Showing 111001 words to 114000 words out of 122467 words

Chapter 38 - Buzu Book 2 Complete

Unknown   

26 Aug 2026

41

kawar da zancen, yana ci gaba da lissafa yadda za je Nigeria ya taho da Nana, dan ya san tun da Hammad ya dawo, yanzu duk inda za shi su na tare.

Da ?warin gwiwa yanzu Nana take girki, kasancewar ta sa wanda take yi wa girkin.

Bayan da Nana ta kammala girkin rana tana shirin, kai wa sashen Imam, Asal ta same ta ta ce "Ba sai kin kai wa Imam Abinci ba, baya nan sai dare zai dawo, ki shirya masa abincin dare kawai"
Nana ta amsa mata da to.

Tun da Imam ya dawo, yake kaiwa yana komowa yana jiran ya ga ta ina za a kawo Abinci, saboda yunwar da yake ji. Ga shi dududu ?arfe goma ya dawo, amma Asal har ta kwanta bacci. Ya yi hamma bai san adadinta ba, saboda yunwar da yake ji.
Sallamar Nana ta saka ya kalli hanyar shigowa, wannan karon a kwando ta zubo kayan Abincin.
Sai dai yau saSanin hijjabi, doguwar riga ce a jikinta milk, da mayafin rigar. Tun da ta yi sallama ya amsa a ?asan ma?oshinsa ya sunkuyar da kansa ?asa bai kuma magana ba.

Ta ?arasa ta ajiye kwamdon, ta sauke kwanukan, har za ta yi masa zancen sa?on nan da aka bayar, sai ta fasa dan kar ta wargaza shirinta. Da wani na iya ganin halin da zuciyar wani ke ciki, da Imam ya daWe da jin kunya, saboda bugun zuciyarsa, ga wani irin azalzalarsa da take yi, ya sake kallon Nana, dan ba ya tunanin ya taSa ganin wanda doguwar riga ta yi kyau kamar ba?ar kukunsa 'yar Nigeria.
Ta zuzzuba masa abincin, ga kayan marmari ga kuma shayi na musamman.
Da ta zuzzuba masa.

Ta numfasa ta ce "?azu na yi girkin rana, aka sanar mini da baka nan, na ce duk lokacin da ba zaka kasance a gida ba, ina son a yi mini izini na dafa maka ka fita da shi, ba zan so shugabana ya kasance da yunwa ba, tun da alhakina ne girka maka Abinci" Ta yi maganar cikin girmamawa tana sunkuyar da kai.

Jin ya yi shiru ya sanya ta Waga kanta, ta ga tuni ya Wauki shayi ya kai bakinsa yana sha. Kawai ta Wan juya ?wayar idonta, tare da yin murmushi. Sai da ya kusa ?warewa, saboda tabbas ya san irin wannan kallon, amma a ina? Yana matu?ar son ya yi mata magana, amma ba ya iya wa. Nana ba ta ba shi damar Waukar wani mataki ba, ta tashi ta nufi hanyar fita. Tun da ta tashi ya bi ta da ido har ta fice.

Abin duniya duk ya dame shi, Nana kuwa ta cika da murna, ganin sa?onninta na isa yadda take so, sai dai tana bu?atar ?ara samun kusanci da shi.

Cikin marairaicewa yake kallonta, fuskarsa Wauke da damuwa ganin yadda take kuka tamkar ranta zai fita, ga shi ta yi duhu ta rame, ba kamar yadda ya santa ba a baya.

"Ma vie, ki yi mini afuwa, ba laifina ba ne, ina jin yadda ruhinki yake motsi a cikin jikina, dan Allah kar ki yi fushi da ni ki yi mini uzuri " Ya yi maganar yana ?o?arin rungume ta ya rarrashe ta. Ja da baya ta yi tana girgiza masa kai tana kuka ta ce "Ba ka so na Sayyid, ka yada al?awari ka tafi ka bar ni, ka manta da ni, ka bar ni da dakon ruhinka, da ya hanani sukuni sai da na fito nemanka, ba ka yi mini adalci ba Sayyid"

"Ma vie, ban ya da al?awari ba, gangar jikina ce a Nijar, amma ruhina yana Nigeria dan Allah ma vie"

Asal ta yi ?uri da ido tana kallon yadda ya haWa gumi a cikin bacci, sai numfarfashi yake yi da kyar yana faWin "Ma vie, ke rayuwata ce, ban yi miki butulci ba"

AYSHERCOOL
1K NE VIA 0069685771
Aisha Adam stanbic bank
08081012143
76

Asal ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah.
Shiru ta yi jikinta ya yi sanyi tana kallonsa, sai dai ta yi shiru ta ci gaba da kallonsa. A razane ya farka, sai dai ya juya ya ci gaba da? baccinsa.

