Showing 48001 words to 51000 words out of 122467 words

Chapter 17 - Buzu Book 2 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

30

amma ya aka yi ba ki gaya mini ba, bayan kin san ?udurina a kanta?"

Jamila a ranta ta ce "Da yake ki ka halicce ta ba"

A zahiri ta ce "To ai ni ban san haryanzu ana bu?atar jininta ba, da na ga ba ki kuma yi mini maganarta ba, na zata shikenan ya wuce"

Kamar ta rufe Jamila da duka ta ce "Amma wallahi ba karamar shashasha ba ce, Waga miki ?afa kawai na yi ki ?ara dawowa hayyacinki, aikuwa ko ki nemo Nana a samu jininta, ko kuma ?ungiya ta nemi jinin wani sha?i?inki, sai ki zaSa".
Jamila ta waro ido ta ce "Sha?i?ina kuma Mummy, na shiga uku na lalace"
"Ahh to dabara ta rage ga mai shiga rijiya ai, sai ki yi tunani, ni na haura sama zan yi bacci" Gaba Waya jikin Jamila ya yi sanyi, ta bi bayan Hajiya Sa'a da wani irin kallo.

Har rana ta Waga gurin ?arfe goma, Nana na zaune a rilar gidan nan, sai da rana ta tarar da ita, sannan ta yin?ura, ta Wauki jakar kayanta, ta koma barandar da ke kallon gidan, ta zauna.
Mai gidan da ta kwana ya fito zai tafi kasuwa, kawai ya sake ganin Nana, da hijjabinta da wannan bagcon kayan nata ya gane ta. ?arasa fitowa ya yi, da niyyar ya tambayi Nana me take nema ne? Amma su na haWa ido da Nana ya kawar da kansa cikin sauri, saboda wata irin mummunar faWuwar gaba da ta ziyarce shi.
Sum-sum ya wuce ya tafi, ba tare da ya ce wa Nana komai ba.
Rana ta fara zafi, ta sake Waukar jakarta ta yi gaba, ta din ga nanata lahaula wa la ?uwwata illa billah. Hasbunallahu wa ni'imal wakil.

*****
Alhaji Zailani yana zaune a falo, tare da Hajiya Amina, Yusuf ya shigo falon.
Hajiya Amina ta kalle shi ta ce "Yusufa daga ina?"
"Aiken ki na je Mami"

Ta ce "Wanne daga ciki?"

Ya zauna tare da faWin "Ba shekaranjiya muka yi zancen Nana da ku ba? Gidansu na je, daga gidan nake na samu babanta a waje, ya gaya mini wai mijinta ne ya Sata ta bi shi Nijar neman sa"

Hajiya Amina ta dafe ?irji ta ce "Ya Sata kuma garin yaya? Ko shi ma Wauke shi aka yi kamar yadda aka tafi da 'yan uwansa? Anya ba wani laifin suke aikatawa ba hakan ta faru? To ta san inda yake a Nijar Win ne?"
Yusuf ya ce "Wallahi nima ban sani ba, haka dai ya ce mini"

Alhaji Zailani da hantar cikinsa ta kaWa ya ce "Wai maganar wa ku ke yi ne?"

Cikin dakiya ta ce "Nana mana, yarinyar nan da ta kula da Haidar, wadda babanta ya aura wa Buzun nan"

"To sai aka yi yaya?" Yayi maganar yana tsare ta da ido, yana tunanin ko Hajiya Amina ta ci gaba da bibiyarta, ta gaya mata abin da yake tsakaninsu.

"A'a dama Shukura ce ta ce, kwana biyu shiru, kuma ba ta samun ta a waya, nima kuma ba na samun ta, shi ne na ce masa dan Allah idan ya biya ta hanyar gidanta, ya tsaya ya karSo mini lambarta, to kuma wai sun tashi daga gidan. Shi ne ya je gidansu aka sanar masa da ta bi mijin Nijar" Ya yi wata Soyayyiyar ajiyar zuciya ya yi shiru bai kuma cewa komai ba.
Hajiya Amina ta yi ta jajanta lamarin, tare da tausayawa Nana.

