Showing 87001 words to 90000 words out of 122467 words

Chapter 30 - Buzu Book 2 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

23

ba ta motsa ba.

Ya matsa kusa da ita, ya ri?o hannunta, ta fizge hannunta ta haye kan gadon ta kwanta.
Bai ji haushin abin da ta yi masa ba ko kaWan, ya san idan ba ta son sa ba za ta yi kishinsa ba, sai dai ita ma Yusra tana bu?atarsa tun da tun farko bai kamata ya sake ta saboda larurarta ba.
Ya tashi ya kashe mata fitila, har zai fita ya koma gaban gadon, ya dur?usa daidai fuskarta ya ce "Ki yi mini afuwa Shukura, ban yi haka domin na cutar da ke ba, ko na muzguna miki, dan Allah ki kwantar da hankalinki saboda lafiyarki da abin da yake cikinki" Daga haka ya tashi ya fice. Sai da ya fita sannan ta ba wa hawayen da suka ma?ale a ?irjinta damar zirarowa, zuciyarta ta din ga yi mata ?una, tamkar ta tashi ta bar gidan.

Duk da ya fita da damuwar halin da Shukura take ciki, amma bayan wani Wan lokaci tuni ya manta, suka ci suka ?oshi da shi da Yusra.
Bayan sun gabatar da salla, sun yi addu'oi, suka yi zamansu kawai su na hira.
Sai gurin Waya saura sannan suka tashi suka kwanta.
Yadda Sagir yake murna da kasancewa da Yusra, ko aurensu na fari bai yi haka ba, tuni wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da su, daga shi har ita.
Shukura kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, ga wani irin zafi da ya addabe ta duk da na'urar sanyaya Waki da ke cikin Wakin.

Washegari sai ?arfe sha Waya na safe ya shiga Wakin Shukura.
Idonta kawai ya kalla ya ga alamun rashin bacci a tattare da idanunta, sun yi jawur sun kumbura.

"Oum Haidar" ya kira sunanta, yana zama a kan gadon, tana shan tea.

"Ina kwana" ta faWa a ta?aice.

Idanunsa ya sauka a kan ledar da ya kawo mata, babu alamar ko taSa ledar ta yi.

"Shukura me yake damunki ne haka? Na kawo abu ko taSawa ba ki yi ba, kin yi bacci makuwa"

"Sagir, dan Allah ka tashi ka bani guri, ni bana bu?atarka a kusa da ni, kaWaici nake so"

"Ni ki ke cewa na fita na baki guri?" Ya yi maganar yana nuna kansa.

?o?arin mayar da hawayen da ke shirin zubo mata take yi, amma abu ya gagara kawai ya fara zubowa ba tare da ta shirya hakan ba.

Jikinsa ya yi sanyi, ganin yadda take kuka sosai da sosai.

Cikin kwantar da murya, yake ?o?arin rarrashinta, amma ta tashi ta shige banWaki ta bar shi a gurin.

Ya yi shiru ya rasa abin da yake yi masa daWi, shi babbar damuwarsa ma cikin da take Wauke da shi, ga matsalarta ta hawan jini.

*****

Tamkar bayi haka su Nana suke aiki, kullum za a Waukkosu daga wancan gidan da Asal take, a kawo su nan su wuni su na aiki. Har mamaki take yi wannan mutanen su kuwa har su nawa ne, dan kamar har da almubazzaranci a cikin lamarin.
Sai dai kowa cikin kaffa-kaffa yake aikin tare da fatan kar wani abu ya biyo baya da za a kama su da laifi.

Kwana na uku, wanda ranar suka dafa normal Abinci, sauran kwanakin kayan snacks ne suka din ga yi. Duk cikin su Nana ce 'yar Nigeria, sauran duk 'yan Nijar ne, sai dai galibinsu ba?a?en buzaye ne.

Sai da suka kammala aikin, aka ba su wasu kaya fararen dogwayen riguna, da rigar girki, aka saka su kai Abincin wani Waki.
Katafaren Wakina da dogon tebur, an gyara shi sai tashin ?amshi yake yi. Sai dai gabanta ya yi mummunan faWuwa da jin irin ?amshin da yake tashi a Wakin.
Take jikinta ya hau rawa, har ta nemi ta kifar da abin da ta Waukko.
Ta Waga kanta a hankali ta kalli jerin manyan frames Win da ke Wakin, sai dai mutanen jikin hotunan, dukkaninsu fuskokinsu a rufe yake, ba ta iya gane kowa daga cikin su ba.