Da safe ya lura da Asal ba ta walwala, ta ?i sakin jiki da shi ma gaba Waya.
Har ya share ta sai kuma ya tambaye ta ko lafiya?

"Lafiya kalau" ta amsa masa a ta?aice.

Ya fita Wan tattaki, yana jin mafarkin da ya yi a jikinsa, amma ya kasa tuna mafarkin abin da ya yi. Cikin girmamawa ma'aikatan ke ta risunawa su na gaishe shi.
Babu yabo babu fallasa ya din ga amsa musu. Zuwa ?arfe goma Nana ta kammala girki. Sai dai yau ba su haWu ba kwata-kwata.
Har lumshe idanunsa yake yi bayan da ya sha kunun gyaWar da ta yi, ga lafiyayyen ?osai mai zafi.
Ya karya tsaf ya gama, Asal ta fito daga Waki ta cika ta batse. Kallo Waya ya yi mata ya maze, ganin ya basar da ita ya sanya ta ?ura masa ido ya kalle ta, yana mamakin dalilin da ya sanya ta ke yi masa wannan kallon.
"Imam ina fatan inda ka tafi, ba cin amanata ka yi ba"
Kallon rashin fahimta ya yi mata ya ce "Me ki ke nufi?"
"Ni kaina ban kai ga tantance abin da nake nufi ba, amma na fara ganin wasu abubuwa me da ban gane musu ba, abin ya tsaro ta ni ne"

Ya ce "Yi mini bayani"

"Ka na kiran wata da rayuwarka a cikin baccinka"
Ya yi mata ?uri da ido, sannan ya ce "Kin tabattaa?"

"Ba ka yarda ba ?arya nake yi maka kenan?"

"A'a ban ce haka ba, amma kin ce bacci nake yi, kin ga mai bacci kuma bai san abin da yake aikatawa ba. Wata?ila shirmen mafarki ne kawai, wata?ila ma ke na gani a cikin baccin nake kira da rayuwata"

Sai kuma ta yi murmushi ta ce "Kuma haka ne, wallahi har na ji zuciyata ta yi sanyi, ka yi ha?uri da abin da na yi "
Ya yi murmushi yana kashingiWa ya ce "Ban ha?ura ba tukuna"

Ta ce "Ai ba zan sake ba, ina kishinka ne sosai. Da ina da hali ko fita sai ka daina yi. Ina sane da duk masu ?o?arin yi maka kyautar 'ya'aynsu su na so ka aura. Imam kai nawa ne nikaWai Imam Hammad, babu wata mace da za ta iya samun kafar da za ta shiga zuciyarka. Inda na gode wa Allah, ka yi daban Imam, ba ka da rawar kai, da kule-kulen nan, da ko a cikin barorin nan, da suke rawar ?afa ka yi saWaka da su, sai ka saurare su. Shi yasa nake ?ara ?o?arin na kare gidana ina fatan ba ka ga laifina ba"
Ya sanya hannunsa yana shafa gashin kanta, ya ?an?ance idanunsa yana kallonta, daga bisani ya saki murmushi ya ce "Gimbiya Asal, sarauniyar mata masu kishi ta duk faWin Agadez"

Ta zumSura baki ta ce "Ta duk Duniya dai, ni in dai a kan ka ne. Da ina da yadda zan yi ma sai ka daina kallon kowace mace, sai maza kawai" Ta yi maganar har cikin zuciyarta.
Kawai ya kama dariya, dan shi gaba Waya dariya ma ta ba shi.
"Ya ka ke dariya kuma?"