Alhaji Zailani kuwa rikicewa ya yi, cike da kiWima. Domin yana ta tsara yadda zai samu Nana ko ta halin ?a?a domin samun biyan bu?atar sa. Yaronsa da ya bawa ragamar bibiyarta, bai taSa gaya masa ba, ce masa kawai ya yi ta koma Kurna.
Wani irin gumi ya fara keto masa, ta ina za a fara neman ta yanzu har a gano ta, a Nijar.
Sai ya Wora wa kansa alhakin sakacinsa ne, da ya din ga bin al'amuran a sannu, duk da hakan ya faru a dalilin halin da yake shiga, a duk lokacin da ya yi yin?urin aiwatar da wani abu a kan Nanan.

****
Nana kuwa wuni ta yi tana gararanba a titi, daga wannan inuwa ta koma waccan, ga uban kaya ga kuma ciki. Dama Abinci ba damunta ya yi ba. Buredinta da ta yi guzuri ta ci abin ta, ta kora da ruwa.
Tana son samun muhalli, tun da akwai kuWi a hannunta, akwai na Nigeria akwai na Nijar, sai dai amana ta yi ?aranci, ba ta san wa za ta tunkara ya taimake ta ba, tana tsoron a cutar da ita.
Dare ya yi bayan sallar Isha'i, ta sake lallaSawa ta koma gidan nan ta kwana a rila, da Asuba mijin matar ya sake ganin ta, hakan ya sanya hankalinsa fara tashi, ga shi ya kasa magana kamar wanda aka yi wa asiri.
Yau bayan magariba da ya koma gida, sai ya sanya wa rilar sakata, ya kulle ta ciki.
Sawu ya Wauke, Nana ta lallaSo ta zo ta kwana, kawai ta tarar da rilar a rufe, ta jijjiga ta ji an gar?ame ta ciki.
Jikinta ya yi sanyi, ga shi duk inda ta tafi ko ta yi niyyar ta yi gaba ta tafi wani gurin, sai hankalinta ya kasa kwanciya sai dai ta koma gidan nan.
Ga yau wani irin bacci take ji, kamar ta kifa, ga shi tana son yin wanka, saboda yadda kayan jikinta suke mintsininta, tun da ta zo da su take yawo.
Ta samu gefen gidan ta takure, tun tana hamma har bacci sosai ya yi awon gaba da ita.
Da Asuba ta ciro jarkar ruwan da ta saka wasu yara suka zuba mata a cikin ?aramar jarka, ta yi alwala ta yi raka'atanul fajr. Tana kallon mai gidan ya fito ya tafi masallaci yana haske-haske, amma bai gan ta ba, har ya tafi.
Ya dawo daga masallaci kansa tsaye zai shiga gida, ya ga Nana a cikin rilar. Wata irin razana ya yi, ya kuma kasa magana sai kallonta da yake yi fuskarsa na bayyanar da tsoro ?arara.
Nana ta ce "Ka kulle rilar gidanka, jiya a waje na kwana, duk da ban ga laifin ka ba, amma da ka tambaye ni, me yasa nake kwana a nan"

"Wa..wa.wace ce ke? Me ki ke yi a nan?"

Ayshercool
08081012143

63

Nana ta ce "Dan Allah ka kwantar da hankalinka, kar ka tsorata wallahi ni mutum ce, ba abin da na isa na yi maka na cutarwa, ba kuma ni da nufin cutar da ku"

"To me ki ke yi mini a gida?"

"Wallahi ba?uwa ce ni, ranar da na sauka a garin nan, na shiga gidanka, matarka ta bani gurin salla, har da abinci, dan Allah taimakona za ku yi"

Ya ce "Baiwar Allah wallahi mu ma talakawa ne, ba wani taimako da za mu iya yi miki"

Ta ce "A'a amma ai ku musulmai ne, gudun zargi dan Allah idan babu damuwa, mu shiga ciki a yi maganar a gaban matarka, ku ji taimakon da nake bu?ata idan za ku iya yi mini, idan kuma ba za ku iya yi mini ba, babu komai sai na nema a gaba"
Kamar ya ce a'a, amma yanayin Nana sai ta ba shi tausayi, ya bata dama suka shiga gidan, yana gaba tana bin sa a baya.
Nana ta tsaya a tsakar gida, ya shiga ya taso matarsa. Ta fito tana mustustuke ido, ya nuna mata Nana ya ce "Kin san wannan?"
Ta Wan yi shiru sannan ta ce "Kamar shekaranjiya ta zo, ta ce mini ba?uwa ce za ta yi salla"

Ya ce "Yauwwa, sau uku ina ganinta a rilar gidan nan. Wai a nan take kwana, ta ce mini taimako take nema, amma a zo a gaban ki, sannan ta faWi me take son mu yi mata".

