake sanya ran ku zama sadsukarwar ?arshe da zan yi a ?ungiya. Sai dai kafin nan, ina ro?on afuwarki ko ba komai ke ma kin ci albarkacin dukiyata. ?anki da ki ka rasa ni na yi amfani da shi" Daga nan ya Wauki wayarsa ya yi gaba abin sa hankalinsa a kwance, kamar bai aikata komai ba.
Wani irin gunji Shukura ta din ga yi tana kuka mai tsuma zuciya, ta din ga fatan ina ma mafarki ne ba gaske ba. Tabbas wannan babbar jarrabawa ce, a ce mutum irin mahaifinta shi ne mahaifinka, gara a ce an haife ka ba ta hanyar aure ba, ko makamancin haka. Amma uba irin Alhaji Zailani ba shi da wani amfani. Duk wata gwagwarmayar sa da faWi tashinsa a kan iyalinsa ya zama na banza, a dalilin wannan mummunar hanyar mara Sullewa.
Abubuwan da ya gaya mata sun shallake tunaninta, yanzu yadda ya tafi haka zai je ya ci gaba da rayuwa da Hajiya Amina duk da zaluncin da ya yi mata. Ta ji dama ta ba wa Sagir damar kai ta Asibiti wata?ila da ba a samu damar sace ta ba. Cikin kuka take ro?on Ubangiji Allah ya tona wa mahaifinta asiri, saboda a yadda zuciyarsa ta ?e?ashe Win nan, babu wani abu na rashin imani da zalunci da ba zai iya aikatawa ba.

Can gida Sagir ko abinci ba ya iya ci. Yusra kuwa abin ka da ba cikakkiyar lafiya ce da ita ba, sai ta kwanta rashin lafiya, saboda yadda ta addabi kanta da Worawa kanta alhakin Satan Shukura, dan cewa take saboda ta dawo gidan Sagir Shukura ta tafi.
Haka Hajiya Amina ma, Addu'a kawai take yi a kan Ubangiji Allah ya bayyana Shukura a duk inda take. Sosai take jin tamkar 'yar cikinta ce ta Sata, tun tana daurewa har ta kasa ta fara zubar da hawaye, kasancewar babu wani labari mai daWin ji da zai nuna an kusa gano inda Shukura take.

****

Asal ta na tsaye a banWakin cikin Wakinta, bayan tabattar da Imam baya Wakin, ta danna wata lamba ta kira.
Can aka Wauka mutumin ya ce "Na'am ina jin ki"

"Ina da labari ne"

"Ina sauraren ki"

Ta numfasa ta ce "Hannun Imam babu zobensa na tambari, na tambaye shi ya ce mini karyewa ya yi ya kai gyara, daga bisani kuma ya ce mini bai san inda yake ba"
"Kin tabattar da hakan, ba kuma Soye shi ya yi a wani gurin ba?"
Asal ta ce "Eh na tabattar ai zobe ne da ba ya cire shi, tun da ya dawo babu zoben a tare da shi"
Mutumin ya numfasa ya ce "Madalla, ki ci gaba da sanya ido da sanar da ni duk wani abu da yakamata na sani"
Ta jinjina kai tamkar yana ganinta ta kashe wayar ta fita.
Jikin Nana tamkar an yi mata duka, saboda azabar gajiya da ta yi. Ta kammala aikinta tana ta gyaran kitchen, sai ga Balaraba ta shigo da ?atuwar jarka. Ta ajiye ta ta ce "Gashi nan madarar ra?umi ce da Imam yake sha"

"To sannu da ?o?ari Mama Balaraba"

Ta ce "Yauwwa kukun Imam, Allah ya taimake ki"

Nana ta yi murmushi ta ce "Kar ki ba ni kunya mana"

"Ba kunya zan ba ki ba, ai ke yanzu duk wata kuku a gidan nan a ?ar?ashinki take, ke kaWai ki ke dafa abincin da zai ci, dole mu girmama ki saboda kema shugabarmu ce"

"A'a ni ba shugabarku ba ce ba, ni da nake bare ma a cikinku. Amma dan Allah Mama Balaraba wai su wa ake cewa Imam Win nan ne? Dan na ga wanda ake kira da hakan da yawa"

"Eh su Biyar ne, galibinsu jikoki ne na gidan sarauta, su na cikin jerin waWanda za su iya gadon kujerar Sultan. Shi Imam Hammad a gidansu su biyu ne? da shi da Imam Abdallah, sai Imam Zahradeen shi ma jikan marigayi Sultan ne, akwai Imam Asadullah yayan Asal, sai Imam Omar, waWannan su ne jerin waWanda ake sanya ran za su gaji kujerar Sultan. Duk da su na ganin cewa Sultan na yanzu nuna son kai ?arara na son Imam Hammad ya gaje shi a cikin yaransa. Imam Hammad yana da 'yan uwa da suke uba Waya amma su biyu ne suka cika ?a'idojin zama Imam.
A ?asar nan ana girmama duk wani Imam fiye da zatonki, mu na ?asa mu na son Imam Hammad sosai mussaman ba?a?en buzaye da fararen ke? yi mana kallon kamar ba 'yan uwansu ne mu ba, bayinsu ne kawai.
Idan kin lura galibi hadiman gidan nan ba?a?en buzaye ne, fararen kaWan ne ?arara yake ?o?arin ya?i da kyamar da fararen buzaye suke yi mana, yana ta fafutukar nema mana 'yanci, da ?o?arin mu ma a din ga bamu dama a cikin shugabanci, bai kamata iyayenmu sun ?are a bauta mu ma mu ?are a haka ba. Amma manyan nan ba sa son shi sam, gani suke yana ?o?arin hana su rawar gaban hantsi. Ni tun da ya dawo ma duk ya canza mutum ne mai sanyin hali, amma kaifi Waya ne, ba sani babu sabo.
Shi ne shugaban majalisar duk Imam Win ?asar nan. Duk da a cikin su akwai wanda suka girme masa, amma a haka dole su girmama shi kamar yadda yake a dokar ?asar nan.
Tarihin masarautar Agadez yana da yawa da kuma faWi Nana, bari na tafi na je na ci gaba da aikina.
Nana ta jinjina kai ta ce "To shikenan na gode sosai da sosai"
Bayan fitar Balaraba Nana ta naWe hannunta a ?irjinta, tana nazari da tunani.

Jiki a sanyaye ta koma Wakinta, ta duba kayanta ta lalubo takardar nan da aka kawo sa?on aka ce a ba wa Sayyid. Ta ?are wa takardar kallo.
"Ko a cikin Imams Win nan ne wani ya aiko da wannan takardar?" Ta yi maganar tana tuna maganganun da ta ji suna yi ranar da aka kai su yin girki a gidan Sultan. Ta koma ta lalubo zoben gurin Sayyid ta din ga jujjuya zoben ta ce "Ko kai a ke nema ne? Idan kai ne ta yaya zan ba shi abin sa, tun da ban san iya adadin muhimmancin sa a gare ka ba, idan na baka ka manta ni ta yaya zan yi bayani a yarda da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login