Hammad ya ce "To ya ba zan yi dariya ba, ina ji ina gani an bani kyautar mata na mayar da hannun kyauta"

Fuskarta Wauke da damuwa ta ce "Dama ka na so kenan?"

"To waye ba ya son mace? Ina so mana. Amma tawa kawai"

"So ka ke sai ka saka ni kuka" Ta yi maganar idanunta na cika da hawaye.

Lumshe idanunsa ya yi yana buWewa, yana kallonta. "Ga abinci ki karya" Ta no?e kafaWa.

Nana ce ta yi sallama, Asal ta kalli inda ta shigo, ta tsuke fuska haka kurum yau ta ji haushin Nana ya ninku a zuciyarta.

Nana ta yi saurin sunkuyar da kanta, dan Asal a zaune take a kan cinyar Sayyid.
"Zan kwashe kwanuka" ta yi maganar muryarta har harWewa take yi, saboda abin da ya taso mata.

"To ni dai yanzu ka kira ni da rayuwarka a zahiri, tun da ka ce ni ka ke kira a mafarki" Ta yi maganar kamar ba ta san Nana ta shigo ba.
Ras gaban Nana ya faWi, ya lumshe idanunsa yana murmushi ya ?i magana.
Kawai Nana ta fusata ta tattare kwanukan za ta yi waje.

"Malama ki ajiye ban karya ba, ki fita kya dawo ki kwashe" Ko waiwayowa Nana ba ta yi ba, wata irin zabura ta yi cikin matsanancin fushi, amma ya ri?e ta ya ce "Cherie na sha gaya miki, irin wannan halayen naki ga na ?asa da ke, babu abin da za su janyo miki sai tsana da raini. Ita kuma rayuwa a na son ko kana guzurin ma?iyi ka yi na masoyi"

"Amma Amour kana kallon abin da ta yi mini, ko sau Waya sai na sanya a ladabtar da yarinyar nan ta san matsayina a gidan nan"

Ya ce "A'a, ke ce baki kyauta ba abin da ki ka yi. Ita ba ta tashi cikin jerin hadimanki ba, kawai dai kin Waukko ta ta yi miki aiki ne, dan haka sai kin din ga yi mata uzuri"

"Wane uzuri ne ba na yi mata, abin da ta yi mini wula?anci ne tana sane, ban da yadda take kula da abincinka na aminta da ita a kan hakan, da sai na hora ta sannan na kore ta ta bar gidan nan"

"Shikenan ki yi yadda ki ke so, tun da ba zan faWa ki ji ba"

Ya yi maganar yana ture ta daga jikinsa.

"Imam fushi ka yi da ni a kan wannan mummunar yarinyar?"

"Ba a kanta na yi fushi ba, yadda ba kya jin magana ne ya Sata mini rai, idan ki ka ci gaba da sanya wa ma'aikatanki ?iyayyarki, babu abin da ba za a iya haWa kai da su a yi miki ba. Idan na isa a bar maganar nan. Ba na son yadda ki ke tafiyar da ma'aikatanki wasu lokutan, ba na son yawan shiga maganar ne, amma raina ki za su yi"

Asal ta yi shiru ta tsuke fuska, ta sauka daga kan cinyarsa baki Waya.

****
Alhaji Fatuhu ma duk da yadda yake fama da kansa, sai da ya je gurin jana'izar Abba, kuma da shi aka yi zaman makoki. Ya ji mutuwar nan sosai da sosai, saboda Abba mutuminsa ne. Ko da yake jinya a sati ya kan je sau biyu ko uku duba shi. Ya kan zauna su yi hira sosai mussaman idan ya tarar jikin nasa da sau?i.
Kusan kullum Hajiya Sa'a gani take mafarki take yi, idan aka wayi gari za ta ga Abba bai mutu ba, amma ta ga babu alamun hakan. Ba ta ?ara kiWimewa ba sai ma da aka yi kwana bakwai da mutuwar, kowa ya watse ya bar gidan.
?akin Abba ta tafi da daddare, ta buWe Wakin tana rintse idanunta tana jin tamkar za ta gan shi ya Wago, da wannan murmushin nasa irin na fuskar mahifinsa.
Amma ta ga Wakin nasa wayam, babu komai.
Wasu irin zafafan hawaye suka shiga sintiri a kan kumatunta, ba ta taSa dana sanin shiga ?ungiyar asiri da duk wasu miyagun laifuka da take aikatawa ba, sai da ta rasa tilon Wan da Allah ya ba ta a rayuwa. Wanda babu irin ?o?arin da ba ta yi, domin ganin ta kare shi da sadaukarwar ?ungiya. Ashe bonono ta yi rufe da Sarawo bayan janyo Jamila cikin harkar ?ungiya, wanda ta yi hakan ne, domin janyo Jamila kusa da ita yadda za ta samu mallakar jinin Nana.
Ta zauna a gaban ?atuwar katifarsa, ta din ga wani irin kuka mai sauti, da sai da ?irjinta ya fara yi mata zafi.