Matar ta kalli Nana,ta ce "Baiwar Allah, wane taimako za mu yi miki?"

Nana ta ce "Ni ba?uwa ce daga Nigeria, dan Allah ku taimaka mini da inda zan zauna, ban san kowa a ?asar nan ba. E"

"Gaskiya baiwar Allah, ba bu gurin da za mu iya ajiye ki a gidan nan" matar ta tari numfashin Nana.

Nana ta ce "A'a ba a nan za ku ba ni gurin zama ba, da kuWi a gurina, sai dai ban san kan kuWinku na ?asar nan ba, ina da wasu ma na Nigeria, ban san yadda zan canza su ba. Kuma ina tsoron na faWa hannun da ba na gari ba a cutar da ni. Haka kawai na ji na nutsu da nan tun lokacin da ki ka karrama ni, ko na tafi sai na dawo nan na kwana nake samun nutsuwa. So nake ku taimaka a sama mini gidan haya, ko Waki da zan kama dan Allah. Kuma wallahi ni ba macuciya ba ce ba zan cutar da ku ba. Ku yi wa Allah da ma'aiki ku taimaka mini, dan Allah"

Ya kalli matar matar ta kalle shi, ta Wan jinjina masa kai.
Ya kalli Nana ya ce "Kin san harkar taimakon ce wuya ne da ita yanzu, sai ka taimaki mutum amma ya sanya ka a masifa.
Nana ta ce "In dai kun yi niyyar taimakona, ko macuciya ce ni, Allah ba zai ba ni damar cutar da ku ba. Ku taimaka mini dan Allah, ko iya gidan hayar a sama mini"

Ya kalli matarsa ya ce "Hajara, bata guri ta zauna, zuwa gari ya ?arasa wayewa, sai mu san abin yi, mu duba girman Allah da ta haWa mu da shi"

Hajara ta ce "To shikenan babu damuwa" wata irin ajiyar zuciya Nana ta yi, ta risuna ta ce "Na gode, Ubangiji Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi, yadda ku ka taimaka mini Allah ya taimake ku haka"

Suka amsa da Amin. Matar ta kai Nana wani Waki, ta Waukar mata kayanta ta shiga da su.
Tana fita daga Wakin, Nana ta zube ta yi sujjada tana gode wa Ubangiji buwayi gagara misali, ta san wannan Waukin kai tsaye daga gare shi ne, amma ba dan haka ba ta san ba ?aramar wahala za ta sha ba.
Sai yanzu da ta nustu, ta din ga jin ta a takure, saboda rashin wanka, ga cizonta da kayan jikinta suke yi.
Gari ya yi haske matar ta shigo ta ce wa Nana "Ki na bu?atar wani abu ne?"

Nana ta ce "Eh dan Allah zan yi wanka"

"To shikenan babu damuwa, da kin sani tun ranar da ki ka zo, ki ka yi mini bayani, ga ki da juna biyu, amma a ce ki na kwana a waje bai dace ba"

Nana ta ce "Larura ce, ba yadda zan yi, kuma babu daWi ka Wora wa mutane Wawainiya sama ta ka"

Ta ce "Haka ne" ta haWa wa Nana ruwa, Nana ta duba kayanta ta Wauki soso da sabulu, da brush.
Ba ?aramin daWin wankan nan Nana ta ji ba. Ta koma Wakin da suka sauke ta, ta fito koma Wakin da aka sauke ta.
Ta fito da mai ta shafa, ta saka kaya. Ta ji wata sassanyar iska na ratsa ta. Ta Waukko jakar kayan turarrukan Sayyid, da kayan gyaran gashin sa, ta yi zuru da ido, tana kallonsu.
"In sha Allah za mu haWu Sayyid, ina fatan Allah ya ?addara haWuwarmu nan kusa" ta yi maganar a sanyaye.
Sallamar Hajara ce ta sanya ta mayar da kayan cikin bagcconta, ta mayar da hankalinta kan ta.