"Ke Nana ki kai mana kin ja kin tsaya" Nana ta jinjina kai jiki a sanyaye ta ?arasa gaban teburin. Ta ajiye kayan, ta Waga kai ta kalli yadda ginin Wakin yake da matu?ar tsayi.
Jiki a sanyaye ta ci gaba da kai komo, su na shirya abincin.
Bayan sun sha?e teburin da uban kayan Abinci, aka ba su umarnin su tsaya kar wanda ya fita.
Su na tsaye Nana ta kalli agogon Wakin, ?arfe goma na dare.
Wani ?aton mutum ya shigo, ya kalli gurin da yadda aka shirya teburin, ya kalli su Nana ya ce "WaWanan ne suka yi girkin?"

Balaraba wadda ita ce ta jagoranci su Nana gurin girke-girken ta risuna ta ce "Eh su ne ranka ya daWe"

"Wace ce wannan? Na ga kamar ba tamu ba ce" Ya yi maganar yana nuna Nana, da gaba Waya rabin hankalinta ba ya jikinta.

Balaraba ta ce "Gimbiya Asal ce ta zaSo ta, ta saka ta a cikin masu girkin"

Ya yi shiru yana kallon Nana, daga bisani ya jinjina kai ya kalli Balaraba ya ce "Ki je, su su tsaya" Ta jinjina kai ta fice.
Wata ?ofa aka buWe, wani matashi ya shigo fuskarsa Wauke da murmushi, gaban Nana ya yi mummunar faWuwa, dogo ne sanye da farar jallabiya ya Waura hirami a kansa, ba dan ta yi wa Sayyid kyakykywan sani ba, za ta iya cewa shi ne. ?irjinta ya tsananta bugawa, sai dai kafin ta daidaita nutsuwarta, wani ma ya biyo bayansa, shi ma dai kamarsa Waya da Sayyid Win.
Tunani ta fara yi ko Giyaz da ?aisar ne suka fara yi mata gizo suke yi mata wasa da tunani.
?aya bayan Waya suka din ga shigowa, sai da ta ?irga mutum biyar cif, biyu kamar su Waya sak, sauran ukun kuma su na kama amma ba sak da Sayyid ba. Duk suka jeru a kan kujerun teburin nan. Sai dai babbar kujera babu kowa a kai, kujerun gefe da gefen kujerar ma babu kowa a kai.

?aya daga cikin su ya ce "Ko waye zai hau wannan kujerar?" Ya yi maganar yana nuna Waya daga kujerun da babu kowa a kai.

"Wannan karon dai za mu ji me Sultan zai ce mana a kan maganar"

"Nima dai abin da nake son ji kenan, magana ta gama cika gari ba a san inda yake ba, ana ma tunanin ko ya mutu suke Soyewa"

Nana ji ta yi ana busar sarewa a ?ofar bayan su, gaba Waya suka ja gefe domin bayar da hanya.

Wani dattijo ne fari sol, mai dogon gemu ya shigo jallabiyarsa ba?a, ya lulluSe kansa da hiraminsa.
Gaba Waya ta ga abokan aikinta sun rikice, duk sun sunkuyar da kansu ?asa, Nana kuma ta yi masa ?uri da ido. Sai dai ba shi take kallo ba, ji take tamkar numfashinta ya Wauke, kamar ba a cikin duniya take ba, duniyoyin da ?aisar ya saba kaita ne ya caza mata kai, banda haka wani irin mummunan gizo ne wannan?.
Gaba Waya matasan suka mi?e tsaye, cikin matsanancin mamaki suna kallon na bayan dattijon.
Tamkar yana tausayin ?asar haka yake taka ta, yana Wan yin rangaji kaWan, sassanyan ?amshin turaren sa da ko a mafarki ta ji shi tana tantancewa ya karaWe ilahirin gurin, fiye da ?amshin turarukan da ke tashi a gurin.
Ta kusa da ita ce ta ja hannunta da ?arfi, saboda yadda ta tsare shi da idanunta ko ?iftawa ba ta yi.
Ya zo zai gifta ta, amma ko gurin da suke bai kalla ba, Waya bayan Waya suka din ga rungume shi, cike da murnar da wasu har zuci, wasu kuma iya ta fuska ce. Ta ga ya zauna a kan kujerar da ake tababar wa zai zauna a kai kafin ya shigo.
Abdou ya ce "Kun yi mamaki ko? Ba ku yi zaton ganinsa ba?"