*****

Asal ce zaune a kan carfet, saman kujerar da take kai kuma wani babban mutum ne, cikin shigar buzaye, kansa Wauke da rawani.

"Ki na ji na da kyau ko?"

Ta jinjina kai cikin nutsuwa, ko ?wa??waran motsi ba ta yi.
"Ina fatan haryanzu ba ki manta dalilin da ya sanya ki ka auri Hammad ba"

Ta amsa da "Eh ban manta ba"

"To barka, yanzu ya dawo, kuma babu abin da zai canza, za ki ci gaba da gudanar da aiki, kamar yadda yake a baya. Ba na bu?atar kuskure ko kuma wani uzuri. Duk wani motsinsa da duk abin da yakamata mu sani mai muhimmanci ki sanar da ni, idan kuma ki ka bari ni na gano ba ki sanar da ni ba, ranki zai yi mummunan Saci"
Jiki a sanyaye ta jinjina kai. "Dole a ci gaba da aiki tu?uru, domin nesanta shi da kujerar Sultan, da mahaifinsa ke ta ?o?arin kusantar da shi da ita, mu na bu?atar kujerar nan ko ta halin ?a?a, dan haka ina nan ina saka miki ido da kuma sauraren ki"
Asal ta sake jinjina kai, jikinta babu ?wari ta tashi ta fice.
Da ?yar take Waga ?afafuwanta, damuwa duk ta cika mata kai, ta ma rasa wane tunanin yakamata ta yi.
Da ta koma gida, ta tarar da hadimai na gyara Sangaren Imam, ga ?amshin turaren sa, da alama bai daWe da fita ba.
Cikin tsawa ta kore su gaba Waya, ta ce su ajiye aikin su fita daga sashen, sannan su kira mata Nana. Jiki na rawa suka ajiye suka fita.
Nana tana tsaka da karatun Alkur'ani sa?on Asal ya iske ta, sai ta hau tunanin kiran me take yi mata. Duk da ta san abin da ta yi mata da safe.
Nana ta tashi cike da ?warin gwiwa, dan ji take yi daidai take da Asal, tun da duk abu dai ba za ta raba ta da ranta ba.
Nana ta shiga fuskarta a haWe ita ma, ta shiga Wakin ta tsaya, tana ta huci tana son ta balbale Nana da faWa, sai kuma ta kasa ganin yadda Nanan ta tsuke fuska ita ma, ta yi mata wani irin kwarjini.
Amma duk da haka ta maze cikin dakiya da ?arfin hali ta ce "Amm tambaya nake son yi miki, ban sani ba ko nice a ?ar?ashinki, da zan din ga yi miki magana kina ji na ki yi mini banza"
Nana ta Waga kai tana kallonta. "Ko ba ki gane me nake nufi ba ne? Abin da ki ka aikata da safe"

Nana ta ce "Na gane, gani na yi bai kamata na tsaya ina kallon ku a yanayin da ku ke ba, ko na din ga sauraren maganganunku ba. Hakan zai zama kamar munafunci ne, shi ya sanya na tafi, amma ki yi ha?uri"

Asal ta watsa mata wani banzan kallo cike da tsana ta yi ?wafa sannan ta ce "Daga yanzu aikinki ba iya girkin Imam ba ne ba, har da gyaran sashen sa, ba na bu?atar kowa ya din ga raSar inda yake."

"Amma Waukko ni ki ka yi na din ga girki kawai, ya za ki haWa mini da aikin shara da goge-goge. Kuma masu yin aikin su uku ne, ni kuma nikaWai ce, aikin bai yi mini yawa ba kuwa?"