"Ko ki na bu?atar wani abun ne?"
Nana ta girgiza kai fuskarta Wauke da murmushi ta ce "A'a ba na bu?atar komai, na gode sosai da sosai"

"Ba komai, bari na kusa gama abin karyawa"

Cikin murmushi Nana ta ce "Ba raina miki na yi ba, amma ni wannan taimakon da ku ka yi mini ya wadatar, ba sai kun ba ni Abinci ba, na gode sosai da sosai"
Hajara ta ce "Haba dai, ya ma za ayi ki na ba?uwarmu a ce ba za mu ba ki Abinci ba, ai ba zai yiwu ba sam"

"Ai kar Wawainiyar ta yi yawa ne, abin da ku ka yi mini ma, na gode Allah ya biya ku"

"A'a babu wata Wawainiya" ta yi maganar tana fita waje.
Ta so tambayar Nana me ya kawo ta Nijar, ga tsohon ciki, kuma ta ce ba ta da kowa, amma ta kasa saboda wani irin kwarjini da Nanan ta yi mata.
Tun da ta bawa Nana abincin safe, da rana ta bata fura Nana take amai. Har sai da Hajara ta ji babu daWi, ta yi zaton ko Abincinta ne ya saka Nana amai.
A sanyaye ta ce "Ko Abincin nawa ne ya saka ki amai?"

Nana ta yi murmushi ta ce "A'a kar ki damu, dama haka nake fama tun farkon cikin, ni na riga na saba ma"

"Kayya ai ba a sabo da wahala, kin yi amai ya kusa goma, ko Asibiti zamu je?"

"A'a zan daina in sha Allah"

Gaba Waya Hajara ta damu, ganin yanayin da Nana take ciki.

Nana ta ce "Ba ki taSa haihuwa ba ne? In dai mutum ya haihu ya san irin wannan larurar ta ciki ai"

Hajara ta ce "Ina fa? Watanmu takwas da aure, ban haihu ba".
Nana ta yi murmushi ta ce "Allah ya kawo mai albarka"
"To ai ni duk na tsorata ne, wannan aman ya yi yawa"
"Ai ni na riga na saba ma, ba ya damuna yanzu" haka suka Wan din ga taSa hira.

Mijin Hajara bai dawo ba sai isa'i, Nana na Waki tana shafa'i da wuturi. Ya ce wa Hajara "Ina ba?uwarmu?"

"Tana nan sai dai ba ta da lafiya"

"Me ya same ta?"

"Wallahi tun da na ba ta Abinci take amai, haryanzu jikina duk ya yi sanyi"

Ya ce "Subhanallah, kuma bai tsaya ba?"

"Tana dai ta yi"

Nana ta idar ta yi addu'a, sannan ta fito, ta dur?usa ta gaishe shi, ya amsa yana yi mata ya jiki.
Ta ce "Jiki Alhamdillah"

Ya ce "Baiwar Allah ba a samu gidan haya ba, duk inda na tambaya, sai masu tsada, kuma babu lallai a bayar, mussaman idan aka san ke kaWai za ki zauna, kuma zaman ki ke kaWai babu Namiji babu tsaro ko kaWan.
Amma na kuma bayar da cigiya ko za a samu wani, wanda yake da mutane a ciki sai a kama"

Nana ta jinjina kai ta ce "Na saku Wawainiya, Allah ya saka da alkhairi"

Ya ce "Ba komai" ya kalli Hajara ya ce "Bari na je na dawo, ko za ku yi hira kar na takura muku"

Nana ta ce "A'a ba komai, ka zauna ni sai na koma Waki"

Ya ce "A'a dama zan fitan"

Hajara ta raka shi soro, ta tsaya can su na hira Nana tana jiyo dariyar su. Sayyid ya faWo mata a rai. Yana daga cikin manyan ni'imomi da nasarorin rayuwa, mutum ya auri wanda yake son sa, ya kuma dace da shi. Ta yi musu addu'a da fatan samun dauwamammen zaman lafiya da kuma zuriya ta gari masu albarka.
Hajara ta dawo, ta zauna su ka ci gaba da Wan taSa hira da Nana.
Ta cewa Nana "Ko sunanki ban sani ba"
"Nana Asma'u, amma Nana ake ce mini"
Ta ce "Allah sarki, amma ki na da aure ne?"
Nana ta yi murmushi, ta ce "Kin yi mamakin yadda na taho inda ban san kowa ba ga tsohon ciki ko? Na san wata?ila, kina tunanin ina na samo ciki ne?"