?aya daga cikin su ya ce "Gaskiya ne"

Sultan ya yi murmushi ya ce "Kamar dai yadda na gaya muku a baya, Imam Hammad yana Faransa neman lafiya, bayan tsawon wannan lokacin, yau ya kasance tare da mu a liyafarmu ta ?arshen shekara, dama wannan ne bazatar da na ce zan yi muku"
Nana ta kalli hotunan nan, sai ta yanzu hotunan babu rawani, kowa hoton fuskarsa ce. Ta tsayar da idonta a kan hotonsa da aka rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. A take ta tuna da sunan gidan cin abinci da ta yi wa su Al Hussain aiki. H.J Agadez.
Sunan rukunin gidajen da ta fara zama da Asal shi ma sunan da ke jikin symbol Win unguwar kenan. H.J Agadez.
Duk surutun da ake yi, da murnar ya dawo, yana ?ame a kan kujera, fuskarsa babu yabo babu fallasa.
Sai daga bisani ya saka hannunsa Waya a kan ?irjinsa ya risunar da kansa ya ce musu "Merci(Na gode)
Duk da a hankali ya furta, amma ko cikin murya dubu Nana ba za ta gaza tantance ta Sayyid ba.

Abduou ya kalli su Nana, ya kalli mutumin Wazu da yake tambayar wace ce "Guda biyu daga cikin su ta zo ta WanWana Abincin nan"

Mutumin ya ?are musu kallo, ya nuna Nana ya nuna wata ya ce su je su ci kafin a ci.
Nana ba ta san a yadda take iya Waga ?afafuwanta ba, saboda ba ta jin su a jikinta, zuciyarta kuwa kamar za ta tarwatse saboda bugun da take yi fiye kima. A hankali ta ?arasa gaban teburin. ?ayar ta din ga bubbuWe Abincin, ta fara WanWanawa.

"Ke kina da gaskiya kuwa? Ki WanWana aka ce?" Abduou ya yi mata maganar cikin tsawa.

Rikicewa ta yi gaba Waya, ya Waga idonsa ya kalli inda jikinta yake rawa, suka yi ido huWu, ya kawar da kansa yana mamakin yadda take a ruWe.

Ta Webo shinkafa a cokali, amma hannunta karkarwa kawai yake yi.
Sultan ya ce mata "Kina lafiya kuwa?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Sultan ya ce "Na fuskanci a tsorace take ne kawai, a kaita ta je ta huta, wata?ila mun yi mata kwarjini ne"

Aka saka Nana a gaba aka fitar da ita daga gurin.

Fitarsu ke da wuya, jikin Nana ya din ga wata irin kyarma, ha?oranta na haWuwa da juna, wani irin jiri ya din ga kwasarta.
Balaraba ta nufo su da sauri, ganin Nana na dafa bango.
Ya kalli Balaraba ya ce "Maza ki kaita ta huta, wata?ila ta yi aiki da yawa ne ta gaji, gaba Waya ta rikice, a kirawo likita kuma ya duba ta.






*****

A hankali Nana ta yi juyi, ta buWe idonta ta ganta a Wakin da take kwana.
Wata irin ajiyar zuciya ta yi, da ta tabbatar da mafarki ta yi ba gaskiya ba ne abin da ya faru.
Hamdala ta yi ta ce "Ni dai na san mafarki ne da ma, dan babu yadda za ayi Sayyid ya ganni ya kasa kula ni, ya nuna kamar bai sanni ba. To wannan idan gaskiya ne ma, ta ina zan fara bayanin ni matarsa ce a yarda da ni? Mutumin da na ji ana batun ya daWe a faransa yana jinya, anya ma Sayyid Wina ne? Tun da dai mafarki ne duk da sau?i.

Sallama aka yi a Wakin, ta ga Balaraba ta shigo Wakin. Ta ce "Kin tashi?"

Nana ta yi shiru tana kallonta.