"Kin san a kan kuWi nawa na biya na Waukko ki? Ko a Nigeria ba na tunanin ko za a sayar da kaf danginku, za ku iya biyan kuWin da na biya na karSo ki ba. Dan haka ina da hurumin sanya ki duk abin da na ga dama"

"To Gimbiya Asal, babu damuwa zan yi abin da ki ke so. Duk da dangina ba za su iya biyan kuWin da ki ka biya ba. Amma na san wata?ila mijina zai iya biya ya fanshe ni" Nana ta yi maganar tana murmushin da Asal ba ta gama gane kansa ba.

Nana ce ta ?arasa aikin gyaran falon nan, ta yi goge-goge. Ha?ur?urtar da kanta ta din ga yi, da ta tuna mijinta take yi wa wannan aikin. Duk da ayyukan sun yi mata yawa. Ita dai fatanta Ubangiji Allah ya sanya Sayyid ya tuna ta domin ta san matsayinta.
Tana kammalawa ta koma kitchen, ta Wora girkin rana. Ta kammala ta kai ajiye.
Ta ?ara goge Wakin saboda ta san halin Asal sai ta tafi za ta huta, za ta sanya a kirawo ta, ta hau yi mata kinibibi da sanabe kala-kala.
Ta gama aikin goge-gogen kenan, ta gano wani photo album. Ta Wauka ta nutsu tana dubawa, duk rubutun French ne a jiki.

Shafin Farko hoton Sultan ne, wanda ba dan yanayin shekaru da fuskarsa ta nuna ba, sai ka ce Imam Hammad ne, wanda tsananin kamannin har Muhsin da ta baro a gurin Nene.
Ta buWe Waya shafin ta ga hoton wani, shi ma fari tas mai kama da su Sayyid sai dai shi ma babba ne. Kowanne a ?asa da sunan sarautarsa.
Sai kuma ta shiga wani shafi mai Wauke da hoton Sayyid a ?asa an rubuta Imam Hammad Jalal Agadez. Wani murmushi ya suSuce mata ta ce "Ka fi kowa kyau a cikin album Win nan Shugabana." Ta furta cikin murmushi. Hotunan wannan matasan da suka yi wa girki a gidan Sultan su ma kowanne da sunansa a ?asa. Amma a farkon sunan kowanne da Imam.
Nana ta din ga mamakin to kowa ma Imam ne kenan?.

Muryar Asal ta jiyo sun nufo cikin falon, ta hanyar da take kyautata zaton a nan turakar Imam take, kuma tana tunanin Waya hanyar sashen Asal za ta mayar da kai, kai tsaye.

"Imam, wai ina zobenka ne?"
Ta yi maganar tana Wago hannunsa, Nana kuma tana hango su daga inda take zaune.

"Ya karye yana gurin gyara"

"Gurin gyara kuma Imam? Ya za a yi dakakkiyar azurfa kamar wannan a ce ta karye? Ka san fa muhimmancin da zoben nan yake da shi a gurinka, ya za a yi ya karye?"

Daidai lokacin suka ?araso tsakiyar falon, ya ce "Zobe ya Sata ban san inda yake ba, ina fatan kin gamsu yanzu. Kar ki sake yi mini maganarsa.
Yanzu zan fita, kar ki manta da sa?ona"
Sai a lokacin suka ga Nana da ke zaune a cikin falon.

"Me ki ke yi a nan?" Asal ta tambaye ta.

"Babu komai, gyra Wakin na yi"

"Kuma sai ki nemi guri ki zauna sai ka ce Wakinki? Imam yana da ba?i anjima, za ki sake dafa wani abin, kuma za su sha shayi, ba na son wauta ko makamancin haka" Nana ta jinjina kai ta kalle shi ta ce "Barka da yammaci Sayyid, in sha Allah zan yi"
Asal ta Wan yi shiru tana nazari jin ta kira shi Sayyid ba Imam ba.

A Wan corridor Win ta tsaya tana zancen zuci, jin ana maganar zobe. Wane zoben kenan? Ko dai zoben da ya Wauka ya ba ta ne? A'a ba ta tunanin haka wata?ila

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login