Hajara ta ce "Laaa a'a wallahi"

Nana ta ce "Ai babu damuwa idan ma kin yi tunanin haka, Wabi'ar zuciya ce. Matar aure ce ni, ko a yanzu haka ka ma ina da igiyoyin aure uku a kaina, wani dalili ne ya kawo ni ?asar nan, kuma in sha Allah da na kammala, zan koma gida"

"Allah sarki, Allah ya tabattar da alkhairi, ya sanya a samu abin da aka zo nema"

Nana ta amsa da "Amin na gode sosai"

*****

Su na zaune sun tattara hankalinsu a kan likitan, cikin matsananciyar girmamawa Likitan ya gaishe su.

"Ya ya jikin Imam?"

Ya amsa da "Jikinsa Alhamdillah, yana samun sau?i sosai da sosai"

"Ba yana samun sau?i muke son ji ba, mene ne sakamakon binciken ku da aka gudanar?"

Likitan ya ce "Eh sakamakon gwaje-gwaje, ya nuna babu abin da aka yi masa na cutarwa a jikinsa, gaba Waya babu wani abu na cutarwa a tare da shi"

"Shi kuma matsalar zuciyar fa?"

"Wannan yana da nasaba da hawan jini da yake da shi tuntuni, wata?ila ya daWe ba a kan magani ba. Shi yasa ya shafi zuciyarsa. Sai dai matsala Waya"

Cikin damuwa dattijon ya ce "Wace matsalar?"

"?wa?walwarsa, mun kasa gano abin da yake faruwa da ?wa?walwarsa, haryanzu bai samu nutsuwar da zamu tattauna da shi ba,???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yana bu?atar kulawa ta musamman a bangaren ?wa?walwa"

Sultan ya dafe goshinsa, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali, idanunsa suka yi jawur. Ya Wago ya kalli Likitan ya ce "Ko gida za a mayar da shi, a saka duk abin da ake bu?ata na kula da shi a Wakin, ya zamana yana kusa da ni, hankalina ba ya kwanciya, yana nan ina can"

Abduou ya ce "A'a Sultan, idan aka mayar da shi gida, za a iya gane halin da yake ciki, wanda ba ma fatan hakan, dole a ci gaba da toshe duk wata kafa da za a san halin da yake ciki, har zuwa lokacin da zai warware. Kuma za a ci gaba da matsa yaran can, har sai ya yi mana bayanin abin da suka yi masa a Nigeria. Kuma Asibitin nan akwai tsaro babu wanda ya san yana nan. A kula da shi har zuwa lokacin da za a yi tafiyar"

Sultan ya yi ajiyar zuciya cike da gamsuwa, ya mi?e tsaye ya ce "Mu je na gan shi"

Su ka mi?e gaba Waya, Likitan yana gaba su na biye da shi a baya.
Cikin sauri suka ?arasa gaban gadon. Idanunsa a rufe yana bacci.
Sultan ya ?arasa gaban gadon, fuskarsa Wauke da damuwa.
Ya din ga dudduba jikinsa, tamkar yana son gano wani abin. Ya kalli Likitan ya ce "Kun tabattar a jikinsa babu wani abu na illa ko cutarwa a tattare da shi?"

"Babu ranka ya daWe, lafiya kalau yake, ba a yi masa komai ba, sai wannan matsalar ta ?wa?walwarsa. Ba na tunanin an tafi da shi Nigeria ne dan a cutar da shi, akwai dai wani abu...

"Ya isa ba kai ke hurumin zartar da wannan hukuncin ba, sai abin da bincike ya tabattar"
Babu shiri likitan ya ja bakinsa ya tsuke.

Sultan ya Wago hannun Imam na hagu, ya kalli yatsunsa ya ga yatsunsa biyu sanye da zobuna, ya Wago hannun damansa, ya ga babu azurfa Waya sai Waya. Cikin tashin hankali ya ce "Abduou. Babu zoben Imam guda Waya" Cikin sauri Abdou ya ce "Wanne daga ciki?" Ya Wago wa Abdou hannun Imam.
A rikice Abduou ya kama hannunsa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login