"Ina ga aiki da ki ka sha a kwanakin nan ne, ya sanya ki ka gaji zazzaSi ya kama ki, Likita ya ce a bari ki huta sosai da sosai. Gimbiya Asal ta ce a baki hutu na kwana uku ki warware kan ki koma bakin aiki."

Nana ta jinjina kai kawai, tana kokawa da ?wa?walwarta, domin ta tabattar gaske ne, ko kuwa dai mafarkin ne? Ta tashi ta yi alwala ta yi salla, sai dai gaba Waya jikinta ciwo yake yi mata, ga matsanancin ciwon kai da ji???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ri da take ji, dan haka ta nemi guri ta sake kwanciya.

*****

Jamila ta Wauki jakarta Wauke da wannan tarkacen da take kira da tarkacen jaraba, ta fita waje, ta samu ta sayo fetur a 'yar jarka, ta samu guri ta zuba musu fetur Win ta kunna musu ashana ta ?one su.

Ta tashi tana kallon yadda suka din ga ci da wuta, ta bar gurin.
Kai tsaye ta tari abin hawa ta tafi gidan Hajiya Sa'a.
Hajiyar ta yi iya ?o?arinta gurin Soye jin haushin Jamila da take yi, ta karSe ta hannu bibbiyu har ta taya ta lissafin kuWin kasuwancinta da kuma kayan da take da su a ?asa.
Bayan sun kammala ta ce "Ni kuwa Jamila, yaya batun ?ungiya wa za ki bayar ne?"
Jiki a sanyaye ta ce "Haryanzu ban gama tunani ba ne ba"

"Tsoron dai ki ke ji haryanzun ko?"

"A'a na rage ji"

"To ki yi ki hanzarta ki yi abin da yakamata amma kin tsaya. Ni kalli nawa nan na shirya komai aiwatar wa kawai ya rage mini, sai na je gidan zan yi, na sake bayar da Wan Fatuhu"

Jamila ta kalli drower da Hajjya Sa'a ta janyo, tana nuna mata 'yar tsanar nan.

Jamila ta ce "To idan ban kai kowa ba, akwai wani abu da zai faru ne?"

Ta ce "Au da kara zube za ki zauna ki ?i bin umarnin ?ungiya? To idan ba ki kai kowa ba, jininki aljanin zan shanye ki mutu" Cikin Jamila ya yi wata irin ?ara bayan tuna ta ?ona kayan. A tunaninta shikenan ta huta sun rabu.
A ranta ta ce "Wannan wane irin bala'i ne na jefa kaina a ciki, Ubangiji Allah ka kawo mini agaji na rabu da wannan masifar.

*****
Fafur Nana ta ?i yadda zuciyarta ta amince abin da ya faru gaskiya ne ba mafarki ba, saboda ta riga ta saba da irin wannan cazan kan da ?aisar ya kan yi mata wasu lokutan, har ta gaza banbance abin da yake zahiri da kuma mafarki.

Su na Wakin girki su na ta Worawa da saukewa, ta kalli shugabar su ta ce "Dan Allah a gidan nan, babu yadda zan yi na samu waya, ina son na kira gida ne, na ji halin da yarona yake ciki"

Balaraba ba ta bata amsa ba, ta ji Muryar Asal ta ce "Babu wannan damar, sai dai idan kina bu?ata ki zo gurina ki karSi wayar ki kira"
Nana ta Wan yi shiru sai kuma ta girgiza kai ta ce "A'a ki bar shi na gode"

"Me yasa ki ka ce haka? Kina tunanin wani abu a ranki ne?"

"Bana tunanin komai, kawai dai na fasa ne"

Ta yi murmushi ta ce "Shikenan, ga sa?o can daga gidan Sultan, tukuicin aikin da ku ka yi na girki"

Balaraba ta risuna tana yi wa Asal magana da yarensu, Nana kuma ta cigaba da aikinta, tana sane ta cewa Asal ba ta so, dan ba ta gama gane ina Asal Win ta saka gaba ba, da kuma cikakkiyar manufarta a kanta ba. Tana tsoron ta yi amfani da wata dama da za ta samu ta cutar da ita.

Dogwayen riguna na alfarma Nana ta samu, guda uku da kuWi. Ta yi murna sosai da kayan, saboda rigunan na alfarma ne.

Katafaren Wakin bacci ne, mai Wauke da kayan alatun more rayuwa irin na masu mulki.
Duhun dare ne, sai dai hasken fitilun Wakin ya gauraye ko ina, kai ba ka ce dare ne ba.
Yana zaune a gefen gadon, tare da dattijon. Cikin kamala dattijon ya ce "Imam, ina ?ara yi maka gargaWi da jan kunne a kan ka ?ara kula da kan ka. Kar ka Wauka kowane murmushi ne na soyayya, wani murmushin na babu yadda aka iya da kai ne. Kar ka kuskura ka faWi wani abu da zai rusa shirinmu, mun Soye abubuwa da dama a game da kai, duk abin da baka fahimta ba, ka tambaye ni, kar ka wani ya bu?aci sanin wani abu daga gare ka, ka sanar masa kawai jinya ka yi tsawon wannan lokacin.

"Abii"

"Na'am abin ?aunata" Imam Hammad ya yi murmushi ya ce "Me ka ke Soye mini ne, akwai abubuwan da suka hargitse a rayuwata, tsawon wani lokaci na Wauka ina jinya ba a hayyacina ba?"

"Ka na ji na? Haryanzu ba ka warke ba, ka na bu?atar hutu mussaman a ?wa?walwarka, kar ka takurawa kanka da tunanin abubuwan da suka faru. Jita-jitar da ake yaWawa a kan ka, da surutai daban-daban shi ne dalilin da ya sanya muka dawo da kai ?asar nan, a shaida dai kana raye, cikin ?oshin lafiya"

"Mahaukaci ne ni kenan? Tun da ina iya tuna yadda ciwon nawa ya fara, amma ban san yaya ya ?are ba"

Sultan ya tsuke fuska ya ce "Ya ishe ka haka. Kar ka kuskura na ji labarin nan ya fita, waye ya ce kai mahaukaci ne? Larurar zuciya ce take damun ka, babu daWi babu ?ari daga haka. Babu wata larurar hauka a tattare da kai".

"Amma Sultan ko zaka saka na Soye wa duniya, yakamata na san matsayin lafiyata...

"Hammad!" Tilas ya ja bakinsa ya yi shiru, ganin yadda ya fusata Sultan Win.

*****

Tun da garin Allah ya waye, Nana take jin faWuwar gaba da matsananciyar fargaba, ga sanyin da take jin yana ratasa ta, ta san ba na lafiya ne kawai ba. Dan haka ta Waura alwala take ta addu'a.
Bayan fitowarta ta cika da mamakin ganin yadda ma'aikatan gidan, suke ta aiki tu?uru suke gyara gidan duk da ko ina a gyare yake.
Ko ta ina ?amshin turaruka ne ke tashi daban-daban. Har sun so su yi yawa ma.
?angaren da take aiki, sai azalzalarsu ake yi, ta fahimci dai wani ba?o ne mai muhimmanci zai sauka a gidan.
Har mamaki take yi yadda suke ba wa abinci muhimmanci, ba?o Waya sai a saka a yi masa abinci biyar, kuma duk da an san ba iya cinyewa zai yi ba.

Ta fito kenan ta ci karo da Asal, ta sanya zani da doguwar riga na shadda ba?ar shadda, kanta babu Wan kwali, hannayenta da yatsunta duk zobunan gwal ne, uwa uba wata irin sar?a da ta saka ta zinari tun daga wuyanta har cikinta. Gashinta ya sha ado, ta sake shi har kafaWarta, shi ma ta sanya masa wata siririyar sar?a da ta kwanto har goshinta.
Duk hassadar mai hassada babu yadda za a yi ka kalle ta ka kushe ta, jawur da ita a cikin ba?ar shaddar sai ta haska shaddar.

Ita dai Nana tun da ta zo gidan, ba ta taSa ganin Asal da miji ko 'yan uwa ba, sai tarkacen ?awayenta, su ma a wancan gidan ne, wannan gidan ba sa biyo ta su zo. Kuma duk abin nan Nana ba ta taSa bin diddigi ta ji wace ce Asal ba, me yasa kuma take rayuwa a gidan daga ita sai masu yi mata hidima ba.

Da daddare Nana ta ji su Balaraba su na yare, su na faWin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login